← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 60

Sashe 21

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni barin ma inje in canza wannan kayan sun dameni"ta yi maganar tana mikewa sannan ta sa hannu ta kwashe duka kwalin sigarin dake gaban anty Teema.
Riko hannunta Asmita ta yi idonta sunyi ja sosai ta ce"Sabriyah wai ke bakya tunanin gida ne,bakya son barin nan?"dawuwa ta yi ta zauna ta fuskanci Asmita ta ce "to yazanyi?koma ina son komawa gida su waye iyayena?bansan su ba ku kadai nasani se kuma tajuju na kullum shine yake zuwa mini a mafarkina,ku kadai nake dashi shisa ma ni ban taba kwadayin barin wannan gida ba domin inna barshi ma bansan ina zani ba.kefa kina son barin nan?"ta gama maganar tana jefawa Asmita tambaya gyada mata kai Asmita ta yi"tabbas ina son zuwa gida ina son gani n mamata in jini acikin jikinta sannan in tara kudin da yakai yawan million dayan inje in samu fuskan babana in watsa mishi su wannan shine burina"sosai Asmita tabawa Sabriyah da anty Teema tausayi domin daga yanayin muryanta kadai ma in ka ji kasan deep down her heart akwai babban ciwo arayuwarta domin kullum se ta yi mafarkin lokacin da malam Mamman ya rabata da gida ya je ya siyar. da wannan dalilin ne yasa ta faɗa harka shaye_shaye ko hakan ze taimaka mata ta manta da komai amma hakan be samu ba,shafa fuskanta Sabriyah ta yi ta ce"za ki je gida wata rana tashi muje mu kwanta mubar anty Teema ta huta"mikewa sukayi suka mata sallama suka shiga nasu dakin bin bayansu da kallo kawai anty Teema ta yi tana rayawa aranta ina ma ace tana da damar kubutar da wa'yannan yara guda biyun.

Dakin nasu balaifi ɗan matsakaici akwai katifa ga gefe kuma wadrobe na sa kayan su se risho da wasu tukuye da kwanukan da basu fi biyar ba.
Suna shigowa Sabriyah toilet ta shiga bayan ta watsa sigarin da ta dauka a gaban Anty Teema a cikin dustbin,ta cire kayan jikinta ta yi wanka ta daura zani a kirjinta ta fito ta zauna abakin katifa tana duba basilin dinsu ganinshi ta yi ta dauka ta fara shafawa Asmita ma wanka tashi ga bayan ta fito ne ta dauko musu wani yalolon riguna masu dogon hannu suka saka suka kwanta dan yau a gajiye suke sosai musamman Sabriyah da tayi rawa.

Washe gari basu suka tashi ba se misalin ƙarfe goma dukkansu brush sukayi suka yi wanka suka zo suka zauna a dakin nasu Asmita ta ce"my Tom nikam bazamu karya bane kin wani kwanta"mikewa ta yi ta ce "naga ai bakice kinajin yunwa ba nadauka se anjuma ne ai"tsaki Asmita ta yi ta ce "Wallahi kina da matsala kinsan karfe nawa ne yanzu? nikam in akwai kudi a hannun ki bani inje in nemo mana abinda zamu karya dashi"kasan filo Sabriyah ta daga mata kudin da ta damfari mutumin jiya ne naira dubu goma ne ta dauko dubu biyu ta ce"ya yi ko in ƙara?kar mu cinye kudin kuma muzo muna muzurai tunda Kinga kowa a gidan nan shi yake ciyar da kanshi" " gaskiyan ki ne hakan ma ya isa tashi muje mu dawo se mu daura nasan anty Teema ma ta farka."mikewa sukayi suka fice dukkansu babu wanda yasa gyalle balle hula duk gashin su a fake kamar wasu arna Asmita na sanye da riga me guntun hannu red color da wando trequater grey color,Sabriyah kuma riga ce ajikinta yar guntuwa ya tsaya mata a guiwa duk da rigar play ce amma seda tudun hips dinta suka fito hankali kwance suke tafiyan su har sunyi nisa suka jiyo murya a bayansu tana"ku jirani dan Allah" dakatawa sukayi suna jiran nata Asmita ne ta ce "Nabiha kuma ina zataje take wannan saurin" "wa ya san mata ne"cewar Sabriyah.iso wajen su tayi ba laifi itama tana da ɗan kyau black beauty ce daga ita se wata guntuwar mini skirt da karamar riga kanta yasha kitson attachment ta ɗan yi kwalliya a fuskarta.
"Ina zakuje"Sabriyah ce ta bata amsa da"bakin titi zamuje siyan kayan karyawa! kefa ina zuwa?"murmushi ta yi ta ce"wani sabon kamun kifi nayi yace inzo da safen nan shine na fito" "okay to munje in yaso ke kya tsaya abakin shagon nasan za ki samu abun hawa"cewar Asmita tafiya sukeyi suna hira har suka iso shagon da zasu shiga din nan suka rabu da Nabiha ita kuma ta hau mashin ta tafi.
"Me shago kabamu idomie da kayan shayi da biredi" Asmita ta faɗa ko ajikinta duk da ta kalli layi ake bi a shagon juyowa mutanen sukayi suna watsa musu harara wata krista ce ta ce"uban wa kuka fi gadara anan da zaku zo kuga layi bazaku bi ba sede ku wani ce abaku kaya"ke Sabriyah da bada ke akeyi ba yar ta ran aradu da ka a harzuke ta ce "ubanki mukafi gadara shisa mukace abamu" "kan uban can ubana kika zaga?" "Iyi shi na zaga ko akwai matakin da za ki dauka ne"ganin su Sabriyah sun fita budewar ido yasa ta yi tsaki ta ce "aikin banza zakisan kin zageni" me shagon ganin zasu tayar mishi da faɗa a shago ne ya ce "me za'a baku?"sake faɗa mishi Asmita ta yi aikuwa da sauri ya haɗa musu ya mika musu suka bashi kudinsa suka tafi, akan hanya suna kan dawowa Sabriyah ta ja dogon tsaki kallon ta Asmita ta yi ta ce "me kikewa tsaki haka"da ido ta nuna mata gabansu wata farar jeep ce a fake mutumin ciki ya zubawa Sabriyah ido kamar wani tsohon maye kasa_kasa da murya Asmita ta ce"my Tom kin san shine naga yana miki irin wannan kallon kwarillan?" bata rai Sabriyah ta yi ta ce"ehh nasanshi jiya bayan na gama show cele yazo yasameni wai mutumin na kira na,ni Wallahi be burgeni" "ohhh nagane amma Wallahi karki kuskura mutumin nan ya tafi be baki wani abu ba ahh! kinsan de kayan abincinmu yakare "yanda Asmita take mata magana cike da umarni ne abin yabata dariya.
Isowa sukayi kusa dashi basu ce mishi komai ba ya ce "ku shigo mana in sauke ku?"girgiza kai Sabriyah ta yi ta ce"ba bukata ya akayi?me ya kawo ka?" Kare mata kallo ya yi ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce"yau de ina neman alfarma kizo ki tayani kwana" cike da gadara ta ce"okay naji"murmushi ya yi"yawwa hot girl ga shi bari in baki transport ga kuma address dina"ya yi magana yana fito da band din dubu daddaya guda biyu daga cikin aljihun shi ya mika mata wanda a ƙala ze kai dubu ɗari.karba ta yi ta ce"okay "sannan suka wuce shi se da suka tabbatar da ya tayar da motarshi sannan suka fito da kudin suka kirga dubu ɗari ne cas tafawa sukayi Sabriyah ta yaga address din nashi da yabata ta ce"bari anjuma cele yazo zan bashi yaje ya siyo mana kayan abinci".

Bayan sun koma ne sukayi abin karyawa sukaci dama sun rigada sun kaiwa anty Teema nata duk suna baranda suna hira su uku boss lady ta shigo tafiya ma dakyar take iya yi saboda kiba da ya mata yawa ita da wani dan daudu suka shigo dauko mata kujera anty Teema ta yi fuska ba yabo ba fallasa boss lady ta ce" ba zama ne ya kawo ni ba wajan wa'yannan marasa jin maganan yaran naki nazo yiwa kashedi"gaban Asmita ne ya yanke ya fadi domin ita tana matuƙar tsoron boss lady, Sabriyah de da ido take binta kawai kallon Sabriyah ta yi ta ce"iskanci n da kike yi hot girl ya fara isa na a gidan nan maza goma suna kawo mini ƙaranki akan abinda kike musu to ki bude kunne kiji in faɗa miki wannan iya shegen naki ya fara isana in kinsan bazaki je mutum ya biya bukatarsa dake ba kar ki ƙara karban kudin wani"turo baki Sabriyah ta yi ta ce"boss lady nifa haryanzu banga namijin da zan bata lokacina akanshi ba sannan kuma maganar karban kudi kuma ke kika koya mana. in bamu karba kudi ba dame kike so muci abinci kowa ciyar da kanshi yakeyi a gidan nan,ko da munyi show na rawa kudin gaba daya kikeso a kwashe miki dame zamu yi rayu....."bata gama maganar taba boss lady ta sharara mata maruka masu zafi a kumatu.

"Ke har za ki tsaya ina magana kina bani amsa ko kin manta a karkashin ikona kuke nice nan gatan ku duk duniya baku da wacce tafini shashasha wacce bata san inda yake mata ciwo ba ko an gaya muku na siye kune dan inzuba muku ido"hawaye ne suka zubowa Sabriyah tana riƙe da kuncinta ta kafe boss lady din da ido Asmita na rungume da ita,anty Teema ne ta ce"dan Allah boss lady kiyi hakuri ita din yarinya ce bazata sake mayar miki da magana,ke Sabriyah bata hakuri"sanyi_sanyi anty Teema take magana, sunfi minti biyu suna jiran Sabriyah tabawa boss lady hakuri amma taƙi.anty Teema ce ta ce "dan Allah Sabriyah" ganin antynta na haɗata da Allah ne yasa murya ciki_ciki ta ce "kiyi hakuri boss"hararanta ta yi ta ce "Sabriyah ki ka sa kunne kijini da kyau jibi za ki iya yin baƙo kuma ko mutuwa zakiyi se ya more ki domin tun kafin yazo ma ya turo mini da dubu dari uku babban mutum ne naɗe faɗa miki ga wannan kije ki siya abinda baku dashi".

Boss lady ta yi maganar tana cilla mata kudin da yakai Naira dubu dari da hamsin,kuma ta bata kudin ne saboda shi bakon yace mata yana son yarinya yar gayu shisa yabada kudi akan bawa Sabriyah ta je ta yi shopping.

Boss lady na gama magana tafice a sashin duk jugum_jugum sukayi Asmita tana rungume da Sabriyah har lokacin anty Teema jikinta ya yi sanyi sosai saboda ita tasan halin boss lady fiye da wasu,sa hannu Sabriyah ta yi ta dauki kudin ta ce"my Jerry dena daga hankalin ki akan maganar ta yau Allah ne ya kashe yabamu bazama mu jira cele ba tashi muje babban kasuwa.yanda take magana ranta fes kamar babu abinda yake damunta.
Chapter 21 · 0% Book details