Sashe 14
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Napep malam Mamman ya tara suka shiga ciki ya fadmɗawa me napep inda ze kaisu , tafiya suka yi me matukar nisa da seda yasa Asmita ta gaji ta kwanta ajikinshi har bacci ya fara daukanta taji napep din ya tsaya fitowa ya yi da ita ya sallami dan adedeta sahun ya yi tafiyarsa , wata dankareriyar bakar jeep yanufa yana rike da hannun Asmita lokacin da ya iso motar kwankwasa gilashin ya yi aka sauke wasu murɗa_murɗan maza nagani zaune aciki fuskar su babu alamar imani , malam Mamman jiki na rawa ya ce" yawwa ga yarinyar na kawo muku ita seku ban sauran cikon kudin nata " fitowa daya daga cikinsu ya yi. ya karbi Asmita a hannun malam Mamman tirjewa tafarayi tana kallon babanta agaban idonta aka fito da kudin da suka kai kimanin naira dubu dari biyar aka ba shi, wanda yake zaune acikin motar ya ce" da farko mun baka dubu ɗari biyu yanzu ga cikon saura nan du ka yakama ka siyar mana da yarinyar dubu ɗari bakwai kenan " hannu na ɓari yakarbi kudin yana " eh hakane ranka ya dade Nagode sosai" sa Asmita sukayi a motar suka zuge gilas din motar tana kuka kamar ranta se fita ko ajikinsu suka ja motar suka tafi , se da sukayi nisa da suka ga kukan nata ze damesu suka shaka mata wani abu a hanci nan take bacci ya kwashe ta. ( kai rayuwa abin tsoro ne Allah karabamu da sharrin zuciya. )
Hankali kwance malam Mamman ya koma gida seda yakusan isa gidan tukun ya zuba kasa a jikinshi ya yi futu_futu yakoma kalar tausayi ya shiga gida abakin kofa yasamu Maryam ta doka uban tagumi tana jiransu ganin ya shigo shi kadai ne yasa ta mike tsaye dasauri ta ce" malam har kundawo ? yana ganka kai ɗaya ina Asmita?" Goge guntun hawaye ya yi ya ce" Maryamata munje munkai dinki mun fito zamu dawo taga yar baby ta ce ina siya mata acikin rububin mutane na nemi Asmita na rasa neman duniyar nan na mata amma ban gantaba" kukan kura Maryam ta yi ta cukumi wuyan malam Mamman" karya kakeyi dan iska munafuki mara tsoron Allah wallahi seka fito min da ƴata dama tunda naga ka fara son yarinyar nan zuciya ta ya rayamin wani abu mugu azzalumi kaje ka salwantar min da rayuwar yarinya " duk wannan maganar da takeyi da karfi takeyi tana kuka kuma tana damke da wuyan malam Mamman da iya karfinta, makobtansu jin hayaniya ya yi yawa yasa suka shigo , matan ne sukaje suka samu suka raba Maryam ajikin malam Mamman faduwa kasa ta yi tana kuka da birgima abin tausayi wannan zafin uwa ce kadai zatasan zafinshi in aka rabata da ɗanta .
Ɗagata sukayi suka kaita ɗaki suna tambayar ta abinda yafaru dakyar ta isa sanar musu su kansu hankalinsu yatashi nan take aka bazu aka fara neman Asmita hade da yin shela acikin garin damaturu.
*MAIDUGURI*
Suna dawuwa gida ko part dinsu bataje ba ta nufi part din Tajuddeen , ya fito daga painting room kenan ya ji an rungumeshi durƙusawa ya yi ya iso tsayinta yana ƙare mata kallo sosai ta yi kyau da uniform din slice smile ya yi ya ce" kinyi kyau" fari ta yi da ido ta rike kugu ta ce " tajujuna let's go and play on the field" be bata amsa ba yaje jikin bedside locker ya ɗauko wata hadaddiyar camera hoto yake so ya yi mata saboda uniform din sunyi matukar yi mata kyau sosai ɗaukanta a hoto yafara se iyayi take zuba mishi shi kuma yana snapping dinta se da ya gaji dan kanshi kafin ya ce" okay go and take up your uniform" tanajin haka ta fita da gudu zuwa part dinsu. uncle Hameed na kokarin fita yaci karo da ita " Asrah har kun dawo ?" Gyada mishi kai ta yi sannan ta ce" Daddy ka ciremin uniform dina zamuyi wasa da tajujuna " janta ya yi bakin kujera ya zauna ya ajiye wayoyin hannunshi ya cire mata uniform din sannan ya dauketa yaje ya mata wanka yasa mata kaya marasa nauyi ya ce " to adawo lafiya" tun be karasa cewa komai ba tafita da gudu tana mishi bye-bye murmushi ya yi sannan ya koma ya canza kayanshi dan ruwa yaɗan taɓa shi da ya mata wanka.
Wasa sukeyi a field din dagashi se ita yana koya mata gudu tun tana iya yi harta gaji tana zauna a tsakiyar filin tana turbune fuskanta daukar ta ya yi yasata awuyanshi suka koma ciki .
Kowa ya gama cin abinci sun gama abinda zasuyi har sun shiga ciki an kwanta se kuma asuba ta gari .
( *BISHARA'S FAMILY MEMBERS*)
*KAƊAN DAGA CIKIN TARIHIN AHALIN BISHARA*
Mubarak Yousuf Bishara shine babban ɗa awajan Yousuf Bishara, Mubarak Bishara shine tsohon gwamnan jihar Borno yanada mata uku,matar shi ta farko ita ce Hajiya Badeeya sunyi auren soyayya da ita duk da lokacin mata biyu ze aura saboda yana soyayya da Hajiya hamdiyya to se aka fara auren shi da Hajiya Badeeya bayan kamar wata uku
Kuma ya auro Hajiya hamdiyya tsakanin Hajiya Badeeya(Hajiya babba) da Hajiya hamdiyya (Ammi) akwai kyakkyawar fahimta suna zaman lafiya sosai kusan a tare suka samu ciki sede Hajiya babba ce ta fara haihuwa ta haifi ƴarta mace aka sa mata suna Sakeena bayan wata ɗaya Ammi ta haifi ƴarta itama mace taci suna Sameera tare suka taso yaran suna son junansu sosai saboda ganin yanda iyayen su suke zaman lafiya bayan shekara uku Hajiya babba ta sake samun ciki ta haifi na miji Aka sa mishi suna Abbas tana cikin renon Abbas ciki ya bullo tanaji tana gani tayi ciki da goyo wata tara ta sake haihuwa ta haifi na miji shima aka sa mishi suna Ahmed ,tsakanin Abbas da Ahmed be wuce shekara ba. ana haka Abbie ya sake aure ya auri Hajiya khareema tundaga nan ne kuma zaman lafiyan gidan yafara ƙaranci saboda Hajiya khareema ta tsani a zauna lafiya kuma ahakan ma Ammi da Hajiya babba basa biye mata, Hajiya khareema itama ta haife ɗanta na miji aka sa mishi suna Hafiz shekara daya da rabine tsakanin su da Abbas da Ahmed.
har izuwa wannnan lokacin Ammi bata sake samun wani cikin ba saboda dama planning takeyi domin karatun da takeyi bata so ta samu ciki ya ka tse mata karatu. Su Abbas nada shekaru huɗu kwatsam se ga ciki ya bayyana ajikin Ammi tunda ta fahimci tana da ciki ta fara kokarin ganin ta zubar dashi batare da kowa yasan akwai wannan ciki din ba,duk wani nau'in maganin zubar da ciki Ammi seda tayi amfani dashi amma ciki yaƙi fita yana zaune daram dam_dam hakan yasa ta tsani cikin kamar ranar mutuwarta,yanke shawara ta yi domin zuwa asibiti a yi flushing din cikin kawai nan ne doctor da taje wajen shi ta faɗa mishi abinda za'a mata shi kuma ya kira Abbie ya sanar dashi abinda take shirin aikatawa sosai ran Abbie ya ɓaci yazo asibitin ya sameta ya dauketa suka koma gida nasiha ya yi mata akan abinda takeson yi amma ta rufe ido ta nuna mishi ita batasan wannan ciki saboda karatunta yafiye mata shi.hatta Hajiya babba babu irin shawaran da bata bawa Ammi ba amma haka taƙi sauraran su hakan kuwa ya jawo musu babban saɓani ita da Abbie.wanda har ya kusa jawo sanadin aurenta wanda se da yakai manya sun shiga cikin lamarin acikin wannan matakin da ake ciki Isma'il Yousuf Bishara (Abbu)wato ƙani agun Abbie ya yi aure ya auri Hajiya hurairah.
Ammi babu yanda ta iya domin manya sunyi magana badan ta so ba haka ta reni wannan cikin amma inta kalle shi kamar ta sa wuka ta tsaga cikin ta fito dashi yabar jikinta takeji.ranar da ta haifeshi juyin duniya anyi amma taƙi ta bawa wannan jaririn nata nononta ɓacin rai da takaici ne yasa Abbie ya saki Ammi saki daya,hakan ne yasa ta nutsu bata tafi ko ina ba tana gidan saboda jegon da takeyi Hajiya babba ce tasamu ta shawo kanta da kyar ta fara shayar da shi ranar suna yaro yaci suna *TAJUDDEEN* nan ma da kyar aka samu Ammi ta yi hoto dashi a ranar sunan.haka Ammi ta dinga nunawa yaron nan tsana da kuma halin ko in kula in yana kuka ko kadan bata damu da daukan shi ba.Tajuddeen nada wata uku Hajiya khareema ta sake haihuwa ta haifi yara yan biyu maza wato Salim da Sahil bata jima da haihuwar su ba Hajiya hurairah ta haifi na miji itama aka sa mishi suna Sudais duk babu rata a tsakanin su.
Hajiya khareema ganin Ammi bata wani damuwa da Tajuddeen yasa ta daukeshi taci gaba da renon su tare shida su Salim da Sahil nan ne tasamu daman cusawa yaron ƙiyayya,tun yana karami kullum se ta faɗa mishi yanda aka sha fama da Ammi kafin ta yarda ta haifeshi har ya zama wa Tajuddeen kamar karatu kullum se ta maimaita mishi domin so takeyi maganar ya samu guri ya zauna dam acikin zuciyarsa.aikuwa haka akayi yaro yafara girma da wasu irin murɗaɗɗun hali da shegen taurin kai wanda ko ita kanta uwar riƙon nashi bayayi mata magana sosai ita dasu Abbie se suka fara tunanin ko de bebe ne baya magana.domin har ya kai shekara hudu baya wani magana kuma lafiyarsa kalau.daga wa'yannan shekarun ne fa Ammi ta fara kokarin jawo shi ajikinta domin farat daya taji son ɗan nata ya shiga xuciyarta lokacin tana da cikin jawan sede time is too late Hajiya khareema ta riga da taci nasara akanta domin ta juyawa Tajuddeen tunani ta hanyar makircinta ko da Ammi ta kira shi ba ya zuwa ko kusa da inda take hakan yasa hankalin Ammi yafara tashi danasani yafara ɗawainiya da ita.