← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 60

Sashe 54

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yasa ke dakikiya ce kam Naziya!?,ke kullum a ce bazaki nutsu ki san ciwon kan ki ba!?,to ko mutuwa zakiyi se kinzo Maiduguri kuma bazan taɓa canza abinda na yi niya ba,gwara ma ki rufawa kan ki asiri ki zo ki dangwali arziki ki barsa a inda yake,in kika auri Tajuddeen ai ba ma mu kadai ba,gaba daya danginmu sun warke,amma tsabar doloncin da ke damun ki,kin ƙi nutsuwa ki bani haɗin kai.to na riga da na gama magana ta gobe_goben nan za ki ta ho.saura kuma ki zo ki dinga nunawa mutane wannan shegen sanyin halin naki"ita de tunda antyn nata ta fara magana kawai jinta take yi amma ita ko kadan bata son zuwa musamman ma da tasan manufar da ake son amfani da zuwan nata.ita ta riga da tasani ko mutuwa zatayi tasan bata ishi LTG kallo ba ɓalle har ya ce ze aure ta shisa ta ke ajiye kan ta inda Allah ya ajiye ta,ko zuwa Maiduguri ma sau biyu kawai ta taba zuwa.

Cikin sanyi murya irin na ta,ta soma magana.
"Anty khareema da kinyi hakuri da wannan burin na ki,ni takura min kikeyi,tun ba yau ba,kinsha min wannan maganar amma na nuna miki banida wannan ra'ayin.mijin da zan aura har gida ze zo ya sameni in sha Allah,amma kin dauki buri da son abin duniya kin daurawa kan ki.ki ji tsoron Allah anty khareema.ni de bazan zo abanza ki dinga ja min wulakanci ba".

Cike da Masifa da ya rufe mata ido ta ce"kam uban can dan uwarki Naziya Ni ki ke cewa in ji tsoron Allah?,in ban ji tsoron Allah ba tsoron ki zanji,yar iska bagidajiya,kar ki ga dan kina kanwata kice zaki faɗa min maganar banza in kyale ki,yar karamar ƴata ita ce sa'ar ki!,amma saboda reni ya shiga tsakanina dake har ina magana kina bani amsa ko Naziya???".ya mutsa fuska ta yi kamar tana gaban Ammuh din.

A hankali ta ce"ai dama ita gaskiya ɗaci gareta,to nide banaso babu yanda za'a yi in yarda kiyi mini dole akan wanda baya sona baya ra'ayina, shine kawai anty khareema".

Ummah dake gefen Ammuh suna saurarar abinda ta ke faɗa, domin wayar na a handsfree.

Ta mata alama da ta danne fushinta, ta lallaba Naziya din wuyarta tazo ne ai.

"Shikenan yar kanwata yanzu de mu bar maganar Tajuddeen ki shirya gobe ki zo ki kawo min ziyara".
"Ni fa anty khareema na san halinki kawai de wayo kike son ki min, Wallahi in na zo bazan wuce sati daya ba zan dawo,taraba!".
Haɗiye bakin cikin da ya tokare mata wuya ta yi, saboda inde ta ce zata tsaya suna sa'insa da Naziya tasan ba zuwa zatayi ba.
"Shikenan na amince yanzu zan tura miki 100k a account din ki,ki biya kudin motar".

Tabe baki ta yi ta ce"to Allah yakaimu goben da rai da lafiya ".

Ko amsa mata ammuh ba tayi ba ta kashe wayar dan haushin Naziya take ji,ita halin ta daban, se ka ce ba ciki daya suka fito ba.komai se ta dinga nuna tsoron Allah da kuma tausayi se kace tafi kowa,ga shi ita kuma ta kwallafa rai akan se ta haɗa LTG da Naziya aure,ita kuma Naziya na kokarin ba ta matsala..

Dafa ta ummah ta yi"haba Hajiya khareema,ke yanzu a ganinki in kina binta a haka kina tunanin zata yarda ta zo ne?,lallabata yakamata kiyi,kin tsaya kina mata tsawa da Masifa, ba kin san yaran yanzu ganin kansu suke yi dede da na kowa ba . abu me wuyar shine ta zo gidan nan, muddin ta riga da taxo tofa magana ya ƙare,duk da naga ita ma Naziya akwai taurin kai in ba haka ba,ana nuna miki hanyar arziki amma kina kaucewa tsaban yarinta da hauka".

Ajiyar zuciya ammuh ta yi,ita da ace tana da wata karamar ƙanwa tofa babu abinda ze sa ta tsaya bata lokacinta akan Naziya.tun ba yau ba suke kai ruwa rana da ita akan cewa tana son ta auri LTG amma ta nuna sam ita bazata auri wanda baya son ta ba.

"Ke de bari kawai Hajiya hurairah na daɗe banga jakar yarinya mahaukaciya ba irin Naziya. wai ni ina dubawa kanwata yanda rayuwarta ze yi kyau, amma wannan yar iskar yarinyar tana kokarin watsa min kasa a ido.ni banida matsala da Tajuddeen tunda da boka mauzau zamu haɗa sa Kinga kuwa ai soyayya shi da ita dole".

Ta yi shiru tana girgiza ƙafarta dake daure akan daya.
"Yanzu de bari ta zo din se mu ga ya abin ze kasance".cewar ummah.

Suna tsaka da magana masoyiya Parsa ta shigo dakin da wannan murmushin nata kwance akan fuskarta ta zauna tana me kwantar da kanta ajikin Ammuh.dakatawa da maganar sukayi saboda shigowar ta.
"Parsa daga ina haka"kallon ammuh ta yi ta ce "Ammuh ina falone, dama ina so in gayawa ummah gobe zamu je gidan anty Sameera ne nidasu Umaisha"haɗe fuska Ammuh da Ummah sukayi jin sunan da ta kira"meye zakuje yi gidan Sameera?",da mamaki ta kalli Ammuh kafin ta kalli ummah.
"Ziyara zamu kai mata tunda gobe weekend ne so i thought that was a good idea".
"To naji amma bazaku je gobe ba se next week,yanzu kije ki huta".
Murmushi ta yi ta ce"to ummah"ta shiga bedroom din Ummah ta kwanta.

Bin bayanta sukayi da kallo, Ammuh ta ce"Hajiya hurairah kinsan me nagani kuwa!?"girgiza mata kai ummah ta yi.

Ammuh ta sa'ke cewa"me ze hana mu haɗa Parsa da Salim aure,ni a ganina sun yi matukar dacewa".jimantawa ummah ta yi kafin ta ce"to ai ba mu san ko suna ra'ayin juna ba,sede mu tuntube su".
"Eh hakane kam in sha Allah zan yi wa,Salim din magana ke ma se kiyiwa Parsa din "cewar Ammuh.
A haka suka bar maganar tasu.(lallai kam, sunan wani abu wai kwamachala.parsa na son Sahil,nan kuma Ammuh da Ummah suna shirin haɗa ta da Salim).

Zaune suke a falon su,sun nutsu suna yiwa Asmita da Sabriyah lessions.
Kusan tsawon awa daya suka kwashe kafin nan suka gama,kai school bags din su bedroom sukayi suka dawo.

Asmita da take fama da ciwon kai ne,ta zauna tana daura kanta akan kafadar Sabriyah. tunda ta ga haka ta san akwai abinda yake damunta.

Shafa kanta ta yi "my Jerry meyafaru ne naganki haka!?".
"Kai na ke min ciwo sannan kuma se in dinga ganin jiri na son kwashe ni".
Rameesa da hankalinta ya tafi gaba daya wajen ganin wani memes na abun dariya a facebook ta ce "kinsan dama you're still under medication dole wata rana kiji irin haka,in ya tashi miki Kisha maganinki se ki samu ki kwanta ki huta".
Miƙewa Sabriyah ta yi,da niyar ɗauko mata maganinta tasha,ta rike hannunta.
"Maganin wajena ya ƙare,sede bansan ko akwai a wajen ya Saghar ba".
"Eh shikam baze rasa ba"Zoya ta faɗa tana tapping bayanta.
Maida kanta kan cinyar Zoya Sabriyah ta yi,ta fice a falon ta nufi part din Saghar sallama ta yi hatta gaji amma bata ji alamar mutum ba,hakan yasa ta nufi downstairs, Hajjatiye kawai ta samu anan.
"Barka da hutawa Hajjatiye ".
"Yauwa sanariya,wa kike nema haka!?".
Yar guntun murmushi ta yi sannan ta ce"ya Saghar nake nema zan ƙarɓawa Asmita maganinta ne".
Kamar wani abun tashin hankali ne ya faru Hajjatiye ta soma salati tana riƙe haba.
"Yanzu abinda Saghar din yake aikatawa har ya kai haka,ohh ni hajja yau ni naga bak'ar mugunta, yarinya ba lafiya amma ya bata magani ma abu ya faskara ".
Baki a bude take kallon Hajjatiye jin yanda ta juya fahimtar maganar daban ita da ta ce tana neman sa ta ƙarɓawa Asmita magani,amma Hajjatiye tana wani magana daban yanzu wani in ya ji ai se a yi wani tunani daban.

Saukowa downstairs ummah ta yi ta ji abinda Hajjatiye take faɗa ga Sabriyah a gabanta nan take ta ji ranta ya ɓaci.

"Yanzu har kin samu damar da zaki iya kawo kar'ar ɗana dan kawai be bawa wancan kazamar magani ba,saboda yana taimakon ku yana dubata.shine har zaki samu kwarin guiwar kawo kar'ar ɗana?,da ma ɗan Adam butulu ne ba'a iya masa,duk yanda za'a yi wajen kyautatawa mage tofa bazata gani ba".tun da kika zo gidan nan dama naga kanki na wani fisga yana hayaki, wannan dalilin yasa, na ke kauci rashin kunyar ki,amma yanzu dole in taka miki burki tunda har yakai ki fara kawo kar'ar ɗan masu gida shida gidan ya kasance na ubansa ne. ku kuma fa taimakon ku akayi a ka bar ku anan amma yanzu dole zaman ku ya ƙare anan".
Jikin Sabriyah ne ya yi sanyi dama ita tasan in ba wai mutum me fahimta ba,ze yi wuya duk wanda yaji yanda Hajjatiye take mayar da magana ya fahimci kan zancen,dole za'a ga kamar kar'ar Saghar din ta kawo wajen Hajjatiye.

"Ummah kiyi hakuri ki fahimce ni bawai kar'ar ya Saghar na kawo ba. kawai ina neman sa ne in ƙarɓawa Asmita magani"daga mata hannu ummah ta yi alamar ta dakata bata son jin komai.
"Rufe mini baki bak'ar munafuka ke yanzu ki dubi kan ki, yanzu da kuma yanda kukazo gidan nan a tsiyace a wulakance wanne ku kafi kyau?,yau har kin yi gogewar da za ki iya taka ɗan masu gida!?,kina karuwa dake dube ki fa,mara asali, wacce ta gama rabarwa mazan titi kanta,da ke da wancan mahaukaciyar yarinyar yau din nan zaku bar gidan nan tunda ba gidan uban ku bane".
Jin yanda take goranta musu da aibata su ne yasa Sabriyah ta fara kuka, maganganun ummah ya so sa mata rai ta ci mutuncin su ta tozarta su.
"Yi mini shuru mara mutunci yanzu Huraira ko kunyar idona bakiji ba kika tsaya kina gorantawa yarinyar nan,anya kina da hankali kuwa?,". murmushin takaici ummah ta yi"Hajjatiye kenan dama ai bayansu zaki bi yaran da suka fito daga gidan karuwai ai babu abinda bazasu iya ba dan ganin sun siye zuciyar kowa amma banda nawa, kuma bazan taɓa lamuntar reni daga wajensu ba wa ni ko wa ya'yana".
Chapter 54 · 0% Book details