Sashe 6
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kewarta"batama fara nufar sashensu mama ba"mamyn na zaune a parlourn tana lazimi da Alama sallar Azahar ta idar"Darma na zaune gefen kujerah yacire p.cap nasa ya aza k'afa d'aya kan d'aya goran ruwa me sanyi Ahannunsa yana sha"sai tambayarsa Ina Ahyaan d'in mamy keyi ?sau d'aya yace gata nan zata shigo.....Mamy najin sallamarta ta mik'e tsaye cike da murnan ganin y'ar tata tana fad'in ga Ahyaan d'in Mamy da daddy"da gudu Ahyaan d'in ta rungumeta tana fad'in I miss you so much my mamy! ta k'are maganar suna cika juna suka zauna kan kujerah"Ahyaan na d'an murmushi ta wani baje kan kujerah tana kallon parlourn sbd yadda ya canza mata"Ahankali tace"Ayyah broth troley d'in nacan Amota yamun nauyi bazan iya d'auka ba pls"ta k'are maganar cikin marairaice murya"Aranta dama Tasha Alwashin shine zai koma ya d'akko mata shi "d'ago kansa Darma yayi yabita da kallo saidai tak'i yadda ta kallesa"jin yayi shiru yasaka Mamy cewa katashi mana ka shigo mata da troley d'in "beyi mgn ba yanata cin magani ya mik'e tsaye Ahyaan ta kallesa suka had'a Ido"gwalo ta masa ta d'auke kai tana fad'in Mamy su khaleel fa?"sun tafi skul harma Autah"dukda yanata murnan dawowar ki"Allah sarki baby hamza"Amma mamy parlourn nan yayi kyau wlh "Eh Nura ne yamasa wannan gyaran"gaskiya broth ya kyauta daya k'ara gyara mana parlourn mu"ta fad'a cikin jin dad'i"Adaidai nan ya shigo cikin parlourn rik'e da troley d'in kayanta yana turowa"Amamakinta fuskarsa bbu irin d'aurewar nan"sai kuma taji gabanta yafad'i! kodai ya shirmun wani abun ne?"ta tambayi kanta"sai kuma ta basar dashi cikin jin k'warin gwiwar ganin daidai take dashi"har d'akin baccin mamy ya shigar mata da troley d'in kafin ya dawo inda ya zauna ya d'auki p cap d'insa"itadai tana satar kallonsa tana mamakin yadda ya koma yakuma canza.... Ahyaan tashi kiyi wanka kici Abinci?"to mamy Amma Ak'oshe nake sai Anjima zanci"to shikenan me kikeso na k'walama sai Asiyo miki?"kauda kansa Darma yayi ya mik'e tsaye da nufin yanufi dining area yaci Abinci"karma Mamy ta sara masa Aiki game da Ahyaan " . Ahyaan kuwa na lura dashi sai tayi murmushi tace "Ai mamy yanzun nadena irin wannan yawan ciye ciyen musammun Abu me sanyi sosai"ko ice cream yanzun bana sha"Amma dai bara na fito sai naga meye nake so?"to shikenan kinje can cikin gida wajensu mama?"ah ah banjeba"to tashi kije ku gaisa saiki dawo kiyi wankan"dato ta Amsa ta d'auki mayafinta daya zame ta aza saman gashin kanta dake d'aure yaji gyara"kan idon mamy ta kalli darma ta masa gwalo ,shi kuma ya wurgo mata harara "d'auke kanta tayi tamkar bata gansuba"Ahyaan ta fita shi kuma ya zuba Abincinsa ya fara ci Anutse yana lumshe Ido sbd mamy ba bayaba wajen iya girki..... Da murnah da farin ciki mamah ta tarbi Ahyaan da Asma'u Autah da bata jima da dawowa daga skul ba tana js3 yanzun"yayinda ummah gaisuwa kawai ta had'asu da Ahyaan"ba k'aramin haushi tajiba da irin yadda ko yaushe Ahyaan d'in canzawa takeyi"saidai Aranta tace Abanza kyau ba miji"ko Aikinma bazaki samesa ba indai Ina numfashi ta fad'a Aranta"Khadija kuwa da k'yar tace mata Ahyaan Ina wuni?"ko Amsawarta bata jiraba ta saki labulen parlourn mama tayi gaba"Ahyaan taci face tana jan tsaki tace"mama ni yarinyar nan zata kira sunana tsagaga?"ko khaleel da Abdul Aziz Anty suke kirana sai ita?....bance ki damuba balle harki tada kanki ki kallah "ita rayuwa kome kayi me kyau ko marar kyau sai Ammaka"iya sanina kin bata shekara goma sha biyu da haihuwa"Amma bance kice komai ba"kima tashi kije ki watsa ruwa"in kuma Anan zakiyi shikenan "ni can zanyi wankana wajen Mamy nah"mama na murmushi tace to shikenan Ammah ta kirani tace kin sauka? nace mata Eh kawai"Amma ki kirata ko?"Eh dama zan kirata"Abba be dawo ba?"sai yamma keda ganinsa gaskiya"Abdul kuma exams yakeyi shida Affan duk sai yamma zaki gansu"okay kawai ta fad'a ta mik'e tsaye ta nufi wajen fridge ta bud'e taga ruwa swan da lemo na roba jere"ahhh su mama kun zama y'an gayu keda mamy nah ko Ina yak'ara kyau"ta fad'a tana d'aukar lemo guda d'aya ta rufe fridge d'in ta zauna tanata y'an kalle kalle cikin parlourn"kedai bari Ahyaan duk Aikin Nura ne daya dawo ya canza mana kujeru Akayi soma ,yamana fanti"drinks kuma khaleel da Abdul ne suke kamana wai musha muba bak'i "gaskiya ne inaga broth yayi kud'i"murmushi mama tayi tace"Ai yanzun dai chemist yake zuwa zaidai fara Aikin dai koda safe munyi mgn da Alh"yacemun kema yake jira ki dawo Akwai Abokinsa da sukayi mgn game dake yace akawo takardun naki za'a samar miki Aikin in sha Allah "ihun murna Ahyaan tayi ta rungume mama"bazaki girmaba ko Ahyaan? "ta fad'a tana murmushi "itama tana murmushi tace burinah dana gama karatu na sami Aiki mama kodan sbd nadinga kyautata muku keda mamy nah Ina saku farin ciki....mamah na k'ok'arin mgn inna Asabe yayar Abba ta yaye labulen d'akin ta shigo fuska Ad'aure tanata y'an Harare Harare"sau d'aya Ahyaan tace mata Ina wuni?"daga haka ta mik'e tsaye "Adak'ile ta Amsa tana kallon mamah dake gaisheta tace"yauwa zainab bani 300 zan bama me nafef na jirana waje"d'an murmushi mama tayi sbd tuni tasan matar nayi mata hassada"koda take makka bata fasa kiranta da zainab kai tsaye ba"sai tace Aiko banida changi"to ki bani Asamo mana"murmushi ta koma saki kai tsaye tace banyi niyar bayarwa ba"kije wajen y'ar uwarki luba ta baki mana"iyye! lallai zainab kin Isa"to ko iliyasu k'asa dani yake balle ke"in bacin nasan kud'in na dan uwanane kinma Isa nazo nace kiba nii?"banza mamah tayi mata ta d'auki remote ta kunnah tv"Ahyaan kuwa Azafafe ta fita ranta Ab'ace "wani irin tsanar dangin mahaifin nata na k'aruwa Aranta"bayan mama data haneta da k'in shiga sabgarsu da wlh ta gaya mata mgn"tana fitowa daga cikin parlourn Mubarak na shigowa tsakar gidan"yayi wani shegen aski irin na mararsa jin mgn da tarbiya"ga asdown yayi baki yayi bak'i k'irin sbd shaye shayen da yakeyi Ab'oye"saidai Abin mamaki yana ganin Ahyaan ya had'e rai ya d'auke kai beko kalli gefen da take ba"itama nunawa tayi tamkar batama tab'a sanin saba"dan idan jin kai da izza yakeji to ita tafishi iyawa fintin kau.....tana k'ok'arin shiga parlourn shi kuma yana k'ok'arin fitowa"da sauri tayi baya sbd takusan fad'a masa"yamutsa fuska yayi yatsaya yak'i matsawa yana binta da kallo"Atake ya fahimci ranta Ab'ace yake"dallah mlm ka gyara na wuce"ta fad'a cikin masifa"shi kuwa dayake jiranta yakeyi saiya fake bakin k'ofar parlourn yak'i matsawa"ta saki k'aramin kuka tana turashi da kiran sunan mamy"Adaidai nan taji sallamar inna Asabe "pls broth ko tace kabata 300 kace baka dashi"matsa na wuce"bece komai ba ya janye ta wuce ciki da sauri"shi kuma be bar wajen ba"jikinsa na bashi innah Asabe tayima Ahyaan wani rashin kyautawa"harga Allah shima dangin Abba basuyi masaba"in bacin sbd mamy da mama ko gaisuwa bazata had'asu dasu ba"Ina wuni?"ya fad'a da k'yar zai rab'ata ya wuce"lafiya qlau Nura"dan Allah ko Akwai 300 wajenka zan sallami me nafef, wlh babu chanji" *bani dasu* shine Abinda yafad'a yana yin gaba Abinsa"Aransa yana mata tur da Allah wadai"Akallah zatayi shekara sittin da wani Abu Amma ta tsaya tana rok'o"ada tayi niyar shiga wajen Mamy komai ta tuna oho saita fasa tayi gaba tana mai tsananin jin zafin nura.... Ahyaan duk tana lab'e ta window tana ganin komai"bayan ta tafi ta shiga yima mamy dake zaune tana kallonta bayanin komai...."Ai Ahyaan mutanan can basuda hali"bansan meye suke so su maida Abbanku ba?"daga ita har harira basu sati d'aya basu zoba"suci na dare nan suci na rana nan"abasu kud'in Abin hawa"yanzun da sukaci suka gyare sai in sunzo suce abasu kud'i subama me nafef"koda ta shigo wlh nima bazan bataba"basuda tausayi kansu kawai suka sani"sai yawan bani bani da suke matsama Abbanku dashi suna zubar da mutuncinsu"cikin takaici Ahyaan tabar parlourn ta wuce d'akinta......bayan sallar isha'i tana zaune a parlourn kan kujerah Tasha wankanta da k'ananun kaya jikinta tana kallon indian firm"yayinda Mamy tana sashen daddy"ada itada khaleel ne ke fira a parlourn saiya fita"sbd ya Aiki hamza be dawoba shine yabi bayansa"tana cikin kallon taji fad'uwar gaba "hakan kuma yayi daidai da aka turo k'ofar parlourn, k'amshin turarensa me ratsa zuciya ya kaima k'ofofin hancinta ziyara"cike da shan k'amshi ya shigo da sallama "yana sanye da jallabiya Ash me gajeran hannu kuma ta d'an d'age masa Abinka da dogon mutum"Ahyaan kuwa sarai tasan shine ya shigo saita d'auke kanta kamarma bata san dashi ba"ko sallamar tasa Aranta ta Amsa "kai tsaye Darma gefenta ya zauna ya aza mata ledar ice cream saman cinyarta "cikin tsare gida da shan k'amshi yace" baki iya Amsa sallama ba?"k'in mgn tayi Aranta tana murmushi sbd sanyin dataji gefen cinyarta ya tabbatar mata ice cream ne"wato sbd yaji tace bata shansa yanzun shine sbd mugunta ya siyo mata"to dama tana sha sbd yasiyo ta masa haka"tasan tace tana so ba siyo mata zaiyi ba.....dayake son k'untata mata yakeyi shine yasiyo...lallausan k'afarsa daya Aza saman tata ya take yasaka ta dawo tunaninta"saida taji tsikar jikinta ta tashi da k'afafuwansu suka had'u,gashi daga ita har shi ko wane k'afarsa ba takalmi"cikin b'oye yanayinta ta d'ago kanta ta zabga masa harara had'e cewa wai meye haka?"saida ya jingina bayansa Ajikin kujerar da suke zaune tamkar bazaice komaiba"kusan shud'ewar mintina 3 kafin yace "irin Abinda na koyo a London shine nafara saukewa Akanki"ga ice cream nan na siyo miki"dole kiyi Abu biyu"na farko kice yaya nurah na gode,na biyu kuma ki shanyesa yanzun nan ta Arzik'i sbd bazanyi Asaran kud'i naba"ban damu da baki shaba yanzun sbd wani dalili can naki"kimun musu ko gaddama kuwa zai saka na miki Abinda baki tab'a tunani ba"mamyn dakike tak'ama da ita tana sashen daddy kin sani?"yak'are maganar cike da rainin wayo yana wani basarwa cikin shan k'amshi.......... wannan book d'in na kudine ! Regular grp 500 Vip grp 1000 Special grp 2k wato 3pages in a day zaku biya kud'in ku ta wannan acc number 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251 500 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira Y'an nijar kutuntub'i wannan n +227 88 01 90 50 Regular 300f