Sashe 8
Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama ta yi akan gadon dakin tana kallon fatime da taci gaba da zanenta tana runtse ido saboda zafin da takeji.
Kiran sunanta Asrah ta yi" fatime!" "na'am Asrah ya akayi?" saukowa kasa Asrah ta yi, ta yi zaman dirshen agabanta kamar me neman gafara " fatime nima kimin irin wannan zanen inaso " zaro ido waje fatime ta yi" ke rufamin asiri karkisa akoreni dan Allah" girgiza kai Asrah ta yi ta ce" noo ai mommy ce ta ce inzo kimin dazun taga kinayi" ko ajikinta ta shararawa fatime karya, kallonta Fatime ta yi cike da tuhuma domin takasa yarda da maganar Asrah din taya anty amarya zatace wai ayiwa Asrah wannan zanen tana yar karama da ita.fahimtar da ta yi fatime bata yarda da ita bane yasa ta mike tsaye da niyyar tafiya dan Asrah akwai shegen wayo ta ce " shikenan bari inje incewa mommy kince wai bazakiyi ba " dasauri fatime tajawo hannunta har hantan cikinta yakaɗa ,saboda ita kaffa_kaffa takeyi bakaramin so takeyiwa aikinta ba kuma ta lura mutanen gidan nada kirki , insuka koreta batasan aina zata samu irin wannan gidan ba .
" Haba Asrah meyasa zakimin haka bakince mommyn kice ta ce ayi miki ba.. to zo ki zauna " maƙe kafada Asrah ta yi " no zancewa mommy kince bazakiyi ba" jawota ta yi ta zaunar da ita akasa ta ce" ah ah zan miki mana wani kallan zane zan miki " murmushi Asrah ta yi cikin murna da farin ciki ta ce " tajuju zakimin " tana magana tana cire rigarta ta ajiye akan gadon fatimen, juya mata baya ta yi , itade fatime yau tana ganin ikon Allah babu yanda ta iya haka tabude jakarta ,tafito da sabon karfen zanen tasa laita takona bakin karfen seda yahuce sannan ta daurashi abayan Asrah fargaba fal cike a ran fatime amma inta tuna kancewa anty amarya ce tace ayiwa Asrah se taji nutsuwa ya ziyarceta.
Gefen bayanta na hagu fatime tasaka karfen gabanta na faduwa tafara rubuta Tajuddeen, runtse ido Asrah ta yi da karfi jin azaban zafin da ya ziyarceta nan take ruwan hawaye yafara zarya afuskarta , dake ita tasa kanta yasa ta danne kukan ya ƙi fitowa dan tasan sarai ta fara wannan kukan fatime zatace bazata mata ba .
Haka fatime tagama mata zanen sunan Tajuddeen abayanta da manyan harufa gakuma dan karamin fulawa da tayi akasan sunan , se tsatsafo da jini wajan yakeyi ya yi jaa sosai ya ɗan kumbura abinka da farar fata , yar towel fatime tasaka da warm water ta goge mata bayan nata ,tadan gasa mata shi sannan tasa mata toka , zagayowa ta yi ta gaban Asrah taga yanda idonta ya yi jaga_jaga da hawaye hancinta shima ya yi ja ga majina , sa towel din ta yi ta goge mata fuskanta tanayi mata sannu.
Tashi ta yi tabawa fatime rigarta tasaka mata sannan tafita jiki ba kwari dake ita ce ta ce tanaso mit ko tari batayi ba balle ajita , ahankali_hankali take tafiya ta nufi part din Tajuddeen abude tasamu kofar falon,tashiga wucewa direct bedroom dinshi ta yi ,azaune ta sameshi yana game a tv tsayawa ta yi daga bakin kofar tana hawaye ,ɗago kai ya yi yakai kallonshi inda ta ke tsaye ganin yanda jikinta duk asanyaye ga fuskarta da ya yi ja tsabar kuka , kashe Tv ya yi.
Inda take tsaye ya isa yadauke ta suka koma kan kujera yana tambayar meya sameta amma ta yi mishi shuru taƙiyin magana harya gaji da magana, shi zaton shi ma ita da yan gidan ne , cikin rashin sani yakai hannunshi bayanta yana shafawa hade da rarashinta , taɓo inda aka mata zanen ya yi batare da ya sani ba wani gigitaten kara tasaka da seda ilahirin part din nashi yadauka, kafeta ya yi da ido yana nazarin ta na wasu sakonni , juyar da ita ya yi ya sa hannu ya cire mata rigar jikinta , sauƙe idonshi ya yi akan sunanshi dake rubuce agadon bayanta ga wajan ya yi ja sosai ,runtse idanunshi ya yi yana ji tamkar ajikinshi ne, bakaramin ɓaci ran Tajuddeen ya yi ba ,daka mata tsawa ya yi ya ce" uban waye ya miki wannan zanen abayanki ?" cak lokaci daya kukan da takeyi ya tsaya tafara tsilli_tsilli da dara_daran idanunta, tsoronshi ne Yakamata saboda bata taɓa ganinshi a irin wannan yanayin ba.
Sake daka mata wani tsawan ya yi,murya na rawa ta ce" Ni ne nacewa fatime tamin sunanka" watsa mata harara ya yi,kafin yadauketa akafadarshi suka fito tsakiyar main falon gidan .
Murya da karfi yafara kwala kiran sunan " fatime!fatime!fatime" kowa dake cikin gidan seda sukaji shi , babu shiri duk suka fito , baiwar Allah fatime jiki na kyarma hantar cikinta se kaɗawa yakeyi haka tafito ta tsaya a gefe hankali atashe , Abbu ne ya ce" meyafaru Tajuddeen?" be furta mishi komai ba yana tsaye yana watsawa fatime mugun kallo , Abbie ne ya ce" meyake faruwa ne kake wannan kwala mata kira duk ka tayar mana da hankali "
" saboda nishadi na yi , ita nakira ai bance kowa yafito ba " ya yi maganar shi kai tsaye batare da wani shakka ko wani abu ba be kuma kalli inda suke ba . " Ke zo nan " jiki anarke fatime ta karaso kusa dashi ta tsaya . Zura hannayenshi ya yi a aljihu ya ce" uban waye yabaki damar yiwa wannan yarinyar zane da karfe?" kulululu haka ta ji cikinta yabada ƙara, Hajiya khareema na upstairs tana tsaye tana kallon abinda yake faruwa se tabe baki takeyi .
Mamaki sukayi jin abinda Tajuddeen yafaɗa ga kuma fatime takasa cewa komai se ma rawa da jikinta yakeyi da hawaye ,da sauri Hajiya babba ta karasa gaban Asrah dudduba jikinta ta yi bata ga komai ba hakan yasa ta cire mata rigar jikinta ta juya bayanta , sosai ranta ya sosu saboda jikin Asrah danyen jikine da ita kuma yarinya , jikinta yasaba da hutu bazata iya jure zafin da ze mata ba kafin ya warke,itama kanta ranta yabaci , duk kallon bayan Asrah din sukayi duk basu ji dadi ba runtse idanu anty amarya ta yi dan bazata juri kallon bayan ƴarta a haka ba. amma bazasu yanke hukunci ba se sunji ta bakin ita fatime din hakan shine adalci.
Hajiya babba ce ta soma magana " fatime meye yasa za ki mata wannan zanen bakiga itadin yarinya bace , da hankalinki da tunaninki" goge hawayen da takeyi ta yi sannan ta kwashe duk yanda sukayi da Asrah ta faɗa musu ta kara da" wallahi ina tsoron rasa aikina shisa na mata gudun kar anty amarya ta ce , banbi umarnin ta ba akoreni " dukkansu sallallami sukayi da rike baki tabbas sun sani Asrah batajin magana ga kuma karambani zatayi fiye da haka duk kallonta sukayi sun ƙasa ce mata komai, ita kuma Asrah se wuri_wuri take yi da ido kamar wacce ta yi sata wa sarki,Abbie ne yacewa fatime ta koma dakinta tare da mata gargadi karta sake maimaita irin wannan kuskuren, godiya ta yi musu hade da basu hakuri ta wuce dakinta kaltume ma tabi bayanta.
Tajuddeen kam tsaban takaici ma kasa magana ya yi,ya ja doguwar tsaki yajuya ze wuce part din shi , Asrah ta fara binshi ,juyawa ya yi ya kalleta " karki yarda inganki a part dina yau tunda bakyajin magana " fashewa ta yi da kuka ta zauna zaman dirshen akasa tana kuka , part dinshi yashiga yasa key yazauna yaname tausaya mata ,kara jinjina rashin ji da karambanin Asrah ya yi.
Daukanta Ammi ta yi ta wuce da ita part dinta ta mata wanka ta shafa mata magani awajen sannan tabata pain reliever, ta samu ta yi bacci .
Anty amarya,Abbu,Abbie ,Hajiya babba su kadai suka rage afalon suna jinjina lamarin Asrah.
Haka tasha baccinta har yamma ya yi su iklas suka dawo makaranta .
" Dad ! Meyasa yafini komai duk abinda ya nema yana samu , kuma familyn su yafi namu karfin suna , babanshi shine tsohon governor Maiduguri , dayan ƙanin babanshi babban alƙali ne a court of appeal , dayan kawunshi kuma babban doctor ne da kowa yasanshi a fadin duniya . wallahi dad na tsani Tajuddeen Mubarak Bishara! natsane shi!" ya ƙarishe maganar da karfi yana dukan glass table din dake kusa dashi seda ya fashe, matashin yarone wanda kusan zasu iya jerawa a shekaru da Tajuddeen , kyakkyawane shima fari , yanda yake magana zallar wutar ƙiyayyar Tajuddeen ne a cikin kwayar idonshi .
Wani babban mutum ne a gefenshi wanda daga gani mahaifin shi ne , da fa kafarɗar shi ya yi ya soma Magana" Fu'ad kenan duk yanda ka kai da tsanar su baka kaini ba , musamman inna tuna lokacin da nake neman kujeran governor ,saboda Mubarak Bishara na rasa kujeran nan daga karshe shine ya mulki Maiduguri,kuma ni zan tsaya maka se kafishi komai baze taba nasara akanka ba ,se ka nuna mishi kaidin jinina ne , Fu'ad Abubakar daula "
Murmushi ya yi ya ce" Dad sekayi alfahari dani amatsayin ɗanka domin ni din nan dakake gani nafika rashin imani!se na zamewa Tajuddeen babban matsala a rayuwarsa bama shi kadai ba gaba daya mutane se na zame musu bazana" kecewa sukayi da dariya harda tafawa kamar wasu abokai.
Damaturu