← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 60

Sashe 6

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dukkansu biyu sun shirya sahil ya kammala necktie yake sawa. shikuma salim takalmin makaranta yake sawa batare da sun ɗaga kai sun kalleta ba suka hada baki wajan faɗin" fatime ya akayi ?" Mamaki ne yau yakamata ganin yau sune akazo aka samu sun shirya suda kullum se sunyi letting kafin su tashi jinjina kai ta yi aranta ta ce" ahh lallai yau sahil da salim sunyi abin kai " afili kuwa ta ce" dama nazo in tasheku ne ,kuzo kuyi breakfast". " okay" salim ya furta suka ci gaba da shirin da sukeyi .
Fita tayi anasu part din ta shiga na Saghar , Jawan da Sudais , su kam ma a falo ta samesu sunfito hannunsu rike da school bag gaisheta sukayi ,ta amsa tarike haɓa kafin ta ce " dama ku zanje in taso kuzo kuyi breakfast saboda karkuyi letting " murmushi kawai suka mata , suka wuce ta .
Daga karshe part din Tajuddeen ta nufa tana tunani yau kuma wani irin wulakanci zeyi mata , sadaƙarwa ta yi kawai ta shiga part din kai tsaye ta wuce bedroom dinshi knocking ta yi taji ji shuru babu amsa , hakan yasa ta sake gwadawa duk da tasan abune mawuyaci Tajuddeen yabude. haka tai ta gwadawa kusan mintin ta goma a tsaye awajan cire rai ta yi da ze bude ta juya tafara tafiya ta ji , yabude kofar dawuwa ta yi ta tsaya kanta akasa domin kuwa dukda Tajuddeen beda wasu Shekaru bata iya kallon fuskarshi tunda tazo gidan saboda yana da matukar gwarjini ga wannan golding eyes din nashi da in ya tsare mutum dasu tofa se ka sha jinin jikinka.
Yana sanye da kayan bacci fuskar nan yaci murr ga idonshi da har lokacin akwai alamun bacci acikinta yawatsa mata harara dashi, cikin daga murya da rashin nuna ko In kula ya ce" meyafaru kikazo kina dokamin kofa da wannan safiyar ?" Hadiye wani yawu ta yi muryanta yafara rawa dakyar ta iya furta dama nazo in tasheka ne ! ka shirya zuwa makaranta kuma angama breakfast kai kadai suke jira " wani banza kallo yabita dashi ranshi yayi matukar ɓaci " daga yau se yau karda ki kuskura insake ganinki a part dina da sunan kinzo tashi na daga bacci , sannan wa'yanda suka turoki ki tasheni din kije kice musu bazanje makarantar ba" ya yi mata maganar cike da gargadi da izza da rashin kunya sannan yana kammala faɗa mata abinda ze faɗa ya rufe kofar da karfi kamar ze ɓalle ta , ya koma ciki yana tsaki yana rike kanshi dan ji ya yi kamar ze faɗi , ɗan duk sanda a ka tashe shi daga bacci tofa se ciwon kai ya ziyarce shi.

Jikin fatime a sanyaye takoma falo taje ta samesu duk suna zaune a dinning table suna zaman jiran Tajuddeen dukda sun san mawuyacin abune yafito tunda yariga da ya yi pepper tare da yan ss3 ya dena zuwa makarantar, jiran admission dinshi kawai yakeyi , dukda sun san ba lallai yafito ba amma basu da ikon cin abinci harse ance baze fito ba , domin wannan shine dokar gidan basa cin abinci a ware , Jawan ne ya ce " fatime yaya Tajuddeen din ya ce baze je ba ko ?" gyada mishi kai ta yi , tun daga nan be sake cewa komai ba ya ja plate din omelette din gabanshi yafara ci.
Salim ne ya ce " hmm dama ai bro Tajuddeen ba lallai ya fito ba tunda shi yanzu ya rena kowa agidan " dakatawa da cin omelette din dayakeyi Jawan ya yi ya kalli salim ya ce" babu ruwanka da rayuwar dan uwana ka ji da abinda yake gabanka, banason reni yaya Tajuddeen ba sa'anka bane " tsaki salim ya yi be kula Jawan ba , sudais ne ya kalli salim ya ce" salim karka sake irin haka , wannan rashin kunya ne " tunda akayi haka babu wanda sake cewa komai harsuka karisa cin abinci , fita sukayi izuwa packing space , motaci uku suka shiga se escort din da suka bi bayansu zuwa makarantar.

Tajuddeen ba shi ya tashi daga bacci ba har 10:00am toilet yafada ya yi wanka yafito ya shirya cikin ƙananan kaya riga da wando saman rigar yadaura rigar sanyi me hula, hular yarufe mishi rabin fuskar shi, sannan ya yadauki headphone dinshi ya toshe kunnenshi dashi . Kafin yafito kai tsaye dinning ya wuce.
duk a dinning din yasamesu wasu sun gama cin abinci wasu kuma suna kan ci , se hira sukeyi gwanin burgewa ,Hajiya khareema na sashinta bata fito ba.
Jan kujera ya yi ya zauna batare da ya kallesu ba balle su sa ran ze gaishesu, kallon fatime dake tsaye akanshi ya yi murya kamar wanda aka tilastawa dole ya yi magana, ya ce " in banida rabon abinci ne yau kifadamin in tashi in tafi " ya faɗa yana me tsareta da wa'yannan mayun golding eyes din nashi da se ƙyalli sukeyi kamar wa'yanda aka kunna kwan fitila, hannun fatime na rawa tafara bubbude food flask din da suke wajan domin ya zaba wanda zeci , gama bude gaba daya food flask din dake kan dinning ta yi tana jiran yazaba wanda ze ci ,dan gudun kartasa mishi wanda ba shi yake da niyyar ci ba ta yi laifi . ganin ta budesu bata zuba mishi bane yasa yagane me take nufi slide murmushi ya yi ya ce " karki damu kisamin ko wanne in bawai akwai poison aciki bane " dukkansu da kallo suka bishi domin sun san da biyu ya yi maganar, girgiza kai Abbie ya yi kawai bece komai ba, Ammi da tasan da ita yakeyi ka sa hakuri ta yi ta ce" Taj waye kake tunanin zasu sa maka poison din ?" Shuru ya mata be kula ta ba , kamar ma besan da shi takeyi ba , nunawa fatime food flask din da ke dauke da sinasir ya yi da sauri tazuba mishi da miyar taushe da ya ji kayan hadi .

Anty amarya ce ta taɓa hannunshi ta ce" Tajuddeen Amminka na maka magana " ɗago kai ya yi ya kalli Ammi da itama shi ta tsurawa ido tana kallonshi , sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya ce " mutane da yawa mana , wa'yanda suke son ganin na mutu ".
Ran Abbu ne ya ɓaci dan yasan Tajuddeen da Ammi yakeyi " yanzu kai Tajuddeen ɗan bakada hankali mahaifiyartaka kake cewa tana son taga ka mutu anya Kanada cikekken hankali kuwa ?" Cikin natsuwa ya ke cin sinasir dinshi kamar be san Abbu na mishi magana ba , Abbas ne ya ce" dan Allah kuyi hakuri ku mishi uzuri in sha Allah zedena wa'yannan abubuwan da yakeyi " " hmmmm! Abbas kenan ai dama kai da Ahmad da sameera bakwa taɓa ganin laifinshi kullum cikin daure mishi gindi kuke " cewar Abbu ɗan har lokacin be sauko ba saboda ba karamin bata mishi rai maganar da Tajuddeen yafaɗa ya yi ba .
Ammi mikewa ta yi tabar musu dinning table din dan dama ta gama cin abincinta hiran da akeyi ne ya tsayar da ita , Abbie, da Hajiya babba basu sa musu baki ba a maganar su kawai mafita suke nema ta yanda , zasu ga Tajuddeen ya komar da rayuwarshi irin na kowa .

Mikewa ya yi ya yagi tissue ya goge hannunshi ya juya ze tafi dan surutun da suke mishi ya ishe shi , ta kasan ido ya kalli anty amarya murya a dakile ya ce" anty amarya ina Asrah ?" Fushi takeyi dashi hakan yasa batako kalleshi ba ta ci gaba da shan kakƙaurar tea dinta da fatime ta haɗa mata, se uncle Hameed ne ya amsa mishi da" tana bacci ".
Harya soma tafiya Abbie ya kira sunan shi " Tajuddeen" cak ya dakata kafin yajuyo batare da yakarisa inda suke ba , hannu Abbie ya mikawa uncle Hameed,. Ya miko mishi da wata envelope me girma , tashi Abbie ya yi ya isa inda Tajuddeen din yake tsaye ya mika mishi " ga shi addmission dinkane na U.S millitary academy at West , nan da two weeks zaka tafi ka zama cikin shiri . Allah yabada Sa'a" har ranshi ya ji dadin wannan addmission din nashi da ya fito ,domin wannan shine burinshi kuma ga shi ya samu,beyi tsammanin yanda Abbie ba ya son shi ba ze cika mishi burinshi ba ( shifa Tajuddeen gani yakeyi duk gidan babu wanda suke sonshi,domin akan hakan Hajiya khareema ta daurashi kullum cikin zigashi takeyi da hure mishi kunne ).
Duk da basason yatafi yabarsu amma sun taya shi murna , sunyi tsammanin yau kam rana daya da yasamu abinda yake so zasuga farin ciki a tattare dashi ,amma se sukaga sabanin hakan , komawa Abbie ya yi kan kujeran da ya tashi babu wanda ya yi tsammani kawai suka ji Tajuddeen ya furta " thanks" sannan ya haura upstairs part din anty amarya da uncle Hameed.
Chapter 6 · 0% Book details