← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 60

Sashe 19

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Teema baby da Rash ne suka shigo dakin nasu domin dubasu ko akwai abinda suke bukata amma da mamaki se suka ga babu su a dakin hakan yasa suka dauki lema da torchlight suka fito suna dudduba su har suka hangosu da sauri suka isa inda suke bakaramin tashi hankalinsu ya yi ba ganin halin da suke ciki ba ga Sabriyah dake sume a ƙasa cikin ruwa cikin rudewa Teema baby ta ce "Asmita meya fito da ku awannan ruwan?me ya sami Sabriyah?"ta jero mata maganar a yayinda ta sa hannu ta dauki Sabriyah din ta saɓata a kafardata, Asmita dake rawan sanyi kuwa bata samu damar bata amsa ba haka suka koma sashin su kwantar da Sabriyah Teema baby ta yi akan gado ta cire mata kaya da sauri haka Rash ma ta canzawa Asmita kaya har lokacin Sabriyah bata farfaɗo ba hakan yasa Teema baby ta dauki lema ta nufi bangaren boss lady domin sanar da ita halin da ake ciki.sosai ran boss lady ya ɓaci wato yaran so suke yi su gudu ta yi asarar kuɗinta kenan jinjina kai ta yi a ranta ta ce"zan yi maganinku" kafin ta daga waya ta kira wani doctor ta sanar dashi akwai mara lafiya in ruwa ya dauke yazo ya dubata kafin ta kashe wayar ta juya kan Teema baby ta ce "ku kuna ina lokacin da su ke kokarin guduwa?nace kuna ina ?ko ba cewa nayi ku kula dasu ba kuɗi da yawa nasa na siye su da ace kudi kaɗan ne ko mutuwa sukayi Ni bazan damu ba amma bazeyu inyi asarar wa'yannan yaran ba,amma dake ku din ballagazazzu ne ga shi kun barsu suna shirin guduwa to wlh duk sanda yaran nan suka sake kokarin guduwa Teema abinda zan aikata agareki se kinyi da nasanin rayuwarki.banza kawai ɓace mini da gani ko na dauke ki da mari wa'yanda basu san darajan kuɗi ba" sosai idanun Teema baby ya cicciko da ruwa ta bar sashen boss lady da sauri tana me tausayin rayuwarta da kuma sauran da suka tsinta kansu acikin wannan halin nan ne ta sake jin kaunar Sabriyah aranta sosai domin yaran tunda ta gansu dazun taji tana mugun tausayinsu kuma ta yi alkawarin zata kula dasu sosai.

Wannan kenan,bayan ruwa ya dauke likitan da boss lady ta kira yazo ya duba Sabriyah kuma ya gano ta kamo da (pneumonia) nimoniya hakan yasa ya rubuta mata magani sannan Asmita ma ya rubuta maganin mura sannan ya kara musu da kar a dinga barin Sabriyah tana mu'amala da ruwa sosai musamman ma me sanyi Sannan ya tafi abinshi.

Washe gari se karfe goma Sabriyah ta farka daga bacci Teema baby ne a dakin se Asmita ruwan wanka ta daura ta mata wanka da ruwan zafi ta haɗa mata shayi da biredi yanda Asmita ta karya.

Bayan ta gama ne tabata magani ta sha haka Teema baby ta dinga kulawa da Sabriyah hatta warware.
Bayan sati daya su Asmita, Sabriyah sun shaƙu sosai da Teema baby da Rash kamar da can sun san juna haka suka koma kiran su da anty Teema da anty Rash,dake sun samu masu ɗebe musu kewa har sun fara sabawa da wajan kuma har zuwa lokacin boss lady ba ta zo ba.

Yau ma suna zaune Sabriyah na gaban anty Teema tana yi mata kitso amma dake gashinta yanada tsantsin gaske se yaƙi kitsuwa haka ta gyara mata gashin,agefe daya kuwa anty Rash ne da Asmita suna kwance suna baccin rana akan katifa,basuyi tsammanin zuwan boss lady ba kawai ganinta sukayi akan su"ke Teema baby tashe min Rash da wancan yarinyar"tashi anty Teema ta yi taje ta tashi Anty Rash mikewa sukayi suna gaisheta ta amma sannan ta maida kallon ta kan Sabriyah da Asmita ta ce"wato naji kuna kokarin guduwa ko? warning nazo muku duk sanda kuka sake yunkurin gudu karnuka zan sa su biku su cije ku,su cinye naman ku har se kun mutu.kun ga wannan gidan duk wanda ya shigo gidan nan baya fita har abada sede ko in mutuwa ya yi,to nan gaba in kuka sake yunkurin guduwa mutuwa zakuyi kunde jini ina?."cike da tsoro sukace mata to sannan ta ce wa Anty Rash"kizo ina neman ki."

Bayan fitan su ne Anty Teema ta sake musu faɗa ta ce kar su sake kokarin guduwa.

Haka su Sabriyah da Asmita suka ci gaba da rayuwa a gidan karuwai tare da yaran da aka kawo su tare har an fara musu duk wasu training din da boss lady ta ce ayi musu salo kala _kala ana koya musu tun suna ganin abun wani iri har ya bi jikinsu.

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73

🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹

Page 12

*_ story & written_*

By

*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️

Page 12

*This is just the beginning*

AFTER TEN YEARS OF LIFE (bayan shekaru goma na rayuwa)

Gidan rawan cike yake da mutane maza da mata ga manyan mutane masu zuwa daukan yanmata suje su kwana dasu,in banda filin da za'ayi rawan babu wani space aciki ko ina damke yake da mutane kowa so yakeyi yaganta yakuma ga rawanta na musamman da takeyi me daukan hankali,shisa duk karshen sati suke biyan kudi suzo su ga rawanta,kamar yadda aka saba yauma karshen sati ne ranar Lahadi kenan karfe 8 nadare, duk sun zauna ita kawai ake jira ta karaso.
Kunna wata wakar India akayi wanda nora fatehi tayishi me suna kusu_kusu.
Cike da yanga take tafiya jikinta se juyawa yakeyi kamar wata macijiya,tundaga tafin kafarta nafara ƙare mata kallo har sama.

Kalar fatarta fara ce irin farin nan mai kyau da tafiya da hankali babu mis ko ta ina fari sumul ga jikinta da se sheki yakeyi , doguwa ce amma ba can sosai ba matsagaiciya ,Siririya bata da jiki sede akwai shape sosai tana da hips ga kirjinta dake cike taf da tula_tulan dukiyar fulani suna atsaye se daukan ido suke ,cikinta a shamule yake sosai kamar wacce batacin abinci, komar da kallona nayi izuwa fuskanta, innalillahi wa'innailaihi rajuun tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawa ce ta ajin farko tana da ɗan dogon fuska me dauke da dogon hanci kamar anzana pencil,kumatunta kuwa na dauke da dimple aduka biyu bangaren, wanda ko murmushi tayi se sun lotsa balle ace ta yi dariya ko kuma ta yi magana,tana da manya_manyan idanu masu jan hankali cikin idon din nata na dauke da oiling eyeballs ga dogayen gashin idonta dasuke ajere reras kamar wacce tasaka eyelashes sunyi gazar_gazar, bakinta dan karamine sosai pink color yanayin suffan bakinta kamar heart aka zana mata,gaban goshinta na dauke da lallausan saje dake kwance luf_luf gashin kanta ya zubo tundaga kanta har izuwa kusa da kugunta yanada tsayi da kuma cika sosai ,duk inda za'a sako kyakkyawa tofa wannan ita ce zatazo a farko domin makura ce wajan kyau, jikinta na sanye da wasu tsinannun kaya wanda dasu da babu duk daya , irin kayan da nora fatehi tasaka a wakar kusu_kusu , irin kayan nan na yan rawa da India ko larabawa ke sawa , dogon skirt ne wanda ya kasance a rabe biyu gefe da gefe ga ya matseta sosai hips dinta sun fito kayan se daukan ido yakeyi yana walwali rigan skirt din kuma bashi da maraba da breziya sede yadan fi breziya girma kadan tula_tulanta duk suna waje kadan ne acikin rigar , tsayin rigar ko cibiya be kaiba se wasu chain ne da aka musu kwalliya dashi ,hannunta na dauke da abun hannu kalan kayanta baƙi se kuma wani abun hannun da ya kasance silver color me kyau da design din suna ajiki yazauna dass a hannun, yarinya ce yar shekara goma sha bakwai.
Chapter 19 · 0% Book details