← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 60

Sashe 35

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sabriyah kin ka sa sakin jikin ki damu,kingan mu nan ko kadan bamu da matsala Please ki saki jiki,mu zama Kamar yan uwa"Umaisha ta gama magana tana riƙe hannun Sabriyah, kamar zatayi kuka ta ce"kaina ciwo ya ke,bazan iya fita ba"
"Ayyah sorry my dear Allah ya ƙara sauki bari inje part din ya Saghar in dubo miki medicine"Iklas ta faɗa tana fita daga dakin dan zuwa part din Saghar dubo mata maganin.
Zama sukayi tare da ita suna dan magana sama_sama,ba su san hakan damun Sabriyah yake yi ba,bazasu taɓa gane halin da take ciki ba ,gani take su basu da wata matsalar komai din su yana tafiya dede a rayuwarsu,amma ita daga lokacin da tasan kanta ta fara gwagwarmayar rayuwa komai sede ta yiwa kanta,da Asmita harta rawan da takeyi tana yine dan su dinga samun abinda zasu ci,da kuma abinda zasu sawa jikinsu, lokacin da Anty Teema ta fara jinyan cutar ƙanjamau nan ne nauyin ya sake ninkuwa mata, maganin Anty Teema duk yana kanta,haka take damfaran maza domin ta biya musu bukatunsu na yau da kullum,domin Asmita rawa kawai take yi wani lokacin ma bayi takeyi ba,saboda bataso .sede Sabriyah ta wakilce ta.
Musamman Asmita da take da babban ciwo a rayuwarta wanda inde bata cika wannan buri nata ba na watsawa Mamman kudin da kullum shine maganarta, har ya zamana wannan shine mafarkin da in ta kwanta barci se ta yisa,ga kuma shaye_shaye da take son mayar dashi jiki a wajenta.
Gaba daya bata san jin dadi ba daga wannan se wannan ga shi ita kanta ba isheshen lafiya ne da ita ba,ciwon nimoniya dinta in ya tashi kamar zata mutu.
Tagumi ta yi kawai ta zuba musu ido bawai dan tana fahimtar su ba, ankara da ita Rameesa ta yi "yan mata ya da tagumi".
"Hmmm!bazaku gane bane,babu bukatar sanar da ku". Sabriyah ta bata amsa tana cire tagumin.
"Sede in ba ki faɗa mana ba amma zamu gane..."cewar Iklas da ta shigo hannunta riƙe da sudrex da kuma glass of water.
Karba Sabriyah ta yi badan taso ba tasha ta kwanta ta juya musu baya kamar bacci zatayi saboda tana so su dan ba ta guri,ga breziyar a hannunta taki ajiye wa.
"To iyayen shegen surutu let's leave her alone to rest"cewar umaisha,gyada kai suka yi sannan suka fice.

Se da ta tabbatar da sun fice sannan ta mike ta garkame kofar da key ta dawo ta zauna tana buɗe zip din breziyar nata,sannan ta fito da memory card din ,ganin yana nan ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana "yauwwa,yana nan".mayar dashi cikin breziyar, ta wurga breziyar kasan gadon domin gani take yi se yafi samun tsaro a wajen.kwanciya ta yi tana jin ranta duk babu dad'i,mutane uku ne suka tsaya mata arai da bata san halin da suke ciki ba,mutum na farko farin cikin ranta wato Asmita na biyu kuma anty Teema,mutum na uku kuwa shine Fu'ad tana son sanin yana ina kuma meyasa wa'yannan mutane suke farautar rayuwarsa.aranta ta ce"Allah sarki Fu'ad kai din mutumin kirki ne Allah ya tsare ka da sharrin wannan mugun".

Haka ta dinga saka da warwara tana kwance,har bacci barawo ya yi awon gaba da ita.

Duk wani abinda takeyi,yana zaune ya yi relex a cikin dakin binciken dake cikin part dinsa yana kallon ta yana shan coffee cikin kasaita, murmushi ne ya subuce akan kyawawan libs din shi.ganin in da ta wurga breziyar na ta, kwantar da kansa akan kujerar da yake zaune ya fara juyawa dashi ahankali_hankali.
wato shi wannan yarinyar zata gwadawa wayo,shi da ya dauki tsawon shekaru goma yana karatun bincike da kuma karantar mutane da sauran abubuwa shine zata gwada masa tana da wayo.shafa lallausar sumar kanshi da ke da yawa ya yi,sumar ne ya shige cikin ɗan karamin ɓulin dake cikin abin hannunsa,da dabara ya shiresa, ya dawo da hannun fuskarsa yana kallon abin hannun nasa,kasa janye idanunsa yai akan abin hannun,ya daura hannun akan kirjinsa yana lumshe sexy golding eyes dinsa yana jin wani nutsuwa na shigarsa ta ko ina.
A lokacin da yake USA ko da yaushe cikin binciken Asrah yake ba ji ba gani ta dalilin nan ne ma yasa ya gagara dawuwa Nigeria,seda binciken nan ya dawo hannunsa ya dawo.
Amma a yan kwanakin nan yana mamakin kansa da ya dena neman inda Asrah take ,domin yana jin kusancinsa tare da ita,ji yake yi kamar yana a tare da ita,tunda ya shigo Nigeria yakejin wani kwanciyar hankali da nutsuwa.
Ajiyar zuciya ya yi wanda ya fito da sunanta"Asrahhhhh...".
Tunaninta ya fara lokacin da take yar karama da ita,wani wurin in ya tuna ya ɗan girgiza kai wani wurin kuma ya ɗan sa'ki yar karamar murmushi.
"My little stubborn girl!am feeling your presence in everywhere".
Yana gama faɗar haka ya mike cike da jarumta ya fice daga dakin binciken ya koma bedroom dinsa,ko minti biyar be kai da zama ba kira ya shigo cikin wayarsa be yi picking ba,seda wani kiran ya sa'ke shigowa, mika daguwar kyakkyawar hannunsa kan filo ya ɗauki wayar.
se da ya kusa katsewa kafin ya daga yasa a handsfree"assalamualaikum! Tajuddeen fatan kuna lafiya!?".
"Alhamdulillah! Abbu ya aiki?"
A bangaren Abbu dake kusa da Abbie shima wayar a handsfree yake,"Alhamdulillah mun gama duk wani abinda yakaimu, we're expecting to be back within next week in sha Allah".
"That's good,ina Abbie my regards to him, tell him I missed his jokes and ......"kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin bakinsa ya gaji da maganar saboda ta yi tsayi sosai bayan haka kuma yau ya yi magana me ɗan yawa....
Daga can bangaren su jin ya carke yasa suka fahimci cewa ya gagara karasawa ne,saboda da gajiyar da ya yi.
Abbie ne ya karbi wayar"Son don't stress your self!you need to rest,inna dawo zan koya maka doguwar magana okay?".
"Uhmmmm"kawai LTG ya ce sannan ya hanging phone din.

"Kaga wani ikon Allah ko Isma'il!?,yanzu har Tajuddeen ne ze iya wannan maganar lallai nasha mamaki'.cewar Abbie,yana faɗawa Abbu.
"In sha Allah addu'ar mu na tare dashi babu wani mugun mutum ko aljani da zeyi nasara wajen ruguza rayuwarsa, ba ma shi kadai ba duka yaran namu".
"In sha Allahu!da yardar Ubangiji", Abbie ya yi maganar yana kiran number Ammi.

Ammi dake zaune akan gadon ta tana gyaran farcenta ne taga kiran Abbie ya shigo da sauri ta daga tana murmushi.
"Sarauniyata fatan kina cikin koshin lafiya!?". dariya Ammi ta yi tana jin farin ciki na mamaye ta har cikin ranta, duk da yanzu sun manyanta amma hakan be hana Abbie kiranta da sunaye masu dad'i ba sede in suna gaban ƴaƴansu ne.
"Lafiya klau alhmdllh,ya aiki ya abbu duk kuna lafiya?".gaisawa sukayi da juna kafin ta bashi labarin yarinyar da LTG ya ɗauko,shima Abbie ya yi mamaki duk da,basu san meye dalilin sa ba, amma yana addu'ar Allah yasa alkairi ne.
Sosai suka sha hira kafin ya sanar da ita sun kusa dawuwa.a haka sukayi sallama.

"Hajiya khareema!ina so ki faɗa mini meye kike nufi dani tunda burukan ki suka fara cika,kika yasar dani agefe wato amfani na ya ƙare ko!?,na gama miki amfani shine za ki cire ni daga lamarin ki.bari kiji in faɗa miki Wallahi muddin kikayi tunanin yi mini butulci tofa zan tona mana asiri kowa ma yasan abinda ya faru tunda kince ke butulu ce"cike da ɓacin rai ummah ta ke faɗawa Ammuh maganganu,ita kuma zaune take tana kallon ta hankalinta kwance.
"Am sorry Hajiya hurairah,bawai na cireki a kan wannan shirin bane,ko dan saboda kin gama mini amfani, ah ah!na ɗan janye jiki dake ne saboda na lura Abida tafara zargin akwai wani abu tsakaninmu ko kuma muna da wani manufa.to wannan ne yasa nafara nunawa kamar bama shiri sosai, amma ke kin sani,kinsan yanda nakeji dake,kece ginshikin wannan aikin namu.kiyi hakuri kin ji?".se a sannan ne ta ji hankalinta ya kwanta,yanda Ammuh ta cireta a plans din ne yasa ta fara shirya yanda zata tona musu a siri.
"Se yanzu naji hankalina ya kwanta, yanzu aina muka kwana".
"Ko kefa Hajiya Huraira abinda nakeson ji kenan,yanzu shirina na gaba shine dawo da Tajuddeen karkashin ikona,zan haɗa shi aure da yar autarmu,Naziya, Wannan shine shirin gaba".
Murmushi ummah ta yi"kina ganin Naziya zata iya janyo hankalin Tajuddeen!?".wani shegen murmushi Ammuh ta yi"Naziya is a very innocent and kindhearted girl,da ita zanyi amfani ".
Suna tsaka da tattaunawa Tajuddeen ya shigo part din,shuru sukayi suna tunanin kode ya ji tattaunawar da suke yi,tsayawa ya yi a kusa da Ammuh"Ammuh! i need fryed egg"
"To ɗana bari in soya maka"ta faɗa tana mikewa ta nufi kitchen ummah kuma ta fice daga part din.

Zaune take a kan kujerar karfe, an haɗe hannunta da ƙafafunta an daure a jikin kujerar ga bakinta manne da gam,gashin kanta duk ya hautsine kallo ɗaya zaka mata kasan cewa bata cikin hayyacinta musamman yanda idanunta suka gagara tsayawa guri daya bata iya rufesu haka kuma bata iya buɗesu.
Cikin wani ɗan karamin daki madaidaici babu komai acikin dakin se kayan karafuna,ko fulasta babu acikin daki ɓalle kuma fenti.
Wasu ƙartan maza ne masu ji da karfi suka shigo dakin kallonta sukayi suka ga haryanzu bata dawo hayyacinta ba.
"Yarinyar nan fah ta ƙi faɗan inda ta ajiye memory nan,dole mu sa'ke shaƙa mata cocaine din nan ko zata yi magana".
Cikin takaici dayan ya mishi kallon banza"Samuel kai wani irin mugu ne kam,ita din fa macece ba wai na miji ba,yau kwana biyu kenan safe da yamma kullum se an shaƙa mata haba abin ya yi yawa ze iya mayar da ita mahaukaciya".
"Yeeeeeeeh!tahhh shut up you dey craze? kana son mu a kashe mu kenan?, wannan yarinyar dole ta yi magana in ta ƙi kuma tabar duniya".
Shide be ce mishi komai ba yasa hannu ya ɓare mata gam din bakinta.
Kamar me koyan magana tana hado kalmomi dakyar ta iya furta"sab......ri..........yah......"
Oho sude basu fahimci me take cewa ba,suka sake rufe mata baki suka barta.
Fita sukayi a wajen,aka barta ita daya a dakin.

After one week
Chapter 35 · 0% Book details