Sashe 22
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.
Comment,like and share 🖋️🖋️
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹
*_ story & written_*
By
*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)
*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️
Page 13
Se yamma liris tukun suka shirya dan zuwa kasuwan suna kokarin fitowa cele ya shigo kai tsaye dakin nasu ya shigo"mutumiyar yau fa ban ganku ba kwata_kwata"kwasan kudin Sabriyah ta yi tasa acikin jaka sannan ta ce "iyi yau ka yi nisan kiwo naga alama"yar dariya ya yi ya kalli Asmita dake zaune tana bin su da ido"Asmita yau ba magana ne?"tsaki ta yi ta kau da kanta gefe"ai ni Wallahi cele kabani mamaki har in ce ka kawo min abu ka ƙi"se da ya kalli Sabriyah kafin ya ce "nifa karki ga laifina hot girl ce ta ce kar ta sake kallon a na kawo miki kayan more wa"Sabriyah najin su amma ko kallonsu ba ta yi ba ta ce"ku tashi mu tafi in kunyi niya"ta yi gaba abunta bin bayanta sukayi har suka cimma ta.
"Wai kunji labarin jibi manyan alhazawa zasu zo ko?" "Ehh haka mukaji"cewar Asmita murmushi Sabriyah ta yi ta ce"ai za'a ci uwar sabada Wallahi ko a wasan rawa ma nasan zan samu kudi sosai ɓalle kuma ace na nuna musu na yarda da bukatar su, nifa kun san abinda yake burgeni kuwa?kawai in ga ina wasa da hankalin namiji shine kawai ya ke burgeni kuma in ci kudin su son raina saboda wannan karon lokacin samun kudin mu ne so nake in haɗa kudaden in bawa my Jerry ta je garin su"duk sake baki suka yi suna kallon ta Asmita ne ta ce"ke a tunanin ki zan bar gidan nan ba tare da ke bane?ai ƙafana ƙafarki yawwa" dariya cele da Sabriyah suka yi harda tafawa Sabriyah ta ce"ke waya faɗa miki zan taɓa barin gidan nan tabb ai ina nan daram dam_dam se munga abinda ya turewa buzu naɗi. burina kawai shine in ga rayuwarki ya yi kyau Asmita."
"uhmmm"kawai Asmita ta iya cewa dan bataso su ja maganar ya yi tsayi ranta ze iya ɓaci saboda ta lura Sabriyah dagaske take bazata bar gidan ba tarasa me yasa Sabriyah batason barin wannan gida da ba komai take amfanuwa dashi ba.
Bayan sun gama siyayyan kayan abinci ne suka koma cikin kasuwa saboda siyan kaya, Asmita kiran me siyar da karas ta yi yazo saboda tanaso sosai. mutumin ɗan dattijo dashi ta ce ya bata na dari uku har ya zuba mata ze tafi se ya kuma tsaya ya kalli Sabriyah daga sama har ƙasa sannan ya ce "ƴata amma ke musulma ce kuwa?" kallon tara saura ta mishi batace mishi komai ba taci gaba da abinda takeyi shi kuma ganin hakane yasa ya ce "karku ga kamar na yi muku katsalandan amma be kamata ba kuna yaran musulmai kuna wannan shigar, duk suran jikin ku awaje dan Allah ku gyara"duk zuba mishi ido sukayi suna ganin wani karfin hali irin nashi Sabriyah ta ce"ka ga malam babu abinda ya shafe ka damu je ka ci gaba da siyar da karas dinka bawai shiga rayuwar mutane ba,haba wannan ai gulma ne"girgiza kai ya yi kawai ya ce"to Allah shi kyauta"ya fece dan ya lura yaran ba kunya ne dasu ba, za ma su iya zagin shi in beyi wasa ba.
A gajiye suka koma gida Lokacin har 7:50pm ya yi Asmita ce ta musu shinkafa da mai da yaji su uku harda cele sun kusa cinye wa Nabiha ta shigo jiki a sanyaye alamar ma kuka ta yi idonta ya ɗan kumbura dakatawa sukayi suna tambayar ta"Nabiha lafiya meyafaru ne?"zama ta yi akan bakin katifarsu kusa da cele da shi ma ya cire hannu acikin abincin da suke ci.
"Boss lady ce ta ce a kira mata duk wata matashiyar yarinya a gidan nan an sace mata sarkan gold dinta"gaban Asmita ne ya faɗi jin abinda Nabiha ta faɗa ita de Allah ya zuba mata tsoron boss lady kamar dodo yanzu tsoronta bata san wani irin hukunci boss lady zata yi musu ba.
Jin sharrin sata ne jikin su ya yi sanyi sosai saboda sude sun san basu dauka ba kuma bama shiga wajan boss lady din sukeyi ba se in ance ana bukatar su,ganin yanda Nabiha har lokacin take hawaye ne hankalin Cele yaɗan tashi saboda yana matukar sonta amma babu wanda ya taɓa faɗawa hakan har ita kanta Nabihan bata sani ba.
"Tunda kude kun san baku dauka ba ku kwantar da hankalinku babu yanda boss lady ta iya daku ku tashi kuje kar aga kun daɗe a yi tunanin ko wani abun kukeyi"cewar cele ya faɗa yana mikewa,jikinsu a sanyaye su ma suka mike suka fita abincin da basu karasa ci ba kenan.
cele ya tafi dan zuwa gidansu saboda shi bayi da nisa da afafa saboda shakuwar da ya yi da su Sabriyah ne yasa ya koma abokin su kullum suna tare ko da safe ko da dare.sashin Boss lady suka nufa tun shigowar su suka ga yan matan dake cike duk sunyi carko_carko ga magajiya boss lady na hakimce a zaune a tsakiyar gidan se hura hanci takeyi suma tsayawa sukayi a layi kamar yanda suka ga sauran sunyi boss lady ta fara magana.
"Wato ku yanzu satan naku ya komo kai'na kenan ko? a cikin ku wace tsinanniya ce ta shiga ta ɗaukar mini sarkan gold ɗita?, wanda aƙalla yakai darajan Naira miliyan daya da rabi!?"ta yi maganar tana zare musu ido.
duk rantse mata suka fara yi ko wacce da abinda take faɗi, daga me cewa "Wallahi boss lady bani bace"se me cewa"na rantse da Allah boss lady ban masan wani kala bane ban taɓa kallo ba"haka suka dinga rantse mata.afusace ta mike tsaye ga ɗan daudun dake take mata baya a gefenta se wani yauki da yanga ya keyi kamar mace ta ce"kenan sarkan ya yi ƙafa ya gudu ko?haka kuke nufi ko!?"shuru sukayi kansu a ƙasa, Asmita, Nabiha da Sabriyah su de babu wanda ya yi magana acikin su.
"Kai caje mini su daga pant din su har breziya ko wacce a cikinsu maza_maza"ta yi maganar tana kallon dan daudun.fara cajesu ya yi daya bayan daya har yazo kan Nabiha ko ajikinta tabar shi ya cajeta hannu yakai kan Asmita yana kokarin sa mata acikin riga da sunan cajewa ta ja gefe tana watsa mishi harara"kai meye haka ƙaton gardi dakai zaka wani yi kokarin sa mini hannu a nono"Asmita ta yi maganar tana ci gaba da zabga mishi harara Sabriyah murmushi ta yi kawai saboda dama jira take yi kawai dan daudun yazo kan Asmita tasan za'a dibi yan kallo.kowa zubawa Asmita ido sukayi suna ganin ikon Allah har wasu ma sun fara tunanin ko de ita ce ta sace sarkan gold din,boss lady daka mata tsawa ta yi "ki barshi ya caje ki kar ki bari Wallahi in iso wajan nan Asmita"duk da yanda Asmita take matukar tsoron boss lady amma ja baya ta yi murya kasa_kasa ta ce"nide boss lady ki sa wata macen ta cajeni amma banda wannan ƙaton ƙazamin"iya ɓaci ran Boss lady ya ɓaci ganin Asmita na kokarin yi mata rashin kunya ɗauketa ta yi da wasu gigitattun maruka har guda biyu runtse idanu Sabriyah ta yi saboda ita taji zafin nan take idonta ya cicciko da ruwa,dafe kuncinta Asmita ta yi tana hawaye damƙar gashinta boss lady ta yi ta ce"mutumiyar banza wato har kin yi girman da za ki dinga maida mini magana!ko kin manta nice uwarki nice ubanki gabaki ɗayan ku baku da kowa sama dani tunda na riga da nayi muku lasisi to nayi muku komai a duniyar nan. shegiyar yarinya tsinanniya wato ke ce barauniyar da kika sace mini gold dina kenan!?shisa kika ƙi yarda a caje ki to fito dashi ko kuma na lahira yafiki jin dadi"kuka Asmita ta fashe dashi saboda yanda boss lady ta rike mata gashin kanta azaba kawai take ji,a tsorace Sabriyah ta fito ta zube akasa ta rike ƙafar boss lady saboda tasan yau Asmita tunda ta shiga hannun boss lady kasheta ne kawai bazata yi ba.cikin rawan murya Sabriyah ta soma magana"dan Allah boss lady kiyi hakuri Wallahi Asmita ba ta daukar miki sarka ba yau tun safe muna tare ki rabu da ita niiii....zan caje miki ita yanzu ma kuwa"haka ta dinga bawa boss lady hakuri amma daga karshe saboda rashin imani irin na boss lady hannu tasa ta dago sabriyan ta gashin kanta itama dukan su rike gashin kansu ta yi ta ce"baƙaƙen munafukai ku fito mini da sarka na ko kuma dukkan ku in kai ku dakin horo Wallahi se kunyi sati daya aciki"duk yan matan dake wajan sunyi matukar tausayawa Asmita da Sabriyah domin kuwa yau sun faɗa tarkon boss lady.
Duk kuka suke yi musamman ma Asmita"boss lady dan Allah ki rabu da Asmita batasan komai ba, nice na ɗauke sarkan gold din"Sabriyah ta faɗi haka saboda ta kwaci Asmita a hannun boss lady in yaso ita se amata hukuncin,duk da irin zafin da Asmita take ji amma hakan be hanata faɗar"boss lady karya Sabriyah takeyi!! ta faɗi hakane saboda ki kyaleni amma ni na dau sarkan gold din"hararanta sabriyah ta yi ta ce "Asmita meyasa kikeyin haka dan ki ceceni, bazan taɓa barin ayi miki hukuncin da nice da laifi ba boss lady karki yarda da ita nice nan na sace!".