← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 60

Sashe 4

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun kafin anty amarya ta karaso Hajiya babba take watsawa Asrah dake goye abaya hararan wasa tana fadin " gaskiya Asrah kinji kunya, shame on you ahakan kikeso in aura miki ɗana Tajuddeen? Kin girma bakinsan kin girma ba no!no bazeyu ba , jibeki katuwa dake abayan mamanki gaskiya bazaki auri Tajuddeen ba" dariya Ammi da anty amarya sukayi banda Hajiya babba da ta danne nata dariyar ta koma serious face dan tasan yanzu zasu ɗibi adashen tsiya ita da Asrah.
Kokarin sauka tafarayi abayan anty amarya ta name kwabe fuska jin abinda Hajiya babba ta faɗa, sauketa ƙasa anty amarya tayi . Wajan Hajiya babba Asrah taje ta tsaya ajikin kujerar datake zaune, ido tabb da hawaye ta ce " adiya babba dan auri tajuju ko " girgiza mata kai ta yi ta ce" no bazaki aureshi ba ,cos he don't loves you" da karfi ta ce" he loves me " ta faɗa tana goge guntun hawayen idonta sannan ta ƙara da fadin " kuma ! Kuma seya aureni din " ta karishe maganar tana murguda dan karamin bakinta , tabe baki Hajiya babba ta yi ta ce" to ai se ya aurekin mugani " anty amarya de da Ammi yan kallo suka zama domin kuwa sun san mudin Asrah ta shaqa tofa gidan nan yau ba zaman lafiya dan rigimarta ma kadai seya hanasu bacci , saboda tasan me ake nufi da kalmar love duk da kananun shekarunta , tunda tashin turai ce. yara tun suna ƙanana zakaga wai sun san meye soyayya,shisaka duk ranar da akace Tajuddeen baya sonta ko kuma baze aureta ba tofa ranar akwai chakwakiya agidan.
Kuka tafarayi a hankali tana " tajuju loves me and we will get married tomorrow" bakaramin dariya Maganar ta yabasu ba hakan yasa suka sa dariya dukkan su harda Hajiya babba dake tsokanar nata , dariyar da taga sukeyi mata ne yasa ta sake hassala ta fashe da kuka da karfi .

Tun bayan rabuwar ta da anty amarya ta shiga part din Tajuddeen bude kofar bedroom din ta yi ta zuba mishi ido , yana kwance yabawa kofar baya.
idanunshi a rufe amma jikinshi yabashi ana kallon shi , murmushin mugunta Hajiya khareema ta yi aranta ta ce " Tajuddeen Mubarak Bishara kaida samun farin ciki arayuwarka sede bayan na mutu amma mudin ina raye , sena rabaka da kowa " cikin kissa da kisisina ta shigo bedroom din ta zauna a bakin gadon shi tasa hannu ta yaye bargon dayake rufe dashi " my son bacci kakeji ne ? gaskiya bazan barka ka kwanta haka ba, tashi ka zauna bari in sa akawo maka abinci ka ji?" tana magana hade da kallon fuskarshi da babu walwala a cikinta ,mikewa ya yi ya zauna yana facing dinta, riko hannunta ya yi murya akarye ya ce " Ammuh duk faɗin gidan nan ke kadaice kika damu dani kuma kika damu da damuwata, duk da ci miki mutunci da ake yi akaina amma hakan besa kindena sona ba" yana magana yana sauke ajiyar zuciya saboda be saba magana me tsayi ba , murmushin samun nasara ta yi kafin ta koma kalar tausayi kamar wata mutumiyar kirki ta ce" ɗana Tajuddeen, banida burin da yawuce inga yan uwanka da iyayenka sun fara sonka narasa wace iriyar tsana sukayi maka , karkaga laifina idan nace hakan yasamo asali ne daga wajan Amminka , ɗan da ace ta nuna maka soyayya dakuma janka ajikinta tofa da kowa ze so ka, amma ah ah ta fifita sauran yan uwanka akanka , kullum kokarina shine inga na nunawa Hajiya hamdiyya abinda takeyi bata kyautawa ita da Hajiya babba amma daga nafara faɗa musu gaskiya sesu fara zagina da cin mutuncin hade da faɗin ina ruwana dakai , nikuma wallahi Tajuddeen bazan iya juya baya akan rayuwarka ba. Allah ya samun sanka tun daga ranar da kazo duniya na mayar dakai ɗana" ta karishe magana tana hawayen munafurci tasaka gefen gyallenta ta goge hawayen, kallonta yakeyi cike da tausayawa saboda Tajuddeen shi gani yakeyi ita kadaice masoyiyarshi acikin gidan daga ita se anty amarya se kuma Asrah da ya mayar da ita wani bangare na rayuwarshi.
Ci gaba ta yi da magana tana nuna mishi hannunta da ya gurje lokacin da anty amarya ta hankaɗata ta fa di ƙasa ashe ta gurje a hannu , yana fitar da jini kadan_kadan dake farar macece se wajan yayi jawur " kaduba ka ga abinda Amminka dakuma Abida suka aikata agareni" rai abace ya ce " Ammi ce tayi miki haka ita da anty amarya?" Cikin salon makirci ta ce" su sukamin haka Tajuddeen saboda naje nasamesu inayi musu magana akanka ,shine sukamin koran kare danaƙi tafiya kuma shine su biyun suka tureni nafadi aƙasa.
Amma bawai na faɗa maka hakan ɗan in tayar maka da hankali bane kokuma in shiga tsakaninka dasu ba kayi hakuri karka musu magana ,in sha Allah wata rana se labari komai ze wuce ." Tana magana ne hade da satan kallonshi ta ƙasan ido .

Tunda ta fara magana yake kallonta jikinshi duk ya yi sanyi jin wai ta dalilinshi akayi mata hakan lumshe idanunshi yayi ya makasa cewa komai saboda shi ba ma'abocin so da kuma yin dogon magana bane,shisa yarasa wata kalma zeyi amfani wajan bata hakuri akan abinda Ammi da anty amarya suka mata , kamar yanda ta faɗa .

Mikewa ya yi slowly yanufi toilet ze dauko first aidbox domin yayi mata treatment din ciwon da taji . Ya riko first aidbox Yana kokarin fitowa yaji kamar kukan Asrah dinshi, ka sa kunne ya yi dan ya tabbatar shin dagaske ita ce din take kuka ko kuwa, sake ji yayi hakan ya tabbatar mishi da antabo mishi Asrah fitowa yayi daga toilet din da sauri batare da ya dauko first aidbox din ba ɗan hankalinshi ya koma kan Asrah da take kuka , be ko kalli inda Hajiya khareema ke zaune ba yanufi hanyar barin bedroom din.
da mamaki take binshi da kallo ganin irin saurin da ya keyi kamar wanda ze tashi sama ,yana daff da barin bedroom din ya tsinkayo muryanta ,tana fadin " son saurin me kake yi haka " amsa yabata da" kukan Asrah naji shine zanje in daukota " beko jira abinda zata faɗi ba ya fice , afusace ta ce " bazeyuba dole in fara ka war da Asrah domin ita ce zata hanani cika burina akan wannan yaro saboda ba karamin so yake mata ba ,in banyi wasa bama zata iya wargaza min aikina danayi shekara da shekaru inayi . Dole indau mataki akanta" ta faɗa tana huci.

Comments, share and like 🥰🥰

Share fisabilillahi

🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹

*Story & written*

By

MRS🌹ISHAM🌹
( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹

📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️

Page 04

" Se tajuju ya aureni ! se munyi aure ! and we love each other" kalmomin da tadinga faɗa kenan tana kuka , tun suna mata dariya har suka koma lallashinta ƙin sauraransu ta yi , ta ci gaba da kukanta jikinta har rawa yakeyi lokaci daya ta haɗa zufa saboda kuka , daukanta Hajiya babba ta yi ta daurata akan cinyarta tana lallashinta amma sam taki shiru.
Abbie, Abbu , uncle Hameed suna zaune suna tattaunawa suka ji ihun kukan Asrah dafe goshi uncle Hameed ya yi. murmushi Abbie ya yi ya ce" to yanzu kuma wa ya taɓo wannan rigimammiyar " ya faɗa yana mikewa yar dariya sukayi su ma suname bin bayanshi , su iklas dasu Abbas duk suna part din Hajiya babba gaba dayansu , yaran matan sun duƙufa suna homework Hafiz na gyara musu in basuyi dede ba , saghar tun da suka shigo be kula kowa ba ɗan har iya zuwa lokacin fushi yakeyi ,yakoma gefe aranshi kuwa yana aiyana irin mugun dukan dazewa Asrah aduk lokacin da Tajuddeen yatafi U.S.A , idan ya tuna Tajuddeen zeyi nesa dasu ne yake jin ranshi nayi mishi sanyi ɗan hakan ne ze bashi damar cin zalin Asrah yanda yaga dama.
Kukan Asrah suka faraji da rigimarta kallon juna Abbas da Ahmad sukayi sukasa dariya , Ahmad ya ce" tabb dijam ! Yau anya zamu yi bacci kuwa? gaskiya Asrah akwai shegen rigima " " ni wallahi kukan yara dagamin hankali yakeyi , Allah de yasa Tajuddeen na gida , ɗan kuwa inde baya nan banajin akwai wanda zesa yarinyar nan ta yi shuru" cewar Abbas .
Dogon tsaki saghar yaja ahassale ya ce " wannan iskancin da yarinyar nan takeyi guri ta samu ,aikin banza " ya mike yabar musu part din,girgiza kai kawai Hafiz ya yi bece komai ba.

" zoya,parsa,umaisha,rameesa kuzo muje gurin Asrah kunji tana kuka ko " cewar iklas da ta mike tana jiran sauran yan uwan nata su tashi suje, mikewa sukayi su ma suna kokarin tafiya, daka musu tsawa sahil ya yi ya ce" common ku zauna babu inda zakuje, ta yi kukan jini ma ina ruwanku " duk tsilli_tsilli sukayi da ido kamar wasu marasa gaskiya, basu zauna ba kuma basu tafi ba . sake daka musu tsawa ya yi yana kokarin mikewa suka zura aguje sukayi part din Tajuddeen ɗan saboda suna kyautata zaton Asrah na can.
Kwafa sahil ya yi ya ce" zamu haɗu ai duk senayi maganin ku " Abbas, Ahmad,Hafiz de basu ce musu komai ba karshema tashi sukayi suka bi bayansu parsa zuwa part din Tajuddeen din.
Chapter 4 · 0% Book details