← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 69

Sashe 47

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sama bashida hawan jini da fad'uwar da yayi yanxun komai zai iya faruwa"Akwai wata mgn da Aka sanar masa marar dad'i itace ta haddasa masa bugun zuciyar"Amma yanzun Ana buk'atar ya huta"kansa kawai daddy ya gyad'a masa cikin damuwa"yayinda Dr darma ya fita daga cikin parlourn yana tunanin wace irin mgn ce Aka sanarwa Abba marar dad'i da har zai shiga irin wannan yanayin?? k'arfe 10:5 pm haka Agogon dake cikin parlourn ya nuna"daddy ya kalli Abba da baifi mintina goma da farkawa ba yace"Alh iliyasu kai nake saurare ka sanar mun meke faruwa?wace irin mgn ce ta tashi hankalinka harka zube haka?"idanun Abba jajir yace"Akan maganar Auren Ahyaan ne Alh kabeer "Ashe yaron nan yaron banza ne ba shida mutunci"iyayensa k'ananun mutane ne"yazo d'azun da yamma sbd na kirashi batun yakawo motoci Aje inda Akayi order d'in kayanta su kwashe Aje Ayi jere"Abin b'acin rai wai sai gashi da zancen dan Allah nayi hak'uri wlh yanzun bazai iya Auren Ahyaan ba"badan ta masa wani abu ba kawai yaji bazai iyaba..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! wace irin maganar banzace wannan?"wlh kuwa"babban tashin hankalina meyasa be sanar da wuri ba saida wuri ya k'ure?munyi gayya gobe d'aurin Aure"gashi yana so ya zubar mun da mutunci da mutuncin y'ata"yanzun me kake zaton wasu zasu d'auka Akan wannan maganar na fasa Auren Alh kabeer ? wlh ko mahaifiyar yarinyar nan ban sanarma da wannan tashin hankalin ba"ban nuna masa na damuba sbd ban gaji da y'ata ba"nace kawai yaje gobe da safe yazo ya Amshi tsiyar lefensa"dama Allah yasa bata tab'a komai ba Aciki"saidai bayan ya tafi na kira mahaifinsa ta waya na sanar masa. hankali tashe yace be san komaiba suma shirye shiryen bikin sukeyi Amma bara yajirashi yazo suyi mgn baza'a fasa ba"nace ah ah nima na fasa bada y'ar tawa suzo su Amshi kayansu kawai"ban gaji da itaba,bazan bayar da itaba inda ba'a bukatarta"tunda ya nuna haka koda Anyi Auren bisa tursasawar iyayensa baza tayi wani farin ciki ba.wannan gaskiya ne! Ina goyon bayanka d'ari bisa d'ari daka nuna musu haka"Aure kuma baza'a fasashi ba da izinin Allah"Allah be kunyatar dakai ba bbu wani mahaluk'in daya Isa ya kunyatar dakai"dukda Abin yazo Amakare Amma wannan ba wani abu bane"goben in Allah ya kaimu za'a d'aura Auren nasu da Nurah "sbd dama Abaya na fahimci suna son juna dashi"bedai furta bane"bayan haka Ina ganin shak'uwa me girma tsakaninsu"bana zaton zamuyi dana sanin wannan had'in "Ajiyar zuciya Abba ya saki yace"kana ganin nuran bazai k'iba kodai Akirashi Aji ta bakinsa ne?"ah ah Alh iliyasu dashi da ita duk yaran mune mun Isa dasu, muke iko dasu"jikina na bani Nurah sai yaji dad'in wannan Aure "hakama itama mamanah"tsabar farin ciki hawayen dad'i Abba yakama yi ya ce" nagode nagode!! Abokina kuma d'an uwana"Allah yabarmu tare ya tsaremun daga sharrin shaid'anun mutane...daddy ya matso yana murmushi ya dafasa yana fad'in karka damu Abokinah tun muna yara muke tare"mu kashe mu rufe bbu wanda ya sani"sbd haka kadena mun godiya"bana son kowa yasan da maganar nan har sai And'aura kowa yaji"may be daga baya kayima zainab d'in bayani,Nima nayima Maryam d'in bayani"Nura kuma bayan And'aura zan sanar masa"sbd mahaifiyarsa ta tabbatar mun da cewa yana son Ahyaan "kaji ikon Allah Allah ! saiya b'oye yak'i sanarwa Ashe ita d'in rabonsa ce"ni kaina Abaya idan Ina ganinsu tare saina dinga zaton hakan"saidai data kawo wani saina cire batun Araina.hakane kam"tarewar tasu munji ta bakin Nura d'in ko yaushe ne.....sun jima suna fira sai wajen sha d'aya saura Abba ya tafi cikin gida"aka rufe gidan baki d'aya.. saida daddy ya shigo ya sanar ma mamy da Ahyaan Abba ya sami lafiya yamaje ya kwanta, sannan kowaccensu ta samu nutsuwa"haka nan Ahyaan tajita cikin wani irin farin ciki"koda ta kwanta bacci saida tayi mafarkin wai gata nan itada Dr darma sanye da fararen kaya cikin ciyayi kore yana mik'a mata filawa.adaidai nan ta farka ta ganta ta makara har gari yafara haske"hakan yasa tayi saurin shiga toilet tayi Alwallah"bayan ta idar da sallah mamy tasaka tayi wanka da break fast ,wanda tea ne kawai tasha"me make up sukazo tare da Khairiyyah aka fara yimata"cikin y'an mintinah sashen nasu yafara cika da mutane y'an uwa na nesa dana kusa da makota"saidai gaba d'aya zuciyarta bestie d'inta take son gani....misalin k'arfe 11:00 pm d'aruruwan jama'a suka shaida d'aurin Auren *Aminatu iliyasu lawal & Nurah kabeer Darma* ! Akan sadaki nera dubu d'ari biyar...... Alk'awarin Allah yacika Ahyaan ta zama ta Dr darma wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000 Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251 dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba #Mommyn fareesa #Dr Nura Darma #Ahyaan #mr Mahuta #AA mashi #mu'az #Khairiyyah #Ammah #Ummah #ikkhee 7/21/24, 11:01 - Buhainat: *AGE MATES* *55&56* *Littafin kud'in ne*! ........kammala d'aurin Auren yayi daidai da tsananta bugawar zuciyar Dr darma dake d'akinsa kwance ya rufe kansa Aciki.gaba d'aya duniyar ta masa zafi da k'unci"ciwon kai da zafin zuciya had'e da rad'ad'i sune ke Addabar rayuwarsa"tun lokacin da yaga lokacin d'aurin Auren ya kusanto yakejin tsinkewar zuciya"sunan Allah kawai yaketa Ambata"koya samu sauk'in Abinda ke damunsa"zirarowar hawayen bak'in cikinsa yayi daidai da wayarsa ta d'auki ruri"yana dubawa yaga daddy ne"Atake k'irjinsa ya buga! yasan zai tambayesa Ina ya shiga be gansa wajen d'aurin Auren ba?"wanda tun bayan sallar Asuba yake nan kwance Adak'in"ko office bashida Alamar tafiya kuma yau Friday....har wayar ta tsinke be samu damar d'agawa ba"iyaka kawai ya tsurama wayar kyawawan idanuwansa da sukayi jajir yana kallo kamar me nazarin wani Abu cikinta."yana tambayar kansa shikenan yarasa bestie d'insa"shikenan yarasa Abokiyar firansa da fad'an sa da raharsa"me kankat kuma masoyiyarsa???....be gama wannan tunanin ba kiran mu'az ya shigo cikin wayarsa"yaja dogon tsaki sbd Aganinsa mu'az yafi kowa sanin matsalarsa to Akanme zai damesa da wani kiran banza?"harta tsinke be d'aga ba"ya tab'e baki ya gyara kwanciyarsa ya kashe wayar gaba d'aya yana goge hawayen dake zuba gefen idanunsa"Afili yake furta Ina miki fatan Alkhairi *Aminatu*! Allah yasa bak'in mutumin nan ya rik'e munke Amana "in sha Allah zan bama mamy gift naki ta baki kafin su tafi dake gidanki"saidai bazan tab'a bari ki ganni ba koni na ganki....shiru yayi sbd wani mahaukacin knocking da yaji"Azuciye ya sauka daga saman bed d'in yana fatan Allah yasa ba wanda yakejin nauyi bane ke masa wannan shegen bugun k'ofar"sbd yana son cin uban ko waye.be tsaya tambayar ko waye ba? ya bud'e k'ofar yayi tsaye daga shi sai boxer da farar vest.....Ango Ango!! nayi Alk'awarin dama nine mutum na farko da zanzo na maka Albishin d'in cewa *Ahyaan ta zama taka* "cewar mu'az daya wanku cikin shadda sky blue yana tsaye yana kallon sa"fuska Ad'aure Dr darma yace"kafi kowa sanin halin danake ciki mu'az"be kamata ka tsokaneni ba"pls kaje kawai bana buk'atar kowa"yak'are maganar yana juyawa cikin jin zafin mu'az....wlh wlh!! da gaske nakeyi darma" kaine mijin Ahyaan Ayanzun dakai Aka d'aura "da farko danaji ban yarda ba, na sake kashe kunne sannan naji"dukda haka saida na tambayi daddy yace"Eh dakai Aka d'aura....tamkar Acikin mafarki haka yaji kalaman mu'az"ya juyo ya dubesa yana nuna kansa da tsantsar mamaki k'irjinsa na wani irin mahaukacin bugu da k'yar yace"mu'az dan Allah da gaske kakeyi?"da gaske ne mana Darma"kasan dai bazan maka rantsuwa Akan k'arya bako?"kafin yayi mgn sukaji sallamar Isma'il Abayansu yana fad'in yaya daddy yace"yabaka nanda mintina 30 kasameshi a parlourn sa"dato kawai ya Amsa"mu'az yace"yanzun ka yadda?"bawai ban yadda bane Abin dubawa taya kuma komai ya sauya?"ka manta da Akace *matar mutum kabarinsa?*"rungume mu'az ya matso yayi cikin tsantsar farin ciki yake furta Alhamdulillah! mu'az nagode sosai Allah yabar mu tare"da bakazo kayi gaggawar sanarmun Aminatu ta zama tawaba da k'ilan zuwa nan da wasu mintina zuciyata ta jima da bugawa"kaine mutum na farko daya mun Albishir na Alkhairin da bazan tab'a mantawa ba Arayuwata"ya fad'a yana cikasa ya juya yayi suyyada"mu'az ya dinga murmushi yana fad'in to Angon bazata maza faka faka kayi wanka ka shirya"ni yanzun zanje na sanarwa Fatima da wasu daga cikin friends namu"sannan zanje Asibintin ku na sanar musu"dukda Abin yazo ba shiri"Amma dole mu cashe"in kun gama mgn da daddyn ko zuwa k'arfe 2 zanzo damai photo Amuku kaida Amarya ko?"to shikenan Abokinah duk yadda kakeso haka za'a yi"tunda Ahyaan ta zama taka ba?"murmushi Dr darma yayi yace"Eh mana "Amma gaskiya Abokinah dole muyi wani gagarumin party na nuna farin cikin mu gaskiya"Dr na nufar bath room yace"zamu iyayi iya mu"Amma matata bazata jeba duk gardawan friends namu su kallemun ita"kama Isa kace bazata jeba?"be kulashiba ya shige cikin bath room d'in"yayinda mu'az ya fita....gaba d'aya tsabar farin cikin dayake ciki da d'oki ya hana ya tsaya yayi wankan cikin nutsuwa"befi mintina goma ba ya fito d'aure da towel yanata murmushi"da godiya ga Allah Azuciyarsa wai bestie ta zama matarsa kamar a mafarki"da wannan tunanin ya goge ruwan jikinsa yafara shirinsa cikin nutsuwa"cikin sabuwar farar shadda y'ar ciki da malun malun ya shirya"wacce aka k'awata da Aikin hannu da bakin zare"kasancewar dama yana yin d'inkuna sabbi ya Ajiye idan muradin saka sabbi ya tashi saiya saka"tun daga kan. Agogo,takalmi,hula duk bak'ak'e yasaka "yayima kansa b'arin zafafan turaruka "Atake jikinsa ya rikice da wani irin mayataccen k'amshi me ratsa zuciya"ya kalli kansa ta cikin mirror yana d'an murmushi sbd ba k'aramin kyau yayi ba shima kansa ya sani"be mantaba last 2 days Ahyaan ta tursasashi da rigimarta wai yaje Amasa gyaran fuska da Aski "ita yafi mata kyau idan yayi gyaran fuska"sai yace to zaije Amma bazata rakashi ba sbd Abinda yafaru kwanaki mazan shagon nata kallonta har tayi masa shagwab'a gabansu"shine sai yaje Akayi masa shi d'aya"ya tabbatar da ba'a yiba fuskar tasa bazata fito irin haka ba.Anutse ya fito daga cikin d'akin rik'e da phones nasa ya rufe ya nufi sashen su mamy "wasu daga cikin Abokan wasan Ahyaan dake haraban gidan y'an d'aurin Aure suka dinga tsokanarsa da kiransa da Ango Ango!! shidai murmushi kawai yakeyi yana basu hannu sukayi musabuha ya wuce ciki....tun bayan An
Chapter 47 · 0% Book details