← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 60

Sashe 60

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Duk da bata da hoton kanta a yanzu Lokacin da take yarinya karama amma tana ganin wannan hoton ta gane cewa ita ce a jiki,ƙaryata kanta ta yi ta bude locker din nan taci karo da folder din hotuna fito dasu ta yi, ta fara gani hotuna ne gaba daya a jiki,da wanda aka yi drawing da kuma wanda aka dauka a camera,bata sake shiga firgice da rudani ba se da ta buɗe wani shafin da taga hotonta da wannan saurayin da take yawan gani a mafarkinta,yana rungumeta da ita aka musu hoton,a ƙasa an rubuta "Asrah din Tajuju"sa'ke folder hoton ta yi ya fadi a ƙasa.jikinta ne ya dau rawa kamar mazari,gani take yi kamar a mafarki taya hakan ze yu, ta ya za'a yi ya kasance ita ce wannan Asrah din da wannan ahalin basu da magana da ya wuce nata.wani irin Flash ta fara ganin a idonta,tana jin muryoyi ana magana.rufe idonta ta yi ta sa hannu ta toshe kunnenta,a cikin idonta ta hango wannan yarinyar da ta gani ajikin album din da anty amarya a filin garden suna wasa,anty amarya na binta a baya ita kuma tana guda tana yiwa anty amarya dariya.
Kokarin faɗuwa yarinyar ta yi,anty amarya ta ce "Asrah becarefull"riƙe yarinyar wani kyakyawan saurayi ya yi yana dagata ya daura a wuya.
"My Tajuju".
Da sauri Sabriyah ta bude idonta waral kamar fitila,nan take numfashinta ya fara fita da sauri sauri.
"Kenan ni ce Asrah?,ni ce Asrah din da suke nema?,taya hakan ze kasance?"faɗuwa ta yi akasa ta na me yin ihu"bani baceeeee"domin har yanzu ta gagara gaskata ita ce Asrah.

Da sauri kuma ta sa hannu ta bude shafi na ƙarshe a folder din hoton Asrah ne tana tsaye ba riga a jikinta,rubutun sunan Tajuddeen baro_baro ya fito a bayanta.
A tsorace kamar wacce taga fatalwa ta yarda folder din a karo na biyu.

Hannu tasa taja zip din rigarta ƙasa ta je gaban mirror dakin nashi ta juya bayanta kadan nan take sunan ya bayyana.

"Innalillahi wainna'ilaihi rajuun shikenan ni da kaina na tura muradin rayuwata wajen da za'a kashe shi,na tura tajujuuuuu na wajen da za'a kashe sa, muddin wani abu ya samu Tajuju to bazan taɓa yafewa kaina ba".
Kamar mahaukaciyar da ta gudo daga gidan asibiti take magana tana kuka kamar ranta ze fice daga jikinta.

Da gudu ta baro part din nashi tana sambatu,kowa na zaune a falo ana jimamin halin da suke ciki ta fito da muguwar gudu zata wuce su,ga kururuwar kukanta da ya cika gidan.

Da gudu Sudais ya yo kanta ya damki hannunta kamar wata me aljanu ta fara fisge_fisge tana "dan Allah ya Sudais kabarni, Wallahi ze kashe shi,ze kashe min shi!,na shiga uku na ze kashe min farin cikin rayuwata".
Ganin yanda take magana ne yasa suka yi tunanin ko aljanu ne suka shigeta, zaunar da ita Sudais ya yi amma ta sake yunkurin miƙewa.
Maida ita uncle Hameed ya yi ta zauna,wasiwasin abinda ya sameta suka shiga yi.

Abbie ne ya ce "Sabriyah menene abinda ya sameki,kuma waye kike cewa za su kace miki?"duk zuba mata ido sukayi suna son jin amsar da zata bayar.

Da karfi ta ce "Tajujunaaaaaaaaaaa"
Sa'ke zuba mata ido sukayi ɗan son tabbatar da abinda ta faɗa.

Anty amarya murya na rawa ta ce "Sabriyah bamu fahimci abinda kike son cewa ba".

Tana kuka ta ce "Fu'ad ze kashe min Tajuju na,nice!nice!nice"ganin yanda take jin kamar ana rike mata wuya ne yasa ta juya musu baya ta ja zip din rigarta kasa nan take sunan Tajuddeen ya bayyana a gadon bayanta.

Tirka_tirka,wani irin shock ne ya kamasu,basu taɓa shiga cikin matsananciyar al'ajabi ba irin wannan.

Kusan a tare gaba dayansu suka furta.
"Asrahhhhhhhhhh?".
Gyada musu kai ta yi tana kuka.
"Wallahi Fu'ad bashida imani ze kashe min Tajuju na,kuma muddin ya mutu Wallahi nima mutuwa zan yi in bar Duniyar nan".

Don't forget to comment, share and like.

Anan na kawo karshen book one,
Book two din na kuɗi ne ga duk me bukata ya min magana ta whatsspp number ta 09024503194.
Chapter 60 · 0% Book details