← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 60

Sashe 29

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayewar garin yau ne Fu'ad ya fara shirin tafiya ji yakeyi kamar kar ya tafi saboda har ya fara kewar su Sabriyah da Asmita duk da ya musu alkawarin ba ze daɗe ba ze dawo, sannan babu yanda be yi da Sabriyah kan ze siya musu gida su bar afafa ba, amma fir ta ƙi ta ce ita babu in da yafi mata can dinm hakan yasa babu yanda ya iya ya kyaleta ya dauki makudan kuɗaɗe ya basu.
Fitowa ya yi da trolley din kayansa ya samesu a falo suna zaune, mikewa sukayi da suka ga yafito su ma da nasu trolley din su a hannu.karewa Sabriyah kallo ya yi daga sama har ƙasa tana sanye da wandon jeans crazy blue color,se riga me daguwar hannu me high neck white color gashin kanta ta sa'ke su a bayanta murmushi ya yi ya ce "Sabriyah kinyi kyau sosai"ba ta bashi amsa ba illa murmushi kawai da ta mishi .duk babu dadi takeji domin sabo turkin wawa ne.fitowa sukayi daga hotel suka shiga motar shi yakai su har afafa,fitowa sukayi daga motar suna wa juna bye_bye,se da ya tabbatar sun shiga cikin gidan sannan ya wuce, komawa hotel din da ya baro ya yi, ya canza daki daban ya kama wani.wasu mutane ne sukayi knocking ya je ya buɗe musu kofar, wasu zabga_zabgan matasa ne su bakwai suka shigo dakin ko ina na jikinsu a murde yake wani irin alama sukayi da hannunsa alamar girmamawa gyada musu kai kawai ya yi,kallon su ya yi cikin harshen yaren French ya ce "kun kama shi ne!?"dayan su ne ya ce "ah ah ya ɓace mana amma ko ta halin ƙa'ƙa se mun kama shi domin inde wannan daukan ya fita shirin mu ya tashi a banza!" "To ku gaggauta yin hakan, in kuma ba haka ba ku fuskanci hukunci,domin ya riga da ya kwashi duk wani sirrin mu a cikin wannan daukan da ya yi.gobe zan bar Nigeria ku tabbatar kafin in tafi kuzo mini da albishirin kun kasheshi."ya gama maganar idon shi na kansu. Sa'ke yin wannan alamar sukayi kafin dukkansu suka haɗa baki wajan faɗin "we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union."suna gama fadin hakan suka fita acikin dakin hotel din suka tafi.

A bangaren su Sabriyah kuwa ko da suka shiga ciki basu samu Anty Teema ba,zama sukayi acikin dakin suna ta hiran irin kyautatawar da Fu'ad ya musu.wayar Asmita ne ya yi ƙara dubawa ta yi taga saurayinta Taheer ne hakan yasa ta dauka tasa a kunne hira sukayi sosai har take sanar dashi sun dawo afafa.

Se karfe biyu na rana Anty Teema ta dawo jin kamar motsin sune yasa ta leka dakin nasu tun daga bakin kofar dakin ta fara magana "in ya!!, yara kun zama ajeboters se yau Allah ya yi kuka dawo kenan?",tayi maganar tana karasowa cikin dakin nasu ,da gudu suka je suka rungumeta sun yi kewarta sosai,shafa kansu ta yi tana dariya ta ce"har wani fresh kukayi abunku!"dariya su din ma sukayi suka zauna akan katifa, nan fa hira ya barke tsakanin su sunata bata labarin rayuwar da suka yi a oriental hotel,da kuma yanda Fu'ad ya dinga kulawa da su,nan Anty Teema ta ce "ai Wallahi Sabriyah gwara da kika ce mishi ku nan zaku dawo in bahaka ba, boss lady har can oriental hotel din zata tura a dauko mata ku,ɓalle ma ke yanda ta mayar dake ATM din ta, yanzu haka ina shigowa naga gidan rawa ana gyara shi alamar yau za'a yi show shine na fara tunanin cewa de ku bakwa nan,ashe ku har kun dawo ma abunku."kallon juna Sabriyah da Asmita sukayi cike da mamaki domin kuwa yau ai ba lahadi bane ɓalle ace suna da show din rawa yau Alhamis ,ta ya hakan ze kasance.

Mikewa Sabriyah ta yi ta ce "bari in je wajan boss lady din in gaisheta in ji yau nice zan yi show din ko wata ce!"ta yi maganar tana saka takalmi a ƙafar ta,ba ta saurari Anty Teema dake mata magana ba ta yi gaba.a hanyar zuwanta wajan boss lady ta hadu da ƙawar Nabiha suka gaisa ta tambayeta ina Nabiha nan ta ce mata sun fita dazun ita da Cele. "Okay in ta dawo kice mata mun dawo dazun" sannan ta wuce. ta shiga wajan Boss lady.a kwance ta sameta ga dan daudun nan yana daddanna mata kafofunta ita kuma tana daga kwance tana shan w'iwi,zama a kusa da ita Sabriyah ta yi ta gaisheta, murmushi Boss lady ta yi ta ce"hot girl manya,yanzu kam nasan zaman da kikayi a wajanshi ya mayar dake cikakkiyar mace,shisa naga ko ina na jikinki ya ciko,ai hannun namiji iri ne."murmushi kawai Sabriyah ta yi dan batasan me za ta cewa boss lady ba hakan yasa ta canza maganar ta hanyar faɗin "boss lady naga anata shirya gidan rawa!,akwai wacce za ta yi wasa ne!?" "Ehh ke da Asmita ne zakuyi wasa saboda muna da manyan ba ƙi,ga kayan nan ki tafi dasu"ta ƙarishe maganar tana daukan ledar sabbin kayan rawan ta miƙa mata,kar ɓan su Sabriyah ta yi cike da nishadi ta tashi ta yi mata se anjuma ta koma sashin su.yanda ta tafi tabar anty Teema da Asmita haka ta same su nan ta faɗa musu yadda sukayi ita da boss lady.ita de Asmita wannan rawan bawani son yi takeyi ba,kawai tanayi ne dan babu yanda ta iya tunda de bata Isa ta ce bazata yi ba.ita kuma Sabriyah babu abinda idan ta yi take samun nishadi irin wasan rawar hakan na kwantar mata da hankali,shisa duk sanda ya kasance ranar zatayi wasa to fa za'a ganta cikin walwala,haka suka ci gaba da hira har lokacin da Cele ya shigo yana ganin su yabasu hannu suka tafa nan fa sabon hira ya barke a tsakaninsu kamar wa'yanda sukayi shekara basu haɗu ba.fita a dakin Cele ya yi ya je ya siyo musu nama da drinks.ya dawo aka daura hira daga inda a ka tsaya.

8:00pm na dare Sabriyah da Asmita anyi musu kwalliya ga kayan da suka saka ya ainihin fito musu da shape din su,har sun zo fita Sabriyah ta lura abin hannunta ba ya tare da ita nan ta fara dubawa,ko ta yarda shi ne a dakin. Asmita da ta lura da kamar abu ta ke nema ne ya sa ta ce.

"My Tom me kike nema ne haka!?" batayi wata_wata ba ta bata amsa,jim kaɗan ta yi ta ce "to ai tun kafin mu bar gidan nan babu shi a hannunki".

Arazane Sabriyah ta kalli Asmita cike da tarin tambaya "bangane ba,me kike nufi da baya hannuna!?".hannu Asmita ta sa ka a saman window dakin nasu ta dauko mata shi ,ta ce "kina bacci ne ya fita a hannunki shine na adana miki, anan kan cewa washe gari in ba ki to kuma se na manta har muka tafi ban ba ki ba ."ajiyar zuciya Sabriyah ta yi har idonta ya cika da hawaye ta ce "Nagode sosai my Jerry,da ace wannan abun ya bata da bansan wani irin hali zan shiga ba,domin wannan din alkawarine tsakanina da Tajuju na,in na batar dashi kamar na batar da soyayyar da nake mishi ne."gaba daya jikinta ya yi sanyi ji ta yi kamar bata kyauta ba da har tabar abin hannun ya fita a hannunta,dafa kafardata Asmita ta yi ta ce"kar kuma jikin ki ya mutu mana,ko kin manta yau ranar nishadin ki ne!?"murmushi ta yi suka rungume junansu kafin suka fita a dakin,suka nufi gidan rawan da ya cika makil su kadai kawai ake jira.
Suna shiga aka hau musu tafi da watsin kudi,nan suka fara gabatar da wasan rawar nasu cikin kwarewa.

Se kusan karfe goma suka kammala wasan nasu, sun sha ruwan kudi na fitan hankali,manyan baƙin da boss lady ta yi se turawa sukeyi a kira musu Sabriyah da Asmita,amma fir sunki zuwa daga karshe ma barin wajan suka yi saboda tsananin gajiyan da sukayi,dakin su Nabiha suka wuce nan suka sameta tana gyara kayanta da ta wanke, zama sukayi gefenta ,kallon su Nabihan ta yi ta ce "gaskiya yau na yi missing banga wasa ba" "uhmmm kin kyauta ai,Cele ya ce mana zakizo se bamu ganki ba"in ji Asmita,ajiye kayan da take ninkewan ta yi,ta ce"ke Wallahi Asmita ba ki iyawa mutum uzuri ba,sugar daddy na ne ya ce in shirya gobe zamuyi tafiya shisa ban samu fitowa ba."

Sabriyah kam zani ta dauka ta daura a kirji sannan ta kwanta ta basu baya tana jin su se hiran su sukeyi,anan wajan suka raba dare har wajan karfe sha biyu sannan suka koma na su bangaren.
Suna isa Sabriyah ta ji wayarta na kara dubawa ta yi taga Fu'ad ne ya mata kusan 10 missed calls,kiransa ta yi suka sha waya sannan ya ce tabawa Asmita wayar su gaisa hakan akayi kuwa nan ma sun bata tsawon lokaci suna hira da Asmita kafin nan sukayi sallama.

Kwanciya suka yi da niyar yin bacci,har bacci ya fara daukan su Sabriyah ta farka, soma yi wa Asmita dake bacci magana ta yi.

"My Jerry kin san abinda ya kamata muyi kuwa gobe!?"

Asmita da idonta duk bacci ga Sabriyah ta tasheta ta ja tsaki ta ce "meye ne ɗan Allah,baccin ma ba za ki bar mutum ya yi ba haba!"

Dariya ne yaso kufcewa Sabriyah ta danne ta ce "gobe ya kamata mu shiga kasuwa tunda kin ga akwai kudaden da Fu'ad ya bamu,mu yi siyayya mu gyara dakin mun nan Wallahi,mu sa mishi komai sabo!"
Chapter 29 · 0% Book details