← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kututun bakin ciki da takaicin Sabriyah ne ya tsaya mata a rai,ta kalli Sabriyah,rai abace ta ce "yanzu saboda wannan banzar maganar kika tasheni Sabriyah!?nikam wai meye nufin kine?kina tunanin zamu tabbata a cikin wannan ƙaddararren gidan ne?,ke shikenan ko da yaushe magana daya biyu baya wuce akan gidan nan,to nikan nagaji Wallahi ko kina so ko bakya do Sabriyah se mun bar gidan nan gaba."yanda Asmita take magana kadai ya isa ya nuna kan cewa ranta ya yi mugun ɓaci, saboda ita ta rasa menene abinda Sabriyah ta gani a cikin gidan da kullum in an tashi magana se ta ce bata da wajan da zataje yafi mata wannan gidan,a duk lokacin da ta yi wannan maganar ran Asmita bakaramin ɓaci yakeyi ba.

Lura da ta yi ranta ya ɓaci ne yasa ta mayar da maganar wasa amma ita kam har ranta tana son zaman gidan saboda muddin tabar gidan batasan ina kuma rayuwarta ze ƙare ba tunda ba iyayene da ita ba
,ɓalle ta ce tasan wata rana zata hadu dasu,bata da kowa,shisa duk irin ɓacin ran da take fuskanta a gidan be sa tayi tunanin barin gidan ba.

"Ke dallah karki mini masifa wasa nake miki,amma de kinga ledar dakin mu ya mutu, se muje mu siya wani goben!".

Watsa mata harara ta yi ta ce"ki fadawa wanda be sanki ba,nayi miki sanin da ko kaina banyiwa ba,kamar yanda kika mini farin sani haka nima nayi miki,dole duk maganar da kikayi in san da gaske kike ko kuma wasa.amma wannan maganar ta ki kam nasan har cikin ranki kika faɗe ta saboda ba tun yau kika saba faɗa ba."

Tsaki Sabriyah ta yi ta juya mata baya ta ce"se kuma kiyi ai kanki ake ji."

Baccin da basu yi da wuri ba kenan saboda cacan bakin da suka tsaya yi daga karshe ma Sabriyah juya mata baya ta yi ta kyaleta,haka Asmita ta yi ta masifa kamar zata aro bakin wani ta ci gaba, babban abinda ya bata mata rai ma shine shareta da Sabriyah ta yi taƙi biye mata su ci gaba da faɗan,hakan yasa ta zuba mata dundu a tsakiyar bayanta.

Sosai dukan da ta mata ya yi mata zafi amma ɗan neman magana kawai se tafara munshari irin bacci ya yi nisa da ita, tana dariya kasa_kasa,haka Asmita ta gaji da masifar ta kwanta ta yi bacci.

Tunda garin Allah ya waye babu wanda ya kula wani acikinsu kowa harkan gabansa yakeyi, Kamar kullum Asmita ce ta musu abin karyawa ta zuba musu a plate sukaci, Sabriyah ce ta fara yin wanka sannan Asmita ta shiga.

Shiryawa Sabriyah ta yi cikin doguwar riga mara nauyi ya dangale mata pink color,yana da open shoulder rigar kafadarta awaje da kuma bayanta ga sunan Tajuddeen baro _baro da yafito abayanta ,gashin kanta kuma ta daure su waje daya da ribbom ta saka hula shima pink.kallon Asmita dake kwance ta yi ta ce "ki tashi muje mu siyo ledar dakin!" ɗa kamar bazata je ba se kuma ta mike ta dau wayar ta,ta ce" muje"

Ledar dakin suka siya sannan suka fara kokarin koma wa gidan hango wata yaloluwar riga Asmita ta yi ta cewa Sabriyah "barin in je in siya ina zuwa".

Tsayawa a wajen Sabriyah ta yi rike da ledar tana jiran Asmita da taje siyan riga. Shuru_shuru Asmita daga siyar riga daya se ta ɓige da duba wasu kayan.

Tsaki Sabriyah ta yi aranta ta ce bari in je in samu wani wajan in zauna in jirata .
Daukan ledar dakin ta yi ta soma tafiya waigawa bayanta ta yi saboda taga ko Asmita ta fito daga shagon.
Gif!taji ta buge abu kamar gini da sauri ta juya dan taga menene mutum tagani a gabanta sanye da kananan kaya fuskar shi da facemask da kuma hular facing cap idon shi kawai da ke binta mugun kallo ta iya gani me kama dana zakin zakuna wanda yafito farauta,kayan hannunta ne ya zube akasa da kuma wayarsa a tare suka sunkuya domin daukan kayansu,tsaban tsaurin ido irin na Sabriyah duk da yanda ta ganshi a murde amma tsaban yanda take fama da rashin kunya ta ja tsaki ta ce "kai makaho ne ko kuma gani ne bakayi zaka wani buge mutane!?" ,a tare suka sake mikewa, kallonta ya keyi da mamaki yarinya karama da ita har tana da karfin halin mishi rashin kunya se kuma ya tuna location din da yake ance duk karuwai ne suka fi yawa a wajen nan take yaji wani tsanar ta me karfi ya kamashi ya fara binta da kallon tsana hannun shi ɗaya yasa ya hankaɗe ta ta faɗi akasa har seda hannunta ya gurje wajen ya yi ja ko juyawa be sake yi ba ya yi tafiyar sa.

Bin bayanshi ta yi da kallo ta daga murya tace "Allah ya isa mugu kawai, azzalumi macuci ma yaudari,ma ha'inci!" Haka ta dinga faɗa da karfi tana hararan bayanshi tana kuma shafa hannunta da ya yi ja,tana tura baki,duk maganar da take yi akan kunnenshi danne fushinsa ya yi domin kuwa yasan muddin ya koma wajanta tofa se ya kasheta,shisa kawai ya yi tafiyar sa ,nan take kuma ya tsaya sakamakon wani irin luguden duka me karfin gaske da yaji zuciyarsa tana yi kamar ze fito waje,duk jarumta irin nashi ya kasa ci gaba da tafiya saboda yanda yaji zuciyarsa take bugawa,ji ya yi kamar akwai abinda ya jefar atare dashi da yakamata ace ya tsaya ya nema ko kuma ya yi mantuwar wani abu.

"Hello LTG. we have found them"muryan major Marry ya ji ta cikin Bluetooth din dake manne a kunnen shi, nan ya dawo cikin hankalinsa sannan ya cigaba da tafiya.

Fitowa Asmita ta yi daga shagon ta hango Sabriyah a ƙasa har lokacin bata tashi ba tsabagen takaici kuma bata bar zage_zagen da takeyi ba kamar zata ci babu.da gudu ta iso wajanta ta dagata ta ce "garin ya ya kika faɗi my Jerry!?"cikin ƙuluwa ta ce "uban waye ne ya ce miki faduwa na yi!?wani mugu mara tausayine ya tureni na fadi."

Sannu Asmita ta yi mata ta dinga dannata ta yi shuru amma ta ki yi se ci gaba da magana takeyi kamar wanda ya tureta din yana gabanta.

Napep suka shiga suka fara tafiya har sunyi nisa kwatsam from nowhere mutum ya faɗo musu cikin napep, jikin shi da raunin se haki yake ta yi damƙar hannun Asmita ya yi numfashinsa na fisga da kyar ya iya furta.

"Na ji ajikina ke din nan za ki taimaki al'umma, dan Allah ko ta wani hali ki tabbatar da kin kai memory card din da zan baƙi wajan hukuma domin al'umma suna cikin hatsari ,saboda yan ta'adda masu hatsarin gaske sun shigo cikin Nigeria"daga Asmita har Sabriyah gaba dayansu tsananin tsorone yasa ko da yawu sun gagara haɗiyewa,yanda yake a firgice yana musu magana haka suma suke a firgice hatta me napep din da ya dauko su shima a tsorace ya ke.

Dakyar Asmita ta iya haɗiye wahalallen yawu da ya wuce dakyar se da yabada sauti 'kwatt' ta ce"tooooo....meneneeee... sunanka!?" Yanda take jan magana ma kadai ya isa ya nuna zallan tsoron da take dauke da shi.

"Sunana Barrister Lameer,ni lauya ne, ina dauke da wani babban sirrin wasu yan ta'adda wanda hakan yasa suke son kasheni,nasan bazan yi tsawon rai ba!dan Allah ku tabbatar da kun damƙa wannan memory wajan hukuma.!"ya yi maganar yana damƙa wa Asmita memory card din gam a hannunta,duk da yanda yake cikin firgici da tashin hankali amma hakan be hanashi ganin digon tawadar Allah guda uku da suke gefen yatsunta ba,da sauri ya ɗago yana faɗin.

"Asmitaaaaaaa......"yana faɗar sunanta wa'yanda suke binsu abaya suka sa hannu suka jawo shi acikin napep din sukayi wurgi dashi akan titi motar ya bi ta kanshi.

Razanannen ƙara Asmita da Sabriyah suka saka,tunda suka zo duniya basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin ba se yau, karan bindiga ne ya din ga tashi ana binsu a baya kankame junansu sukayi suna kuka,me napep se gudu ya keyi,karan bindigan ne ya fara lafawa,leka kanshi me napep din ya yi sannan ya ce "yanzu babu wa'yanda suke binmu a baya" sude hankalinsu be kwanta ba,burinsu kawai su gansu a afafa.

Sauke su ya yi yaja napep din shi ya yi gaba yana me da_nasanin fara sana'ar napep a rayuwarshi.

Tsayawa sukayi a bakin gate din su basu shiga ba,har lokacin rawa jikinsu yakeyi riko hannun Sabriyah Asmita ta yi ta ce"my Tom ki rike wannan memory card din a wajan ki saboda kece me yawan saka breziya masu zip a ta ciki"ta yi maganar tana damƙa mata a hannunta,jiki na rawa Sabriyah ta karba ta jefa memory card din cikin breziyar ta.

Jiki a sanyaye suka shiga cikin dakin su. suka zauna ko wacce da abinda take ai yanawa aranta can Asmita ta ce "my Tom amma ta ya Barrister Lameer yasan sunana "

Kan sabriyah a ƙasa ta ce "nima abinda nake ta nazari kenan aina ya sanki to!?".

Babu wanda ze basu amsar wannan tambayar hakan yasa suka yi shuru har zuwa lokacin kirjinsu na bugawa. haka suka yini a ranar kamar zakaran da ruwa ya yi wa duka, babu wani kuzari a tattare dasu.

Lagos oriental hotel

"LTG. Wannan sune ɗaukan CCTV cameran wannan hotel din."cewar security hotel din,matsowa LTG.Taj ya yi ya fara duba daukan Cameran,shige da ficen Asmita da Sabriyah ne yafara gani lokacin da suke hotel room din da Fu'ad yakama,ga Fu'ad din a tare dasu,se de kwata_kwata fuskar Fu'ad be bayyana ba.

Kallon security din hotel din LTG.Taj ya yi ya ce "meye alaƙarsa da wa'yannan yan matan!?".

Nuna Sabriyah security ya yi ya ce "wannan din ƙaruwar sa ce saboda kwanan su goma acikin wannan hotel din ,dayar kuma ƙawarta ce.".

Zooming din fuskan su LTG.Taj ya yi,nan take fuskar Sabriyah ya bayyana me kyau ajikin screen din.kallo daya ya mata ya tuna haɗuwar su a cikin kasuwa,kallon major Marry ya yi ya ce"with less than 5 minutes, I need more information about her, saboda dole tasan inda shi saurayin nata yake!?.
Chapter 30 · 0% Book details