← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 60

Sashe 59

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Monday tun kafin su Nabiha su tashi daga bacci har sun gama shiryawa cikin uniform driver yakai su school.

Haka suka ci gaba da rayuwar su kamar babu abinda ya faru ko da su ummah suka gansu a gidan basu ce komai ba.

Bayan zuwan su da kwana uku ne aka samarwa Cele aiki.anty Teema kuma aka bata gidan dake cikin gidan,da masu yi mata hidima.

Har yanzu ana kan sace yara da ake yi daya bayan daya,...

Wata ranar talata Umaisha da Iklas sun fita shopping a hanyar su ta dawuwa aka tare su sannan aka kashe driver da ya dauko su,aka ɗauke su.

Shuru_shuru ana jiran dawuwar su,amma Shuru har yamma ya yi nan fa aka fara neman su.motar da ya daukesu aka gani bakowa a ciki se gawar driver dake yashe a ƙasa.

Hakan yasa suka fahimci an yi garkuwa dasu ne.

Lokacin da suka ji wannan labarin hankalin kowa ya tashi.an yi binciken amma Shuru bayan su an sake sace yara yan mata goma.

Har karfe sha biyu suna zaune a Falo sun yi carko_carko,kowa ka gani kasan yana cikin matsananciyar damuwa.

Su Sabriyah sun yi kuka yar sun gaji suna zaune a Falo.

Kiran waya ne ya shigo wayar LTG,kin dagawa ya yi domin a halin da yake ciki bayajin ze iya yin magana da kowa,kira ne kan kira yake shigowa,kallonsa Abbie ya yi "Tajuddeen waye haka yake kiran ka Kaduba ka gani".

Kallon screen din ya yi yaga unknown number.

Picking ya yasa a handsfree,dariya ne suka fara ji yana tashi irin na mugunta din nan,duk ƙasa kunne sukayi su ji kowa waye wannan.

A bangaren wanda ya kira din kuwa ya fara magana cike da izza"Tajuddeen Mubarak Bishara, babban sojan ƙasa da ƙasa,wanda ko ina ake ji dashi.na musamman da babu kamar sa, jami'i me kwazo.wayyo meyasa nake cika ka da wannan dogon surutun yanzu de bari in gabatar maka da kaina.
Ni ne nan shugaban Italian Mafia da ka dade kana nema ruwa a jallo,nasan kasan yan mata talatin suna hannuna idan aka haɗa da ƙannnenka kuma sun zama talatin da biyu, ya ka ji lissafin?"ya tambaya yana kecewa da mahaukaciyar dariya.

Runtse ido LTG ya yi yana jin tsokan namar jikinsa na rawa.wato ɗan ta'adda har yana da gards din da ze kira wayarsa.

"Tun kafin ka fusata ni in yi farautar ka da kaina ka sa'ke yan matan da suke wajen ka sannan kuma ka miƙa wuya". LTG ya faɗa.
"Hhhhhhhhhhhh!,soja ya harzuka.. kana ganin barazanar ka zata yi aiki a kaina ne?,in har kana son in rabu dasu to gobe ka kawo mini kan ka da kanka rayuwar ka shine ze fanshi rayuwarsu,idan kuma ka yi gangancin yin wani dabara irin naku na jami'ai to na rantse maka sena kashe su gaba dayansu,rami me zurfi zan sa a ha ƙa in kunna wuta a ciki,haka zan dinga jefasu daya bayan daya a ciki,nikuma ina dariya domin jin kuka da kururuwansu yana sanya ni nishadi da jin dadi".

Hannu Ammi ta sa ta rufe bakinta ta fashe da kuka"innalillahi wainna'ilaihi rajuun, shikenan ze kashe mana yaran mu!".dafata Hajiya babba ta yi ita kan ta ji take yi kamar ta yi kuka,karfin hali kawai take yi in su suna kuka to waye ne ze rarrashi su Sabriyah dake kuka.

"MRS Bishara ki dena wannan kukan abun me sauki ne, kawai kiyi shahada ki turomin ɗan ki ,se in sa'ke gaba daya wa'yanda suke waje na".ya mata magana cikin shakiyanci.
A fusace Sudais ya ce"ka dena yiwa mahaifiyar mu magana damu zakayi ita din ba Sa'ar ka bace.idona idonka se na yi gunduwaduwa da namar ka". Sudais ya yi maganar jikinsa har rawa yake yi.

Dariya ya yi "ka sassauta Muryar ka,Ko kamanta da Umaisha ne kam?, wannan din nan kanwar taku me shegen surutu babu karya yarinyar ta ji kyau akwai diri da shape ko ina dinta a cike yake,idan ka sa'ke daga min murya to da ita zan huta a wannan daren bayan na more kuma kasheta in ga yanda danayi".
Innalillahi wainna'ilaihi rajuun tabbas ba yi da imani tunda ya iya sace yara masu yawa haka to kashesu ko kuma aikata abinda ya faɗa baze mishi wahala ba.

Abbie ji ya yi jiri na kokarin kwashe sa duk da yana zaune amma ji ya yi kamar ze fadi, Hajiya babba can't hold her tears nan take ta fara hawaye itama,anty amarya kam kukan da take yi baze misaltu ba.jikin Ammuh ya gama yin sanyi.

Sabriyah da Asmita daskarewa suka yi a inda suke zaune jin muryar wanda ko a mafarki suka ji se sun gane waye ne.
A hankali Sabriyah ta furta"Fu'ad?"tunani ta fara yi dama wannan shine true color din Fu'ad?, mutumin da suka dauka a matsayin dan uwa, shine na farko da yabawa rayuwarsu muhimmanci,a she wannan shine asalin sa, gaskiya Allah na son ta daɓe sa ta faɗa tarkon da yaso cilla ta ba.

"Na amince zan sadaukar da kaina a madadin su". LTG ya faɗa a dake domin yasan kamar yanda ya faɗa in bawai zuwa din ya yi ba baze taɓa sa'ke su ba.

"Da kyau soja!, warning na gaba da zan maka shine ko da wasa karka yi gigin zuwa da sojoji ko wasu jami'ai.kasani kasan abinda zan aikata.
Kai sheda ne,ni na kona babban asibitin Turkish dake dauke da mutanen sama da dari tara,Bama se na tsaya ina tuna maka abubuwan da suka faruwa shekara hudu baya ba nasan ka tuna ko?".

"Zan yi yanda ka ce,kar ka yi musu komai".

Cike da nishadi Fu'ad ya ce"Nagodeeeeee, soja".
Ya kashe wayar.

Su de yau suna cikin tashin hankali taya za'a yi su yarda LTG ya tafi wajen mutum me matukar hatsari irin wannan batare da jami'an tsaro ba ko kuma makami ba.

Kallonsu major Marry ya yi"do not make any move,am going there alone"

"Ya Taj babu yanda za'a yi mu Barka ka tafi wajen wannan hatsabibin mutumin kai kadai"cewar ACP Jawan.
Abbie ma ya ce"haka ne Jawan dole a san yanda za'a yi amma kam baze je shi kadai ba".
"Abbie ni kadai zan tafi,ku baku san hatsarin wannan mutumin bane duk abinda ya ce ze aikata to fa se ya yi din"..
Ammi dake kuka ta ce "baze yu ba,ni de bazan yarda kaje ba,ka rufamin asiri ka zauna bana son rasaka".
Murya a tausashe Sudais ya ce"Ammi dole LTG ne ze je amma ba shi kadai ba,dole zamu bishi da kuma sojoji se mu labe daga baya"
Duk sun amince da shawarar da Sudais ya bayar amma shide LTG kawai ya jisu ne, yasan abune ma wuyaci.

Suna nan zaune a falon har kusan karfe uku na dare babu wanda ya runtsa.
Miƙewa Sabriyah ta yi ta faki idon kowa ta shiga dakinsu number Fu'ad ta kira.
Yana dagawa tafara zazzaga mishi ruwan Masifa.
"Calm down my Sabriyah, kin san bazan taɓa cutar da rayuwarku ba,kawai ni Tajuddeen din nake buƙata in kuma be zo ba Wallahi sena kashe su".

A firgice ta ce"dan Allah Fu'ad kar ka yi haka menene Abinda suka aikata maka in ma gaban ka kakeyi ai da ya Taj ne ba wai da su Umaisha ba".

"To in har kina so in rabu dasu dukkansu dole se kin sanar dani duk wani abinda suka shirya nasan sun yi planing din yi min ha'inci".
Tana share hawayenta ta ce"na yi alkawari zan faɗa maka komai amma dan Allah karka cutar da Umaisha da Iklas".
"Karki damu my Sabriyah, muddin kika min yanda na ce nima na miki alkawari bazan musu komai ba".

Kashe waya ta yi dan ta rasa takaicin waye zataji na Fu'ad din ne ko kuma na kanta da ta kasance wawiya ta yarda dashi.

Komawa falo ta yi ta zauna,tana jin duk tattaunawar da ake yi,amma duk wanda ya mayar da hankalinsa akan ta ze gane ba'a cikin nutsuwarta ta ke ba.

Kiraye_kirayen sallah asuba ne yasa su tashi suka je suka gabatar da sallah.

Bayan sun dawo daga masallaci ne, sojoji da yan sanda suka kimtsa kansu domin tafiya hatta su ACP Jawan da Sudais sun shirya.

Fitowa LTG ya yi cikin shirinsa na uniform din sojoji fuskar nan dama ba annuri ne akai ba yanzu yafi ko yaushe ban tsoro.

Addu'a sosai su Ammi suka musu.na samun nasara.

Kirane ya shigo wayar Sabriyah ta inda Allah ya taimaketa wayar na vibration.
Fakan idon su ta yi ta shiga kitchen da babu kowa a ciki daga waya kafin ya ce komai ta sanar dashi shirin da sukayi sannan ta kashe wayar ta,ko muryarsa bata son ji.

Kira ne ya shigo wayar LTG ɗagawa ya yi yasa akunne,bayan ya gama saurarar Abinda aka faɗa ne ya kashe wayar idonsa yana ƙara rinewa yana ja.

Kallonsu ya yi."kowa ya samu guri ya zauna ni kadai zan tafi".

A rude suka kalli shi"meyasa haka LTG?".
Sudais ya tambaye shi.

"Dan Allah karku hana ni,ya riga da yaisamu labarin shirin da ku ka yi,yanzu haka ya kashe yarinya ɗaya, bana son a sa'ke kashe wata,kar ku hanani,kuma kar wanda ya biyo ni".yana gama fadar haka ya fice a falon dan bayason ganin fuskar Ammin sa dake kuka".

Suna kiran sunanshi amma ko juyawa be yi ba,ya shiga motar ya fisgeshi yabar gidan.

Fashewa ta yi da kuka musamman idan ta tuna cewa Fu'ad kashe LTG ze yi kuma ita ce ta bada,taimakonta.da gudu ta bar falon tana kuka, direct part din LTG ta nufa ta tsaya tana kuka.

Ji ta yi tana sha'awar duba part din nashi.
Bedroom dinsa ta shiga wannan hoton da ranar ya hanata gani shi ta dauka tana kallo,zaro manyan idanunta ta yi kamar zasu faɗo ƙasa ganin wacce take jikin hoton.
Chapter 59 · 0% Book details