← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 60

Sashe 25

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk dramar da akeyi Rameesa na daga saman upstairs tana kallon su tunda ga lokacin da Zoya da Umaisha suka fara faɗa har zuwa lokacin da suke guje_guje da kuma shigowar Sudais din.banda dariyar mugunta babu abinda takeyi tana"Umaisha Wallahi in bakiyi wasa ba wata rana sede kiji ya Sudais yasa almakashi ya gimtse miki wannan gashin naki"ita kadai take magana tana dariya.

"Ke kuma ke dawa kike wannan dariyar kamar wata kun kuncecciya!?"cewar Ammi da fitowar ta kenan daga part din Hajiya babba ta hangi Rameesa se dariya takeyi rungume Ammi Rameesa ta yi kafin ta tsagaita da dariyar nata ta ce"Ammi Wallahi su Umaisha basu jin magana wata rana se sun wayi gari sunga anyi musu malu,sun san sarai su ya Sudais,ya saghar,ya Jawan,ya Salim,ya Sahil, se sun musu magana akan saka hula ko dankwali amma su basu ji"dariya Ammi ta yi, ta mata marin wasa ta ce"ja'ira ke dinma yaushe kika fara saka dankwalin ina se da Jawan ya dake ki kafin kikayi hankali?"turo baƙi Rameesa ta yi"ni Ammi dena tuna min."dariya sosai Ammi ta yi kafin ta ce "nikam ɗaga ni,in yi gaba"dagata tayi tana dariya ta yi part din su da gudu.girgiza kai Ammi ta yi aranta ta ce "yaran nan kude bazaku taɓa girma ba".

Duk suna zaune a part din su, Umaisha na zaune har lokacin hannunta na bisa kanta tana shafawa,Zoya ta ce "Allah ya taimakeni da ya Sudais ya ganni Wallahi nasan yau jikina se ya faɗamin saboda yau da safe kafin ya fita aiki seda ya mini rankwashi" "ke nifa tunda ya Jawan ya taba lafiyar jikina nadena yawo ba hula,ku ai bakwajin magana kun san sun tsani suga mutum ba hula akanshi"cewar Rameesa dake zaune kusa da Parsa,gyara zama Parsa ta yi ta ce "bama maganar basa so ba babu kyau ne yawo gashi awaje kuma duk mun sani yakamata mu gyara saboda shedanu"haka suka dinga hiransu Umaisha de batace musu komai ba,dan har lokacin kan nata na mata zugi.

"Anty amaryanmu me kike dafa mana ne naji irin wannan kamshi me dadi haka!?"juyowa ta yi ta ɗan yi murmushi ta ce"abincin dare ne Saghar !me kake so a yi maka?"ta yi maganar tana kallon shi.
"Ni banason komai na fi son abu liquid haka ko romon farfesu kawai amma kar asamin nama kawai romon nakeso."

Rike baƙi Anty amarya ta yi ta ce "ku fa likitocin nan kunfi kowa kinibibi,da kai da uncle din ku kuna bani mamaki wai kuce ku bazakuci abinci da daddare ba sede kawai abu ruwa_ruwa.muda mukeci de ga shi bawai lafiya kuka fi mu ba."dariya Saghar ya yi "Anty amarya bazaku gane bane,da kun san illan cin abinci me nauyi da daddare tofa da kun dena domin ze sa muku upset stomach" "dallah yi mini shuru jeka zan biyoka da romon"sa kai ya yi ya fice yana dariya yabar Anty amarya ma tana darawa.

Bayan sun yi sallar isha kowa yadawo sun hadu a dinning table banda Abbu da Abbie da ba sa ƙasan.

Serving din kowa abincin da ranshi yake so fatime da kaltume suka yi,a tsanake suke cin abincin Ummah ta kalli Saghar ta ce "yau da ka dawo me ya hanaka zuwa ka gaishe ni Saghar?!" Ajiye spoon din hannunshi ya yi ya zuba mata ido domin ta taɓo mishi inda yake mai kaikayi Ammi ce ta daura hannunta akan nashi alamar kar ya ce komai,amma ya gagara shuru"kin zauna agidan ne ɓalle mu ganki mu gaisheki!? kullum kina hanya baƙi da lokacin Abbu ɓalle mu yaranki to aina nasan zan sameki har in ce zan gaida ke ummah!?" "Saghar ya isa haka"cewar Hajiya babba,spoon din ya dauka ya cigaba da shan romonshi ,mikewa ummah ta yi tabar dinning din.

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

Page 15

*_Story & written_*

By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

Page 15

Haka suka gama cin abinci kowa ka kalla zakaga fuskar shi da alamar damuwa, uncle Hameed ne ya kalli Saghar da Sudais ya ce"ina son magana daku biyun"mikewa su Zoya sukayi suka bar dinning din Jawan da Sahil,Salim suma suka tashi sukayi.saura daga uncle Hameed din se Hajiya babba, Ammi,Anty amarya se su wa'yanda akace su tsayan wato Saghar da Sudais.

Maida hankalinshi uncle Hameed ya yi kansu sannan ya fara magana"meyasa kuke haka Saghar, yanzu ga shi tabar dinning din batare da ta kammala cin abinci ba!, ka bata mata rai. ba ko da yaushe zaku dinga titsiyeta akan yawan fitan da takeyi ba kamata ya yi kuje ku sameta cikin lallama da kuma daɗin baƙi ku nuna mata yawan fitan da takeyin nan ba kwa so tun kuna yara ake abu daya ga shi har kun girma kun mallaki hankalin kanku you're all matured enough.kai doctor ne shi kuma Sudais custom,babu wanda yakamata yasan matsalar mahaifiyar ku sama da ku din nan kunga de Zoya da Parsa bawani girma sukayi ba,ni se nake gani kamar akwai wani abinda yake damunta wanda bataso kowa ya sani tabbas tana cikin damuwa,kallon mintuna biyu nayi mata na nazarci hakan a tattare da ita,so please take good care of your mother mahaƙurci,mawadaci".

Sun matuƙar gamsu da maganar uncle Hameed dama su abinda yake bata musu rai shine yawan fitan da takeyin ne,kuma har yau babu wanda ya san ina take zuwa.
Sudais ya ce"in sha Allah zamuyi yanda kace uncle Hameed duk da bamu san menene matsalar ba,ni bawai yini nakeyi a gida ba in na fita 10:00am na safe bana dawuwa se yamma kuma duk da hakan bazan samu ummah a gida ba abin na sosa mini rai matuka."

Haka Hajiya babba da su Ammi suka sake musu nasiha akan kulawa da mahaifiya,kafin daga bisani suka watse sudais ne kaɗai ya yi saura akan dinning din yana zaune yana danna wayarsa, buɗe sakonnin da suke shigowa ya keyi.kusan awan shi ɗaya a wajan masu aiki suka gama kwashe komai aka gyara duk yana zaune.

Fitowa Umaisha ta yi daga ita se riga da wando na bacci masu kauri black color kanta babu dankwali bare hula. saboda batayi tunanin zata hadu da kowa a ko ina ba shisa ta fito haka kanta tsaye ko ajikinta.
Saukowa ta yi dinning ba ta ga kowa ba sakamakon kashe wutan da Sudais ya cewa fatime ta yi hakan yasa bata ga mutum awajan ba ta shiga kitchen dan daukan ruwa da snacks dama abinda ya fito da ita kenan,tun shigowar ta ya hangota girgiza kai ya yi a hankali ya furta "yaran nan ba sa jin magana" gently ya mike ya nufi kitchen din ya tsaya a kofar ya harde hannunshi a kirjinsa yana kallonta rai abace.daukan abinda zata ɗauka ta yi ta juya domin barin kitchen din haɗa ido sukayi nan take tsoro ya kamata batasan lokacin da ta zubar da abubuwan hannun nata ba saboda tasan yau bazata kwana da gashinta ba tunda har ya yi mata warning akan hakan tasan yau shikenan malu Sudais ze yi mata.

Daura hannu aka ta yi ta fara w'iwi da hawaye ta riƙe gashin nata ta soma magana kamar wata zararra"ya Sudais ka yiwa Allah ka yi hakuri bazan sake ba, karka rabani da gashina, wayyo Allah shikenan gashina.ya Sudais daga yau inka sake ganina ba hula kamin duk hukuncin da zakamin, amma dan Allah karka rabani da gashina kaga kowa na dashi su Rameesa zasu mini dariya "tana magana tana yarfa hannunta.tama ƙasa nutsuwa ta yi magana,matsowa kusa da ita ya yi ya sa hannunshi daya ya cire hannun da ta rike gashinta da shi,da hannu daya ya haɗe hannayenta duka biyu ya riƙe su gam.sannan yasa hannu a bayan aljihun shi ya fito da wuka yar karama se sheki yakeyi kamar ba'a taɓa amfani da ita ba ya kalli fuskar Umaisha yaga yanda ta zaro manyan idonta waje ga hawayen da takeyi har lokacin,a tsorace ta ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun!ya Sudais dan Allah kayi hakuri ka rufamin asiri kaga ni yarinya ce dan Allah karka rabani da gashina Wallahi bazan sake yawo ba hula ba, i promise you.in kaaaaaaaaa...aske mini gashi na miji zan koma me malu dan Allah ka yi hakuri".
Ko kallonta be yi ba yasa hannu ya haɗe gashin waje daya ya ce"da na ke ce miki banason ku dinga yawo haka kam ba kun renawa mutane wayo ba!? kullum sekinyi alkawari bazaki sa'ke fitowa ba hula ba yau kam dole fa sena aske gashin nan sede in mutuwa zakiyi amma for sure zan aske".ga nin tabbas dagaske ya keyi askin ze mata yasa ta faɗa jikinshi sannan ta rike hannayenshi da ke rike da wukar tana kuka"ya Sudais bazan sake ba ka ji!?kayi hakuri". Da sauri ya rabata da jikinshi yana watsa mata harara ya ce"munafuka duk senayi maganin ku daya bayan daya tunda kunce ku bakwa jin magana da ƙaton kanki kamar randa, ki wuce ki bani wa..."be ma kammala magana ba ta sa gudu. taku biyu me kyau ya yi, ya riko hannunta ya ce"wa kika barwa kayan nan da kika zubar a ƙasa?!" Jiki na rawa ta fara kwashewa Allah _Allah takeyi tabar wajan gudun kar ya canza ra'ayi,maida snacks din ta yi ta ajiye ta ɗauki iya ruwan kawai ta fice da gudu, murmushi ya yi yabi bayanta da kallo koma wa dinning table din ya yi yadau wayarsa ya koma part din shi.
Chapter 25 · 0% Book details