Sashe 7
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hajiya babba de in banda gyada kai babu abinda takeyi " anya bamuyi ganganci ba kuwa , muda muke neman sassauci akan halin yaron nan shine zamu turashi yaje yasamu horon soja harna tsawon shekaru goma , soja fa ze dawo yakuke tunanin ze koma " shuru suka yi suna nazarin maganar ta, tabbas suma sunyi tunanin haka amma mudin sukaki cika mishi burinshi tofa zasu hadune da fushin Hajjatiye , dan takan Tajuddeen zata tayar musu da hankali su rasa ina zasu sa kansu , amma banda Hajjatiye da bazasu turashi ba se sun ga yafara dawuwa kan hanya aiba tsoron shi sukeji ba , " Hajiya babba kinsan rikicin tsufan Hajjatiye fa tam " cewar Abbas da yake dariya yabar dinning din , bin bayanshi Hafiz ya yi , Ahmad de har lokacin be gama breakfast din ba jin an kira sunan hajjatiye ne yasa shi dariya ba ƙaƙƙautawa har kamar ze gware, watsa mishi harara Abbie ya yi sannan ya ce "wato uwar ta muce abin dariyarka ko, Ahmad ka tashi ka bar gurin nan kafin in dau spoon din nan in dake ka dashi"Abbie ya karasa maganarsa yana kokarin daukan cokali acikin spoon set,da sauri Ahmad ya mike ya dauki plate din abincin shi ya bar dinning din yana dariya,su kansu seda suka murmusa ganin har lokacin da Ahmad yabar wajan dariyar yake yi kuma sun san dalilin da yasa yake wannan dariyar duk be wuce irin rabuwar da sukayi da hajjatiye ba.
Ci gaba da maganar su da suke yi sukayi
" Ya Mubarak hakan da mukayi shine mafita , Allah ya sanya mishi albarka a karatunshi da aikinshi" uncle Hameed yafada jinjina kai Abbie ya yi ya ce" Abida kije ki sameshi dan Allah ki tausasashi ko ze saurareki, tunda kaff gidan nan yafi sauraran Hajiya khareema da kuma ke " cikin girmamawa anty amarya ta ce" in sha Allah zan sameshi ya ya "
Maida hankali kan Abbu Abbie ya yi ya ce " nikam yau me ya hana Hajiya hurairah fitowa cin abinci ne?"fuska da ɗan damuwa Abbu ya bashi amsa da"ba ta gida"ko kadan basuyi mamakin jin wai Hajiya hurairah bata gida ba saboda inda sabo sun saba da shegen yawonta.
haka kowa ya watse a dinning din .
Tun bayan shigowar shi dakin anty amarya ya iske Asrah nata sharara baccinta hankali akwance , tana rufe acikin bargo iya fuskanta ne awaje ta turo wannan ɗan karamin bakin nata , yanayin fuskanta kuwa kamar wacce take murmushi , murmushin gefen baki ya yi can kasan makoshinsa ya ce" sleeping beauty and also sarauniyar rashin ji" zama ya yi akan daya daga cikin lumtsattsun kujerun dake dakin . Bude envelope din ya yi yafara yaga addmission dinshi da su password dinshi da komai dayake bukata takardun duk suna ciki ajiyar zuciya ya yi ya kalli inda Asrah dake bacci yana tuna yazasu ƙa re da rigimarta inya tafi.
Yana zaune yana wannan tunanin anty amarya tashigo ta sameshi zama ta yi akusa dashi ta ce" bata tashi ba ko? " Gyada kai ya yi " Tajuddeen yanaga kamar bakayi farin ciki da addmission din naka ba ne " ka war da kanshi gefe ya yi kafin ya ce" me mika gani " " Tajuddeen gani mukayi fuskanka babu alamun farin ciki ! Shisa ka na tambayeka ai " kwantar da kanshi ya yi ajikin kujeran ya ce" dan ina farin ciki ai ba se na nuna kowa ya sani ba " " tofa wata sabuwa , shikenan to tunda ka yi farin ciki da hakan ,nidama ajikina nasan zakayi murna" ta faɗa tana murmushi " to yanzu_yanzu faɗamin in ka tafi zaka dinga zuwa hutu de ko?" da mamaki dauke akan fuskarshi ya kalli anty amarya yama rasa me ze ce mata jin tambayar da ta mishi na kancewar ze dinga zuwa hutu ,ganin irin kallo da yake mata ne itama yabata mamaki domin bata ga aibin abinda ta faɗa ba balle ya tsaya yana mata wannan kallon .
" Meye kakemin irin wannan kallon??" girgiza kai ya yi ya ce" bakomai ,ke yanzu tunanin ki ya ba ki inna tafi zandawo hutu ?"batare da yabata amsar da ta tambayeshi ba shima yasake jefa mata tambaya. Sake baki anty amarya ta yi tana ƙa re mishi kallo , bazatace Tajuddeen wasa yakeyi ba saboda basa irin wannan wasan da ita bama ya yi da kowa inya faɗi magana tofa har ranshi yafada kuma ba ya shakka ,duk yanda zata maka daci arai shi baze dameshi ba , tunda ta ji ya faɗi haka tasan daga cikin zuciyarshi maganar nan yafito.
Ƙaƙulo yaken dole ta yi ,ta ce " to ita Asrah din taka fa" maida kallon shi ya yi kan makeken gadon da take kwance ya yi , tana kwance tafara mutsu_mutsu tanason ta tashi . Ya ce" Asrah zamu dinga video call da ita " anty amarya de rike habarta ta yi tana mamakin irin wannan hali irin na Tajuddeen.
Yaye bargon da take lullube dashi ta yi ta tashi ta zauna a tsakiyar gadon , tana hamma.
Se mun haɗu gobe in mai duka ya kaimu da rai da lafiya.
Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.
Comment,like and share 🖋️🖋️
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹
Page 06
*_ story & written_*
By
*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)
*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*
~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*
🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️
Page 06
Bata lura da akwai mutane a dakin ba tunaninta ita dayace yasa ta ɓare baki zata fara kuka , " shiiiiii karki yarda ki so ma " tajiyo muryan Tajuddeen na ma ta gargadi.
kallon inda maganar yafito ta yi taga mommynta ne da tajuju zaune , saukowa ta yi akan gadon jikinta nasanye da kayan bacci na yara , wajansu taje ta zauna a tsakiyar su ,shafa gashinta Tajuddeen ya yi yana kallonta , ya mutsa fuska Asrah ta yi ta ce" mommy am feeling hungry" ta yi maganar tana daura hannunta akan cikinta, daukarta anty amarya ta yi suka shiga toilet ta yi mata brush da wanka ta naɗeta a towel tafito da ita , mayuka masu tsada ta dauko akan mirror ta fara shafa mata , mikewa Tajuddeen ya yi" anty amarya inta gama ina painting room" abinda ya faɗa kenan kawai ya fita , Asrah da ba ita ya yi wa magana ba da karfi ta yi magana yanda ze ji ta ta ce" toooooooo! Tajuju ina juwa " lumshe idanunshi ya yi bayan yaji abinda ta faɗa,anty amarya dariya ta yi kawai taci gaba da shiryata ,sannan ta haɗa mata breakfast dan dama ita kadaice batayi karin kumallo ba agidan.
Fitowa ta yi zataje part din Tajuddeen ta yi kyau sosai dan karamin bakin nan anty amarya ta sa mishi jan janbaki, tana sanye da yar karamar riga se wandon legis da take sanye dashi , har ta kusa isa part din Tajuddeen sekuma ta yi wani tunani, fasa zuwa part din ta yi ta juya zuwa part din yan aikin gidan mata , sanda_sanda take tafiya kamar mara gaskiya,dakin kaltume ta leƙa ta ganta tana kwance tana bacci dake dakin abude yake hakan yabata damar kallonta ,wuce dakin ta yi ta nufi dakin fatime , ganin dakin nata yana rufe babu ta yanda zatayi ta leƙa yasa ta kwanta akasa tana leka ta, fatime na zaune a ƙasa hannun ta rike da wani abu kamar aska kamar karfe yanada kaifi , irin zanen da yan da sukeyi ahannunsu wasu zakuga sunyi zanen kaɗangare wasu kuma zanen kalangu kowa da irin nashi wanda yanzu da zamani yacanza aka maida shi tattoo , sosai zanen fulawan da fatime takeyi ahannunta yaja hankalin Asrah dukda hannun nafito da jini.
Cike da yarinta ta tashi tana murmushi domin tasawa ranta se fatime ta yi mata , knocking kofar ta yi jin an bubbuga kofa ne yasa fatime ajiye abin hannunta , tazo ta bude kofar bataga kowa ba , saboda bata kalli ƙasa ba balle taga Asrah maida kofar take kokarin yi tarufe . Asrah ta ce" fatime ni ne fa" kallon ƙasa fatime ta yi da sauri dan batayi tsammanin yara bane dariya tayi ganin Asrah ce yar duƙul da ita agabanta matsa mata ta yi tabata hanya ta shigo sannan tarufe .