← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 60

Sashe 17

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doctor ne yafito daga dakin da akayi admitting din anty amarya ya ce" she's out of danger now sede kubita a hankali kar adinga bata mata rai , ta kamu da ciwon zuciya na farat daya , zuciyarta ze iya bugawa idan har yaci gaba da fuskantar kunci da tashin hankali kuma dole ku dinga kasancewa tare da ita gudun kar a barta ita daya ta faɗa tunani . Kudinga tayata hira domin dauke mata kewa Allah yabata lafiya" duk jikinsu ya mutu jin anty amarya ta kamu da ciwon zuciya dama tana cikin damuwar rashin haihuwa ga kuma yarta daya tilo data mallaka aduniya ansace ta.
Dakyar suka iya amsawa doctor da ameen sannan suka shiga ciki tana kwance tana baccin wahala gaba daya ta tane sosai ta yi fayau kamar ba jini ajikinta bacci takeyi amma hawaye ne yake fitowa daga idanunta zama kusa da ita uncle Hameed ya yi hawaye na zubowa daga idonshi tausayin kansu ne ya kamashi da kuma tausayin matar shi na irin halin da take ciki sun yi rashin babban farin cikinsu da in sun kalleta suke jin sanyi da kwanciyar hankali a tare dasu.ita kadai suka mallaka a duniyar nan ga shi to mara imani sun dauketa. Abbie ne ya tsaya kusa da uncle Hameed ya dafa kafardar shi cikin sassauto da murya ya ce "in sha Allah za'a ganta"
kiran waya ne yashigo wayar Abbu dubawa ya yi yaga DPO ne da sauri ya yi picking , a dayan bangaren aka fara magana"ranka shi dade !a iya binciken mu mungano bawai aikin enemies bane , daga shekaran jiya zuwa jiya ansace yara ƙanana mata sama da goma , daya a Damaturu uku a pataskum , uku a biu sekuma hudu a nan Maiduguri harda yar gidanka itace cikon na goma din kuma binciken mu ya nuna mana yaran nan da masu garkuwar basa cikin garin Maiduguri amma duk inda suka shiga zamu nemosu in Allah ya yarda"Abbu dake tsaye ne yasamu guri ya zauna zufa na tsatsafo mishi be iya cewa DPO komai ba kawai ya kashe wayar kallon shi Abbie da uncle Hameed sukayi dasu Hajiya babba ganin reaction dinshi tambayanshi suka shigayi , "babu komai" ya ce musu jan hannunshi Abbie ya yi sukayi waje nan Abbu ya kwashe duk yanda sukayi da DPO yafaɗa mishi.shi kanshi Abbie jin yara har goma aka sace hankalinshi yatashi sosai , waya yadaga ya kira gomna sukayi magana sosai sannan ya kashe.

Yau kwanan anty amarya biyu a asibiti , kuma har izuwa yanzu ana binciken neman yara mata goma da aka sace amma shuru babu su babu alamar su kamar ba sacesu akayi ba makwamusan sunada matukar basira sosai basu bar alama ko sheda ƙwalli daya ba wanda za'a kamasu ,har suka isa inda zasu isa cike da basira babu wanda yaci nasarar kamasu saboda ba haka suka zauna ba harda tsafi a lamarin kwamushen su shisa ba'a taba kamasu.

Bayan an sallame su sun dawo gida ana kulawa sosai da anty amarya kullum Tajuddeen na tare da ita duk da rashin son yin magananshi ga kuma abinda ya hadu mishi na rashin Asrah hakan ne yasa ya dauwa kanshi alkawarin cewa inya zama babban soja shida kanshi ze nemo Asrah aduk duniyar da take sannan ya kashe duk wanda yake da sa hannu a saceta ,gaba daya ya zama kamar wanda beda lafiya ji ya yi ma zama acikin gidan batare da itaba ya ishe shi hakan yasa ya gama shiryawa gobe ze bar kasar kuma ya fadawa Ammi akan ta faɗa wa Abbie , yanzu ma yazo wajen anty amarya ne yana tayata zama dukda akwai mutane atare da ita saboda inba bacci ba ba'a barinta ita kadai tadena magana sosai tadena shiga cikin mutane komai dinta ya canza , su Saghar duk suna tare da ita haka anty Sameera da anty Sakeena suma kusan kullum se sunzo gidan . Haka de gidan yakoma kamar gidan zaman makoki.

Washe gari misalin ƙarfe goma na safe Tajuddeen ya gama duk wani shirin da zeyi na tafiya kowa an hallara a falo saboda rakashi airport ,fitowa ya yi sanye da wandon sojoji da bakar riga me hula ya rufe fuskarshi dashi falon ya shiga ya zauna kusa da Hajiya khareema (Ammuh) nan suka fara mishi addu'ar samun nasara akan karatunshi, tashi ya yi yaje gaban anty amarya ya tsuguna ya rike hannunta yana kallon cikin idonta ya ce"Anty amarya nayi miki alkawari da hannuna zan dawo da Asrah cikin wannan gida,ko min daren dadewa ina me tabbatar miki da zamuga juna , ki yarda dani " shafa kanshi anty amarya ta yi tana yar murmushi ta ce "na yarda dakai Tajuddeen nasan duk inda Asrah din ka take zaka dawo mana da ita in Sha Allah , zan zuba idanu domin inga wannan rana idan har Allah ya aramin tsawon kwana , Allah yabaka Sa'a akan karatunka" murmushi kawai ya yi ya mike ,Abbie ya zubawa Tajuddeen ido yanaso yaga ko ze mishi magana ko bazeyi ba , kallon Abbie Tajuddeen ya yi ya taka zuwa inda suke tsaya batare da ya ce musu komai ba da fa kafaɗar shi Abbie ya yi yana murmushi ya ce" nasan zaka sani alfahari arayuwata da kowa in ya ganka zece wannan ɗan Mubarak Bishara ne I have trust in you" murmushi kawai ya yi.
Ammi na zaune ta yi shuru ji tayi dama ace kar ya tafi."Ammi" ya kira sunanta murya akarye dagowa ta yi ta kalleshi mika mata hannu ya yi, ta rike ya dagota tsaye sannan suka rungume juna kusan minti biyu , addu'a sosai Ammi ta yi mishi saketa ya yi yaje ya rungumi Hajiya khareema se goge hawaye takeyi " son zanyi kewarka sosai" " me too Ammuh na "murmushi Hajiya khareema ta yi ta ce"ka kulamin da kanka sosai domin na damu da kai da kuma rayuwarka!"gyada mata kai ya yi.
Hajiya babba ma sosai ta yi mishi addu'ar samun nasara arayuwa ya amsa mata.

Fitowa sukayi su Abbas ne dasu Abbie ne suka rakashi airport, fita ya yi a motar yana kokarin nufan wajen jirgi, bin bayanshi Abbas da su Hafiz sukayi riko riganshi Abbas ya yi, juyowa Tajuddeen ya yi ya fuskance su " Tajuddeen mudinma fushin da kakeyi damu na ba gaira ba dalili dashi zaka tafi azuciyarka ba zaka rungumi yan uwanka ka musu bankwana ba?"buɗe musu hannu ya yi dukkansu suka rungumeshi can ƙasan makoshinsa ya ce"zanyi missing naku" suma suka ce "muma haka amma duk end of month zamu dinga kawo maka visit in Sha Allah" haka suka rabu akan idonsu ya shiga cikin jirgi after few minutes jirgin yatashi. Ajiyar zuciya sukayi suka koma motar yau zasu ji gidan wani iri ba Asrah ba Tajuddeen.

Haka rayuwar gidan yaci gaba da kasance babu wani walwala sosai atare dasu, yau sati biyu kenan da dauke Asrah kuma haryanzu anata bincike amma shuru sede muyi addu'a muce Allah ya bayyana su.

Lokacin da Fu'ad Abubakar Daula ya samu labarin an sace Asrah kamar zeyi hauka, bori da faɗe_faɗe babu irin wadan beyiwa mahaifin shi ba Abubakar Daula kan cewa lallai se yasa an samo mishi Asrah din shi ko kuma shi ya bazama duniya ya nemota dakyar Abubakar Daula ya shawo kan Fu'ad ya nutsu gaba daya ya tarwatsa bedroom din shi ya jijjima kanshi ciwo Abubakar Daula ne ya ce "Fu'ad karka damu zan sa a nemo maka Asrah amma ba yanzu ba, se bayan komai ya lafa tukun dan banaso ayi tunanin akwai hannunmu acikin saceta da akayi saboda kowa yasan irin gaban dake tsakanin mu da su just calm down"ya faɗa yana dafa shi,zubewa akan guiwowin shi Fu'ad ya yi rai a matukar ɓaci batare da ya ɗago kai ya kalli Abubakar Daula ba ya ce"dad leave my room bana san ganinka just leave me alone" "Fu'ad I promi....."kafin ya karasa maganar shi afusace Fu'ad ya waigo ya kalleshi ya ce"get the hell out of my room I said I don't wanna see you kafice min da gani kawai"Abubakar Daula sanin halin ɗan nashi ne in be samu abinda yakeso ba yanzu se ya kusan tayar mishi da karamin haukanshi hakan yasa ya fice simi_simi a dakin.
Bin bayan shi da mugun kallo Fu'ad ya yi kafin ya daga kai ya kalli celling din dakinshi da karfi ya ce"shin kina ina neeeeeeeeeee Asrah? aina zan ganki?waye ya sace mini future wife dina Wallahi koma waye se ya yi da nasani arayuwarshi domin ni Fu'ad Abubakar Daula bazan taba kyale shi ba"
Kamar wani zararre haka yake magana kamar da wani a dakin, juyawa ya yi ya kalli yamma da kudu sannan ya ce "noooooooo! bazeyu ba ni Fu'ad Abubakar Daula nayiwa kaina alkawarin ni zan fara ganin Asrah komin daren daɗewa se munga juna,bazan taɓa bawa Tajuddeen damar samunta kafin ni ba,dole nine zan fara nemo Asrah sannan in aureta.tabbas hakan ne ze faru hhhhhhhhhhhhhhhhh"ya gama maganar yana kecewa da wata mahaukaciyar dariya.tabbas Fu'ad yana da matsala a kwakwalwar shi wanda shisaka komai ya yi yake ganin a dede yake.

Tofa ana wata ga wata dukkanin su biyu sun daukarwa kansu alkawari me girman gaske wanda .....
Fu'ad Abubakar Daula ya yi wa kanshi alkawarin shi ze fara samo Asrah,shi ze fara haɗuwa da ita komin daren daɗewa.
A yayinda Tajuddeen Mubarak Bishara ya dau wa kanshi alkawarin shi ne ze dawo da Asrah cikin rayuwar gidansu shine nan ze kawota gida komin daren daɗewa.

Shin waye ne ze fara haɗuwa da Asrah a rayuwa?shin Asrah zata rayu?shin su Hajiya hurairah da Hajiya khareema zasu cimma burinsu?.
Ku biyoni domin jin yanda zata ka ya.

*LAGOS*

A FAFA
Chapter 17 · 0% Book details