Sashe 9
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Wallahi yau se kin barmin gidana ke da wannan shegiyar ƴar taki ,domin wannan ba ƴata bace , ko kuma in kasheku na kashe banza " yana magana yana dukan matarshi dake kwance akasa tana kuka ga kuma wata yarinya yar karama kyakkyawa bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba tana rike da kafar mutumin tana kuka , sa kafa ya yi ya hambareta ta fa di ta fasa hancinta da bakinta , rarrafawa matar ta yi taje ta dauki ƴarta ta rungumeta suna kuka tare ,yarda belt din hannunshi ya yi ya tsaya gantsan_tsan akansu yanuna su da yatsa " wallahi Maryam karki yarda in dawo insamu wannan yar shegiyar a gidan nan in ba haka ba kuwa ƙonata zanyi da ranta sannan in haɗa dake , jaka mara mutunci kawai har ni za ki kalla kice wannan yarinyar yata ce bayan kuma duk cikin ahalina babu farin fata kinje kinyi zinan ki , kinsamu cikinta za ki ƙaƙabamin ita to tun wuri kinje ki fadawa kwarton naki bazan karbi shegiya ba " fuuuu yafice agidan kamar ze tashi sama ,Maryam na kuka tana gogewa yarta jinin dake zuba a hancinta da bakinta ta ce" Allah shine shedana wallahi ni ba mazinaciya bace , wannan yar takace kuma jinin ka, in sha Allah, Allah ze saka mana" kallon mamar nata ta yi ta ce" mama mu gudu kar baba yadawo yasamemu , banaso yadinga dukanki" wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tasa hannu ta share ta face majina ta ce" karki damu Asmita in sha Allah babu abinda ze mana tashi inyi miki wanka se in miki kwaɗon ƙanzo da kuli_kuli kici kijin ko" haka ta dauki yarta ta yi mata wanka da klin dan ko sabulun wanka babu agidan kuma bawai dan bashi da halin siya bane muguntace kawai irin na malam Mamman.
Gyara mata kwanciya tayi akan yamutsatsiyar katifar dake dakinta ta yi ta dauko fallen zanin daurawarta ta shifida mata , datse kofar dakin ta yi da sakata ta yanda koda malam Mamman yadawo baze shiga dakin ba .
Suna cikin bacci sukaji yafara doka kofar dakin kamar ze ballashi , afirgice suka tashi ,rungume Asmita Maryam ta yi ƙam ajikinta muryan malam Mamman sukaji yana " wato ni zakiyiwa wayo ko Maryam to gwarama kitashi ki bude in kuma ba haka ba a dakin zan ƙonaku dukkan ku biyu" .
" wallahi Mamman seda ka ƙona mu amma bazan taɓa bude maka kofar dakin nan ba ,tunda kai babu Allah azuciyarka mara imani kawai . Kuma ko mutuwa ka yi wallahi Asmita nada gadonka domin ƴar kace ta halak"
Ta bashi amsa tana kuka kamar ranta zefita , har lokacin tana rungume da Asmita datake a tsorace gani takeyi kamar baban nata konasu zeyi , babu wanda Asmita take tsoro aduniyar nan sama da malam Mamman domin yatsaneta kullum cikin dukanta yakeyi da aibatata ,kuma yaro yana sake jikine da wa'yanda yake sonshi , ga shi agabanta kullum se ya da ki mamanta.
Kokarin fasa kofar yakeyi amma yakasa saboda kofar karfece, makobtanshi ne suka shigo suna hanashi abinda yake da niyyar yi , komawa kansu ya yi ya karta musu rashin mutunci daga karshe yakoresu ya ce musu kar ya sake ganin ko wani munafikin a gidanshi.
Haka Maryam da Asmita suke rayuwar wahala agidan ko kadan basa samun farin ciki , farin ciki yakauracewa Maryam tundaga sa'in da ta haifi Asmita , jaririyar tana da hasken fata malam Mamman ya ƙyankyashe ƙasa ya ce shi wannan ba yar sa ba ce seda ko maryam na da kwarton da yake amfani da ita.
F and share 🖋️🖋️
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹
Page 07
*_ story & written_*
By
*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)
*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️
Page 07
Yau sati daya kenan , zanen Asrah harya warke dake bata da ƙyan jiki kuma tana samun kulawa sosai ,wajan yabushe ya yi baƙi ga sunan Tajuddeen baro_baro abayanta kullum in za'a mata wanka seta tsaya a gaban mudubi ta karkace gefe ta kalli sunan hakan ba karamin nishadi yake sataba, shikanshi Tajuddeen inya gani yanajin sanyi aranshi .
Kamar kullum tana painting room din Tajuddeen tana zaune Kamar wata uwar mata ta maida hankalinta tana zanen Tajuddeen , shikuma baya nan yana garden yana zaune , dan bazaka taba ganinshi acikin yan uwanshi yana hira ko wani abu da su ba .
Zanenta takeyi cikin kwanciyar hankali batasan su parsa sun shigo painting room din ba , kasancewar yau Friday da wuri suka tashi daga school .
Yanda tamaida hankali akan zanen ma batama san da shigowar su Zoya,umaisha,iklas,parsa,Rameesa ba ,tafiya suke yi sanɗa_sanɗa basa son tasan sun shigo dan so suke yi su dauke drawing din da take yi umaisha ce take directing dinsu yanda zasu yi ita ce boss.
A hankali umaisha tasa hannu tadauki zanen da Asrah takeyi suka gudu daga part din suna ihun" yeeeeeeeh mun dauke_mundauke"
bin bayansu ta yi itama da gudu dan bataso su yaga mata zanen ta, ɓace mata sukayi da gani bata gansu ba, dubasu ta yi ako ina bata gansu alamar ma kamar ba sa cikin mansion din , fitowa ta yi cikin compound din nan ma bata gansu ba , kuka tafarayi tana bubbuga kafa ,ga shi bata haduda yan gidan ba se masu aikine da masu tsaron gidan ne suke ta fita da shiga .
Garden ta nufa tana kukan ɗauke mata zanenta da sukayi kuma bata san inda suka yi ba,volume din kukan nata sake ƙaruwa ya yi lokacin da ta hangi Tajuddeen na zaune acikin garden din ,wajan ta nufa tana isa ta kwanta abayanshi,sa hannu ya yi ya jawota ta dawo gabanshi goge mata hawayen fuskar ta ya yi " hey! Why are you crying?" " to basu zoya bane ba! suka daukemin drawing dina ba suka gudu " yanda take maganar tana turo baki ya bashi dariya amma beyi ba kawai murmusawa ya yi ," Okay kyalesu zasu dawo kinji?" " Tom"
Sake kallonta ya yi ɗakyau ,dama so yake yafaɗa mata nan da kwana biyar ze tafi amma ba ya tunanin tanada wayon da zata fahimta .
Magana yafara yana kallon shuke_shuken dake garden din " Asrah zanyi tafiya ,zan jima amma ba sosai ba .I want you to take good care of yourself " narai_narai ta yi da ido ,se kwabula fuska takeyi tana shirin yi mishi kuka , " wai ke bakida aikinyi se kuka?" Girgiza mishi kai ta yi sannan ta ce" to bakai ne kace zaka tafi kabarni ba, nide se na bika" nan nauyar ajiyar zuciya Tajuddeen yasauke " Asrah sanda zamu tafi inda nake rayuwa daga ni seke na zuwa,za ki bini batare da izinin kowa ba "
Itade jin shi kawai takeyi bawai dan ta fahimci inda maganar ta shi yadosa ba .
Cikin aljihun rigar shi yasa hannu yafito da wani box me matukar kyau , budeshi ya yi yafito da wasu abin hannu masu matukar kyau da tsada me daukar hankali, guda biyu na diamond silver color, yanayin design din ma kawai abin kallo ne ya hadu sosai,abin hannun yana da adjust za'a iya ragewa kuma za'a iya ƙarawa saman shi kuma anyi rubuta " T&A" wato Tajuddeen da Asrah kenan .
Kamo hannunta ya yi na dama yasaka matashi ya ragesa yakoma dede hannunta yanda nan gaba inta ƙara girma ita da kanta zata iya ƙara shi , " woww, tajuju ya yi kyau sosai! I love it " ta faɗa tana shafa abin hannun se santin kyau din abin hannun takeyi , saka nashi shima ya yi a hannunshi bakaramin kyau ya mishi ba , ɗago kai ya yi on a serious face ya kalleta ya ce
" ko da wasa karki yarda ki rabu da wannan abin hannun kinji ko"
gyada mishi kai ta yi tana murmushin farin ciki , mika mata tafin hannunshi ya yi
" Promise me bazaki taba rabuwa dashi ba ko da bama tare. "
Daura hannunta ta yi akan nashi ta ce
" I promise you tajuju , I am going to keep it safe "
Tana gama faɗar haka ta sauko daga kan kujeran ta ruga aguje , da kallo yabi bayanta . Aranshi ya ce
" Nasan zuwa nan da 10 years za kiyi hankali sosai, za ki zama budurwan da babu wanda ze yi gigin neman soyayyarki domin kuwa kedin matar Tajuddeen Mubarak Bishara ce "
Kokarin shiga mansion din ta keyi taci karo da Saghar da Hafiz suna kokarin fitowa , ja baya ta yi sanin Saghar ze iya maketa , watsa mata harara ya yi ganin yana hararanta ne yasa ta murguɗa mishi baki amma shi be ma lura ba Hafiz ne kawai ya gani. yasa kai ya yi gaba yabar Hafiz a tsaye awajan ta . Kallon ta ya yi yaga se washe baki takeyi kamar gonar auduga ,shi dariya ma ta bashi ya ce
" Asrah wannan murnan da akeyi haka na meye ne ?"
Batare da tabashi amsar da ya tambayeta ba ta nuna mishi hannunta dake dauke da abin hannun da Tajuddeen yasa mata, riko hannun ya yi yana " wowwww, gaskiya ya yi kyau sosai wallahi inyaaa Asrah din Tajuddeen dinta " shi kanshi bakaramin kyau abin hannun ya mishi ba yanayin design din so simple ga shi na diamond ne silver color ga shi first alphabet din sunansu ne ajiki T&A ,se yabawa yaketa yi ,
" To kar fa ki yarda shi a garin ƙiriniya kinji ko?"
Gyada mishi kai ta yi kafin ta sa ke rugawa aguje cikin gida abinta duk wanda ta hadu dashi se ta tsaya ta nuna mishi abin hannun da Tajuddeen yabata .