← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 60

Sashe 12

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ammi,Hajiya babba,Anty amarya duk suna zaune a main part suna hira gwanin burgewa,anty amarya ta warware taji sauki dama damuwar da tasawa ranta ne yake damunta haryaso ya kwantar da ita . Shigowa falon Hajiya hurairah ta yi bakinta dauke da sallama atare suka kai idonsu kanta sannan suka amsa zama ta yi akan daya daga cikin kujerun aka ci gaba da hiran da ita, daga zaran sun haɗa ido da anty amarya se ta sake mata wani munafukin murmushi da ita kadai tasan ma'anarshi ranta fes , anty amarya ta rasa gane wannan murmushin da Hajiya hurairah takeyi ma ta na menene hakan yasa ta tsame bakinta daga hiransu ta yi shuru kamar bata wajan saboda dama bawani yi sukeyi da Hajiya hurairah ba musamman da taga sun shaƙu sosai ita da Hajiya khareema.

Kallonta Ammi ta yi kawai ta girgiza kai tasan sarai saboda Hajiya hurairah anty amarya ta yi shuru ,

Hajiya Babba ta ce" Abida ya kikayi shuru kuma?"yaƙe anty amarya ta yi ta ce " ah ah bakomai Hajiya babba" bata yarda da abinda ta faɗa tasan dalilin Hajiya hurairah ta yi wannan shurun.

" yauwa dazun Abbie dinsu naji yana faɗin Asrah itama gobe za'a mata registration a makarantar su iklas tunda yanzu kundawo Nigeria da zama " anty amarya na kokarin bawa Hajiya babba amsa karaf Hajiya hurairah ta riga ta cikin suɓutar baki da ita kanta batayi tsammanin bakinta ze furta haka ba ta ce " ai karma ku wahalar da kanku kan makarantar Asrah bayida amfani" se da ta tuna abinda ta yi kuma ta datse harshen ta cike da da nasanin abinda ta faɗa, duk zuba mata ido sukayi jin maganar da ta yi wai saka Asrah a makarantar bayida amfani hakan yasa suke kallonta cike da son jin ƙarin bayanin dalilin da yasa ta fadi haka,me take nufi kenan.

Yar dariyar borin kunya ta yi saboda batason suyi zargin wani abu dangane da abinda ta faɗa yasa ta ce" eh mana nide aganina bayi da amfani su Abbie ko Abdulhameed su kaita tunda kinga duk suna da wajan zuwa ni zan kaita da kaina shisa nace babu amfani " jinta kawai sukayi , tsaki anty amarya ta yi ciki_ciki ta ce " bana bukata ko ni zan kai ƴata makaranta base kin kaita ba " ta yi maganar tana gyara dankwalin kanta sannan tabar part din fuuuuu kamar zata tashi sama.
kunya ne sosai yarufe Hajiya hurairah saboda yanda anty amarya ta sace mata guiwa murmushi ta yi ta ce" Allah sarki Abida kamar ranta yabaci , bari zanje in bata hakuri " kallon juna Ammi da Hajiya babba sukayi suka tabe baki , Ammi ta ce" karki damu ba se kinje ba zan mata magana " haka ta mike ta basu guri.
" Allah yakyauta to" cewar Hajiya babba Ammi ta ce" ameen ameen".

5:00pm na yamma dukkansu amma fa babu Tajuddeen aciki , sun hallara a spot area Babban wajen dake cikin gidan wanda yafi girman part biyu ko uku , duk wasu kayan nau'in game babu wanda babu awajen ko ina da shi harda bangaren gym , su Jawan suna buga ball , manyan cikinsu su Abbas kuma basa ma gida sunje gidan ya'yunsu da yau wata biyu kenan da yin aurensu Sakeena da Sameera sun kai musu ziyara gidan Sakeena suka fara zuwa daga nan suka wuce gidan Sameera.
Umaisha, Asrah, Rameesa,Parsa,Zoya, Iklas boji_boji sukeyi se dariya da tsalle_tsalle sukeyi cike da farin ciki , Rameesa da idonta ke adaure da ƙyelle tanata lalubawa acikin filin ko zata gansu amma ta ka sa kama ko mutum daya dakyar tasamu ta cafke Asrah, Parsa ce ta kulle mata idanunta su kuma suka boye haka suka ta wasansu har kusan mangrib suka koma ciki saboda suyi sallah .

DAMATURU

malam Mamman ne ya shigo gidanshi bakinshi a washe kamar ba shi ba hannunsa na rike da ledoji niƙi_niƙi ,abakin murhu yasamu Maryam tana durƙushe se hura wuta takeyi tun dazun amma yaƙi kamawa batamasan ya shigo ba , gyaran murya ya yi ,agigice ta juyo ta kalleshi. mamakine ya bayyana ƙarara akan fuskarta da ya haɗa zufa ga idonta ya yi ja saboda hayakin murhun da take kunnawa. sakaka Maryam ta yi da baki tana kallon fuskar malam Mamman da har izuwa lokacin bakin shi yaƙi rufuwa se murmushi yake . Mikewa tsaye ta yi ta gyara kodedden zaninta da take daure dashi miko mata ledar ya yi yana faɗin" Maryam matar Mamman kinsan yanda nake sonki kawai de saboda wannan yarinyar ce yasa nake jin haushinki amma yanzu dukkan ku inasonku sosai wallahi" ita de ta kasa janye idonta akanshi tsaban ruwan mamakin da yabata domin duk abinda yake faɗa ita de bawai ta gasgata bane .
lura da ya yi taƙi sakin jiki dashi ne yasa ya ajiye ledojin hannunshi,yaje can bakin dakinshi ya dauko tabarma yazo ya shimfida , ya jawo hannunta ya zaunar da ita ,buɗe manyan ledojin ya yi yafito da dangwala_dangwalan kaji da suka sha ga'shi se maiƙo sukeyi ga yajin kajin daure agefe , kamshim namar kazar ne ya da ki hancin Maryam, hadiye wani yawu ta yi da se da maƙoshinta ya ce "kwatt" , nan take yawunta ya tsinke. Maryam baiwar Allah rabonta da taga irin wannan tun lokacin da suke shan soyayya da malam Mamman kafin ta haifi Asmita.
Duk da yanda ranta yabiya da namar kazar amma taƙi saka hannunta aciki , malam Mamman ya ce" Maryamata kici mana saboda ke da yarmu Asmita na siyo wa'yannan kayan daɗin amma kin ƙi ci.
Sa ke kallon shi ta yi murya asanyaye ta ce " dagaske Malam ka karbi Asmita amatsayin yarka ?" Jiki na rawa ya ce " kwarai ma kuwa nakarbeta kuma nagane kuskurena! Tunda na dawo ma banganta ba ina take " ya yi magana yana kalle_kalle agidan kwala kiranta ya yi" yar baba Asmita kizoki "

Fitowa Asmita ta yi tana rakube_rakube saboda tsananin tsoronshi da takeji mikewa ya yi ya daukota ya zaunar da ita akan tabarman.
Daga Maryam har Asmita jin lamarin sukayi bankwarakwai , cinyar kaza ya dauka ya bawa Asmita " maza ci yata , ci nama" da sauri Asmita ta karba tafara ci ,haka suka za ge suka ci kaji dakuma su kayan kwalba da malam Mamman yakawo ranar de sunci dadi sosai, da dare ma yasake kawo musu kayan daɗin suka ci suka kwanta , Maryam tana ta murna mijinta yadawo kan hanya.

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

🌹🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹🌹

Page 09

*_ story $ written _*

By

* _ MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

Page 09

Washe gari

As usual kamar yanda suka saba duk sun shirya cikin shiga ta uniform dinsu da ya kasance fari da maron , riga da skirt ɗan guntu se legis fari da suke sanye dashi a ta ciki, se fararen sandals da safa a ƙafafunsu ga baby hijab dinsu suna sanye dashi sunyi kyau sosai sede fah yanda suke tafiya matan su biyar yau ansamu ƙarin mutum daya wato Asrah sun zama su shida yanzu , anyi mata komai da komai zata fara zuwa yau , se murna takeyi itama yau zata cigaba da zuwa makaranta , rabonta da makaranta tunda suka baro California shisa she's very excited yau , duk sun gama breakfast , su sahil suna waje sunyi gaba. Abbu ne yafito hannunshi riƙe da car key ya ce" kuzo in kaiku " dukkansu ihu suka yi suna " yeeeeh yau Abbu ne ze kaimu school" dariya Abbu ya yi ya girgiza kai ya yi gaba suka biyo shi a baya.
Dropping dinsu ya yi acikin school din yana kallonsu seda ya tabbatar sun shiga class sannan ya tafi .
Shiga sukayi class din suka samu seniors din su sun shigo yan SS2 ,kallonsu sukayi sukaga babu yayyunsu maza aciki su Saghar,jawan a SS1 suke. Sudais da Salim,Sahil, sune suke aji daya da su Tajuddeen wato SS2 sede shi ya rubuta paper tare da yan SS3 shisa ya dena zuwa makarantar.

Wuce seniors din sukayi suna gaishesu cikin harshen turanci. Asrah dake bayansu tazo ta wuce bata ko kallesu ba daya daga cikinsu ne ya ce " hey you come here " juyowa ta yi ta kafesu da wa'yannan mayun oiling eyes dinta tana kwabe fuska , sosai Asrah ta tafi da imanin Fu'ad Abubakar Daula ji ya yi be taba kallon yarinya me irin kyau din Asrah ba hakan yasa ya ji yana sonta , magana friends dinshi suke mishi amma shi gaba daya akalar hankalinshi yanaga Asrah.
Matsowa kusa da ita ya yi ya ce " what is your name?" " am Asrah Abdulhameed Bishara by name "ta bashi amsa murmushi ya sa'ke jin yar gidansu Tajuddeen ce ya ce" good go and sit down" wucewa ta yi taje ta zauna a kusa da Zoya .
Chapter 12 · 0% Book details