← Book details Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 60

Sashe 23

Ashe Zamuga Juna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara birkitawa boss lady lissafi suka fara yi ta rasa waye me faɗar gaskiya da kuma waye me faɗan karya acikinsu, Asmita ce ta sake cewa"Wallahi karya ne nice na dau.........."boss lady bata bawa Asmita damar karasa maganar da take kokarin yi ba ta daka musu tsawa da wannan ƙatuwar muryan nata"ya ishe ku haka!ku fadamin waye ainihin wanda ya sace ko kuma dukkan ku biyu ku fuskanci hukuncin saboda kuna kokarin yin wasa da hankalina."Asmita na kokarin yin magana Sabriyah ta tari numfashinta ta hanyar faɗin"boss lady ki yarda dani nice nan na sace miki sarka da safe na shigo na samu kina bacci shine na ɗauke."wurgi da Asmita ƙasa boss lady ta yi ta ce "Allah ya taimakeki bake kika dauka ba"rike kanta Asmita ta yi da duka hannunta saboda azaban raɗaɗin da yake mata ga bakin cikin karbar laifin da Sabriyah ta yi bayan dukkansu biyu babu wanda ya dauka.maida kallonta Boss lady ta yi kan sabriyah dake rike da hannunta da ta rike mata gashi"boss lady akwai zafi gashina ze fita"saketa boss lady ta yi taje ta zauna akan kujera ita kuma Sabriyah ta zube akasa rarrafowa Asmita ta yi kasa_kasa ta ce"my Tom meyasa zakiyi haka duk da bamu muka dauka ba da kin bari ta hukunta ni" "bazan iya gani tana miki azaba ba karki damu,duk abinda zatamin inde akan ki ne bazan ji zafi ba"

Girgiza kai Asmita ta yi" my Tom karki yi haka kinsan halin boss lady ni banaso ta cutar mini dake"

"Ubanme kuke faɗa ne ku ka wani haɗe kai ke hot girl zo nan"boss lady ta tambaye su tana kiran Sabriyah da hannu mikewa ta yi ta je gabanta ta tsaya tana me jin kamar ta shaƙe boss lady ta mutu har lahira.

"Kowa ya watse anan bana san kallon ku sannan duk wacce ta je ta kwana ta tabbatar da takawo mini balance dinta in ga cinikin da ta yi,maza_maza je ku samo kudi yara kuyi manyan kamu, saura kuma inji labarin kun bawa matsiyaci ya ci yabaku dariya biyar ko dubu daya ku ɓace mini da gani".

watsewa sukayi gaba dayan su ya yi saura Nabiha da Asmita kallon Asmita boss lady ta yi ta ce"ke kuma karki kuskura in ga ƙafarki a nan se nan da sati daya kizo ki karbeta yanzu za'a kaita dakin horo anan zatayi sati daya.muddin naga idonki kuwa kema za ki ganki acikin dakin horo"sosai Asmita take kuka jin an rabata da rabin ranta harna tsawon sati daya kuma tunda suka taso kullum tare suke bacci,hira,cin abinci,yawo,komai na rayuwarsu tare suke yi amma yau akan laifin da ba su suka aikata ba za'a azabtar da Sabriyah hankalinta ya tashi matuƙa.

Ɗagata Nabiha ta yi muryanta a sanyaye ta ce "mu tafi Asmita zan dinga ta ya ki kwana"haka Nabiha tabar wajan da Asmita bin bayansu da kallo Sabriyah ta yi tana ajiyar zuciya,se sannan ne hankalinta ya tashi da ta tuna ina ne dakin horo.

Dakin horo wani keɓebben wajene acikin gidan karuwan babban ɗaki ne da bashi da ko da window ɓalle haske ya shigo iya kofa ne kawai a dakin ko tafin hannu mutum baze iya gani ba,anan ne boss lady take hukunta duk wata karuwar da ta yi laifi ko kuma ta karya doka,mata da yawa sun mutu acikin dakin horo saboda tsananin zafi,duhu,rashin samu a shaƙi iska ga tsananin yunwa saboda sau daya kawai ake kawo wa mutum abinci wannan dalilin yasa duk wacce ta shiga dakin horo basa fitowa da rai.

Hankalin Sabriyah be sake tashi ba seda taga wannan ɗan daudun ya nufota jan hannunta ya yi tana tirjewa tana kuka haka ya kaita dakin duhu ya wurgata a ciki yasa sakata ya rufe.
Wani irin haukaciyar tsoro ne ya kamata nan take jikinta yafara rawa musamman ma da ta ga ko tafin hannunta bata iya gani ga shi ji takeyi kamar motsi takeji aciki, haɗe kanta da guiwa ta yi tana ci gaba da kuka.

*LAGOS ORIENTAL HOTEL*

Kwance yake a hadadden dakin hotel din, side din da yake vip ne,ya yi rub da ciki da alama ya tafi duniyar tunani. kira ne ya shigo wayarshi dake kan Centre table din dakin seda ya kusa katsewa tukun ya mike zaune tsaki ya yi kafin ya tashi tsaye,masha Allah kyakkyawa ne.fari dogo yana da tsayi sosai amma be da wani jiki sosai yana da kyawun fuska dede gwargwado very handsome kanshi babu wani gashi sosai an mishi aski lowcut yana sanye da jallabiya baƙi .
Ɗaga kiran ya yi yasa akunne"hello ina wani abu zan kira ki anjuma"be bari ta bashi amsa ba ya katse kiran yana me jan doguwar tsaki ya koma ya zauna hannu yasa ya da ki jikin gadon ya rasa ya zeyi da ranshi kwankwasa kofar dakin nashi akayi ya bada umarnin a shigo namiji ne ya shigo irin masu share_share yazo ya duba ko akwai abinda yake bukata.

"Sir do you need anything?"kallon shi ya yi ya ce"nope am okay"juyawa ɗan saurayin ya yi ze fita a dakin,tunani ya yi se kuma ya sake kiran shi"come here"dawuwa yaron ya yi ya tsaya yana jiran yaji me ze ce.

Karewa saurayin kallo ya yi yaga eh tabbas ya yi kallan gari dan ɗan gaye ne kam. Ya ce"ya sunanka?"saurayin ya bashi amsa da"umar"
Jinjina kai ya yi kafin ya ce
" okay Umar!I need your help,shin akwai in da zan samu a rage mini gajiyata ne anan kusa ?"murmushi Umar ya yi ya ce"haba ranka shi daɗe kode ka manta a garin da kake ne Lagos ne fa! in mata ashirin kake so tofa zaka samu"gyada kai ya yi ya ce"akwai wacce kasani kyakkyawa,me shape wanda ze dau hankali kuma wacce ta iya tsabta?" "Ehh sede ka duba akwai hotunan su da kuma videos a wayata se in nuna maka su kazaba,kasan kaff garin nan babu kn da yakai afafa yawan ashawo."yana maganar yana laluba wayarsa acikin aljihun wandonshi ji ya yi wayam nan ya tuna ya baro wayar a reception ya ce"give me some minutes bari in dauko a reception"gyada mishi kai kawai ya yi.

Bayan kamar minti goma umar ya dawo hannunshi rike da wayar tashi shiga cikin gallary ya yi, ya mika mishi yana kallon hotunan duk yan matan babu wacce ta yi mishi acikinsu miƙa masa wayar ya yi ya ce"banga wacce ta min ba"da sauri ya karbi wayar ya lalubo mishi video wata tana rawa "ga wannan ka kalla na tabbatar da se ta burgeka"karba ya yi ya fara kallo.

Dirin jikinta da skin dinta haɗe da tsawon gashinta ne ya tafi da gaba daya ilahirin imaninshi be san lokacin da murmushi ya subuce mishi ba ya ce "tabbas wannan ta yi sede nafi son virgin wacce ni zanyi disvirgin dinta da kaina" "a afafa take Wallahi dan ma bakaga fuskanta bane kyakkyawa ce ta ajin farko kaff cikin afafa babu wacce ta kaita kyau" daga filo ya yi kuɗaɗe ne zube akan gadon bandir biyu ya lalubo ya ce"okay ga shi karike wannan"hannu na rawa Umar ya karbi kudin a iya rayuwarsa be taɓa riƙe irin wannan kudin ba wanda a ƙalla sun kai dubu ɗari biyu se jujjuya su yakeyi"Nagode!nagode sosai ranka ya daɗe"murmushi ya yi ya ce "karka damu gobe ka shirya se ka rakani can din in je in daukota. saboda bana iya yin bacci se na ji ni ajikin mace,zaka iya tafiya."cike da farin ciki ya bar dakin yana sake gode mishi domin kuwa shi yau ya haɗu da babban rabo.

Washe gari da wuri ya shirya yazo dakin nashi. bayan ya bashi izinin shigowa,zaune ya sameshi daga shi se singlet da guntun wando ga laptops a gabanshi jere akan gadon sun kai biyar mamaki ne ya kama umar aranshi ya ce"mutumin nan meyakeyi da wa'yannan laptops din?an ya ba ɗan yahoo bane kuwa?"shi kadai yake magana kuma yake tambayar kansa sanin babu wanda ze bashi amsar ne yasa ya gaisheshi ya ce"sir na shirya zamu iya tafiya?"kallon agogon hannunshi ya yi yaga almost 10:00am ya ce "eh bari in shirya se muje ka jira ni awaje inna gama zan sameka." "To shikenan"murda handle din kofar dakin ya yi ze fita ya ji yana waya abinda yaji ya futar shine..."wa ya gaya musu zasu iya dani?mutum nake me kama da aljan.just becarefull domin naji an ce shi aka bawa case din kuma yana da matukar hatsari ni na sanshi ku bi umarnina ku cece rayuwark...."be karasa maganar shi ba sakamakon ganin Umar da ya yi a tsaye a bakin kofar be fice ba.daga kai ya yi yaga suka haɗa ido da Umar din yana tsaye be tafi ba duk da yabude kofar watsa mishi harara ya yi ya ce "akwai wani abinda kake jira ne?"da sauri ya fice daga dakin zuciyarsa ya fara zargin shi,"shin wanene shi din?"tambayar da yake tayiwa kanshi kenan duk da a ido beyi kala da mutanen banza ba very gentle man.

Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.

Comment,like and share 🖋️🖋️

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

Page 14

*_Story & written_*

By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)

*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

Page 14
Chapter 23 · 0% Book details