← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 60

Sashe 3

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatawa da danna wayar da Tajuddin yakeyi ya yi ya dago ahankali da shanyayyun idanunshi da se yanzu ne cikinsu suka samu damar fitowa saboda maida facing cap din kanshi baya dayayi manyan idanunshi da eyeballs din suka kasance golden color ne yasaukesu akan anty amarya yafi tsawon minti biyu yana kallonta batare da yace wani abu ba sema lumshe idon da ya yi kafin da narƙekkiyar muryanshi ya ce " anty amarya koda danni kika dafa bazanci ba ki dauka kibawa yar uwarki kawai , and please zaki iya ce mata tafita min a part dina" wannan kalmar da Tajuddin yayi bakaramin girgiza zuciyar anty amarya yayi ba jin yanda Tajuddin yake furta magana kamar Ammi ba ita ce ta haifeshi ba , dukda ba wannan ce rana ta farko ba kuma irin wa'yannan kalaman sun saba dajinsa abakin Tajuddin amma hakan be mata dadi ba, ammi kam dakyar ta iya danne kuncin zuciyarta tafice tabar musu part din bin bayanta Asrah tayi tana " Ammi ki daukeni " tsayawa tayi ta dauki Asrah din suka fice a part din nashi .

Zama kusa dashi anty amarya tayi kamar yanda ta saba ta kalleshi dakyau ta bude baki zatayi magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana " Please anty amarya not again na gaji da jin wa'yannan kalaman naki akan yar uwarki bana bukatar ji " ajiyar zuciya anty amarya tasauke sannan tace " Taj dole sena fada maka gaskiya abinda kakeyi sam be dace ba duk abinda yahaɗaka da Ammi karka manta fa ita ce ta haife ka ko bakomai taci darajan mahaifiya domin ita ce sanadiyyar zuwanka duniya! wallahi Ammi na sanka dan Allah kamanta da komai kadena daurawa kanka damuwa tun kana ɗan karamin ka dakai Please my Taj " tunda tafara magana yake gyada kai kamar wanda yayi na'am da maganar nata jin tayi shuru ne yasa ya ce " kaina ciwo yakeyi i need to rest " yana gama fadar haka kuwa ya kwanta abinshi yabarta a zaune tana binshi da ido, mikewa ta yi ta fita adakin ɗan ta lura bayason ana dauko mishi maganar Ammi kwata_kwata amma itade bazata taba hakura ba seta shirya tsakanin yar uwarta da ɗanta.

Seda ya tabbatar da tafice a part din gaba daya sannan ya mike zaune yana jingina jikinshi a makeken gadonshi , shi da zasu gane da sun dena shiga harkanshi ɗan ba son magana yake yi dasu ba, shisa yake son yasamu addimission din nan yafito yatafi yayi nesa dasu ko zesamu nutsuwa baya kaunar yanda suke dauko mishi maganar Ammi , yafison yanda yadauko rayuwar shi yakare ta ahaka. haka yadinga tunani iri_iri dayan zuciyarshi ta ce mishi to inka tafi ya kake tunanin Asrah zataji ? ahankali yafurta ko ɗan ita zandawo bayan shekara goma zandawo in aureta sannan indauketa muje muyi rayuwar batare da sun addabi rayuwata .

Ammi dakyar ta iya kawo kanta babban falo ta zauna zuciyar ta na radadi hade da ɗaci ,danasani fal acikin zuciyarta abinda yafaru shekaru sha bakwai ne yafara dawo mata ƙwaƙwalwarta datasan hakan ze dawo mata babban firgice da ta rungumi ƙaddararta da tasan zata haifi abin cikin nata kuma tazo tana mugun kaunarsa dabatayi wannan kuskuren ba. tunani tafara tayanda zata shawo kan Tajuddin ya yafe mata se wata zuciyar ta ce mata karfa ki manta bawai laifi daya ne kikayiwa Tajuddin ba ,manyan laifi guda biyu kikayi mishi ta ina za ki fara neman afuwarsa? Sosai jikin Ammi yayi sanyi se saƙa da warwara takeyi , shigowa falon Hajiya badiyya tayi tundaga nesa data hangi Ammi tasan akwai abinda ke damunta zama tayi kusa da ita,tsabar yanda Ammi tayi nisa cikin tunani batasan ta shigo falon ba, taɓata Hajiya badiyya tayi ta ce " Hajiya hamdiyya lafiya naganki cikin damuwa? ko dayake nasan be wuce tsakanin ki da Tajuddin ba " kallonta Ammi tayi ta ce " Hajiya babba wallahi bansan yazanyi in shawo kan Tajuddin ba, abu ne me matukar wuya " ta kare maganar tana zare medicated glass din idonta tana fuskantar kishiyarta ta, ɗan nisawa Hajiya badiyya tayi ta ce " kuskure an rigada anyishi amma duk da hakan kema danaki laifin duk wani ɗa yana bukatar mahaifiyar shi ta jawoshi ajikinta amma Tajuddin be samu haka daga gareki ba ga laifin da kikaso tabkawa tun kafin yazo duniya bayan wannan kinsake yin wani laifin da haryanzu Taj dashi yake kallon ki. Hajiya hamdiyya ke Mahaifiyarsa ce haryanzu kinada damar da zakije ki neme afuwarshi nasan Taj yanada zuciya me kyau idan kikayi mishi bayanin komai dakuma dalilin haka nasan ze fahimceki , kiduba kiga yaron nan tunyanzu yanaso yarikoɗe yakoma boss wannan dalilin ne yasa Abbie dinsu yake tsoron zuwanshi makarantar sojoji domin a yanzu ma ya'ya? Ya muka ƙare da Taj inaga yatafi yaje yayi shekara goma yana daukan horon sojoji. tun kafin yasa ƙafa yabar kasar nan Yakamata muyi kokarin sassauto mishi da zuciyar shi yayi sanyi yasan kedin uwarshi ce bawai maƙiyarshi bace domin khareema tarigada data gama poisoning zuciyarshi da tsanarmu , har kullum cigaba da cusa mishi ƙiyayyar yan uwanshi da iyayenshi takeyi " tunda Hajiya badiyya tafara magana Ammi ta mayar da hankalinta gaba daya kanta domin maganar ta hakane dolene tasan hanyar da zata ƙwato ɗanta daga sharrin Hajiya khareema domin tanason juyawa Taj ne tunaninshi akansu bude baki tayi zatayi magana sega Hajiya khareema tafito tana nufo inda suke, tsayawa tayi akansu ta riƙe kugu ta ce " naji kamar gulmata kukeyi to adeji tsoron Allah adena gulma da munafurci in an girma asan an girma , duk wani kulle_kullen dakuke kullawa agidan nan ina sane daku yanzu muka fara muzuba mugani kaff senayi maganin ku" tana magana tana kallon Asrah dake wasa acan gefen su mugun kallo ta watsa mata cike da tsananin tsana , Hajiya babba da Ammi de acikinsu babu wanda ya kulata balle tacigaba dayi musu rashin kunya hakan yasa taja doguwar tsaki tayi gaba tana kokarin shiga part din Taj.
Girgiza kai kawai Ammi da Hajiya babba sukayi kafin sukaci gaba da tattaunawar dasukeyi.

Tana daf da zata shiga part din Taj ta hango anty amarya tafito malalacin murmushi ta sake da ita kadai tasan ma'anarshi , ka war da kai anty amarya tayi kamar bata gantaba , bangaje anty amarya Hajiya khareema tayi dayasa saura kadan ta fadi , sannan tayi gaba abinta kamar babu abinda tayi .
afusace anty amarya tabi bayanta tasa hannu ta jawo hannun rigarta ta dawo baya sannan itama ta hankaɗeta ta fadi ƙasa warwas kafin ta nunata da yatsa " wallahi khareema ki shiga taitayinki dani acikin gidan nan karki ga idan kinayiwa su yaya suna ƙyaleki ni to bazanyi shuru kice za ki takani ba , ah ah baki isa ba munafukar banza munafukar hofi" yanda anty amarya take magana ranta amatukar ɓace ya isa yanuna kancewa tabbas akwai babbar yar tsama a tsakaninsu.dafa kujeran dake kusa da ita tayi ta mike ta ce....

Comments, like and share for more...

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

*_Story & written_*

By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

Page 03

Da fa kujerar dake gefenta ta yi ta mike ta ce " Abida kenan , duk wani kule_kulen munafurcin da kuke yi dake da wancan munafukar ya'yar ta ki Hajiya hamdiyya dakuma ɗayar munafukar taku Hajiya badeeya ina sane daku kuma nafi karfinku , karkuyi tunanin zan zuba muku ido , ina nan ina bin duk wani takun ku !" Magana takeyiwa anty amarya hade da makirar murmushi dauke akan fuskarta,anty amarya kuwa binta kawai takeyi da kallon tsana saboda duk duniya babu irin mutumin da ta tsana sama da munafiki kuma makiri.
Batare da anty amarya ta ce mata komai ba ta juya tana kokarin barin wurin riko hannunta Hajiya khareema tayi tazo dede kunnenta tafurta mata " hankalina baze taba kwanciya ba sena raba ku da Tajuddeen sannan kuma in mai dashi karkashin ikona se yanda nayi dashi bayan hakan ya faru kuma zan raba shi da farin cikin rayuwa . wannan alkawari ne dani Hajiya khareema na daukawa kaina " tana gama fadin hakan tasaki hannun anty amarya ta wuce tabarta awajan ta shige part din Tajuddeen, kamar wacce aka shuka awajen anty amarya ta ka sa koda kwakkwaran motsi kirjinta se bugawa yakeyi da karfi domin kuwa ba ta raba dayan biyu tasan abinda Hajiya khareema ta faɗa tabbas zata aikata, saboda tun farko ita ce ainihin musabbabin cusa ƙiyayyar kowa acikin zuciyar Tajuddeen aciki kuwa harda Ammi.
"Ya Allah ka shiga tsakaninmu da wannan makirar baiwar ta ka da ta shigo rayuwarmu da muguwar nufi , Allah karka ba ta Sa'a akanmu ." Anty amarya ta yi maganar azuciyarta jiki asanyaye.
ji ta yi an rike hannunta tasan ba kowa bace fa ce Asrah , kai dubanta ta yi zuwa kanta , ƙakulo murmushin dole ta yi ta sawa fuskanta ta tsuguna agaban Asrah ta ce " Asrah din mommynta ya akayi har kingama wasan naki ne ?" Ganin ta tsuguna ne yasa Asrah zagayawa ta hau bayan anty amarya,
ta ce" mommyna ki goyeni muje gun daddy " tashi anty amarya ta yi da Asrah din dauke a gadon bayanta suka isa falo anan ta iske Ammi ( Hajiya hamdiyya ) da kuma Hajiya babba ( Hajiya badeeya ) suna tattaunawa.
Chapter 3 · 0% Book details