← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 60

Sashe 52

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shurun da taga kowa ya yi basu tambayi waye a asibiti ba,yasa ta fara tunanin to waye ba lafiya.
Se kuma ta yi tunanin ko LTG aka kai asibiti tunda jiya bashi da lafiya.
Tabe bakinta ta yi, acikin zuciyarta ta yi maganar amma bata san cewa ya fito fili ba.
"Allah yasa ma shine"kallonta aka yi nan ta fahimci an ji abinda ta faɗa sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana wasa da spoon.

Hajjatiye ta ce "sanariya ke da waye haka". innalillahi ga dariya ga kuma basu isa su yi shi ba yanzu se ran kowa ya kusan ɓaci a wajen,wai sanariya, Sabriyah din ne bata iya faɗa ba take cewa sanariya.

Salim duk yanda ya so rike dariyar sa,abin ya gagara se fa da ya kwashe da wani dan banzan dariya kai kace wani zararre ne.
Cikin basaja ya soma faɗin.
"Haba Fatime taya za ki sakamin ruwan tea da yawa duba kiga duk na shanye,ashe zan iya" maganar yake yi amma dariya ya ci karfinsa.
Kowa na wajen ya gano sa.banda Hajjatiye.
Watsa mishi harara Abbie ya yi,irin zamu haɗu din nan.

Dakyar ya tsagaita da dariyar.
Hajjatiye ta ce"amma yaron nan an yi ja'iri, saboda kawai ruwan shayi ya yi yawa ka shanye ne yasa ka wannan dariyar,to zakaci kwal ubanka dakai da tsiyar tsinantakar ruwan shayin".

Tashi kawai ya yi yabar wajen dan ya lura inde Hajjatiye tana magana tofa baze fasa dariyar ba,har ta gano ita yake yi wa dariya,ga kuma kallon da yaga Abbie na yi masa.

Kammala breakfast din aka yi suka dawo falo suka zauna,anty Sameera na rike da baby a hannunta.
Ta cewa su Zoya.
"Ku din kun shirya ne" "eh a shirye muke"duk suna sanye da hijabs.

Sabriyah de yau ba wani son yin magana take yi ba domin abinda ta ji, jiya dashi ta kwana a ranta,duk tunaninta yanzu ya koma ne ta kan ta ya zata fara sanin menene abinda LTG yake shiryawa.shin taya zata shiga jikinsa yanda zata dinga sanin duk wani abinda yake shirin yi.

"Sanariya!,zo ki kira LTG kice mishi,zamu je asibiti"Sudais ya faɗa,yana tsokanar ta.murmushi ta yi dan ta gane tsokanar ce,wato Hajjatiye de ta sa mata wani suna daban.

Ba dan ranta yaso ba ta mike tana tambayar kanta "dama ba ya Taj bane a asibitin ba!?,to waye ba lafiya haka!?",da wannan tunanin ta shiga part din nashi ,ko sallama ba tayi ba ta kutsa cikin bedroom dinsa.

Baccinsa yakeyi gently,his innocent face looks so cute.
Yana cikin bargo ya rufe ko ina a jikinsa, fuskarsa ne kawai a waje.

"Mtsssw!a kwai kyaun fuska kam,amma babu na zuci.mugu kawai".ta faɗa a ranta.
Karasawa jikin gadon ta yi da niyar tashinsa a bacci da yake yi.wani tunani ta yi.
"Uhmm,yanzu ina tashinsa ze hau ni da faɗa kamar wani ubana,gwara in je in samu ya Sudais in ce masa,ya ce bazeje ba kawai "ta faɗa a hankali.

Tana gama faɗar maganar,ta ji an ja hijab din ta,a tsorace ta kai idonta kan fuskarsa domin ita ta ɗauka ya farka ne ya rike mata hijab,ashe cikin bacci ne ya juya ya daura kansa akan hijab dinta,da bata san ya aka yi ta daurasa kan gado ba.
A hankali ta sa hannuta ta fara kokarin jan hijab din nata yanda baze tashi ba.tana kallon kyakyawar fuskarsa,a lokaci daya kuma tana jan hijab din ta.
A cikin bacci yasa hannu ya riƙo hijab din nata gam a hannunsa ya cigaba da bacci.
Zaro ido ta yi ta bude baki ta ce"na shiga ukuna,yau in ya Taj tashi se ya kasheni"ta yi maganar idonta ya fara raina fata.
Wani irin juyi ya yi da,wanda kafin ta ankara taji ta gaba daya ta faɗo jikinsa.

Ji ta yi kamar zata yi fitsari a wando.ta rasa wata kalma zata yi amfani dashi wajen ceton kanta in LTG ya farka ya gansu a haka.

Jin mutum ya faɗo kansa ne,yasa ya bude manyan rikitattun idanunsa da sukayi ɗan yi ja saboda baccin da be samu a wadace ba, hatta golding eye balls din seda suka ɗan canza kala.

Idanunsu ne ya sarke cikin na juna.bakaramin tsorata ta yi ba da ganin idonsa ga kuma irin kallon da yake mata,babu abinda take tunawa irin rabuwar da sukayi daren jiya ga shi yanzu ta kawo kanta da kanta.
Shi kuma kallon da yake mata,kallon me yakawo ki dakina har kan gado na.

Hannunsa yasa ka ya rike ta gam yanda bazata samu damar guduwa ba,tana kwance akan kirjinsa, fuskarsu na fuskantar na juna.

Bude baki ya yi ze yi magana,tsoron jin abinda ze furta mata ne yasa da sauri,tasa yatsan ta,guda daya ta daura akan libs din sa.tana kallon cikin idanunsa,saukar da idonsa ya yi ya kalli hannunta da ta daura masa akan libs,watsa mata harara ya yi,duk da hakan bata cire ba.

"Ya Taj,an ce ne in zo in tasheka zamu je asibi.....".
Wani mugun kallo ya watsa mata da ya sa ta gagara karasa maganar da take masa.
Hannu yasa ya janye yatsan nata ya maida shi baya ya matse, ƙara ta sa sakamakon zafin da taji ya ziyarci hannunta.
"Kirana kika zo yi shine se kin hau har kan gado na!?"ya tambaye ta murya a narke ba kamar yanda ya saba yin magana ba.
"To ai na baka hakuri"ta faɗa tana murguɗa masa baƙi,tsurawa dan karamin baƙin nata da take murguɗawa ido ya yi,yana jin kamar yasa almakashi ya gimtse sa.
"Tashi a jikina,wato kinga farar fata, mekyau yana shining, shine za ki kwanta akai,yafi na wa'yannan nan kazaman yan iskan samarin naki".tura baƙi ta yi jin abinda ya faɗa.
"Bazaki tashi min a jiki bane,ko se na yi wurgi dake tukun nan!?"ya faɗa yana jefa mata harara.
Kamar zata fashe da kuka dan takaici,ta ce"to ka sa'ke ni mana".
Kura mata ido ya yi,yaga yanda ta ke mutsu_mutsun kwatar kanta.da hannunsa guda daya ya rike ta amma ta gagara kwacewa.

"Meye kike shiryawa!?"kamar saukar aradu haka taji tambayar ya sauka a kunnenta,dago idonta ta yi,cikin tashin hankali,murya na rawa ta ce"bangane abinda kake nufi ba".
Murmushin gefen baki ya yi irin na bakida hankali, ya ce"ina saurayin naki yake!?,ina guje miki yin aikin danasani saboda rashin sanar da ni inda yake dede yake da jefa rayuwar ki, cikin hatsari,ni rayuwata,na ƙasa ta ce,in na mutu nayi shahada,amma ke in mutum daya ya mutu ta dalilin ki,to se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa,je kiyi tunani akai".gaba daya ya kashe mata jiki da maganganunsa,kenan hakan yana nufin ya san tayi waya da Fu'ad kenan?,taya akayi ya san abinda suke shiryawa.
Meye hakan yake nufi to, Fu'ad ya sanar da ita cewa LTG shine yake kokarin zaluntar al'umma,shi kuma LTG ya ce mata,in mutum daya ya mutu ta dalilinta se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa.

Har ya sa'ke ta bata ma sani ba,ta faɗa duniyar tunani.

Ɗagata ya yi a jikinsa ya tashi zaune ya barta akan gadon,miƙewa tsaye ta yi,jiki a mace.

"Kai ma ai zaluntar al'umma ka ke kokarin yi,ka kuma cutar da ni,da yar uwata".
Be kalli inda take tsaye ba ya bata amsa da.
"Ke ba ki kai matsayin da zan tsaya ina miki bayani ba,je ki yi duk yanda kika gadama".

Da gudu ta fice a dakin,tana gudu numfashinta na sauka da sauri sauri,kirjinta ya rike,sun sa ta a tsaka me wuya,yanzu da maganar waye a cikin su tasan zata yi amfani?.

Bayan balcony ta je in da babu wanda ze ganta,ta zube akan guiwowinta tana maida numfarfashi.
Se da ta kusa 20minute a haka kafin ta samu nutsuwa.
"Ko ma me ze faru sede ya faru amma bazan taɓa juyawa Fu'ad baya ba, wannan alfarma ne da ya nema a wajena taya zan watsa mishi kasa a ido in ƙi cika masa burinsa na son ganin al'umma tasamu zaman lafiya".
Ita kadai take magana kamar wata zautacciya.
Se da ta gama samun nutsuwa kafin ta mike ta koma main part Sudais, yana ganinta ya ce"Sabriyah ai na kika tsaya ne!?,ina LTG?"jiki ba kuzari ta ce "ya ce wai baze je ba".
Gyada mata kai ya yi.

Shiga motar sukayi suka wuce asibitin.

shigowar su dakin da aka kwantar da Asmita sun samu ta na jingine da filo.Saghar na gefenta ga kuma fruit agabanta,tasha kadan ta bari,jin sallamar su ne yasa suka maida idonsu baƙin kofar.

Mamaki da al'ajabi lokaci daya ya kama Sabriyah ganin Asmita kwance akan gado ga kanta dake nade da bandage,da gudu ta shigo dakin,ta zauna akan gado, bata gajiya da kallon Asmita da itama din ita take kallo.wato wayo sukayi mata,su ka dinga ce mata Asmita na hutawa,ashe basa son tasan an yi aikin ne.

"My Jerry yaushe akayi miki aikin?,yanzu ya kike jin ki!?,me yake miki ciwo yanzu!?, sannu kinji".ta watso mata tambayoyi ba tare da ta bata damar amsa mata ko daya ba ta sa'ke cewa.
"My Jerry,kanki ba ya Miki ciwo ko!?"murmushi kaɗan Asmita ta yi.
Murya na fita a hankali ta bata amsa da.
"My Tom ina lafiya".
Zata sake yin wata maganar Saghar ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.
"Ba'a son ta dinga magana sosai".
Gyada masa kai ta yi tana riƙe hannun Asmita.
Sannu su kayi mata da jiki kafin suka zauna suna.

Har karfe hudu na yamma suna tare a asibiti mazan kuma sun tafi wajen aikinsu.

Kullum se sunje asibiti duba jikin Asmita, Alhamdulillah jikinta yana sauki sosai, Sabriyah ta fara zuwa school an sa ta a jss 2,an samo malamin da yake koya mata karatun addini a gida,kuma ba laifi tana ganewa sosai da sosai.in ta dawo gida kuma su Parsa haka suke haɗuwa su sa'ke koya mata duk wani abinda bata gane ba,sune malaman lessions din ta.
Chapter 52 · 0% Book details