← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 60

Sashe 36

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ga wannan ranar da Anty amarya ta sa Sabriyah a ido ta ji son ta ya shiga zuciyarta,haka uncle Hameed ma.Sabriyah bata fitowa cikinsu amma,anty amarya zata zo su zauna suyi hira ta yi ta zolayar ta kafin a ankara shakuwa me karfi ya shiga tsakanin Sabriyah da anty amarya, Ammi, Hajiya babba, Umaisha, Parsa, Rameesa, iklas.shirinta da Zoya ne har yanzu jininsu be haɗu ba,haka Ammuh ta rasa dalilin da yasa ta tsani Sabriyah kuma duk sa'in da suka haɗu se ta jefeta da mummunar kalma ta na hantarar ta,dake Sabriyah dinma fitsararriya ce bata raga mata bata shakkar fadawa Ammuh duk maganar da yazo bakinta, ummah kam dama tun lokacin da aka kawo Sabriyah gidan magana ko wani kallon banza be taɓa haɗa su ba.
Duk kayan da aka kawo mata haka ta zauna ta dinga reɗesu da almakashi tana rage musu tsayi, saboda bata saba sa kaya masu tsayi ba,in ta sakama takura mata yake yi.
A bangaren LTG Taj kuwa tun ranar da yasa major Marry ta fito da ita ya fara mata bincike,har yau bata sake sakashi a idonta ba, sede yasa major Marry ta ci-gaba da bincikar ta amma basa fahimtar juna ko kadan domin Sabriyah batajin turanci ita kuma major Marry batajin Hausa, wannan dalilin yasa Khalifa ya dawo shine me mata binciken, duk sanda aka tambayeta meye alaƙarta da Fu'ad amsar ta daya ne shine batasan akan wa suke magana ba.har izuwa yanzu kuma basu fasa binciken ba kuma itama bata canza amsar ta ba.

Washe gari around 12:00pm

Cikin shigar suit da ya ƙarbesa ya mishi kyau ya zo fita a falon,duk suna zaune sun maida hankalinsu kan cartoon din da suke kallo a system din Zoya,basu lura dashi ba har ya kusan fita ya tsinkayo muryan Parsa "ya Sahil in zaka dawo a siyo mini Teddy"hararanta ya yi "masoyiya yaushe na zama ɗan aikenki?"dariya Parsa ta yi,ta mike ta nufo inda yake tsaye,a jikin kofar ta tsaya ta rike handle din tana murdawa, kunyar haɗa ido ta keyi dashi a duk sanda take mishi magana.
"Kin yi shuru kuma wannan bakin ya nuna da akwai alamar magana a cikinsa!"ya yi maganar yana zura hannayensa cikin aljihun wandon suit din,ya zuba mata ido,jin idonshi ta yi yana yawo a jikinta daburcewa ta yi tama rasa meyasa ta taso daga inda take.
"Uhmmm.....ya Sahil teddy please,wanda ka siya min last time ya tsufa,and....and i want a new one"yanda take magana a shagwabe tana jan maganar hade da inda_inda da takeyi ne yabawa Sahil dariya,kallon Rolex wrist watch dinsa ya yi "masoyiya am getting late,bazan miki alkawarin zan siya miki ba,sede zan bawa security kudin ya siyo miki,is that fine for you!?".
Sosa wuya ta yi kafin ta gyada kai,"good girl "ya faɗa yana jan kumatunta sannan ya fita.ka sa komawa wajensu ta yi ta tsaya tana bin bayansa da kallo.
Ita kadai kuma ta rufe fuskarta da hannayenta tana dariya,kowa dake cikin gidan yawancin lokuta da masoyiya suke kiranta amma idan Sahil ya kirata da sunan masoyiya,har ranta take jin dadin sunan,, se taji babu wanda yakai shi iya kiran sunan nata.
Tana tsaye awajen bata san da isowar Salim ba kawai dafata taji anyi kallonsa ta yi tana murmushi,kallon inda ta ke kallo shima ya yi. murmushi ne ya subuce masa lokacin da ya hango bayan Sahil.
Ya riƙe kugu kamar wani mace"to in kina yiwa Sahil irin wannan kallon ai se ki sa ya yita tuntube,a dinga yin kallon kadan_kadan mana masoyiya".
Rufe fuska ta yi tana"ya Salim kabari banaso,zan haɗaka da Ammi"dariya kawai ya yi.
"Bye masoyiya take care"ya barta tsaye a wajen.
Bin bayansa ta yi tana murmushi,komai dinsu iri daya kamanin su ɗaya ainihin identical twins ne,ko kaya kala daya suke sawa sede color ya bambanta,yanzu ma haka Sahil yana sanye cikin Black suit a ya yinda Salim ke sanye cikin white color suit.
Su biyu din sana'ar su iri daya,yan kasuwa ne,matasan yan kasuwan da suke ji da kuɗi,da kuma kyau.

5:00pm dirin motocin LTG da tawagar sa suka diro cikin gidan,fitowa sukayi suka tsaya,bude mishi kofa Khalifa ya yi,yana fitowa suka sara mishi.woww Masha Allah yana sanye cikin full dress uniform,ya fito a ainihin Lieutenant general Tajuddeen Bishara,bakaramin kyau ya yi ba fuskarsa nan me razana marasa gaskiya yana nan a murtuke babu ko da ɗigon murmushi.
Kai tsaye cikin gida ya nufa.
Tunda ya shigo bedroom dinsa ya gane an shigo masa part.bayan shigarsa ciki kuma ya sa'ke tabbatar wanda ya shigon har yanzu yana ciki, be damu da ko waye a ciki ba ya cire uniform din jikinsa ya rage daga shi se short.
"Da alama na samu baƙon gawa"daukar bindiga ya yi,ya seta yana kara'kat!kat!kat'.
Fara bin ko wani dungu na dakin ya yi ,yana nuna bindigar kamar ze harba.
Sabriyah dake cikin labule tana kallon duk abinda yake yi,in hankalinta yakai million tofa se da ya tashi,ita kam ta gama sadakarwa yau mutuwa zatayi,nan take taji wani zawo yana kokarin zuba mata ga zufan dake yanko mata kamar an watsa mata ruwa,aranta kuwa se tsinewa umaisha da Rameesa takeyi buhu_buhu,domin ba dan su ba da babu abinda ze kawo ta part din wannan mugun. duk Wannan gurguwar shawaran su ne,inta tuna dalilin zuwan nata part din nasa ma se ta sa'ke tsine musu cikin kwando_kwando.wai suna son ganin yanda bindigar gaske yake su sede kullum su ta gani agurin Sudais ko kuma Jawan,se kuma major Marry ,suna haka shine Umaisha ta ce me ze hana suje part din LTG suyi video ainihin bindigar su dinga kallo,nan de suka yanke cewa Sabriyah ce zataje ta musu biyon,da farko ta ƙi amincewa amma dake sun fita yawa babu yanda ta iya haka ta amince,Zoya dariyar mugunta ta yi ta ce "Allah yasa LTG ya kamata a part dinshi kasheta ze yi da bindiga"haka suka rakata part din, su kuma suka dawo.

Yanzu de ga shi sun ja mata,karkarwa jikinta yake yi kamar mazari, musamman da taga ya dunfaro ta da bindiga.
Nan take hawaye ya fara wanke mata fuska tasan yau itakam se buzunta......

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹

Page 19 & 20

*_ story & written_*

By

*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️

*Kamar yanda kuka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kadan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi dan banason bata lokaci ina gama book one za'a daura da book two*
*Ga duk me son biya, littafin ASHE ZAMUGA JUNA naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu. Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 09024503194 Mrs isham.*

Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 2309617787 Fatima Abbas UBA BANK.duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min.

Page 19 & 20

Nan take hawaye ya fara wanke mata fuska tasan yau kam se buzunta,bata san wani tsautsayin bane yasa ta biyewa haukar su Umaisha.

Dunfaro inda take boye cikin labulen kamar wata mage,se mutsu_mutsu take yi,ta ka sa tsayawa waje daya,kwashe labulen ya yi, ya maida su gefe yana rike dashi a hannunsa.

Runtse idonta da har lokacin hawaye ne yake faman Zarya kamar an kunna gamfo,jin ya bude labulen da ta boye aciki.tsoronta daya kar ya fasa mata kai da bindiga.

Haɗe hannayenta waje guda ya yi, ya janyo ta tsakiyar dakin.
"Me ya kawo ki bedroom nawa!?"ya tambayeta calmly,yana kallon fuskarta.
Ido a rufe bakinta ya fara motsi,ta ma rasa menene abinda zata faɗa mishi ta wanke kanta, ko giyan wake tasha bata isa ta ce mishi bindigar sa ne tazo yiwa video ba.
Cikin sarkewan magana,irin na marasa gaskiya ta furta"dama banida lafiya ne,shine nake neman magani na ɗauka nan sashen ya Saghar ne".
Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita,hakan yasa kalma daya da ta faɗa be yarda dashi ba.
"Ayya!ka barni in fita ka ji!?"
Bindiga ya daura mata a kai, kamar ze harbeta ta kwala ihu.
"Wayyo na shiga uku na,dan Allah karka kasheni!, banason mutuwa yanzu,bazan ƙara shigo maka sashen ka ba"da iya karfinta take magana tana kuka jikinta gaba daya ya jike da zufa,ga cikinta se ƙa ra yake yi.
"Shut up "tsawan da ya daka mata wanda seda yan hanjinta suka ƙara tsurewa.

A bangaren su Rameesa kuwa tunda suka ji diran motocin LTG suka shiga tashin hankali sun san yanzu haka Sabriyah ta shiga hannu, duk jugum_jugum suka yi abin duniya ya damesu ga da_nasanin turata,jiki a sanyaye Parsa ta ce "ga shi kun ja mata,ni tun farko ban yarda da wannan shawarar ta ku ba,kunsan ya Taj no nonsense ne,yanzu ga shi abinda ya biyo baya".
Su de shuru suka mata dan basu da bakin magana.
Zoya ranta fes ko ajikinta se ma nishadin da take ciki na ganin LTG ya kama Sabriyah a part dinsa.
"Ni Wallahi hakan ya min dede, Allah yasa ya kakkaryata kowa ma ya huta, kunga gobe babu wacce zata sake yin gigin zuwa part dinsa in baya nan!, gaskiya na dade ban shiga farin ciki irin na yau ba".
Takaicin maganganun da Zoya ke faɗi ne yasa duk suka watsa mata harara.
"Ai ke kinyi a sara Zoya,yar uwarki mace na cikin wani hali shine ki ke farin ciki,meye ribarki in ya Taj ya mata wani abu!?,ke wannan mugun halin naki ne yake haɗa ni dake,yar iska kawai"cewar umaisha da ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci.
Rameesa da se yanzu ne ta samu bakin magana"kyaleta de mugun bakinki se ya dawo kanki".
"Can muku de yanzu kam "Zoya ta fada tana danna wayarta bata biye musu ba.
Chapter 36 · 0% Book details