← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 60

Sashe 26

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rameesa da iklas sune suka rage idon su biyu sauran kam duk sun yi bacci a dakin nasu dama haka sukeyi zasu zo dakin Rameesa da iklas su yi hira. suma su koma dakin su duk da a haɗe yake kofa ce kawai ya raba su,yaran matan part din su daban. babban falo ne da two bedrooms komai na jin dadi akwai aciki duk inda suka gadama suna kwana kuma kowa ni bedroom akwai manya_manyan gadaje har guda uku.some times a daki ɗaya suke kwana dukkansu.yau ma haka bayan sun baro dinning suka shigo dakin su Rameesa suna cikin hira umaisha ta ce zataje ta dauko musu ruwa da snacks, kafin ta dawo ne Parsa da Zoya suka yi bacci ya rage saura Rameesa da iklas ne idon su biyu.
Shigowa ta yi tana kuka harda shesheka tasowa sukayi suka je suka rike hannunta suka zauna abakin gado suna tambayar ta me ya faru dakyar ta iya faɗa musu abinda ya faru tsakaninta da Sudais,jikin su ne ya yi sanyi jin saura kadan yau Sudais yayiwa umaisha aski da wuka,sosai suka dinga bata hakuri har ta yi shuru sannan suka kwanta bacci.

A bangaren Sudais kuwa yana shiga part din shi ya tarar da Jawan da Saghar aciki da mamaki yake kallon su kafin ya shigo ya zauna yana faɗin "wai ku bakwajin bacci ne?"kallon shi sukayi a tare Jawan ya ce"ya Sudais wannan ɗan renin hankalin na biyo ya faɗa mini yaushe ze dauki hutu muje wajan hajjatiye, dan Wallahi muka bari tazo mu ba muje ba mun shiga uku tunda abbu da Abbie ma kafin suyi tafiya seda suka ƙara jaddada mana akan zuwan namu amma Saghar kam ya yi burus da zancen"rufe laptop din gabanshi Saghar ya yi ya ce"ya Sudais shi baze gane bane aiki ya mini yawa amma nan da next week se mu shirya mu tafi"shi de Sudais bece musu komai ba se binsu da ido da yake yi, saboda yasan sarai su Abbie suka dawo suka ji basu je ba ransu ne ze ɓaci,yana kokarin musu magana kira ya shigo wayarsa picking ya yi yasa a kunne.
Wata tausassan murya me zakin gaske da kuma amo yana da kauri irin muryan jaruman maza da suke cike da izza,isa,gadara,haɗe da kuma umarni ne ya sauka a kunnen Sudais,ya ce "sa wayar a handsfree "yanayin yanda ya yi maganar kadai ma ya isa ya kwadaitawa mutum yaso ganin wanene mamallakin wannan murya,domin yanda ya ke fitar da maganar ma kadai abin burgewa ne.
Kamar yanda ya faɗa haka kuwa Sudais ya yi yana murmushin mugunta ya saka wayar a handsfree din,kallon Sudais suke yi suna jira suji waye ze yi magana har kusan minti biyar kafin ya futar"ku shirya gobe ku tafi"iya abinda ya furta kenan 'kitt' ya kashe wayar dariya Sudais ya yi dan yasan yanzu kam tunda ya basu umarni yasan dole su je kuma a gobe_goben domin basa jayayya da maganar shi kallon Sudais Saghar ya yi ya ce"ya Sudais meyasa kafadawa LTG.Taj maganar tafiyan!?" dariya me yar sauti Sudais ya yi ya ce "ko kadan Ni banyi wannan maganar dashi ba,duk wani motsin ku yana kallon kowa, kaff gidan nan akwai cameran tsaro, part biyar ne kawai babu daga part din Ammi, Ammuh, Hajiya babba,Anty amarya,ummah.nan ne kawai babu a part din iyayenmu mata ne kawai babu CCTV camera" dariya Jawan da Saghar sukayi.
"Yanzu de zuwa Sudan ya kamamu gobe wajan hajjatiye,amma su ya Sahil sun sani kuwa!?"cewar Saghar "malam kowa fa yasani kude kuyi booking tickets kawai"Sudais ya faɗa yana nufan bedroom din shi.hira sukaci gaba da yi se around 12:00 na dare kafin kowa ya nufi inda yake kwana.

LAGOS ORIENTAL HOTEL

Bayan sun iso hotel din da yake suna ciki an kawo musu lafiyayyun abinci sukaci,nan ya zauna yana jan su dan hira saboda su sa'ke dashi, aikuwa hakane yafaru domin yanda yake musu kamar ya daɗe da sanin su,lokaci daya suka saba dashi,duk wani motsin Sabriyah yana kan idonshi ji ya yi yafasa abinda ya yi niyar aikatawa da ita saboda kallon mata a gareshi ya fara mata duk wani abinda tayi burgeshi takeyi baya gajiyawa da kallonta, Asmita ce ta mike zata fita Sabriyah ta ce "my Jerry ina zakije!?"se da ta bude kofar kafin ta ce "zan leka cikin hotel din ne in dawo!"ta fice, dawuwa kusa da Sabriyah ya yi ya zauna cikin nutsuwa yafara mata magana.

"Sabriyah nasan kinsan dalilin da yasa na dauko ki!?nayi ne saboda in samu wacce zata biya mini bukatata, but bansan meyasa ba tunda na daura idona akan ki se naji bana bukatar yin mu'amalar banza dake,ni bazan boye miki ba kullum sena kwanta da mace amma yanzu da ina tare dake se naji bana bukatar hakan! lokaci daya soyayyar ki ya kama zuciyata yanda bakya tunani.bansan ta ya'ya zan miki bayani yanda za ki fahimta ba,ji nakeyi akwai wata alaƙa me karfi tsakanina dake tunda jimawa wani irin lamari me karfi nakeji a tattare da ke Sabriyah. ki bani damar nuna miki soyayya ta har ki zamo mallaki na."kamar wani mutum mutumi haka Sabriyah ke kallon shi ko kyafta ido batayi ji tayi maganar nashi wani bankwarakwai ta ma rasa wani irin amsa zata bashi saboda ta fahimci he's a good guy amma bazata iya bashi damar soyayya ba saboda akwai sarkinta acikin zuciyarta duk da bata sa rai akan zata ganshi a rayuwarta ba amma ji takeyi intayi soyayya da wani ɗa namiji kamar taci amanar tajuju ne.

"Meyasa kakeson yin soyayya dani?shin babu wata mace a rayuwarka ne!?"ta yi mishi wa'yannan tambayoyin tana kallon cikin ƙwayar idon shi, murmushi ya yi se da ya yi jim kaɗan kafin ya ce"akwai wata acikin rayuwata wacce a ko da yaushe nemana akanta yake, nemanta nakeyi acikin wannan duniyar ba dare ba rana.zan iyayin komai domin in samota zan ka war da duk wanda ya zaɓi ya shiga tsakanina da ita,ban taɓa tunanin zan so wata ya mace bayan ita ba se kuma ga shi bayan ganin ki da nayi se zuciyata ta kamu da sonki,kin san ance zuciya batada ƙa shi,zan aure ki duk sanda na sameta sannan itama in aureta." Ƙayitatciyar dariya Sabriyah ta yi wanda se da ya yi sanadiyar lotsewar kumatunta da suke dauke da dimple kyawunta ya sake fitowa, kallonta yakeyi kamar wani tsohon maye duk abinda tayi burgeshi takeyi, yarinyar she's so simple and dam beautiful.
Dakyar ta iya dakatawa da dariyar renin hankalin da takeyi ta ce "ya ma sunanka dan Allah!?"ya ce "FU'AD na ke" "yawwa Fu'ad Wallahi kabani dariya dakace wai zaka auremu mu biyun,ni ina da wanda nake matukar kauna a rayuwata duk da bansan aina ne zan sameshi ba. amma, ina fatan haɗuwa dashi ko da ranata na ƙarshe a duniya ne ruhina ze samu sallama a duk sanda na hadu dashi."duk da ta faɗa mishi wannan maganar amma har lokacin murmushin kan fuskar shi be kau ba se ma ƙa ru wa da ya yi,ya ce" amma ya sunan shi saurayin da kikeso din!?"langwabe kanta gefe ta yi ta lumshe idanunta ta ce"sunanshi ta..."ba ta karasa ba a sakamakon kiran waya da ya shigo wayar Fu'ad ya ce mata "bani minti biyu bari inyi picking call"gyada mishi kai ta yi,fita a dakin gaba daya ya yi yana waya.dawo da kallonta kan kujerar dake dakin ta yi taga tarkacen laptops kusan biyar ga wayoyi da suka kai goma zuciyarta ne ya biya mata da son kallon abubuwan da suke ciki,mikewa ta yi ta isa har gaban kujerar tana kallonsu mamaki ne Yakamata tafara tambayan kanta to me Fu'ad yakeyi da wayan nan wayoyi da laptops masu yawa haka?, wani kofi ta gani na glass sims ne aciki masu yawan gaske wanda zasu iya kaiwa ɗari,sun cika kofin ga wani farar leda cike da cocaine wato fodar ibilis,duk da shi cocaine din bata san menene ba sa hannu ta yi ta dauki leda daya tana jujjuyawa,cike da karambani irin na Sabriyah yasa takai shi dede hancin ta tana kokarin shaƙa saboda tasan meye aciki,daga bayanta taji ya daka mata tsawa "Sabriyah"da sauri ta ajiye ta juyo tana kallon shi karasowa wajanta ya yi ya ce "me kikeyi anan!?"kallon su laptop din da suke jibge akan kujerar ta yi babu ko shakka ta ce "Fu'ad meye kakeyi da laptops masu yawa ga wayoyi ma,kalli sims masu uban yawa har cika kofi sukayi ,sannan kuma meye wannan a farar ledar nan!?"ta yi maganar tana nuna mishi su ɗaya bayan ɗaya.
Shafa gashin kanshi ya yi,ya yi mata wani irin kallo ta kasan ido sannan ya riƙo hannunta suka koma kan gado suka zauna ya ce "babu kyau taɓa abinda ba'a baka izini ba akai, sannan kuma babu kyau dogon bincike!nidin me siyar da kayan wayoyine dasu laptops ina da babban shaguna a Maiduguri Sannan kuma ina gyaran su. wa'yannan mutane da yawa ne suka bani domin inyi musu gyara sims din kuma in na cire acikine nake ajiye musu."gyada kai ta yi alamar ta yarda da abinda ya faɗa mata ta ce" okay nagane!to shi kuma wancan farin garin fa me kama da foda "kallon cocaine din ya yi ya ce "wannan kuma abin wanke toilet ne" "okay"ta faɗa ta kwanta akan gadon,ta kasan ido yake kallonta yana kokarin danne fushinsa domin yau badan Sabriyah ɓace ta yi mishi wannan abun to da ya daɗe da kashe mutum amma da yake ita yana santa hakan yasa ya shanye mikewa ya yi, toilet ya shiga ya kunna shower, batare da ya cire kayan jikinshi ba ya sakarwa kanshi ruwa yana jiƙa shi hannu yasa yana dukan gefen kanshi da karfi kamar wani mahaukaci yana cikin dukan kan nashi kuma se ya dakata ya kalli yamma da kudu sannan yasa hannu a cikin aljihu ya fito da wata ledar cocaine ya zuba a bayan hannunshi sannan ya ka fa kanshi akan hannun ya shaƙa da karfi,ɗago kan ya yi ya jijiga shi sosai sannan ya samu ya dawo dede.
Chapter 26 · 0% Book details