← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 60

Sashe 13

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bacci yakeyi amma ji ya yi kamar ana kallonshi hakan yasa ya tashi yana Dan mutsuke ido , sauke idon ya yi akan Ammi dake zaune a gefen gadonshi ta zuba mishi idanu kamar zata cinye kauda kanshi gefe ya yi ya tashi akan gadon ya nufi toilet ya yi brush ya wanke fuskanshi ya fito ya zauna akan gadon batare da ya ɗago kai sun hada ido ba .
Ammi girgiza kai ta yi dan tasan inzasu shekara a haka Tajuddeen bazece mata komai ba ta ce " ina kwana Tajuddeen?" tunda yake be taba jin kunya ba irin na yau saboda shi babu agender kunya ma arayuwarshi amma yau se yaji ya kunyata a gaban Ammi, na gaidashi da ta yi hakan yasa ya ji kamar be kyauta ba , kamar yadda yake kuma nature shi yake kullum babu walwala atattare dashi murya ciki_ciki ya ce " ina kwananki " da sauri Ammi ta kalleshi tana tantaman shin maganar nan da gaske daga bakin shi ya fito ko kuma kunnenta ne ya mata gizon jin da ta yi saboda a iya sanin ta bata taɓa jin Tajuddeen ya gaisar da kowa ba saboda hatta a makaranta an sha yin wannan case din ɗan kuwa ko mutuwa malami zeyi Tajuddeen baze taɓa gaisheshi ba,har gwara malamin da yakoyar da su a gida dake wannan ya shafi addini yana iya kokarin shi wajan cewa ya uztaz din "barka da zuwa ya hanya"shikenan iya maganar kenan har malamin ya gama koyar da su ya tafi.

Bata gama wannan tunanin ba ta sake tsinkayan muryanshi yana gaisheta. Muryanta na fita da sauri_sauri ta ce" lafiya lau Taj " tundaga nan kuma shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai , matsowa kusa dashi Ammi ta yi gabaki ɗaya yanayin ta ya sauya kallo ɗaya za'a mata a fuskanci tana tattare da damuwa.

" Tajuddeen jibi ne tafiyanka banason ka tafi da fushin Amminka aranka , shisa nazo na roki yafiyarka daka yafemin akan abinda na maka , kayi hakuri karka tafi dani aranka wallahi ina azabtuwa da yanda kake kin kulani da kuma sauran yan uwanka nayi maka imani da Allah babu wanda yataba sa'ka tsanarka aranshi duk muna sonka ,kaine kawai ka cire kanka daga cikinmu ban taba jin inason wani abu arayuwata ba irin kai ɗana dan Allah dan Annabi ka yafemin wallahi abinda yafaru awannan lokacin sharrin shaidan ne " folding din hannunta ta yi tana ba shi hakuri ga idonta da ke tsiyayo da ruwan hawaye , be taba tunani akwai ranar da arayuwarsa ze zo ya tsaya ya saurari Ammi ba saboda kullum laifinta yake gani ,ita ya yi holding responsible na rushewar farin cikinsa amma da yake tsakanin ɗa da uwa se Allah yasa ya ji , baze jure shareta ba har iya rayuwarsa dukda kuwa girman laifukan da ta mishi , (duk wani ɗan arziki kuma ɗan halak baze taba kaunar ganin hawayen Mahaifiyarsa ba sede kuma in wannan ɗan bayida albarka saboda duk duniya babu abinda zaka gani ka ji ko kuma ka tuna kana da ita ka ji dadi kamar mahaifiya , sune jigon rayuwarmu sunyi mana komai alokacin da bamuda komai muna naɗe acikin tsumma ta kula da mu ta yi mana duk abinda ze samu farin ciki. ta sadaukar da nata farin cikin aduk saboda inganta rayuwarmu kuma har izuwa girman mu , wallahi duk wanda yakeson gamawa da duniya lafiya to yabi Allah da manzonshi Annabi Muhammad saw sannan kuma yabi mahaifiyarsa sau da kafa domin in karasa ta bazaka taba samun wata kamarta ba har duniya yanaɗe, Allah kabamu ikon ci-gaba da yiwa iyayenmu biyayya , ya Allah kamar yanda suka faranta mana Allah kabamu ikon faranta musu Duniya da lahira .)

Juyawa ya yi rungumeta ya kwantar da kanshi akan kafadarta yana sauke ajiyar zuciya , a iya saninshi tunda yasan kanshi be taɓa jin shi ajikin mahaifiyarsa ba se yau hakan yasa ya ji shi gaba daya wani farin ciki ya mamaye shi gaba dayanshi kamar ba shi ba, Ammi kam se godewa Allah takeyi da ya nuna mata wannan rana da ta kasance tare da ɗanta mafi soyuwa a gareta shafa kanshi ta yi ahankali ta furta " Ubangiji Allah ya yi maka albarka yabaka Sa'a aduk abunda kasaka agabanka ya karemin kai aduk inda zakaje ka " " ameen " kawai ya ce raba jikinsu ta yi ta ce ta ce " tashi muje dinning muyi breakfast na fara jin yunwa " har cikin zuciyar shi baya son zuwa amma bayajin ze iya ja da maganarta ayanzu , mikewa ta yi ta riko hannunshi suka fito .

Duk suna zaune a dinning table anyi saving dinsu breakfast amma babu wanda yaci suna jiran fitowar Ammi ne sufara cin abinci, Hajiya khareema dama ita ba wani hulɗa takeyi da su ba yasa bata fito ba tana part dinta in takaice muku ma ba ta fiya cin abinci tare da su ba.

Ammi suka hango tana saukowa daga stairs hannunta rike da na Tajuddeen ware idanunsu sukayi sosai dan son tabbatarwa shin dagaske Tajuddeen suke gani da Ammi ko de basu gani da kyau ba.idan kuwa dagaske suɗin ne ta yau ranar Sa'a ce agaresu shine abinda suka daɗe suna jiran su ga ranar da zasuga haka yau Allah yanuna musu . Har su Ammi da Tajuddeen suka iso dinning table din basu sani ba suna ta al'ajabi hade da farin ciki zama Ammi da Tajuddeen sukayi Ammi da kanta ta yi saving din Tajuddeen breakfast yafaraci batare da ya kula kowa dake wajen ba , Ammi ta ɗan kalleshi tana ɗan taɓa hannunshi ɗago kai ya yi ya kalleta yanda babu wanda zejita ta yi mishi rada a kunne " baka gaishe da Abbie din ku ba da sauran " shuru ya yi be yi yanda ta ce din ba yaci gaba da cin abincinshi ,sude duk ido suka zuba mishi Abbas, Hafiz, Ahmed se murmushi sukeyi sukansu sunyi farin cikin haka da yafaru saboda duk acikin kannensu sunfi kaunar Tajuddeen kullum basu da burin da yawuce suga suna tare dashi suna hira na farin ciki da annashuwa amma hakan beyuba .
Seda ya kusa cinye breakfast din shi tukun kanshi na akasan be ɗago ba ya ce " ina kwana" gaisuwar ya yi be kira sunan kowa ba murmushi kawai sukayi suka amsa atare , haka sukayi breakfast dinsu yau na musamman duk da Tajuddeen tunda ya yi wannan gaisuwar be sake ce musu komai ba har ya gama ya mike ya yi part din anty amarya dan duba Asrah shi duk a tunaninshi tana can tana bacci bayida masaniya akan yau ta shiga school , yana daff da fara haura upstairs Hafiz ya ce " Asrah fa sun tafi makaranta itama yau ta jonasu" kallon Hafiz ya yi ya ce" okay " yawuce part din shi .

Abbie ne ya kalli Ammi ya ce " alhamdulillah hamdiyya gwara da kika je kika samu kukayi magana dashi naga yafara saukowa yanzu , Allah ya sassauto mana da irin wannan zuciyar ta shi " dukkansu da ameen suka amsa amma banda Hajiya Hurairah da ranta ko kadan be so haka ba Allah_Allah takeyi a watse ta je ta samu Hajiya khareema ta shafa mata labarin abinda yake faruwa , domin hakan barazana ne ga kudirin su .

Tun daga safe har yanzu da ya kasance karfe biyar saura sun kusa tashi , Fu'ad Abubakar daula ya shiga ajinsu Asrah yafi aƙirga dan kawai ya kalleta , su kam sunata murna ankusa tashi su dawo gida .
Lokaci nayi aka buga kararrawar tashi driver's din sune suka zo suka daukesu zuwa gida .

Misalin ƙarfe 5:30pm na yamma malam Mamman yashigo gidanshi hannunsa rike da wata atamfa me saukin kudi dakin Maryam yashiga yasameta suna zaune suna shan shayi da biredi ita da Asmita zama ya yi fuska asake ya ce " yar baba gama kizo muje mukai ɗinkin kayan kin nan dana siya miki " cike da yarinta Asmita ta ce" to baba" kallonshi Maryam ta yi ta ce" malam senaga kamar yamma ta yi da kun bari ko go...... "be bari ta karasa faɗan abinda takenso faɗa ba ya yi saurin ta ran numfashinta ta hanyar faɗin" ah ah Maryamata yau zamu kai dinki dan gobe mukayi da telan ze gama mata kayan " sam hankalinta yaki yarda da fitan da zasuyi amma gudun bacin ranshi yasa ta yi shuru , zuciyarta se sake_sake yake mata ga zuciyarta dake bugawa sosai , ka sa ci gaba da shan shayin ta yi ji tayima ba ya mata dadi ko kadan , Asmita na kammalawa ta ce" baba na gama " " yar baba tashi muje " saka mata hijabi ya yi ya dauketa suka fito har bakin kofar gidan Maryam ta rakosu se bye-bye Asmita take mata da murmushi me ƙayatarwa akan fuskanta har suka bacewa ganinta sannan ta koma cikin gida , ji ta yi abu me sanyi ya sauko mata akan kumatunta da sauri tasa hannu dan jin menene wannan ruwan hawaye ta gani aranta ta ce" to menene yasa idona yake zubar da ruwa ?Allah kadawomin dasu lafiya " ta shiga daki ta zauna.
Chapter 13 · 0% Book details