Sashe 18
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jarumtar tashi ya bud'e ward rope ya d'akko towel ya fara rage kayan jikinsa"sannan ya shiga wankan.....cikin mintina 25 ya fito sanye da wondo 3 quarter fari da riga Amles sky blue"idanunsa sun rage haske sun d'an yi ciki sai lumshe su yake yawanyi"kai tsaye sashen su mamy ya nufo yana dariya Azuciyarsa da Abinda yaga Ahyaan ta masa a bath room "zai tambayeta idan tana son kayan wankan saiya siya mata irinsu,dukda yasan itama da irin wa'anda take using dasu....k'amshin girkin daya cika haraban gidan har zuwa main parlour yadaki hancinsa "yad'an shafi cikinsa sbd tsabar gajiya shi yau bema da zab'in Abinda zaiyi bud'a baki dashi"mamy na zaune itada bak'uwa Atsakar gidan "mamy sannunku da gida"yauwa ya Aikin?"Alhamdulillah"yafad'a yana gaida bak'uwar ya wuce cikin parlourn rik'e da leda bak'a irinta shopping "ba kowa sai motsin Ahyaan dake kitchen ta kusa kammala had'a masa Abin bud'a baki da mama ce ta kirata taje ta Amso dawon Awara tace" taje ta had'a da wani abun ta shirya masa Abin bud'a baki.....cikin kitchen d'in ya nufa ya toge daga bakin k'ofar yana hangota tana tsaye tana juya Awarar data ji k'wai tare da doya cikin pripan "yad'an kauda kansa"batada Aiki sai saka k'ananun kaya "yafad'a Azuciyarsa tare da shan Alwashin zai take mata burki"rasa meye zaice yayi sai kawai yamata gyaran murya"ta juyo da sauri"Ido suka had'a ta d'auke kanta tana tambayar kanta meyasa wai idan ta gansa take jin fad'uwar gaba?"sannu da Aiki *Amun dago*"uhmm yauwa kadawo ne ?"bakiga Alama bane?"shiru tayi tak'i mgn"ya matso yana fad'in ga sak'on naki"ki shirya Anjima zan miki Allura"ta juyo Ak'ule ta wurgo masa harara tana fad'in tunda nace maka banida lafiya ko?"ko kuwa kaje kaduba mata nima Akace maka irin sune?"tabbas na duba su harma da haihuwa duk yau na Amsa"ta yamutsa fuska tak'i mgn"yad'an tab'e baki ya matso ya fisgo hannunta data rik'e k'ugu dashi"batare daya kalletaba ya saka mata ledar hannunsa yana fad'in ki dafa mun ruwan shayin me karanfani"be jira cewar taba yasa kai ya fita"ta tab'e baki tana Ajiye ledar ta cigaba da Aikinta "bayan ta idar ta shirya masa komai cikin basket ta d'akko tare da ledar ta fito daga cikin kitchen d'in"mamy na kallonta tace sannunki da Aiki Ahyaan"yauwa mamy"ta fad'a tana Ajiye basket d'in saman center table ta wuce d'aki"gefen bed ta zauna ta duba ledar"cream shaver d'in ne cikin kwalinsa sai ledar pads guda 4, kowace leda guda 12 pieces ce Aciki"ga kuma man kitso babba"sai kuma 2k daban"da mamaki ta d'auki 2k d'in "sannan ta cire cream shaver d'in ta maidasu cikin ward rope tana d'an murmushi Afili tace wani time d'in broth yanada kirki"bara naje naji kud'in meye ?"ta fad'a tana fitowa cikin d'akin"tana fitowa shi kuma yana shigowa cikin parlourn "kusan Atare suka zauna kan kujerah"mamy dai batayi mgn ba tama wuce tsakar gidan sbd tayi Alwallah ta fara Azkhar"Ahankali tace" broth !naga sak'on nagode sosai"Amma kud'in dana gani na meye?"ya kalleta yaga bashine take kallo ba"sai yayi shiru "kanafa jina?"kina mun mgn kina kallon wani wajen "na lura baki son kitso Any time gashinki Atsefe"kuma kina yima mutane girki"gobe in Allah yakaimu kije Amaki kitson da kud'in...... ikon Allah wannan shi Ake kira k'arfin hali wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000 Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251 dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba #Mommyn fareesa #Dr Nura Darma #Ahyaan #mr Mahuta #AA mashi #mu'az #Khairiyyah #Ammah #Ummah #ikkhee 7/21/24, 11:01 - Buhainat: *AGE MATE'S* *19&20* *Littafin kud'i ne!* .......cike da mamaki Ahyaan ke sauraren kalaman nasa har yayi shiru"sai ta saki murmushi irin na rainin wayo tana d'age kafad'a tace"sannu yaya babba! idan nayi girki Anga gashi sai mutum ya cire ko kuma mutum ya hak'ura da cin girkin nawa"nidai nasan gidan nan babu wanda ya tab'a mun k'orafin hakan sai kai"sbd haka ni ba zanyi kitson ba"haka kawai naje Ajamun gashina kaina yazo yayita mun ciwo ko?"tunda ba damuwa kayi da Abinda nakeso ko bana so ba....tamkar wanda ta danne bakinsa da dannau ya kasa iya furta komai sai binta da kallo kawai yakeyi har tayi shiru"sai kuma ganin yak'i tankata ya saka ta mik'e tsaye da nufin ta wuce d'aki"*bani kud'i nah* ! yafad'a tamkar bayaso"yi tayi tamkar bata jiba ta kama tafiya"taku biyu tayi yace"zonan nace miki Ahyaannnnn! ya kirayi sunan nata cikin wani irin salon taushin murya mai Amo da ratsa zuciyar mai saurare"A bazata taji saukar muryar tasa"gaba d'aya saima ta kasa juyowa"idan nazo nan baki zoba komai na miki ke kika ja"nifa gaskiya broth bazan baka ba ai kyauta ka bani"kaga zanci faran 500 yau da dare,gobema ta 500 har na cinye kud'in"bece komai ba ya mik'e tsaye yafara tunkarota"kamar Ance ta juyo ta ganshi yakusan isowa inda take "Azabure taja baya"ki tsaya ki bani nace ko?"menene zata baka?" kaida baka gajiya da tak'alarta"cewar mamy data shigo jikinta da lemar ruwan data yi Alwallah "da sauri Ahyaan ta matsa bayanta tana fad'in wai mamy cewa yayi naje Amun kitso"ni kuma kinsan bana son kitson zafi ke Akwai"shine wai saina basa kud'in daya bani na kitson"ta k'are maganar cikin shagwab'a"mamy ta kallesa yayi tsaye ya wani sha mur yana kallon Ahyaan da tak'i yadda ta kallesa"ita mamy dariyama yabata"tana d'an murmushi tace"Ahyaan ta fika gaskiya "na baka ta rabaka da mutum"nifa ba kyauta na bata ba mamy "kitso nace taje Amata tunda ban Isa da itaba ta bani kud'i nah na wuce mana"k'in tankashi mamy tayi ta kalli Ahyaan tace"wuce muje ciki kiyi Alwallah rabu dashi"ba zaki bayar d'in ba"da kake sakata Aikace Aikace baiwarka ce ita ko kuwa Ajiyeta kayi ne?"bece komai ba ya fita"sbd shine kawai yasan meya keji ga jikinsa"Ahyaan kuwa sai taga kamar bata kyauta masa ba"musammun data tabbatar siyayyar Abinda ya mata zasufi 10k, dama kawai sbd ta jashi ta nuna bazata bayar da kud'in ba.....Bayan An gama sallar magrib d'in tana zaune tana Azkhar ya shigo cikin d'akin"saida gabanta yafad'i dataji sallamar sa"ta d'ago kanta suka had'a Ido, saita kawar da kanta tace"barka da shan ruwa"barka kadai"taso muje! Ina kenan?"bece komai ba ya juya ya fita"ta tab'e baki tana zare hijab d'in jikinta Afili tace na shiryama duk wata fitinarka"komai zakayi bazan bayar da 2k d'in nan ba"ta fad'a tana fitowa daga cikin d'akin "ta samesa zaune kan carpet yana zuba ruwan zafin dayace ta dafa masa"ga wata leda bak'a Ajiye gefensa"Agefensa nesa kad'an dashi ta zauna tana fad'in gani"ya mata banza"matsalata dakai shine k'yaliya"nanma be tanka taba ya kurbi shayin"sannan ya zaro plate ya warware ledar gabansa ya juye balango me zafi yanata tashin k'amshi"yau dake zamuyi bud'a bakin sarkin mita"kai kuma sai Ace maka sarkin shariya ko?"ya mata shiru"tayi d'an murmushi tana fito da kular data zuba masa doya da k'wai da Awara soyayya"kafin tace"zan dai taimaka maka na tayaka rannan Ai baka mun tayi ba saima Ina maka mgn ka wani Amsa Awulak'ance"ta k'are maganar tana gallah masa harara "ya tab'e baki yana fad'in wlh zan koraki d'aki"hmm ! lallai ma "dad'in Abin kirani kayi bani ce nazo ba balle ka gayan mgn "kuma Allah babu inda zani"kamun mugunta na had'aka da daddy Ai yadawo"bece komai ba yaci gaba da shan tea d'insa harya gama ya Ajiye cup d'in ,ya d'auki fork yafara cikin Abinda ta zuba musu a plate"ita kuwa bata fara ciba"shinkafa da miyar kifi tafara zuba masa ta turo masa gabansa"sannan ta d'auki wani fork d'in tad'an koma matsowa gabansa suna ciye ciyensu babu me mgn "saidai dasun had'a Ido zata hararesa koshi ya harareta"da naman yazo k'arshe ta janye plate d'in tana fad'in ni za'a barmawa broth nice fa k'arama "dariya yadinga b'abb'akawa yana kallonta"Ahaka mamy ta shigo ta samesu"ba k'aramin mamakin ganinsu Ahakan tayiba" tamkar irin mata da miji suna cin Abinci haka taga sum mata.... y'ar rainin wayo kawai "Ashe kin yadda dai na girmeki da sati gudan ko?"ta gallah masa harara tana fad'in dama sbd ka barmun ne na fad'a"Amma mamy ba nice babba ba?"murmushi kawai tayi ta zauna kan kujerah "shi kuma Dr darma be koma mgn ba yaja plate d'in Abincin ya fara ci"ita kuwa saida ta cinye sauran naman duka , sannan ta d'auki plates d'in da cup d'in da yasha shayi ta wuce kitchen dasu "bata jumaba ta dawo rik'e da goron ruwa Ahannunta"ki koma ki d'akko mun fanta na gwangwani"dato kawai ta Amsa sbd ganin idon mamy"koda ta dawo samunsa tayi yana Amsa wayar wata mata dake neman shawarah sbd matsalar gidan Aurenta "gefensa ta Ajiye masa da cup kafin ta zauna kan kujerah tana tab'e baki Aranta tana ganin rashin dacewar Abinda matar tayi"Ace duk duniya ta rasa wanda zaya bata shawarah sai wani da bata saniba,Ina y'an uwanta maza da mata da Aminnan Arzik'i?? shiru tayi sbd jin yadda yake jawo mata hadisai da Ayoyi yana fassarasu da bata hak'uri,bisa ga tayi biyayya ga mijinta ta hak'ura da Auren dazai k'ara indai zaiyi Adalci, kuma yanada halin d'aukar nauyinsu"bayan ya Ajiye wayar mamy tace Allah ya kyauta! dama kana Amsa kiran nasu ne?"ah ah sak'o dai ta turo tafiso muyi mgn"shiyasa data kira na d'auka"mijin nata ne zai k'ara Aure"murmushi Ahyaan tayi tace"wlh mamy ta bani haushi"miye ribar kiran wani kisanar masa da sirrinki?"wlh idan nice dashi da yarinyar duk sai kowa yaji ga jikinsa"wasu matan lusarai ne wlh.... murmushi kawai mamy tayi,yayinda doctor be saka musu baki ba yana dai saurarenta yana cin Abincinsa"shi kansa yana ganin nan gaba zai karya layin da Ake turo tambayoyin gaskiya sbd be san takura "musammun wasu ma da ba sbd Allah suke turo tambayar ba"yana wannan tunanin ya gama cin Abincin "ya kalli Ahyaan ya mik'e tsaye yace"kina jin Ana kiran sallah kikayi zaune?"banza ta masa"shi kuma be koma mgn ba ya fita"......washe garin ranar misalin karfe 7:21 am Dr darma ya shigo gidan cikin shirinsa me matuk'ar d'aukar hankalin duk wanda ya kallesa "yadi ne sabo ash colour Ajikinsa, ya Aza hula k'ube wacce tayi daidai da kakar kayan"yayinda har Ana ganin lallausan