Sashe 5
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AGE MATE Story & written by mommyn fareesa *Dominki* my beloved sister hafsat Aliyu D Allah yabaki miji na gari Dedicate to all my commenters Ina yinku irin sau trillion d'in nan Free page 5&6 *cigaban labarin*.....koda ya gama parking d'in kin mgn yayi sai yama cigaba da danna waya "mu'az yayi murmushi kawai yana kallon Ahyaan da tacika tayi fam da rainin wayon Darma Anutse yace"karki damu Ahyaan fita muje ku gaisa da ita"inaso keda ita ku zama friends"ya k'are maganar yana kara wayar sa gefen kunne ya fito daga cikin motar da Alama Fatima yake kira"Ahyaan kuwa tsaki taja tana fad'in wlh mu zuba nida mutum....waye kike ma tsaki? ya fad'a murya Adake"ya juyo yana binta da wani razanan nan kallo, sbd ya tsani Amasa tsaki"cike da rashin kunya ta d'ago kanta suka had'a Ido! Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijinin daya mata da cika waje... Amma dukda haka saita zabga masa harara tana janye Idanunta tace da wanda ya tsargu nake"Azuciye ya fito daga cikin motar har huci yakeyi ya nufi back sit d'in Azafafe"Adaidai lokacin kuma Fatima ta fito daga cikin get d'in gidan su"mu'az nata k'ok'arin dakatar dashi Amma yamasa banza ya bud'e k'ofar"Ahyaan kuwa ta gudan gefen damarta ta bud'e tayi wuf ta fito sbd tsoron Abinda zai mata musammun da taga ta fusatashi"saidai zuciyarta fes da fushinsa tayi tsaye daga gefen motar "be hak'ura ba sai nufarta ya komayi"ta wani tsuke fuska murya can ciki tace"wlh kana cin zalin nawa ba k'yaleka zanyiba saina rama na kuma baka kunya gaban yarinyar "ta kare maganar tana tab'e baki ta wani ci face "d'an dakatawa yayi domin zancen gaskiya beson mutuncinsa ya zube a idon Fatima, musanmun da yau ne zai fara had'uwa da ita"saidai da yake kaifi d'aya ne saiya nuna kamar zancenta be shige saba ya koma had'e rai yana tunkaro gefenta"itama saita dake ta tsaya tana satar kallon mu'az da Fatima da suke kashe juna da murmushi"ta tab'e baki Aranta tana fad'in" *jikinki yakeso* "sbd Aganinta duk idan namiji yace yana son mace tofa jikinta yakeso....wuce muje! sautin sanyayyar muryarsa me cike da dattako ta katse mata tunani "k'in kallonsa tayi"shi kuma be damuba ya matso ya finciko hannunta "kaga bansan wulak'anci Akanme zaka wani dinga tab'amun hannuna?"ko dama London d'in dakaje tab'ara ka koye ne?"idanma Akwai Abinda yafi tab'ara duk na koyo kuma Akanki zan sauke Abinda na koyo d'in"saidai da Alama har yanzun naga kanki na rawa"Amma fa Ashirye nake dana saita miki shi"ya fad'a normal tamkar maganar Arzik'i sukeyi"ita kanta Fatima ta d'auka masoya ne wuf d'aya data kallesu.....zaki wuce muje ko kuwa saina jaki ta k'arfi ne?"d'an murmushi ta saki me sanyi da yayi mata wani irin kyau kamar me rad'a tace "kaima kasan dama idan bata k'arfin ba Ai baka Isa ka tur sasani da kurin kaba har naje "mezai hana ka dena nuna k'arfin "*many Ansha tatala*" ?ta kare maganar tana kecewa da dariya domin tasan ta k'ulesa data fad'i hakan daga k'arshen maganarta ...."tun yana yaro haka yake cewa idan zasuje siyan k'ank'arar kwarbebe"sau d'aya ya kalleta ya maida idanunsa k'asa bece komai ba, saidai yata naji Abinda zai mata da saiya sata kuka"duk yadda taso taga ya fusatu k'in nuna ya fusatun yayi, be kuma cika hannun nata ba yajata da d'an k'arfi suka nufi wajen su mu'az dake tsaye gefen get d'in gidan su Fatima suna mgn.....kaga bansan iskanci ka cika mun hannuna mana"ta fad'a tana son turjewa"tamkar da bango take mgn haka yamata banza"kasan Allah cizonka zanyi! duk ya share yanama kallon wani wajen"saida suka iso gefensu yad'an saki fuska yana musu sallama"Fatima ta Amsa tana murmushi tace"na d'auka Ai bazaku iso da wuri ba sai Angama firan soyayya?"ya mutsa fuska Ahyaan tayi tace"Allah ya kiyaye nayi soyayya da k'a.....nayi soyayya da d'an uwana"ta furta ba shiri sbd wani Arnen mintsini da darma yasakar mata gefen hannunta"gurin har saida yayi ja"kasancewar ta chacoolate colour ce itama fatar jikin ta.... mu'az kuwa dariya ya kamayi sbd jikinsa ya bashi wata muguntar Darma yamata shiyasa tak'i furta Abinda tayi niyar fad'a tun farko"saita canza "Amma sbd kafiya irin tata sai ta kasa cewa yayanta ta juya zancen zuwa d'an uwanta....Masha Allah! Ashe yayanki ne? na d'auka Ai masoya ne ku"Ina wuni ya gida??"ta fad'a tana yaba tsarin had'uwar Abokin mijin nata dashi da sister nasa"Anutse darma ya Amsa mata da tambayarta y'an gida kafin yasaka hannunsa ya d'alli lips d'in Ahyaan yana fad'in baki iya gaisuwa ba?"bata kallesaba Amma taci burin saita rama"saita d'an yi murmushi tare da cewa na bari ku gama gaisawa ne"hakane Ahyaan "my princess ga Ahyaan nan Ina fatan zaku zama friends da ita"cewar mu'az"in sha Allah "ya gida yasu mama?"cewar Ahyaan "Fatima ta Amsa cike da kulawa tana fad'in zo muje ciki ku kuma kuje kuyi sallah"dukda Ahyaan bata so shiga ciki ba kodan sbd karta bi umarnin wannan d'an iyayin Amma saita nuna zata bita da nufin idan sun tafi ta fito ta hau Adaidaita ta koma gida"sai ta koma had'a masa bom wajen Mamy"duk Darma na hankalce da yanayin ta,kuma jikinsa na bashi Akwai Abinda zatayi idan sun tafi yasanta da shegiyar kaffiya kan ra'ayinta"kallonsa tayi ta zabga masa harara tana fad'in bazaka cikamun hannun ba?"be cikaba sai matsowa yayi da fuskarsa dab da tata murya can k'asa yace"kinsan Allah idan muka tafi na dawo na samu kin gudu zane miki jiki zanyi muka koma gida"karkiga kin koma wata y'ar lukuta kiyi zaton bazan iya hukuntaki ba......tsabar yadda ya kasheta da takaici kasa mgn tayi sai Ido kawai"ga k'irjinta nata fat fat fat!! sbd kusancinsu da yayi yawa"ga fad'uwar gaba datake ji"itadai Fatima na tsaye tana satar kallonsu zuciyarta na mata kokonton bata yadda shida ita yaya ne da k'anwa ba saidai ko cousin d'inta neshi"mu'az kuma yasha Alwashin yimata baya nin dangan takarsu daga baya.... Ajiyar zuciya Ahyaan ta sauke sbd cika mata hannunta da yayi"Fatima ta matso tana murmushi taja hannunta suka wuce cikin gidan"tana lura da darma na Aiko ma Ahyaan da harara......sosai Ahyaan ta yaba da kirkin y'an gidansu Fatima"badan tasoba tabi fatima d'akinta sukayi sallah"kafin su gama mamanta ta shiryama Ahyaan Abinci da lemo da ruwa"kasancewar yunwa takeji ga gajiyar mota saita daure ta fara cin Abincin suna fira da Fatima"Ahaka kiran Mamy ya shigo cikin wayarta k'irar IPhone 11 11"d'an murmushi tayi ta d'auka tana fad'in Mamy nah?"daga d'ayan bangaren Mamy ta sauke Ajiyar zuciya tace"Ahyaan duk na damu da naji shiru saida na kira Nura yanzun yace mun wai kun biya ta gidan su yarinyar mu'az zaku gaisa da ita?"Eh hakane Mamy"Ina fatan sababben me miki wani abu ba?"be yimun komai ba Mamy yanzun ma zamu taho gida sun tafine suyi sallah shida yaya mu'az"Amma ga Fatima ku gaisa"ta k'are maganar tana mik'a ma Fatima wayar"ta Amsa suka gaisa da mamy Amutunce kafin suyi sallama"ba'a fi mintina ukku ba da gama wayar tasu ba mu'az yakira yace su fito zasu tafi"Ahyaan ta wani tsuke fuska tana fad'in wlh saina b'ata masa lokaci "saida Fatima ta kashe wayar ta kalleta da murmushi sbd ta fahimci Ahyaan zata girme mata"wai dan Allah keda darma da gaske y'an uwa ne?"uhmm! Amma causin d'ina ne"daga haka tayi shiru taci gaba dacin Abincinta.....sau biyu mu'az na koma kiran su fito Amma Ahyaan tak'i fitowa"ba k'aramin hassala gogan naku yayi ba"sbd yana so yakoma gida yanada uzurin da zaiyi"ya lura saiya biyoma yarinyar ta bayan gida tukum zasu daidaita"Ayanzun beso ya tafi yabarta sbd yasan saiya sani Awajen Mamy"musammun data kirashi yanzun taji lafiya basu isoba sai fad'a take masa"wannan dalilin kawai zai saka ya jirata Amma zata gane kuranta..... gaskiya *Darma* baka kyautawa ko kad'an!ya wuce Ace har yanzun kaida Ahyaan kuna irin y'ar haka tsakanin ku.....kaga mu'az ka rabu dani "sanin kankane bazan d'auki rainiba"Agabanka fa yarinyar nan kemun Abinda ta gadama kana wani bata hak'uri"d'azun harda kama yimun dariya ko?"mu'az na k'ok'arin mgn Ahyaan da Fatima suka fito daga cikin gidan.....kicin kicin darma yayi da fuska beko kalli gefen da take ba, cike da shan k'amshi yace"princess d'in Abokinah zamu wuce"to shikenan ustazah muna godiya da ziyara"d'an murmushin gefen baki yasaki tare da cewa abakin Abokinah kikaji wannan sunan ko?"Eh mana"duk sukayi murmushi Fatima ta rakosu gefen motar ta musu godiya bayan ta Amshi contact d'in Ahyaan sannan ta wuce ciki"wannan karon mu'az ne yashiga driver sit sbd yasan halin mutumin nasa yadda ya shak'a d'in nan zai iya zubar dasu kan titi "saidai ganin Ahyaan taja tayi tsaye tana danna waya yasaka shi fad'in tsayuwar me kikeyi da bazaki shiga mu wuce ba?"ya mutsa fuska tayi tak'i mgn tana cigaba da Abinda takeyi"Afusace ya matso ya bud'e k'ofar back sit d'in "yana k'ok'arin kama hannunta da nufin yaturata ciki sai tayi wuf ta shige ta zauna tana yatsina tace" thanks my k'ani ,dama na tsaya saika bud'e mun k'ofar saina shigo"ta k'are maganar murmushi na sub'uce mata ",duk yadda mu'az yaso danne dariyarsa kasawa yayi saida ya fara"saidai DARMA bece musu uffan ba daga shi har ita"ya zagaya ya shige gefen me zaman banza zuciyarsa na k'una tare dashan Alwashin yanzun suka fara wasan zai barta tayi iya nata idan Aka fara nashi tofa ta shiga ukku"har suka doso cikin layin Anguwar tasu babu me mgn Acikinsu"tun kafin ya gama parking Darma ya bud'e k'ofar ya fito ya wuce cikin gida ko sallama be masaba sbd ba k'aramin haushi yabashi ba"yayinda Ahyaan zuciyarta fari k'ar ta fito tana fad'in dan Allah yaya mu'az bara na turo Ad'auki troley d'in kayan nan"dato ya Amsa ta masa godiya ta fito cikin takunta na Isa tamkar wata tarwad'a haka ta nufi bakin get d'in gidan nasu very slowly "mu'az ya bita da kallo ya girgiza kansa yana mamakin ko tsinin takalmin k'afarta basu takurata wajen tafiya, kamar bada takalmi me tsini take tafiyar ba"may be ta riga ta saba saka irin su"ya fad'a Azuciyarsa...... Akan idon babban yaron Mr mahuta dake bibiyarsu tun d'azun ta shige cikin gidan nasu"hakan ya tabbar masa da cewa Anan ne gidan su"sai kawai yaja nafef d'in ya wuce da nufin zuwa yamma sai ya dawo yayi binciken wacece ita,miye Alak'arta da darma??wanda Mr mahuta ne yabasa yin wannan Aikin.....kai tsaye sashen mamy ta fara nufa cike da