Sashe 27
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana kwance tana tunanin ina kuma Asmita ta tafi da haryanzu bata dawo ta ji ya bude kofar toilet din ya fito ya canza kayan jikinshi da ya jika zuwa brown color din jallabiya kamar ba shine ya gama hauka acikin toilet ba se sakar mata murmushi ya keyi itama ta mayar mishi da martani ta ce "Fu'ad nikam bari in duba my Jerry a waje har yanzu bata dawo ba!" gaban mirror ya je ya tsaya ya ce "karki damu yanzu zata zo ba ta yi nisa ba"suna cikin maganar ta ta shigo,a rude jikinta har rawa yakeyi tazo ta rungume Sabriyah tana sauke ajiyar zuciya,ganin yanda ta shigo ne bata cikin nutsuwarta yasa Sabriyah ta ce "my Jerry meyafaru na ganki haka!?"numfashinta na fita dakyar ta iya cewa "my Tommmmmm,ina wannan din nannnnnn!?"magana take son faɗa mata amma tashin hankali da kiɗimewa ya hanata se jan maganar takeyi numfashinta na kokarin yanke.
Tunda Sabriyah taga haka tasan tofa abinda Asmita ta gani babban abu ne hakan yasa tasake rungumeta tana shafa bayanta duk dan tasamu nutsuwa.
Duk abinda suke yi yana kallonsu ta cikin mirror be ko waigo ba balle yace musu komai.
Dakyar nutsuwar Asmita ya dawo ta tashi ajikin Sabriyah ta ce "my Tom yau naga abinda ya tayar mini da hankali,ina wannan Umar din nan da suka je afafa shi da wannan!?"ta faɗa tana nuna Fu'ad dake zaune a gaban mirror.gyada mata kai Sabriyah ta yi alamar ta ci gaba da maganar.
Ta ce "yanzu aka fito da gawar shi acikin dustbin din hotel din anyi mishi kisan gilla seda aka sassara shi sannan aka jefa shi cikin dustbin."zaro ido waje Sabriyah ta yi tana me tuna lokacin da aka fito da ita daga dakin horo tare ta gansu shida Fu'ad a zaune.
"Allah sarki bawan Allah ko waye ya mishi wannan kisan gillan oho, gaskiya yanzu duniya abin tsoro ne"ta cikin mudubi yake kallonsu yana sakin murmushin da shi kadai yasan ma'anarta a ranshi ya ce "shi ya jawa kanshi mutuwa,babu wanda yake Sanin abu akaina kuma in barshi yaci gaba da rayuwa"yana maganar yana murmushi tsinkayar muryar Sabriyah ya yi tana cewa "Fu'ad Allah sarki wanda kukazo afafa dashi yaron hotel din nan de an kashe shi."nan take ya sauya fuska zuwa na mutanen kirki me cike da jimami ya juyo da sauri ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun Umar din!?"ya faɗa da alamun tashin hankali a tattare dashi ya mike da sauri yabar dakin jikinshi na rawa.
Bin bayanshi sukayi da kallo cike da jimami Asmita ta ce "Allah sarki ji yanda hankalin Fu'ad ya tashi" Sabriyah ta ce "eh ai dole hankalinshi ya tashi,kinsan Umar din yaron shine!shi yake mishi hidima a hotel din nan" haka suka dinga jimanta mutuwar Umar din.
Ba'a yi wani dogon bincike dangane da mutuwar Umar ba saboda Lagos oriental hotel,babban hotel ne a Lagos yana daya daga cikin hotel din da ake ji dashi.idan aka fara bincike kuma ze jawo hankalin al'umma hakan yasa aka kashe maganar kawai dama bashi da wani gata yaron.
Bayan sati daya shakuwa sosai ya shiga tsakanin Fu'ad da Sabriyah and Asmita saboda yanda yake kulawa dasu komai yi musu ya keyi kamar wani ɗan uwansu,ya hana su komawa afafa ya ce su bari in ya tashi tafiya shi da kanshi ze kai su, a yayinda yake kwana a falo Sabriyah da Asmita kuma suna kwana a bedroom,har zuwa wannan lokacin be nemi Sabriyah da wata mu'amala ta banza ba, saboda kamar yadda ya faɗa mata son tsakani da Allah yake mata.
Asmita ta yi wani saurayi acikin hotel din ya dawo daga Indonesiya ya sauka a hotel din a ranar ya hadu da Asmita sosai suke soyayya har waya ya siya ya bata,hakan yasa Fu'ad ma ya siyawa Sabriyah waya Samsung Galaxy S20.
Sabriyah da Fu'ad se Asmita ne zaune a falon hotel din Sabriyah ta ce "nikam Fu'ad ba kace nan da sati daya zaka tafi bane!?,ni Wallahi na gaji da zama a hotel din nan kawani killace mutane haba."dariya shi da Asmita sukayi ya ce"kai Sabriyah kina da matsala yanzu ke hakan be fi miki ba?,akan gantalin da kukeyi afafa!?"harara ta watsa mishi cikin ɓacin rai ta ce "ba gantali mukeyi ba,a haka muka taso kuma ni bani da wajan da yafi mini wannan gidan"tana gama maganar tabar falon domin maganar da Fu'ad ya faɗa ya bata mata rai,kallon juna Asmita da Fu'ad suka yi cike da mamaki domin sude acikin wannan maganar ba su ga abin ɓacin rai ba,bin bayan sukayi domin ba ta hakuri.
THE UNITED STATE OF AMERICA
MILITARY HEADQUARTER.
Manya_manyan sojoji ne masu muƙami a zaune acikin wani keɓebben dakin bincike su biyar kuma dukkanninsu turawa ne daga General, brigadier general,major general, surgeon general, colonel general duk suna zaune da alama akwai wanda suke jira domin su ci gaba da tattaunawar da zasu yi ɗago kai general ya yi cikin harshen turanci ya ce"anya lieutenant general ze samu zuwa kuwa!?"colonel general yana duba wasu files da sukayi ƙura ya ce "tabbas lieutenant general ze zo saboda,burinshi shine criminals su shiga hannunshi su sha azaba,ba ya wasa da abinda ya kasan ce me mahimmanci,kar ku manta shifa sojan ƙasa da ƙasa ne dole ne ma yazo saboda rayuwanka al'ummar ko wata ƙasa yanada alhakin kare su"jinjina kai sauran sojojin sukayi.
bude kofa wata kyakkyawar baturiya ta yi jikinta sanye da kakin uniform din sojaji ga bindiga a gefen kugunta, tana shigowa ta ƙame sannan ta sara musu.
shigowa dakin binciken ya yi cike da jarumta irin na manya_manyan sojoji,yana sanye da army trouser wato wandon sojoji,yayinda yake sanye da riga armless na sojaji yaɗan matse shi,ya nada wata irin sura me matukar razanarwa, rikitarwa da kuma jan hankali haɗe da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne me farfadar kirji a bude yake,ga six packs din shi baro_baro ya cika vest din kana ganin zanen kirjinsa ya fito a ta cikin vest din da ya sa'ka,idan ka kalli damtsen hannunshi kuwa se ka tsorata,kana gani kasan yanada matukar karfin gaske kamar dan wrestling haka surarsa take mutum ne me ji da karfi.
Idan muka je wajan cikin sa kuwa a shafe yake babu alamar yana cin abinci saboda yanda wajen ya yi flat.
Launin fatarsa kuwa fari ne sol irin wannan farin larabawa saboda shidin jinin shuwa Arab ne bugu da ƙari kakar mahaifiyarsa ta kasance baturiya.
A wajan kyau kuwa sede muce tubarakallah Masha Allah domin Allah ya yi masa baiwar kyau me matukar razanarwa da kuma kayatarwa,ko na miji da suke jinsi daya se ya zuzutawa kyawunsa ɓalle mace. bugu da ƙari dogo ne ga murɗaɗɗen,ƙarfaffa duk abinda mace za ta bukata a jikin namiji Allah ya wadatasa da shi.sumar kansa kuwa yana ɗauke da wata irin aski me suna faded hair cut gefe da gefen kan an rage wannan ƙayitatciyar sumar, se ya zamana tsakiyar kan ne ke dauke da suma me matuƙar yawa da tafiya da hankali, sumar baƙine sosai yana kwance se sheki da daukan ido da yake yi,irin gashin larabawa. askin kanshi ma kadai abin kallo ne,hatta gaban goshinsa akwai suma a kwance,gashin jagirarsa kuwa tamkar an zanasa yana cike har suna kokarin hadewa waje daya,idan muka koma kan idanunsa kuwa sun kasance manya masu daukan hankali yana dauke da dogayen eyelashes, Allah ya ba shi kyawawan idanu masu girma da ga su so sexy da kuma tsoratarwa,farare tass da su me dauke da kwayar ido golding color masu shining kamar an kunna haske da kuma daukan ido.yana da dogon hanci me kyau da tsayi kamar pencil ga red libs din shi da suka kasance dan karami kamar ya shafa jan baki.fuskar shi na kewaye da wani irin kwantatciyar saje, da ya yi wa fuskarsa ado.
Hannunsa na hagu na sanye da wrist watch kirar Breguet wanda kudinsa yakai kimanin N=950000 dubu ɗari tara da hamsin.yayinda hannun dama shi ke dauke da wani bangule fashion designer ne silver color ya yi masa kyau sosai.