← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 60

Sashe 49

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarai ya ga hararan da ta yi mishi amma dake yana da important issues da yakamata ya yi clearing dinsu ya sa be bi ta kanta ba,saboda yasan tunda ya ce bazata shiga ba to,babu yanda za'a yi ta shiga sede in taurin kan nata yana kusa.komawa sukayi daga ita har Parsa suka zauna.shi ma zaman ya yi akan kujerar dake facing na Abbie.
Ganin shi cikin uniform ne yasa Hajiya babba cewa"Tajuddeen ina zuwa haka".
"Zamu je wani dan karamin aiki ne".
Ta ce "Allah ya taimaka"ya amsa mata da"Ameen".
Kallon Ammi ya yi yaga idonta na kansa.
"Ammi zan fita".
"Allah ya taimaka yabaka nasara".
Har cikin ransa ya ji dadin wannan addu'ar da Ammin sa ta mishi,.ya amsa da"Ameen".

Kallon yan matan anty Sameera ta yi ta ce" to maza duk ku tashi muje a yi shopping,Sahil da Sudais ku tashi muje ku zaku kaimu".

Hajjatiye da fitowarta kenan ta ji tattaunawar da suke yi ta ce"kayya! dan Allah kwashesu kaf ki tafi dasu ni dama sun isheni,gwara su je su dede ta kansu a yi tuwona mai na".

Yar dariya kowa ya yi, Sahil ya ce"Tabb waya gaya miki Hajjatiye ni zan yi auren gida!?,ai ina da budurwata a kano to kuma me ze sanya ni in yi auren gida ". "Ah ah babu kam se ka kawo mana ita ai mu ganta"cewar Hajiya babba tana dariya domin duk sun fahimci ya yi hakan ne dan raha.

Tunda ya furta wannan maganar murmushi da walwalar dake kan fuskar Parsa ya dauke cak, idanunta suka cika da hawaye,zufa ya fara tsatssafowa wuyanta da goshinta, sunkuyar da kanta kasa ta yi bata san kowa ya fahimci halin da take ciki.ji tayi komai ya dena mata dad'i,kenan dama duk dakon soyayyan ya'yan nata da ta jima tana yi yana da budurwa ba ta sani ba?,duk da tasan ita kadai take san shi,be ma san tana yi ba shi kallon kanwa ya keyi mata,kuma babu wanda ya fahimci hakan a gaba daya ilahirin gidan se Salim,shine ya fahimci ta fadawa soyayyan dan uwanshi amma ko da ya fahimci hakan be sa ya nuna mata kan cewa yasan wani abu ba.

A duk lokacin da ta yanke shawarar taje ta samesa ta sanar dashi irin son da take mishi ko da Allah ze sa ta samu waje a cikin zuciyarsa,amma kunya da gwarjinin da yake mata se ya hanata tabuka komai.ga shi yau kunnenta ya jiyo mata abinda bata taɓa tunanin jin sa ba a wajensa,ashe ita haukanta kawai take yi.(hmmmm,ni ko nace matsalar soyayyar bari daya kenan ".

Salim da ya lura da yanda mood dinta ya sauya ne yasa ya ji wani iri a ransa, yarinyar da babu wanda ze ce ya taba ganinta a cikin wannan ɓacin ran,ko da yaushe murmushi dauke akan fuskarta se gashi yau ta kan abinda ya kasance ba gaskiya ba,ta shiga wani yanayi,yanke shawara ya yi ze samu Sahil din ya sanar da shi Parsa na matukar kaunar domin shi yafi kowa sanin babu wata mace a cikin rayuwa Sahil kawai yanxu ma ya faɗa ne saboda rashin sani da kuma raha.

LTG dake jin hiran na su ne ya ɗan yi tsaki,shi gani yake yi ja musu reni za'a a wajen wa'yannan kananun yaran.

"Ku tashi mu tafi ko,kar yamma ya yi, Sakeena zakije ne!?"ta tambayi anty sakeena dake magana da Hajjatiye,se kus_kus suke yi.
"No sekun dawo kawai"
Ta faɗa mata haka sannan suka ci gaba da maganar su.

"To Allah ya tsare ya kuma kare ku da karewarsa"can kasan makoshi ya amsa addu'ar da Abbie ya musu sannan ya mike ya fice,yana fitowa yaga rundunar sojojin sa shi kadai suke jira,duk a tare suka sara masa gyada musu kai ya yi Khalifa ya buɗe mishi ya shiga yana kokarin rufe motar major Marry ta fito ita ma cikin shirinta tana sanye da uniform.
Dasauri ta iso tana kokarin shiga.

Kallon ta ya yi irin kallon me kike kokarin yi din nan.
Ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta ce "Please LTG I want go along with you".
Cikin harshen turanci ya ce mata bazata je ko ina ba,se jikinta ya gama yin sauki.
Babu yanda ta iya tunda bazata tsaya jayayya da lieutenant general ba uban gidanta.
Ta na ganin su suka fita a gidan ko kadan ba ta ji dadi ba,raunin hannunta nan ne ya kwafsa mata saboda tana son ta ganta a bottle field ana fafatawa da ita.

Komawa ciki ta yi babu yanda ta iya haka take ta kwanta.

Fitowa packing space sukayi, Jawan, Sudais, Sahil suka fito da motocin su dan kai su kasuwa.
Jaleelah ce ta yi hanzarin zama a gaban motar tana murguɗawa Iftisan baƙi.
Kallonta Jawan ya yi,ya kuma ga hararan da Iftisan take yi mata.
"In kin gama neman tsokanar seki fito min a motar"tura baƙi ta yi can kasa _kasa ta ce "baza'a fito din ba".
"Rike kugu Jawan ya yi yana mamaki wato wannan rashin kunyan da ya sansu da shi musamman ma ita Jaleelah da tafi Iftisan sangarcewa yana nan.

Hannu yasa ya buge bakinta.kuka tasa ka tana kama bakinta, karasowa bakin motar anty Sameera ta yi jin kukan Jaleelah,kallon Jawan da kukan nata ko ajikinshi ta yi ta ce "meye kayi mata Jawan!?".
"Zagina ta yi shine na buge bakin"ya bata amsa yana yiwa Umaisha alamar ta zo da hannu.
Cikin kuka ta ce "Wallahi anty Sameera ni ban zage shi ba sharri ya min"hannu yasa ze sa'ke buge bakin anty Sameera ta yi saurin rikesa.
"Yi hakuri,kidena kukan.kai kuma Jawan ka kyaleta please".
Bude murfin motar ta yi ta ce "kuma,ma na fasa tafiyan".
Galla mata harara ya yi,ta shige da gudu tana kuka.
Dariya Iftisan ta yi taji dadin yanda Jawan ya yiwa bakin rashin kunyar Jaleelah.
Sabriyah motar Jawan ta shiga ita da anty Sameera da kuma Iftisan din.
Yayinda Umaisha,Zoya, Rameesa suka shiga motar Sudais.
Baya Iklas ta shiga,Parsa dake tsaye a bakin motar bata ma da niyar shiga,fuska a ɗan haɗe.
Kallonta Sahil ya yi "masoyiya zo shigo Mu tafi".
Maƙe kafada ta yi, ta ce "Iklas ki dawo gaba ni abaya zan zauna"with full surprise a fuskarsa yake kallonta,gani ya yi Kamar ba Masoyiya Parsa ba,da duk lokacin da zasu fita inde har dashi tofa tana gaban motar amma yau ita ce take yin tayin zaman gaban motar.
"Yau kuma!,nikam get in don't waste my time"sa'ke maƙe masa kafada ta yi a karo na biyu.
Da ya fuskanci dagaske ta ke ne yasa ya haɗa rai ya daka mata tsawa da yasa ta shige babu shiri.
"Za ki wuce ki shigo ne ko sena shigo dake da kaina!"zama ta yi fuskarta babu walwala,shima da yaga yanda ta yi kicin_kicin da rai ne yasa shima be bi ta kanta ba,duk da yana mamakin meye haka ya samu Parsa da yau ya ganta a haka.
Shi da Iklas ne suke ta hiransu,ita kam ko tari bata yi ba tunda ta shiga motar.

A motar Sudais ma su na nan suna ta surutu gaba daya sun cika wa Sudais kunne, musamman Umaisha an fi jin muryarta.
Juyowa da kansa ya yi ya watsa musu harara,ai babu shiri duk sukayi shuru.
Har aka isa shopping mall din babu wanda ya sake cewa komai.

Ciki suka shiga suka bar mazan suna waje suna jiran su.

Sosai sukayi wa Sabriyah da Asmita shopping kaya na ban mamaki masu yawan gaske da kuma tsada,kama daga kan kayan sawa,kayan make up, perfumes, shoes, bags,hijabs,gyale, jewelrys,sari(lufaya), shower items, lotions,duk wani abinda aka san mace zata yi amfani dashi seda aka siya musu,wajen pad suka je,anty Sameera ta fara ɗiba musu tana sawa a basket,daukan guda daya Sabriyah ta yi ta matsa kadan taji da laushi.
"Anty Sameera meye wannan din?, amfani me ake yi dashi?"anty Sameera ta ce mata "wannan din pad ne ,ana amfani dashi ne lokacin period".
Sa'ke je fa mata wata tambayar ta yi domin bata fahimci abinda take nufi da period da kuma pad ba.
"Anty Sameera su din meye su to"se yanzu ne anty Sameera ta kalleta da mamaki,dazun da ta mata tambayar menene pad ko kadan bata yi mamaki ba saboda wasu basa amfani dashi,da tsuma suke amfani shisa bata kawo komai a ranta ba.
Danne mamakinta ta yi,ta ce "idan kina al'ada da me kuke amfani ke da Asmita"nisawa ta yi kadan domin anty Sameera ta sa ta a duhu bata fahimci abinda ta ke nufi ba.
"Ban san me kike nufi ba anty Sameera"kallon yan matan ta yi taga babu wacce hankalinta yake kansu kowa tana ɗaukan abinda take so ne.
Ta jawota gefe kadan ta ce "Sabriyah idan karshen wata yazo,in kuna jinin al'ada da me kuke amfani!?", girgiza mata kai ta yi,kamar wata wawiya ta ce"jini?, karshe wata? ni haryanzu bangane ba jini aina!?",ta jefa mata tambayoyi uku at one time.
Jinjina kai anty Sameera ta yi wato de in ta fahimta Sabriyah na nufin ta ce mata,daga ita har Asmita babu wacce ta taɓa yin period a cikinsu,tunda ga shi bata ma san ni ba,ta yi mamaki sosai.ta ce zasu karasa maganar a gida.

Bangaren wayoyi suka je,nan Anty Sameera ta dauka musu waya iphone 12 normal su biyu ita da Asmita,irin na hannun su Umaisha.

Layi me register suka karba guda biyu.komai sun gama siya,an je wajen bill anty Sameera ta bayarda ATM guda daya.
Duk hankalinsu nakan wajen bill suna hira.

Ji ta yi an rike hannunta an cusa mata takarda a hannu da sauri ta juya dan ganin waye haka, bata iya ganin fuskarsa ba se bayansa yana tafiya harya yi nisa.
Kallon takardar ta yi kafin ta bude,suna ne a jiki da kuma number waya.suna an rubuta Fu'ad.
Amma bata iya karatu ba ɓalle ta fahimci sunan.
Chukuikuye takardar ta yi da niyar ya sarwa,se zuciyarta ta raya mata da ta kira number ta ji waye.sake kankame takardar a hannu ta yi tana mamakin to waye haka,kuma aina ya santa.

Yaran shopping mall din ne suka kwashi kayan suka kai musu zuwa motar.
Chapter 49 · 0% Book details