Sashe 40
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kalaci baki yiba tun safe kiketa Aiki Ai rai saida hutu"kai mamy nafa sha Lipton"kinga broth yaji ciwo ga hannu shine saina wanke masa"da Acan bath room nasa zan wanke "sai kuma naga karna jima kiga shiru shiyasama nayishi nan.....iya nan Dr darma da yaji yakoma yabfasa shigowa"dama yana sako kansa bakin k'ofar yaji muryar mamy shine ya dakata"sosai yaji sanyin kalamanta Azuciyarsa"tunda ya tafi Asibiti tana Aransa harya dawo"cike da nutsuwa ya zaro keys ya bud'e k'ofar d'akin nasa"kasancewar dama yanada keys spire....da tray d'in data jero masa Abin break fast ta Ajiye saman carpet ya had'a Ido "ga wani ni'imtaccen sanyayyan k'amshi na tashi cikin d'akin da yayi very need"ya lumshe Ido ko k'ofar be rufe ba ya zauna dabas saman sofa yana tunani"wani irin k'imarta da ganin kirkinta suka nunku Azuciyarsa"gaba d'aya sai yaji yadena jin zafin wayar datayi da Abdallah mashi Ajiya"saidai kuma daya tuna saura fa 3 month ta zama matar waninsa saida yaji k'irjinsa ya buga! can kuma ya gyad'a kansa sbd tunawa da kalaman mu'az da yayi"har yanzun karya fidda rai..... d'an bud'e idanunsa dake lumshe yayi sbd jin sautin zazzak'ar muryarta me taushi da siran taka"ya kalleta yana Amsawa Ahankali"tana rik'e da robar kayan tace"broth dama kadawo ne?"ban jimaba ko minti biyar banyi ba da shigowa"sannu da zuwa! sosai kansa ya fashe ya Amsa da yauwa"ita kuma saita shige bath room nasa da nufin ta shanya masa kayansa Acan....bata fi mintinah biyarba ta fito ta bishi da kallo sbd ganinsa zaune kamar yadda ta barsa"ba break fast d'in zaka yiba?"keme maganar kinyi ne?"kuma gaskiya zaki fad'amun"nasha Lipton broth"Lipton Aiba Abinci bane"canza topic d'in tayi da cewa nasan ka gaji ko?"kamar kin sani"to kayi break fast d'in sai kayi wanka "to shikenan sannunki da Aiki bestie"d'an murmushi kawai tayi "zoki zauna mana"karfa mamy taji shiru broth"k'in mgn yayi yana danna waya"saita zauna gaban tray d'in data shirya masa Abin karin Ahankali tace"wai laifin mena maka jiya Ina mgn shine ka shareni katafi ko?"kuma da safe na gaisheka ka Amsa ciki ciki"bakimun laifin komai ba"kawai dai rainane Ab'ace Alokacin "hmmm! waye ya b'ata maka rai bayan Abinci muke ci?"text message ne wata ta turo"yamutsa fuska tayi had'e dajan tsaki tace"na lura kana bama k'ananun y'an mata sa'annin su husnah fuska shiyasa suke cewa suna sonka"idan mace classic lady ce ta wuce wannan matakin wlh"shidai murmushi yakeyi yana kuma kallonta "beyi mamakin yadda ta nuna ba sbd yasan wacece ita game da Aji da nuna kamun kai....to my Anty inkin gama yimun fad'an kizo muyi break fast d'in ko kuma ki d'auki kayanki"maimakon ta bashi Amsa sai cewa tayi bani text message d'in nagani"oh yah rabbih " nafa goge tun jiya sbd bana Ajiye shirme Awaya ta"shikenan ai"Amma pls zanje wlh yanzun zanyi break fast d'in kar mamy ta gaji da jira kaji dan Allah?"yayi shiru,zata koma mgn hamza ya shigo da sallama kasancewar k'ofar Abud'e take "Ahyaan ce ta Amsa yace"mamy tace kizo"to gani nan zuwa"bayan ya fita ta kalli Dr darma broth! menene?"naga kamar baka ji dad'i ba"kije tunda mamyn bata son kina zama inda nake"bafa haka bane Aiki zata sakani Ai"ya kalleta yasaki murmushi sbd yayi mamakin fara sauyawarta"yasan Abaya da wuya ta bashi hak'uri"idan kuma ta bashi hak'uri to mugunta taga zai mata batada ikon ta rama"bestie kije kiran mamyn"kuma idan bakiyi break fast ba zan gane"zanfa yi broth na maka Alk'awari"shikenan ki shirya sai muje na kaiki gidansu Khairiyyah d'in ko?"inaga saifa da yamma"ba zaki fita da yamma ba "bud'e gashi da tsakkiyar marece beda Amfani sbd shed'anu lokacin suke sakkowa"d'an juya Idanunta tayi kafin tace "bana zaton zamu fita yanzun sbd ni zanyi girki ko?"waike baki zama ki huta ne?"inafa hutawa"tunda na fara zuwa wajen Aiki kusan kullum mamy keyin girki week end ne kawai nakeyi.gara itama ta huta broth ko?"kansa ya gyad'a mata ita kuma tayi d'an murmushi ta fita"ya bita da kallo yana sauke Ajiyar zuciya tamkar wanda yayi gudun tsere "shikansa yasan harda yawan kyautatawarta ga mahaifiyarsa ya saka yake mata wani irin bahagon so .Atsarinsa beso yaso wacce bata son mahaifiyarsa ,yafi son yaso macen dake girmama iyayensa musammun mahaifiya......... kimanin kwana hud'u kenan da faruwar sace Ahyaan "wanda ranar monday AA Mashi ya saki vedio d'in firanta a Acikin cell da Mr mahuta a gidan TV da kuma social media"Atake Aka fara kace nace "lokacin da mahaifinsa Alh Ibrahim ya gani zubewa yayi hawan jininsa ya tashi"musammun da yaji An Ambaci bilkisu na shaye shaye "gashi dama sunsan itada mahutan suna a rufe sai son Asakesu Akeyi Amma Abin ya gagara"mahaifin nasu yabuk'aci jin me sukayi Aka kamasu?"sai mahuta yanuna sharrin magautane kawai."gaba d'aya jama'a wasu cikin kashi biyu sun yadda wasu basu yadda ba"saidai family d'in mahuta sun yadda"Ajiya kuma suka shiga kotu"Aka gabza shari'a me zafi"inda aka yankewa bilkisu hukuncin zatayi sati biyu gidan yari sbd da ita Aka had'a kai Aka sace Ahyaan sbd Acutar da ita. Anso Abiya kud'i ba sai tayiba Amma mahaifinsu yace sai tayi"shi kuwa babban me laifin wata ukku ne zaiyi"sbd harda had'in gwiwar da yayi da y'an daba b'ata gari"an kuma yimasa iyaka me k'arfi da Ahyaan "yayi signing komai marar kyau yafaru da ita shine.....tun bayan faruwar Abin Ahyaan ta rasa gane kan Abdallah Mashi"tun ranar daya kirata yaji tana yiwa Dr darma mgn daga ranar be koma kiran taba "idan sun had'u office iyakarta dashi su gaisa"ko office nata dayake biyota Abaya suna fira yanzun yadena"idanma zasu jagoranci wani shiri zai tsaya normal suyi Amma baya janta da raha ko fira"to itama da yake ba baya bace wajen jin kai nuna masa takeyi ko Ajikinta "ko gaisuwar ma dg Ina kwana shikenan koda yace ya gida?"saita d'auki wasu second take bashi Amsa cikin halin ko in kula"kota chats sun dena mgn....Acikin *gida biyu* kuma ummah na nan ta zuba Ido taji Ankori Ahyaan daga wajen Aiki kuma An fasa Aurenta da Abdallah mashi"yayinda tsakanin Ahyaan da Dr darma wata iriyar shak'uwa ta koma k'ulluwa marar misaltuwa"sbd yanzun ko umarninsa Ahyaan bata tsallakewa.da mamy tayi mgn Ahyaan zata karesa"tun daga ranar monday har zuwa yau tare suke fita wajen Aiki "saiya fara Ajiyeta sannan saiya wuce"da kuma k'arfe d'aya tayi zai dawo ya d'auketa su wace gida "yanzun ba sosai take driving ba wannan kenan.... kasancewar yau Wednesday tun wajen k'arfe 3:35 pm Ahyaan ta gama shirinta "sbd yau ta tashi da period bata yin sallah"itadai mamy na zaune a parlourn saman prayer mate data idar da sallah tana kallonta"ta shirya cikin hijab navy blue har k'asa tayi masifar haska choko face nata"ga hand bag nata ta rataye gefen kafad'arta"k'ananun kaya ne Ajikinta saita Aza hijab"fuskarta light make up ne"sai danne danne takeyi Awaya "can mamy tace" yanzun kuma yaga damar dawowa zuwa dake wajen wa'azin?"dama fa can laifinane mamy shiyasa yadena zuwa dani"bata rufe bakiba k'amshin turarensa yafara yi musu sallama sannan kuma saurin tattausan muryansa me cike da haiba"daga bakin k'ofar ya tsaya yana binta da wani irin kallo ta cikin eye glass d'insa "ya wanku cikin milk d'in shadda "da Akayima Aiki da coffee brown d'in zare.....uztas ba hula! nima dai haka zance Ahyaan "cewar mamy"Ajiye batun saka hular nan bestie Ana zafi"tashi muje ko?"ta kalli mamy tace sai mun dawo"to shikenan Allah ya tsare"suka Amsa da Ameen shi yafara fita sannan ita.suna fitowa tsakar gidan ta wani turo baki gaba tace"nidai muje ka bud'e d'akin ka d'auki hula"ya duba wristwatch d'insa ya girgiza kansa"bata bari yayi mgn ba tace bani key d'in "ke Ina naki key d'in?"yanafa ciki "beyi mgn ba yazaro yabata suna Ida fitowa"shi yatsaya gefen motarsa ita ta wuce ciki ta bud'e ta d'akko masa hula coffee brown ta fito tana murmushi ta mik'a masa "ya Amsa ya saka"wow! to yanzun ba gashi ka Ida yin kyau ba"Ai kin fini yin kyau ko?"ah ah ba gaskiya bane "kin dai fad'a"yak'are maganar yana bud'e mata gefen me zaman banza yace"sarauniya Aminatu Azo Ashiga"kai kuma sai Ace maka sarki ko?"ta fad'a tana shigowa ta zauna"ya zagayo ya shigo yaja motar "suna tafe suna fira sama sama"bayan sun iso yayi parking yana zaro face mask ya mik'a mata "bangane ba?"ki saka "Akanme kuma broth?"sbd kinada saka ranar wani Akanki "ko kuwa kinfi so su kalle fuskarki?"yafad'a yana tab'e baki "nifa na tsani face mask sbd wannan banzar shine ta saka ko?"ya d'an girgiza kansa zai mayar inda ya d'akko"kawo zan saka"bece komai ba ya mik'a mata"sai bayan ta saka suka fito yayi lock d'in motar suka wuce ciki.....kusan Awa biyu sukayi sannan suka fito Aranta tana mamakin meyasa duk yawan cin Malaman Addini basuda kunya sun fitsare?."ta lura Dr darma baya jin kunyar zaro mgn kuma ko Ajikinsa"yanzun dai suna maudu'in *Ado da kwalliya* sun gama na tsabta"duk idan ta tuna time d'in da yake cewa duk wani namiji yana son mace data iya ado da kwalliya"kunfi so mazan ku su fita su kalli na waje?"ko kuwa kinfi buk'atar kina gida kina gayu Amma dakinyi Aure zaki koma gaki nan ?ba Ado ba kwalliya duk inda miji ya shafa baya jin k'amshi Ahaka kuma kike Amsa sunan y'a mace.....Ina zamuje sbd deb'e kewa kafin 40 minit ta cika?"yafad'a lokacin da suka shige cikin motar"numfashinta sauke ,saida ta juya Idanunta Alamar tunani kafin tace"muje *Maryam Park*"okay ya fad'a yana bama motar wuta "basu jumaba suna tafiya mu'az ya kirashi ya d'auka suka fara fira"tun firan tasu bata ba Ahyaan kunya harta fara bata "sai cab'o mgn Dr darma keyi"wai kar mu'az ya dinga yawan haikema Fatima ba'a son yawan sex da mace me yaron ciki....kasa jurewa tayi Abazata yaji ta fusge wayar ta kashe tak'i yin mgn "bestie meye haka?"harara ta zabga masa tana fad'in wlh bakuda kunya kaida shi"okay zan sanar masa ko kuma idan muna tare dake muka had'u saina fad'a masa"daka gama dani"to ki bani wayata"bazan bayar ba"duk tana maganar ne hankalinta na waje"ganin tak'i bashi wayar ya saka yabarta"suna isowa kai tsaye suka wuce ciki"ice cream dasu shawarma da sauransu ya musu order ,kafin su zauna yana ta satar kallonta ita kuma tak'i kallonsa"yayinda maza da mata kowa keta harkan gabansa...wai ba zaki shaba ?"uhmm"bazai yuyuba kema kin sani bestie"komai da nayi order nan sbd kene fa"to shikenan zan sha ice cream Amma sauran Amana take aways