← Book details Damata Biyu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 129

Sashe 123

Damata Biyu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amira kam ta zama kaman wata celebrity, her aunts ta wajen uwa da sukasan ta dawo called her mom and asked her to give amira waya,data karba sai su fara cewa
"Kar kikara gudu kibar gida...in basu sonki ni ina sonki...Kar in karaji...Kar in kara gani..." Wata daga cikin sister hajiya dake maiduguri ta fadawa amira, she just smile, her dad Rush back and he hugged her yana hawaye yana cewa
"Am sorry am less of a father..." Ya fada rungume daita, he feels so angry ba kadan ba dukda she's back, shima Ismail came home, haka nazifa data haihu, asiya da nasir came together tunda tare suka fita, nasir came and stand besides her irin yana tunanin where have this woman been for this long. He didn't talk or say anything, kawaii only staring at her and she stares at him too, the more he grows the more he looks like his father, her mother prepared dankwake for her tunda shi ta fada mata tana shaawa. Old room dinta aka gyara mata ta shjga tayi wanka tayi sallah, around 8pm tana zaune dakinta sanye da doguwar riga ta lumshe idanuwa ta saki ajiyan zuciya, the contraction continues from time to time. She calls latifat suka sha hira, faiz called her sanda suke wayar da latifat, he calls after 5 minutes again Amma still she's on another call. She went and gave her mother the phone hajiya ta dingayiwa latifat adua da godiya. Basu dade da gama waya ba fajz ya sake kiranta, tana picking yace
"Dawa kike waya..."was what he asked
"Latifat..." Ta amsa mashi tana dafa mararta,
"What are you doing..." Ya tambayeta calmly
"Nothing...ni dai marata ke ciwo...I think am having a contraction..." Ta fada mashi ahankali as she knows it's becoming serious
"Contraction?...meye contraction..." Ya tambayeta sounding kind of confused
"Labour..."ta amsa mashi atakaice
"Oh my goodness...oh my gosh...wow... should I come...bari inzo... in kaiki hospital..." Ya fada yana mikewa da sauri sounding so anxious, Dariya amira tayi tace
"Am joking. " Ta fada tana Dariya dukda she's not tasan if ba natsuwa gareshi ba,
"Are you sure?.." ya tambayeta
"Yes mana...ka taba ganin Inda mai labour take iya rike waya har tayi hira?..." Ta fada tana Dariyar karfin hali tana dafa waist dinta, tunawa yayi da sanda bintu zata haihu sai yaga yes she's not in labour bai san kowa da yanda yake so mashi ba,
"Kinsan am missing you already...ni dai ban san how comes nake sonki haka ba..." Ya fada sounding so calm,
"Hmmm...ba dole kayi missing ba...tunda kabi ka cinye ne ba bu saura?.." ta fada tana Dariya, dariya yayi yace
"Kina kam da saura...wani abun ma sai kin dawo...Kinga yanzun that zai zama mu biyu kadai we will travel...do hajj together... go-to umrah every year...do so many fun things kafin yara suyi mana yawa...don ni ina son haihuwa sosai..." Ya fada mata shuru amira tayi for a moment before saying
"Pls bari in shjga bathroom...let me ease myself..."
"Kar ki kashe...ki je ki dawo..." Ya umarceta
"My battery is low...zanyi charging wayata..." Ta fada to get rid of him
"What ever call me..." Ya fada mata yana kashe wayar shi. Itama zata kashe wayar sai ga kiran ahmed,they gist for a while before sukayi sallama.kashe wayar tayi ga baki daya mum dinta ta shigo sukasha labari. Har 11 basuyi bacci ba suna hira tana fadawa mum dinta how lagos is, tana fada mata yanda ake neman kudi a chan that ba kowa zaiyi lalata ba sai if ka sakawa kanka lalata,one thing da hajiya ta lura is yanda take yawan shjga bathroom after 10 minutes
"Amira are you alright?..." Ta tambayeta, shuru tayi for a moment before saying
"Wallahi marata...ke ciwo...tun muna cikin jirgi nake jin ciwon..." Amira ta fada mata kaman she have been waiting to asked.
"Oh my... sorry...kou mu tafi hospital...I think we should go to hospital..." Hajiya ta fada tana mikewa, amira batayi mata gardama ba, it's like having what she didn't have before, Amira kallon ta ta dingayi har ya fice daga dakin, tana fita sai ta saki ajiyan zuciya ta saki murmushi feeling so happy, babu abinda ke da ban haushi kaman wanda ya kamata ya soka ya ki sonka, when you're hungry for the love and affection and all of a sudden you got it sai kaji wani irin sanyi, ta dade bataji irin farin cikin da take ji ba, she so loved, murmushi ne kwance kan face dinta dukda the contraction continues, dafa gadon tayi har mummy dinta taje ta fadawa alhaji amira tana Labor, he asked his driver to get ready to take her to the hospital, dawowa tayi amira ta kalleta tace
"Mummy it's not serious fa...kou dai a barshi kawai..." Amira ta fada tana kallon ta,
"Aa... noway...kawai muje hospital...zan Kira hajiya lantana zata sameki hospital... yanzun kuje da asiya...sai dai bamu da komai na baby ..." Hajiya ta fada kaman ba ita ba, it's like she's even happier than amira, amira saka doguwar riga tayi tare da hijab sukayi waje, asiya hajiya ta tado suka fita tare, amira na zuwa wajen mota ta dan dafe kugunta tare da rike asiya gam kaman zatayi Kuka, it's getting worst, she just prayed ba fajz ya jawo mata wannan early labour ba don her Dr said in next two to three weeks dukda yace it can be less, she feels fluids under again ba kadan ba, bata san sanda tace
"Wash ." Ba, kasa shiga motar tayi wanna lokacin sai da taji ta lafa ta shjga mota, haka suka tafi hospital with nothing, she sees her dad gave asiya money Amma bata san kou nawa ba, this time was so different, the hospital is the hospital da suke zuwa tun suna yara, it's one of the best a kano, she already paid for everything har da delivery dinta over 300k gashi wannan ya zama waste, she feels more and more contraction, bata dade da zuwa ba matar da mum dinta ta kira mata tazo, sanda aka dubata da farko akace she's in 4cm, bats da experience din wannan don duk bata samu wannan a na farko ba, like joke abun ya zama gaskiya, tun ciwon yana zuwa yana daukewa har ya kaiga if ya zo sai ta dinga bugun gadon, the pain was so unbelievable, na nasir is a gift kan wannan,
"Komai naka matsala ne..." Ta fada under her breath as she thought of fajz, around karfe biyu ta kalli agogo with her weak and tired eyes tana tunanin yana chan yana bacci, ba karamin wahala tasha ba, har karfe hudu she's still at 7cm, hajiya kam batazo hospital ba Amma tafi wacce ke hospital din shjga tashin hankali, sai ta Kira every five minutes, tasa an kawo wasu kayan amira ta kira ismail ya kai baby wears hospital tunda tasan bazai rasa ba since his wife is pregnant , bai dade ba ya kawo some of the unisex daya saya. Har asuba amira bata haihu ba, taci kuka babu hawaye,
"Wayyo ku kirashi...ku kirashi...pls a Kira faiz.. I can't take it anymore..." Ta fada tana Kuka sosai Amma face dinta babu hawaye kou guda, voice dinta ya dishe. She asked the nurse to tell them to call faiz,
"Ai if kina da number shi kina iya kawowa in Kira maki shi..."inji nurse din dake dakin da amira take amira data sha bakar wahala girgiza kai tayi tana
"Wayyo Allah...wayyo.. " to fada tana fara fadin number, tana daukan long time after each digit, she's not crazy so she knows his number, the pain baiyi erasing memory ba don kou jiya I yanzun she knows what he was doing to her, he shouldn't be sleeping while she suffer in the whole pain, tana gama fada mata number tayi dailing zata mikawa amira wayar amira data gigice kasa amsar wayar tayi tace
"Pls.. ki sakamin...a loud speaker..." Ta fada tana yarfa hannuwa as the pains goes more and More
"Insha Allah tunda kin shiga 8cm kin kusa .." nurse din ta fada mata tana saka mata wayar daya fara ringing a loud speaker 🔊
A bangaren faiz kam bayan sunyi waya da amira he tried calling her severally Amma her phone is phone is off, dayaje sallah asuba ya dawo he still called still switch off,
"So baki son magana dani kenan..." Ya fada yana cire jallabiya da yaje masjid dashi, kwanciya yayi yana latsa wayarshi. Unknown number ce ta kirashi and he feels that he's not going to pick Amma ganin it's still dark yasa yayi tunanin it's something serious, dagawa yayi ya kafa a kunne tare da sallama, amira na jin yayi magana cikin kuka tace
"Ka...zo....na.. gaji..." Ta fada sounding so exhausted, fajz mikewa zaune yayi idanuwanshi waje wondering who's talking
"Amira..." Ya fada cikin daga murya as he feels she's the one,
"Na..." Sai da ta fara amsawa bata san sanda ta saki wayar ba as another hard one come in, wani irin nishi ta saki cikin wahala
"The baby is coming..." Inji nurse din dake wajen amira ta fada,, dr ce ta shigo,
"The baby is coming..."nurse din ta fadawa dr, wayar is already far away from their mouths Amma faiz can still hear what's going on, wato amira is in labour kuma bata fada mashi.
"One more push...and you're done..." Dr ta fadawa amira da duk ta gigice as she hears the head pushing forward,
"You're really doing great...kina kokari sosai.. " inji the dr, wani the next push came with power data batasan tana da shiba and she pushed sosai again and it's over, kukan jariri take over the room, faiz dake parade a dakinshi lumshe idanuwa yayi tare da furta
"Alhamdulillah... alhamdulillah... alhamdulillah..." Kawai ta dinga maimaitawa saboda farin ciki hearing the baby cry, it's the cry every father wants to hear, kashe wayar yayi tare da sujudul shukur saboda farin ciki.
Chapter 123 · 0% Book details