← Book details Daneen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 49

Sashe 36

Daneen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun lokacin da ta ji wannan kalaman nasa ta ji wasu irin hawaye sun tarar mata cikin idanu, sai dai ga mamakinta wannan raunanniyar zuciyar tata, sai ta neme ta ta rasa, kawai dai wani irin zafi take ji da kuma raɗaɗi mara misaltuwa. Maganganun nasa sun matuƙar ɓata mata rai, wato nuna wa yake shi ɗin mutumin kirki ne. Abin da ya fi komai tsaya mata a rai, shi ne maimaita yana rayuwa ne ta dalilinta. Idan ta tuna ta sadaukar da ƙodarta ga mutumin da ya zama silar mutuwar Ameer ɗinta, ji take gaba ɗaya ta tsani kanta, ji take da tana da hannun dawo da agogo baya, da ta dawo da shi, ta ƙi ba shi ƙodarta.
Tana nan zaune har zuwa lokacin da Hidaya da Sultanah suka shigo. Ko ɗaga kanta ba ta yi ta kalle su ba, don gaba ɗaya ba ta ƙaunar ganin su. Duk da yadda zuciyarta ke raya mata ba su san waye ɗan'uwansu ba, amma yau dole ta bi abin da wani sashe na zuciyarta ke raya mata. Ci gaba da kaɗaicewa ita ɗaya shi ne mafita. Su ma ba su takura mata ba, suka ci gaba da zama kawai.

Bayan kwana bakwai.
Abubuwa da dama sun faru a cikin kwana bakwai, ciki kuwa har da ci gaba da kula da lafiyar Tareeq da kuma Daneen. Ta kowanne ɓangare Alhamdulillah ana samun ci gaba. Sai dai Daneen da kullum tamkar ana ƙara mata kewar Ameer ne. Duk lokacin da kewar ta tashi, sai dai ta zauna ta yi kukanta ta gode wa Allah. Don ma dai in da aka samu sauƙi, tana jin sassauci idan ta tuna abin da ya ci gaba da zaunar da ita cikin asibitin. Duk da ba ta da tabbacin idan ta koma ƙauyensu za ta tarar da Innarsu, amma dai tabbas daga zarar komai ya kammala can ɗin za ta nufa.
Kullum sai Tareeq ya zo duba ta, ta ɓangaren ta ban da wutar fansa da ke ci gaba da ruruwa a cikin zuciyarta babu abin da zuwansa ke haifar wa sai hakan. Dalili kenan da ya sa ta ga alamun zai shigo za ta fake da bacci ko dai wani abun, wanda zai sa ba za ta haɗa ido da shi ba, saboda yadda take jin wata irin tsanarsa a can ƙarƙashin zuciyarta. Ta ɓangaren sa kuwa, samunta tana bacci ko wani abun bai taɓa damunsa ba. A wajensa ma ya fi son hakan, ko babu komai za ta sake warwarewa sosai. Ya kuma san a cikin kwanakin dole ne ta ci gaba da kewar ɗan'uwanta. A lokacin ne kuma aka sallame su su duka, da niyyar za su din ga dawowa ana duba su lokaci zuwa lokaci.

... "Doctor Adam ya sanar da ni Yohana ɗan'uwanki ne wanda kike da shi shi kaɗai yanzu bayan ɗan'uwanki da kika rasa. Sai dai yau kuma na ji wani batu daban, ya ya abin yake kenan?" Abeey da ke zaune kan kujera ya faɗa yana kallan Daneen da ta yi shiru ita ma tana zaune, kanta na kallon ƙasa. Sai da ta runtse idanunta sannan ta buɗe, ta tuna maganar da suka gama da Yohana yanzu, inda yake jaddada mata kada ta manta, kada ta taɓa ambatar tana da iyaye, idan har da gaske tana son ɗaukar fansar ɗan'uwanta. Don haka ta ɗan sauke numfashi kafin ta soma faɗin

"A wajen kishiyar kakarmu muke, wadda ta haifi Innarmu, ita ce ba ta sonmu, kullum cikin muzguna mana take. Ameer da kansa ya ce mu gudu mu bar mata gidan kafin ta ƙara yi mana wani abun. Shi ne ma dalilin da ya sa muka baro ƙauyenmu. Muna so ne mu gina rayuwarmu kafin mu koma mata." Jinjina kai Abeey ya shiga yi kana ya ce

"Iyayenku fa..?" Wani irin bugawa ƙirjin Daneen ya yi, sam-sam ƙarya ba halinta ba ne, ba ta saba yi ba kwata-kwata, shi ya sa take ta kame-kame. Yanzu kuma ga shi ya yi mata tambayar da ba ta tunanin za ta iya amsa ta. Ta ya ya za ta buɗi baki ta kashe iyayenta? Innarta fa?

"Ayyah, ba dai sun mutu ba?" Ta jiyo muryar Abeeyn kamar ya san me take tunani. Jiki a saluɓe ta ɗaga kai ba tare da ta kalle shi ba, don gani take kamar idan ta ɗaga kai ta kalle shi zai karanto ƙaryar da ta masa.

"Ya Salaam.. Allah Ya gafarta musu, Ya sa sun huta." Ba ta iya amsawa ba, sai shi ya amsa abarsa da kansa. Bai kuma damu da hakan ba, don ya san wataƙila ta tuna da iyayen nata ne. Don haka ya gyara zamansa kafin ya ce

"Ki kwantar da hankalinki, In Sha Allah daga yau kin zama ɗiyata. Zan ɗauke ki na tafi da ke gidana a matsayin 'yata albarkacin wannan alfarmar da kika yi wa shalelena. Za ki rayu a gidana ba a matsayin wata daban ba, a'ah kamar yadda na faɗa miki daga yau ke ɗin 'yata ce. Zuwa nan gaba kaɗan, In Sha Allah ni da kaina zan kai ki ki ziyarci ita kakar taki, ba kuma da niyyar in mayar mata da ke ba. A'ah, zan kai ki ne kawai ku gaisa, don za ki zauna tare da ni ne In Sha Allah har Allah Ya kawo miki mijin aure." Ɗaga raunanan idanunta Daneen ta yi ta kalli Abeey cike da mamakin jin abin dake fito wa daga bakinsa. Lallai wannan mutumin akwai karamci. Duk wasu alamomi kuma sun nuna bai san waye ɗansa ba, bai san abubuwan da yake aikatawa a ɓoye ba. Sai da ta harhaɗa kalmomin da za ta faɗa sannan ta buɗe baki da ƙyar ta furta

"Na gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi." Cike da yabawa da hankalin 'yar ƙaramar yarinya mai juriya ya ce

"Allah Ya yi miki albarka, Ameen." Daga haka ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa. Kafin ya kai ga ci gaba da tafiya ya ce

"Ki shirya duk abin da kike buƙata, za a shigo a ɗauka, sai ki fito da su Hidaya mu wuce."

"Tom." Nan ma ta faɗa a sanyaye. Sai da ya fice daga ɗakin sannan ta miƙe tsaye, idanunta a lumshe take hango yadda za ta kasance cikin gidan na Alhaji Dikko, da niyyar ɗaukar fansa. Kamar daga sama ta jiyo jagwalgwalalliyar hausarsa lokacin da yake faɗin

"Na gode wa Allah." Dalili kenan da ya sanya ta buɗe idanunta da sauri ta sauke a kansa. Hannunsa ya zura a aljihu ya fito da wata babbar waya ya miƙa mata. Bin wayar ta yi da kallo, kafin ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya jinjina kai yana nuna wayar da bakinsa.

"Karɓi ki ji mana." Ya faɗa a ɗan dame. Hannunta ta saka ta karɓi wayar, daidai lokacin da ya soma faɗin.

"Ki riƙe wayar nan, zan din ga kiran ki a cikinta lokaci zuwa lokaci. Ki kasance ko da yaushe kina kusa da ita, kar ki yi nisa da ita, saboda yadda zan din ga jin duk abubuwan da suke faruwa. Kar ki yi wasa don Allah. Kusanci kawai nake so ki samu da 'yan gidan, daga nan zan sanar da ke abin da za ki yi mini." Jinjina kai Daneen ta yi, kafin da muryarta da har lokacin ba ta koma ainahin tata ba ta ce

"Ban iya amfani da ita ba."

"Riƙe, zan sanar da ke yadda za ki yi amfani da komai. Na saita miki komai, idan kuma na kira, za ki ga wajen accept nan za ki danna." Jinjina kai dai Daneen ta kuma yi ba tare da ta ce komai ba. Ya juya baya da sauri jin kamar motsi.

"Bari na tafi, don Allah ki yi komai cikin takatsantsan, don kada a fahimci abin da ya kai ki cikin gidan." Daga haka bai jira ta ce komai ba ya fice daga É—akin. Wayar hannunta ta bi da kallo na tsawon sakanni, kafin ta juya ta ta shiga kallon bayanta, sai kuma ta matsa ta ja wasu kaya da ta ga Hidaya ta haÉ—a É—azun, wanda da alama nata ne ta jefa wayar ciki, bayan ta nannaÉ—e cikin wani É—an kwali.

Lokacin da Abeey ya sanar wa da Dada ji hukuncin da ya yanke a kan Daneen, murmushi ta yi ta ce

"Haba kai kuwa Alhassan, kana tsammanin zan ce ban amince ba? Ni kuwa da wace irin uwa ce? Yarinyar da ta ɗauki ƙodarta ta ba wa Tareeq don ka ce za ka ɗauke ta cikin gidanka sai in hana?" Ta dakata a nan tana girgiza kai, kafin ta ci gaba da faɗin

"Ina maraba da ita É—ari bisa É—ari. Allah Ya sa zaman ta alkhairi ne a cikinmu."

"Ameen." Ya amsa yana murmushi.

Duka a harabar ƙaton haɗaɗɗen asibitin suka haɗu, sai a lokacin Daneen ta nutsu tana ƙarewa wannan waje da ake kira da wai asibiti, wannan kyakykyawan waje kallo. A mota suka ɗunguma, inda driver ke jan su. Dab da za su fita daga asibitin ta ji wani irin hawaye masu zafin gaske sun sauka a kan kuncinta. Sun shigo tare da Ameer, sai ga shi ta fita ita kaɗai ba tare da Ameer ba. Lamarin da tun da take ba ta taɓa zata ba. Ba ta taɓa tsammanin akwai ranar da za ta zo su rabu da Ameer ba, rabuwa ma irin ta har abada. Wani sabon miki ne yau ɗin ya tayar mata a zuciya, kewar ɗan'uwanta ta dawo mata sabuwa. Don haka ta shiga rera shi, tana ji ina ma ina ma a ce mafarki ne take yi, ko kuma wani wajen Ameer ɗin ya tafi zai dawo su ci gaba da rayuwarsu. Har suka isa gidan na Alhaji Dikko ba ta daina kukan da yau ɗin ya dawo mata sabo ba. Tun kafin su sauka, masu aiki suka ƙaraso suka soma kwasar kaya suna shigar da su cikin gidan. Ko samun nutsuwar kallan irin ɓarin kuɗin da aka yi a ginin gidan ba ta tsaya yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ba ya wajen.

"Sultanah ku je da ita ɓangaren ku." Abeey ya faɗa yana kallan su.
Chapter 36 · 0% Book details