← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 60

Sashe 44

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta duddubata a bangaren sama bata ganta ba hakan yasa bata da wani zabi da yawuce ta dawo downstairs.
Kusan yawanci ma basa nan,matar ya Hafiz ce a falon se Zoya da kuma yara.

Bata tambayi ko daya daga cikinsu ba. da taga de bata falon kawai ta fita,a waje ne ta tambayi securities ko sunganta,dayan su ne ya sanar da ita tana garden ,yana gama faɗa mata ta nufi garden din da sauri,tun kafin ta iso ta hangota zaune akan lilo dake cikin wajen.girgiza kai ta yi, ta karasa wajenta ta baya batare da tasani ba ta rike lilo ya tsaya ,juyawa ta yi tana ɓata fuska "my Tom ki bar mini lilo na" "Asmita meyasa kika baro can ki ka barni ina ta nemanki gaba daya hankalina ya tashi,banason sa'ke rasaki a karo na biyu".
Tasan abu ne ma wuyaci ta fahimci me take nufi.hakan ya sa ta ci gaba da turata a lilon,ita kuma tana dariyar farin ciki,haka suka kwashe mintuna Ashirin a haka.

Dakatawa Sabriyah ta yi,gaba daya ta gaji tana riƙe ciki ta ce"My Jerry zo mu tafi se anjuma mu dawo ko?",gyada mata kai ta yi ta sauko akan lilon.ta rike hannunta suka bar garden din suka koma ciki.

Muryar Ammi sukaji tana musu magana ."Sabriyah kuzo ku nan dama ku nake nema"karasawa wajenta sukayi ,kallon Asmita Ammi ta yi kafin ta maida kallon ta kan Sabriyah "tun dazun!,su Rameesa suke neman ku,Abbie yabada naku tsaraban abaku,ki dena yawo da wannan kayan sun matse miki jiki sosai Zoya ta faɗa mini cewa duk kayan da aka kai miki rage su kikeyi.nasan baki saba sa irin wa'yannan kayan ba amma ki daure ki dinga sawa ke macece,mace kuma an santa da kamun kai da kunya ,suturta jikinta"shuru Sabriyah ta yi,jikinta ya yi sanyi ba'a taba tsayar da ita an faɗa mata haka ba.

Murmushi karfin hali ta yi wanda kana gani kasan cewa be kai zuciya ba"Ammi!,na taso ne a inda babu me ce mini dede nakeyi ko kuma akasin haka, wa'yannan kaya masu nauyi kuma ban saba da su ba bana iya samun nutsuwa a cikinsu.Ammi yanda nake rayuwata bazance inajin dad'i ba kuma ba zance banajin dad'i ba".sosai Ammi take kallon idon Sabriyah domin iya gaskiyar ta take gani, tabbas an yiwa rayuwar yaran nan illa me muni ma kuwa.

"Bakomai Nasan in kina tare damu duk za ki saɓa da hakan"gyada kai kawai ta yi,ta ja hannun Asmita dake wasa da flowers din kan table.da tun tsayawar da Sabriyah ta yi wajen Ammi ita kuma ta tsuguna ta fara wasanta.

Suna haurawa stairs Asmita ta ce "my Tom" "uhmm"
"Ni banga me kyau ba ina yaje,nayi lilo shi be yi ba"bata amsa mata ba, suna ci gaba da tafiya ne ta ce"yau yana aiyuka sosai,ba zaki samu ganinsa ba"bata rai ta yi da alamu bata ji dadin maganar Sabriyah ba,ita tana son ganin me kyau suje su yi lilo kuma ya bata chocolate.
Har suka shiga daki bata sake magana ba se da Sabriyah ta ce "my Jerry ki dena fita batare da nasani ba,kina tsorata ni in naga bakya nan,kinji ko"gyada mata kai ta yi alamar "to".

Wanka ta shiga tayi yau duk bata samu ta sake yin wani wankan ba,tun na safe da ta yi ga shi yanzu har yamma ya yi.

Bayan ta fito daga wanka ta bude wardrobe din kayan kallon kayan da aka saka musu, ita da Asmita zuba musu ido ta yi tana tunanin wanne zata ɗauka,ga maganar Ammi da taji yana mata yawo a tsakar ka.

Runtse ido ta yi tasa hannu ta dauko wando falazo da riga.sakawa ta yi ta gyara gashinta kawai ko mai bata shafa ba.

Hawa gadon ta yi wajen Asmita da ta kwanta kamar me bacci amma idon ta biyu ta zubawa bango ido.
"My Jerry tashi kiyi wanka"maƙe kafada ta yi,"yi hakuri shalelena tashi kiyi wanka kinga dare ya kusan yi, sa'ke make kafadar ta yi.
Dafa goshi ta yi"haba my Tom ki tashi mana meyasa kike da taurin kai ne ?,"da karfi ta ce"banason wankan banaso "ta yi maganar tana bubbuga ƙafafunta akan gado,tuna maganar da Saghar ya gaya mata yasa ta kyaleta domin ya ce bata da buƙatar a dinga takura mata, lallabata yakamata a dinga yi.

Ya Abbas suna falon Abbie ana hira, matansu kuma suna wajen su Ammi suma.

"Tajuddeen be san mun dawo bane?"Abbie ya tambayi Sudais dake zaune kusa dashi.
"Ehh gaskiya ba lallai ne yasan kun dawo ba"ya basa amsa.
"Shikenan ni zanje ai in same shi".
Se da aka kira sunan Tajuddeen ne ma Saghar ya tuna da ya sanar dashi cewa yana son ganin sa da, Sudais da kuma Jawan.

Taɓa Jawan ya yi "kaga na manta ko, LTG ya ce yana son magana da mu, da ya Sudais".
"Shikenan se dare se muje "cewar Sudais.
Abbie yana matukar son ganin Tajuddeen se zuba ido yake yi ko ze zo amma shuru babu ko alamar sa,ana hirar ma shuru kawai ya yi burinsa kawai yaga Tajuddeen yazo masa sannu da zuwa ya rungumesa,amma tunda yaga har zuwa yanzu be zo ba tofa baze zo din ba.

"Yawwa nikam Hameed yarinyar waye naganku tare dazun!?"Abbu da ya kasa hakuri ya sa'ke tambayar uncle Hameed.
"Ita ce wannan yarinyar da Tajuddeen ya kawota gidan nan yana bincike akanta".
"Ikon Allah, lokacin da kuka tsaya tare se tayi kamar ƴarka"abbu sake faɗa domin shi yaga kamar Sabriyah da uncle Hameed.
Dariya kawai suka yi. Saghar da ya manta da allurar Asmita da zeje ya mata, seda a ka kira sunan Sabriyah ne ya tuna da ze mata allura.
Gyaran murya Abbie ya yi sannan ya soma magana "gobe Hajjatiye zata zo,kun san Allah wanin ku ya kuskura ya ɓatawa uwarmu rai tofa ba babu ruwana da girman da kukayi jikin ku ze baku labarin shekaru sha daya da yawuce tam"yar darawa sukayi, Ahmed ya ce"duk sanda Hajjatiye zata zo se anyi mana warning yanzu fa mun girma yakamata a dena maimaita mana Abbie ".
Cikin harshen shuwa abbu yace"da yafi muku".
Yaron ya Hafiz ne ya shigo dan shekara biyar hannunsa rike da bindigar wasa,ya zauna a kusa da Abbie"ah ah Ameer kar de mu za'a harbe da bindigar nan"Abbie ya tambaye sa cikin wasa, maganar cike da gwaranci irin na yara ya ce "nooo!terrost za'a halbe ko kaka"dukkansu dariya sukayi,"naga alama babanninka Tajuddeen ko Sudais ko kuma Jawan zaka ga'do "uncle Hameed ya faɗa yana shafo kan Ameer dake wasa shi da bindiga.

Sosai suka sha hira,ganin har lokacin LTG be shigo bane yasa Sudais ya kirasa,3missed calls ya mishi amma beyi picking ba daga karshe ya turo mishi da text,bude sakon da LTG ya turo masa ya yi.
"Bro!call you back,am in important meeting right now can't talk".
Murmushi Sudais ya yi,shi dama yasan zeyi wuya in LTG na gidan.
Shima ya rubuta mishi message kamar haka.
"Okay,Kayi sauri ka dawo Abbie is eager to see you".
Har bayan 5mint bayi mishi reply,yasan yaga message din.
"Abbie LTG baya gida yana meeting shisa ka ji shi shuru"Sudais ya faɗa masa,se yanxu yaji sanyi a ranshi,domin tunda suka dawo yakeson ganin sa it has been a while rabon da ya gansa.

"Ammi Tajuddeen fa tunda nazo ban ganshi ba"Anty Sameera ta tambaya,anty sakeena dake sawa karamin ɗanta pampas ta ce"Nima abinda nakeson tambaya kenan,ko baya nan ne" "ehh ya fita,nikam bazaku koma gidajenku bane dare fa yanayi"Ammi ta tambayesu ,tana bin ko wacce su da kallo dariya Anty amarya ta yi "haba Ammi yakike korasu ne"hararanta ta yi ta ce "to ai naga dare ya fara ne ai,kuma banga alamar zasu tafi ba, ko kuna nufin haka zaku bar mazajen naku su kadai a gida!?", marairace mata suka yi "ayyah Ammi dan Allah ki bar mu mu kwana, Wallahi seda muka sanar musu zamu kwana kafin muka taho kuma sun yarda"cewar anty sakeena.
"Se kuma kuyi ai,yanzu nan ko wacce ta shirya ta wuce gidanta,babu wacce zata kwana",Hajiya babba tana zaune tana jinsu bata sa musu baki ba.
"Ammi kiyi hakuri ki barsu tunda sun tambayi mazajen nasu,kuma kinga Hajjatiye da Rumanatu duk gobe zasu zo,su Abbas ma duk anan zasu kwana"anty amarya ta roki alfarma..
"Shikenan Allah yakaimu "suka amsa da Amin.

Yau su Umaisha ana wajen Abbie da Abbu,a wajensu suka tare se surutu suke musu,rabonsu da part dinsu tun karfe biyu basu sake komawa ba.

Sabriyah bata sake jin d'uriyarsu ba,kuma hakan be dame ta ba,tana tare da Asmita suna ta shirmensu, knocking aka yi ta ce "a shigo".
Saghar ne ya shigo hannunsa rike da kwalin chocolate din da yace ze bada a kawowa Asmita ya manta.
Tana jin muryar sa ta mike ta tsaya akan gadon tana ihun"me kyau!me kyau!me kyau"murmushi ya mata,tana daga kan katifa ta rungumoshi a jikinta kamar wani ɗanta,wani shock ya ji tundaga tafin ƙafar sa har cikin kwakwalwarsa da sauri ya raba jikinsa da nata beyi taba kawo tsammanin zata rungumesa ba.
Tura masa baki ta yi"me kyau na hau lilo babu kai"se ta nutsuwarsa ya yi kafin ya ja hannunta ya kaita gaban mirror ta zauna Sabriyah na zaune tana kallonsu,komawa ya yi wajen da ya ajiye kwalin ya bude ya fito mata da chocolate ya kawo.
Buɗe mata chocolate din ya yi,yabata raba chocolate din gida biyu ta yi tabashi rabin girgiza mata kai ya yi alamar bazesha ba.
Fara sha ta yi idonta akanshi,kawar da kansa ya yi, ya haɗa allurar ya mata cikin dabara,se da ya gama ze tafi tukun ta ce baze tafi ba se yasha chocolate din,karba ya yi gudun kar tayi kuka,yasha ya ce "shikenan!?", "Ehh".

Sabriyah ta ce "my Jerry ni baza'a ban chocolate din ba?",sake raba chocolate din ta yi tasa mata abaki.

Fita Saghar ya yi adakin yana dariya.abincin darensu Fatime ta kawo musu fuska a sa'ke suka gaisa.

Bude kofar bedroom din ya yi yaje ya zauna akan gadon Abbie yana jiransa,daga wanka ya fito beyi tunanin zega mutum a ciki ba,da mamaki yake kallon LTG dake zaune akan gadonsa.
Chapter 44 · 0% Book details