← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 60

Sashe 2

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga bayansu sukaji daddadar muryanshi yana fadin " come here my Asrah waye ya taɓamunke?" duk juyawa sukayi suna kallonshi , dan matashin saurayi kyakyawa ajin farko fuskanshi a turnuke daga gani ranshi amatukar ɓace yake yana sanye da wandon sojaji three quarter se baƙar riga kanshi na sanye da facing cap . Asrah najin muryanshi taraba ta tsakiyarsu taje da gudu ta rungumeshi tana sheshekar kuka. gaba dayansu seda sukasha jinin jikinsu banda Abbas da Ahmad da Haris ,amma daga kan su Umaisha,Iklas, zoya ,parsa,rameesa, saghar,salim,Sahil,sudais , kallonsu yayi da rikitattun idanunshi murya adaƙile yana shafa bayan ya ce " Asrah waya taɓaki acikinsu " yayi maganar yana dagota ajikinshi kallonsu itama tayi kafin tafara nunasu da ɗan yatsanta ta ce " all of them dukansu sun zageni kuma sun dakeni" a kausashe ya ce " na rantse da Allah duk wanda ya sake sa hannunshi ajikinta da sunan duka kokuma yi mata tsawa ko faɗa ze hadu da fushi na " yana gama fadin haka yadauketa yadaurata akan wuyanshi suka bar wajan spot din, sude da kallon mamaki kawai sukabi bayansu saghar kamar zeyi kuka ya ce " Allah sena kama Asrah nayi mata ɗan banzan duka sede Tajuddin ya kasheni " ya karishe maganar hawaye Tabb a idonshi, girgiza kai Haris yayi ya ce" karufawa kanka asiri dan kasan halin Taj zakajane yamaka duka inde akan Asrah ne , sede kuyita hakuri da ita harta saba da halin nan tunda kunga ai ba anan ta tashi ba kuma karamace " kwafa saghar yayi yabar wajan sudais yabi bayanshi duk watsewa sukayi suka shiga cikin mansion din.

Yana dauke da ita akan wuyanshi tanata dariya suka shiga cikin tamtsamemen mansion ne na gani na faɗa komai na ciki anzuba dukiya kamar ba'a so , tundaga kan kayan furniture har izuwa kayan alatun dasuke falon duk yan kasar waje ne saboda irin kyaun su da tsarin su kai daga gani ma base an fada ba kasan cewa wannan babban gidan alfarma ne ganin yanda dukiya ke kuka , ga manyan kujeru masu numfashi da ɗaukan hankali. Cikin ƙatuwar haɗeɗɗiyar falon na dauke da stairs matakalar bene kusan fiye da goma inda duk wanda kahau ze sada ka da part din wani ,shi kanshi matakalar benen abin kallo ne saboda yanayin design dinshi, in har nace zan tsaya fada muku irin kyan da gidan yake dashi tofa ko one page baze dauka ba kude ku ƙiyasta kawai .

Kamar bega kowa a falon ba yanufi part dinshi shida Asrah duk maida kallonsu sukayi kansu.

Uncle Hameed ne ya ce " Taj ba magana ne ?" Kallonsu Taj yayi batare da yace komai ba yahaura upstairs yanufi part dishi kamar bega Abbu da Abbie da kuma uncle Hameed dasuke zaune afalon suna mishi magana ba.

Girgiza kai Abbie yayi ya ce " Hameed bansan yazanyi da Tajuddin ba gabaki daya shi fa rayuwarshi a murde yake yaro tun be tafasa ba haryafara konewa ? ni agaskiya nafara canza shawara akan samo mishi addimission a U.S military academy at west ,saboda Tajuddin be zama soja bama ya muka ƙare dashi balle kuma idan yazama sojan ƙasa da ƙasa bana tunanin wannan shawara ce me kyau " Abbie ya ya karishe maganarsa da damuwa akan fuskarshi.

Abbu da uncle Hameed sukansu lamarin Tajuddin na damunsu domin Taj mutum ne da inzaku zauna tsawon shekara ɗari tofa seyayi ra'ayin maka magana kafin yayi ,ba koda yaushe bane yake magana ba.

Abbu ya fuskanci ya'yan nashi wato Abbie ya ce " ya Mubarak ni aganina canza shawara akan makarantar dazeje bashida fa'ida tunda ka san wannan shine babban burinshi yanason yazama soja wannan shine mafarkinshi kuma dukkanmu munsani , to ruguza mishi mafarkinshi kuma dede yake da ruguza mishi rayuwarshi , muda muke neman hanyar da zamu dinga faranta mishi ko Allah zesa yadawo mutum kamar kowa yadinga walwala wallahi tun marigayi baba Allah yajikanshi ,nadade banga mutum irin Tajuddin ba amma gado yayi agun baba"

Yawwa muddin kunaso muci gaba da tafiya yanda Yakamata shine nadinga ganin comments dinku hakan ne ze tabbatar min da kuna biye dani 😒😒😒😒.

🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹

*_ story & written_*

By

*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️

Page 02

_______ " abinda kafada hakane kam ya Ismail saboda hanashi yin abinda yakeso zesa murɗeɗen halinshi sake ninkuwa fiye dana da,kaga garin neman gira kuma an rasa ido "cewar uncle Hameed jinjina kai Abbie ya yi dan ya gamsu da maganan ƙannen nashi , amma shi a har kullum burinshi yaga ɗan shi yadawo kamar kowa , but lamarin Taj kullum gaba_gaba yakeyi du ka nawa yake amma tun bekai haka ba shi kadai yatara zafin zuciya, miskilanci,rashin damuwa da damuwar kowa, karfi ga kuma tsastsauran ra'ayi da murdeden hali , kamar ba'a gidan yake rayuwa ba. Haka suka dinga tattaunawa akan Taj da bemasan sunayi ba yana can a part dinshi shida Asrah suna painting room domin kuwa Tajuddin da Asrah Allah ya yi musu baiwar drawing wato (zane) duk sanda suka shigo painting room shida Asrah tofa kafin su fita Asrah seta zana hotonshi fiye da goma.
__________ yanzu ma kamar yanda ta saba tana zaune agaban painting board hannunta rike da pencil ta tsurawa Tajuddin ido tana kallonshi tana zana shi , shikuwa yana drawing din ɗawisu duk kallonshi da takeyi yana sane da ita kuma yasan shi take zana wa ɗan inde yashigo da ita nan tofa shine abin zanawarta setayi fiye da goma. Gama zanen ta yi, ta dauko papper da ta yi ta nufeshi tace " tajujuna kalla kagani yayi kyau?" sa hannu yayi yakarba yaci karo da kyakkyawar fuskarshi ga facing cap din dake kanshi ya ce " ehhh not bad yayi kyau" murna tafara yi harda tsalle leƙa kanta tayi tana son ganin meyake zanawa , ganin ta zuro kanta ne yasa ya juyar da kanshi gefe da kuma paint board din yaci gaba da zanenshi zama tayi akan kujera tana kallon nata drawing din,bayan wasu mintuna yazaro papper batare da yace mata komai ba ya miƙa mata, sa hannu tayi ta karba ta kalli zanen dakyau ita ce ya zana tana zaune acikin garden ga ɗawisu zagaye da ita hannunta kuma na rike da dan karamin yaron zomo, da iya karfinta ta saka ihu me karfin gaske wanda seda yasa part din nashi dauka, du ka hannunshi biyu yasa ya toshe kunnuwanshi yana runtse idanunshi domin ihun datayi seda yaji gaba daya ilahirin kanshi yadauka nan take yaji ciwon kai , itakuwa Asrah duk farin ciki ne yasata haka ganin irin kyaun din datayi gata ga dan jaririn zomonta datake mugun so shisa ta daukoshi tundaga California. baƙinta dake dauke da kananan hakwara da wasu sunfita tafara fanfara ta budesu se dariya takeyi tana tsalle sannan ta rungumeshi daga kanta tayi ta kalleshi ta ce " my tajuju what's that me ?" ka sa ce mata komai yayi ɗan har lokacin kanshin na damunshi girgiza mata kai kawai yayi .
Bude kofar bedroom din Tajuddin tayi ta shigo hankalinta atashe gaba da ta firgice,kai kallo daya zaka mata kasan eh tabbas ita ce ta haifi Asrah saboda suna kama sosai, ga wata hamshakiyar mata kyakyawa abayanta fuskanta manne da medicated glass fari , matar na kama sosai da ita mahaifiyar Asrah sede ta girmeta , ganin Asrah da Tajuddin din basa bedroom dasauri suka nufi painting room din Taj , tana bude kofar painting room din hankalin Asrah dake rungume ajikin Taj yadawo kansu taje wajansu ɗan nuna musu zanen da Taj yamata ɗagata sama anty amarya tayi tana kallonta ganin babu abinda yasameta hasalima farin ciki takeyi hankalinta akwance.mamaki ne yakama anty amarya da Ammi ganin babu abinda ya sami Asrah din sauketa ƙasa anty amarya ta yi ta durgusa agabanta ta ce " my baby girl meyasameki mukaji ihunki " da fa anty amarya Asrah tayi tace " mom there's nothing wrong with me my tajuju ne yayi drawing dina am so happy and excited" tafada cike da yarinta tana nuna musu zanen ,dafe goshi Ammi tayi anty amarya kuma tasaki baƙi tana kallon yar tata, duk sun ƙasa magana jin abinda Asrah ta faɗa musu wai saboda kawai anyi drawing dinta ne yasata wannan ihun da ya matukar daga musu hankali duk sunyi zaton mugun abune yasameta shisa cikin gaggawa suka nufo part din Taj din amma with their surprise babu abinda yasameta sema samunta dasukayi tana farin ciki da nishadi , sake jinjina ƙiriniya dakuma sangarcewar Asrah sukayi , girgiza kai kawai sukayi Ammi dakyar tasamu bakin cewa " Asrah you're unbelievable yanzu just because akan zane yasa kike wannan ihun " ta tambayeta tana karasowa kusa dasu gyada mata kai Asrah tayi ta ce " yes Ammi my tajuju made it for me" satan kallon Tajuddin Ammi tayi ta kasan ido dake zaune abakin gado yana danna wayarsa kamar besan da ruwan alamarsu a dakin ba ɗan ko kallon inda sukema beyi ba tun shigowarsu, yar murmushi anty amarya ta yi ta ce " Allah ya shirya min ke " kafin tasa hannu ta dauketa taname mayarda kallonta kan Tajuddin " Taj ina cikin yi maka favorite dinka kawai naji ihun wannan sarkin rigimar zakazo kaci ne ko in kawo maka shi!? koɗe in bawa Ammin ka zakazo kaci a part dinta ?" ta fadi hakan tanameson jin abinda zece zuciyarta a karye , Ammi ka war da kanta gefe tayi kamar batasan akanme suke magana ba .
Chapter 2 · 0% Book details