Sashe 32
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shafa bayanta ya yi be ce komai ba,kaff gidan kowa yana son yarinyar saboda ko kadan bata da damuwa, she's very unique,kusan ma za'a iya cewa ita ce logon su,weak point din su,ji sukeyi da ita kamar yanda ake ji da kwai.wannan dalilin yasa kowa na gidan yake son ta hatta shi kanshi LTG yana ji da ita.
Kowa dake falon seda suka mishi sannu da zuwa duk da bawani amsawa ya keyi ba.
A bangaren Sabriyah kuwa tunda LTG ya sauka take kallonsa musamman damtsen hannunsa da kuma farfadar kirjinsa, tunda take bata taɓa ganin mutum me irin zubin halittar jikinsa ba,hakan yasa ya koma tv awajanta.can kuma ta tuna da sace ta da ya yi, ga kuma mutanen gidan sun wani tsaya se wani sannu da zuwa suke mishi sun manta da sabgarta hakan ne yasa,ta matso kusa da shi.
Ta ce "wato raunin da ka ji mini a kasuwa be isheka shine ka sato ni,to baka isa ba kawai in kanason kwanciyar hankali da kai da mutanen gidan nan ka maidani gidanmu!"ta karasa maganar tana wani girgiza kai kamar dukan shi zata iya yi ,ga ta yar karama a gabanshi se ta daga kanta tukun take kallonsa duk da itama tana da tsayi dede gwargwado.
Ko kallon in da take tsaye be yi ba bare ta sa ran ze amsa mata,se ma juyawan da ya yi ze koma part din shi.da sauri ta bisa a baya tana"kazo ka mayar dani dan Allah,akwai yar uwa ta da aka sace zan nemo".
Su de su Ammi da kallo kawai suke binsu,domin kuwa sun rasa dalilin da yasa LTG ya daukota ya kawota gidan.
Haurawa ya yi ko juyowa be yi ba,ganin ya haura ne yasa ya tsuguna agun ta fashe da wani sabon kuka, babban damuwarta ita ce Asmita,bata san wani hali take ciki ba, batasan su waye suka sace ta ba.burinta kawai taga ta samo Asmita,gaba daya abubuwa sun haɗe mata kai ta rasa da wanne zata fara guda daya.
Ganin ta tsuguna tana kuka ne a matattakalar benen yasa Ammi ta haura ta ɗaukota suka dawo kasa,zaunar da ita ta yi, akan kujera.hajiya babba ce ta matso ta zauna kusa da Sabriyah ta ce "yarinya ya sunanki!?",se da ta goge hawayen fuskarta tukun ta iya cewa" sunana Sabriyah".
"Meyasa kike kuka kuma meye ya haɗa ki da Tajuddeen!?", Hajiya babba ta sake je fo mata tambayar,tsaki Ammuh ta yi ta ce "gaskiya mutanen gidan nan akwai ku da son yin gwaninta!,karuwar ce ku ka tsaya kuna wani lallabata!?"ta faɗa tana harare_harare kafin ta sa'ke jan wani tsakin ta wuce part dinta,ummah part dinta itama ta wuce dama ita tunda ta fito batace komai ba.sude su Sudais da su Zoya duk suna tsaye a falon sun zubawa Sabriyah ido,gani sukayi tana kusan yanayi dasu,ga kuma kyawunta me jan hankali kukan da takeyi ma ƙara mata kyau ya yi, girgiza kai Hajiya babba ta yi kawai sannan ta ce "kar abinda ta faɗa ya dameki faɗa mini inajinki",kwashe gashinta da ya zuba ta gefen wuyanta tayi ta maida shi baya kafin ta ce"ah ah maganar ta be ɓata mini rai ba,kuma ai gaskiya ta faɗa!,na haɗu da wannan mugun ne a kasuwa ban taba ganinsa ba amma ranar da muka haɗu dan kawai munci karo da juna shine ya yi wurgi da ni,na faɗi se da naji ciwo a hannuna,ranar da wasu wa'yanda bamu san ko su waye ba suka sace mini yar uwa ta,aranar shima ya sace ni ya kawo ni nan."jinjina kai sukayi bayan sun gama jin abinda ta faɗi su de har yanzu basu ga wani dalilin da har ze sa, LTG ya sace yar mutane ba,abin ya daure musu kai,duk shuru sukayi basu ce komai ba, kowa da abinda yake saƙawa a ransa,ɗago kai Sabriyah ta yi ta kalli Ammi ta ce"ki yiwa wannan mugun magana ya mayar dani inda ya dauko ni,in je in nemo yar uwa ta".murmushi Ammi ta yi jin yanda Sabriyah ta ke kiran LTG da mugu duk da har ranta bataji dadin kalmar ba amma yanda Sabriyah ta yi mata magana cikin shagwaba ya bata dariya hakan yasa ta ce"shikenan ki kwantar da hankalinki zanyi mishi magana kuma ze mayar dake nice mahaifiyar sa,in Allah ya yarda za ki koma garin ku."gyada kai Sabriyah ta yi,kallon su Umaisha Ammi ta yi ta ce Umaisha zo ki dauketa kuje part dinku ku zauna tare.
"Okay Ammi"umaisha ta faɗa tana yiwa Sabriyah murmushi,yatsina fuska Zoya ta yi,cikin mamaki ta ce"like serious Ammi!?, gaskiya wannan karuwar bazata je mana part din mu ba,najasa ce f......"wani irin tsawa Sudais ya daka mata wanda ya hanata karasa maganar da zata faɗa."will you be quiet,you idiot!in na sa'ke jin muryarki se na ci ubanki a gidan nan mahaukaci kawai."nan take ta nutsu ta sun kuyar da kanta dan tasan karamin aikin Sudais ne yanzu yamata ɗan banzan duka.
Hajiya babba ta ce "Zoya wannan banzar halin naki ki gaggauta barinsa nade gaya miki yarinya kenan se bakin hali"haka Hajiya babba ta dinga surfa mata masifa.duk cikinsu babu wanda ya ji dadin maganar da Zoya ta faɗa,saboda duk yanda mutum yake baze ji dadi ba in aka kirasa da wannan abun.
Rike hannun Sabriyah Umaisha ta yi ta ce "sis ta shi muje part din mu"fisge hannunta Sabriyah ta yi,ta ce "babu inda zani fa,bazan taɓa motsa wa anan ba se wancan mugun ya fito ya maida ni"ikon Allah yau ake yin ta,yau Allah ya hadasu da me taurin kai da naci,ga ta daga ido de ba za'ayi tunanin za ta yi taurin kai ba, se de duk wanda ya mata kallo ɗaya yasan za ta yi masifa da tsiwa da kuma rashin kunya amma alamar taurin kai be nuna a tattare da ita ba.
Kallon Zoya Sabriyah ta yi ta galla mata harara ta ce "ke kuma dakikiyar banza da kike cewa karuwa bazata shiga muku waje ba ,to ni me ma ze kaini ko an gaya miki ina son in ƙara ko da second daya a gidan nan ne!?,ki shiga taitayinki nafiki hauka tam.karki ga ke yar masu kuɗi ce, ki ce zakimin tijara.sauya miki kamanni zanyi babu abinda yashamin kai".yanda Sabriyah take magana da masifa_masifa kamar zata je ta da ki Zoya ne ya bawa Sahil,Salim,Jawan dariya ganin sun samu wata comedian a gida.
"Yi hakuri Sabriyah,tashi ki bi umaisha kuje ku ciki, lokacin breakfast ma ya wuce kuyi sauri, Umaisha ki nuna mata komai tayi wanka,ki bata kaya tasa"Hajiya babba ta yi magana tana kallon umaisha sannan ta kalli kayan dake jikin Sabriyah ta girgiza kai aranta tana tambayar kanta ko yarinyar nan musulma ce.domin kuwa shigar jikinta kwata_kwata beyi tsari ba.
Rike hannun Sabriyah Umaisha ta sakeyi a karo na biyu,bin bayanta Sabriyah ta yi badan taso ba,bataso ta tsaya musu da su Hajiya babba da Ammi ne. saboda duk fitsaranta bazata iya musu ba.har sun haura upstairs Ammi ta kira sunan Umaisha juyawa ta yi,Ammi ta ce "Umaisha give a decent dress please" "okay" sannan sukaci gaba da tafiya,Zoya de tunda Sabriyah ta zazzage mata salon nata rashin kunyar da tsiwa ta yi shuru bakinta ya mutu murus,part din Ummah ta yi fuuuu,kamar zata fire sama.bin bayanta sukayi da kallo,Jawan cikin daga murya da tsokana ya ce"gaba ma da gabanta aljani ya taka wuta,kin haɗu da wacce ta fiki rashin ji ai"ko waigowa Zoya bata yi ba se ma kara saurin da ta yi,dariya duk sukayi, Parsa ta ce "Rameesa, Sabriyah kyakkyawa ce ta burgeni sosai "dariya Rameesa da iklas sukayi.iklas ta ce "honestly she's very gorgeous" "to yanzu de kuzo muje muyi wanka se mu fito a yi breakfast"cewar Rameesa da ta fara tafiya bin bayanta sukayi su dema.
Zama Saghar da Jawan sukayi kasa_kasa da murya Saghar ya ce "amma Jawan kai a naka tunanin me zesa LTG guda ya sato mace!?",shima Jawan kasa da murya ya yi,ya ce"that's what am still wondering!me ze sa ya Taj ya sato wannan zankaɗeɗiyar budurwan batare da dalili ba!?".haka suka dinga magana kamar wasu munafukai,babban abinda basu sani ba shine su Sudais Sahil, Salim, Ammi,Hajiya babba duk sunji abinda suka faɗa.tafa hannu Hajiya babba ta yi "la'ilahaillahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama,yanzu dama maganar da ake faɗa a gari cewa gulma ya tashi daga kan mata ya koma kan maza ashe da gaske ne!ikon Allah wato Saghar da Jawan kude bazaku dena wannan iya shegen naku ba.tabb dijam ahhh lallai lamarin ku ya girmama,ku de bari Tajuddeen ya ji ku". tunda Hajiya babba ta fara magana suke dariya har su masu gulman saboda su kwata_kwata basu yi tunanin ana jinsu ba.tsagaitawa da dariyar Salim ya yi ya ce"ai Hajiya babba kaff gidan nan babu irin Saghar da Jawan a wajen fannin sa ido da gulma ne"tabe baki Hajiya babba ta yi sannan ta ce"yooo ai naga alama,bari ma in shige ciki."haurawa part dinta ta yi tana tafiya tana tafa hannu irin abin ya bata mamaki.(hhhhhhh, Hajiya babba kema akwai abin dariya ba laifi,to ai gulma ya daɗe da koma kan maza mutanen mu).
Ammi de se murmushi take musu maida hankali ta yi kan Sudais ta ce "rabu da wa'yannan naga yau su basu da niyar yin breakfast din ɓalle suje wajen aiki".kallonta sukayi atare su biyun suka haɗa baki wajan faɗar "Ammi abin kuma wariyar launin fata ne!?"Saghar da Jawan suka faɗa,marairace fuska twins Sahil, Salim sukayi sukace"ayyah Ammi muma fa yan gaban goshin ki ne,shine za ki cewa Sudais shi kadai ya ke da niyar zuwa gun aiki!", kwaikwayon yanda sukayi maganar Sudais ya yi yana"yen!yen!yen!ƙatti da ku agaban ƙannenku kuna wani shiririta shame on you guys" Ammi de ce musu ta yi"ku de ba'a iya muku,se anjumanku mu haɗu a dinning kawai".ta faɗa tana barin falon.
Duk watsewa suka yi a falon kowa yaje dan ya shirya .