← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 69

Sashe 17

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamar bata san meke faruwa ba??"saidai fa ran ummah ya b'aci da Abba yak'i mgn ya wuce ciki.... *2 days ago* Tun ranar Friday da Dr darma yacewa Ahyaan ta wuce ciki be koma tanka taba"itama haka daga nata b'angaren tayi biris dashi"dukda cikin kwana biyun week end ne Amma yayi busy sbd Monday zai fara fita office,ga zuwa chemist ga Aikin ginin gidansa da Aka fara babu wanda yasanar mawa"sai ya zama tun safe idan ya fita sai yamma yake dawowa"mamy na lura Acikin 2 days d'in break fast da lunch wajen mama yake zuwa yayi"saidai tayi murmushi kawai sbd ta lura fushi yakeyi da ita sosai .... Ayau yakama ranar monday! Abinka da sabon ma'aikaci tun 7:00 am ya gama zazzafan shirinsa ,sbd ba break fast zaiyi ba "kasancewar yana Azumi "kuma yayi Alk'awarin 8 am a office zata dinga yi masa"k'ananun kaya ne riga da wondo na t shirt da jeans Ajikinsa "sai ya Aza jacket Asama"ba k'aramin kyau yayiba"yasha sabon Aski jiya da gyaran fuska"sajen nasa har walkiya da d'aukar idon me kallo yakeyi tsabar yadda yaji gyara"ga wani irin k'amshi me kashe jiki da zuciya daya zaunah Ajikinsa"shidai sau guda ya kalli kansa ta cikin mirror ya d'auke kansa yana koma d'aure fuska "dan yau da y'an jin kan yatashi"hakan kuma ba k'aramin kyau yayi ba...wata jaka ya d'auka da Aka bashi laptop ya saka ciki "sai kuma ya nufi gaban mirror ya duk'a ya saka takalminsa sawu ciki coffee brown irin kalar suit jacket d'insa, yana k'ok'arin tashi tsaye....wani irin harbawa da dokawar k'irji ce ta samesa duk a lokaci guda, Adalilin jin sautin zazzak'ar muryarta me kama da busar sarewa tana yi masa sallama"d'aure fuska ya k'arayi yana jin wani iri"sanye take da hijab har k'asa me hannu wacce ta lafe Ajikinta ta fiddo shape d'in jikin nata, sbd kayan dake jikin nata robber ne,kuma sun matseta.....kanafa jina nayi sallama shine ba zaka Amsa munba?"yayi shiru yak'i tankata"Kai wai mika d'auki kanka ne? Duk yanda zuciyarki ta baki ?.yafada cikin cool voice ya nufi bakin k'ofar d'akin"ta d'an kallesa"kaje daddy na kiranka"bayan hakan kaima kasan Akanme zan wani shigo cikin wannan tsamin d'akin naka? Mittsoww! banda lokacin ki"Ak'ule tace " ban hanya na wuce" idan nak'i fa?"rayuka su b'aci "tunda Ai naga gaba kakeyi dani ko? nike gaba dake ko kece kike gaba dani?? wlh duk ranar da nake miki mgn kika koma yimun tsaki sai kinyi nadama"Agabana kike gaida su khaleel"ni meyasa bakya girmamani Ahyaan?"shine zakiga laifinah sbd na fita harkan ki kamar yadda kika nuna bakiyi dani?"bana cusa kaina inda Aka d'aukeni Awulak'ance kin gane ko?"wai yanzun duk dan sbd na maka tsakin kake wannan fad'an?"ya mata banza"okay yayi kyau bani hanya na wuce"duk tana maganar ne bata re data yadda ta kallesaba "shi kuma gaba d'aya ita yake kallo"ganin yak'i tankata kuma yak'i ya gyara saita saka k'aramin kuka tana fad'in wai ba zaka gyara na wuce ba?"sai kin bani hak'uri sannan zaki tafi"kanta ta d'ago suka had'a Ido "harara tayi jarumtar watso masa tana d'auke kai"sai kuma tace"ba yau zaka fara fita office ba shine kakeso kayi latti?"to ai kece kika ja"ki bani hak'urin shine kike jin girman kai? naji shikenan kayi hak'uri "banida sunane?"to broth kayi hak'uri "dama shine sunana?"shi mu'az kina kiransa yaya ni banda ni?"murmushi ta saki har beauty point d'inta na lub'awa tace"kaima kasan Ai ya girmemu ko?"sannan kaiba k'an....kina k'arasa fad'a Ina falla miki Mari"ya fad'a yana tsareta da manyan idanunsa ya wani tsuke fuska"hmm !wlh da Anyi y'ar mare mare kuwa"kadai ce nadena maka tsaki na baka hak'uri ko?"kuma duk na baka"to nima karka koma cemun yarinya ko kuma K"idan nak'i fa meye zaki iya yimun?"banza ta masa tak'i mgn saiya matsa suka fito"zata wuce yace jirani mana"ta wani turo baki batace komai ba tana satar kallonsa sbd ba k'arya yana bama wanka lokaci"bayan ya rufe ya mik'a mata jakar ungo rik'emun ki jirani gefen mashin nawa. sai nazo na Amsa na wuce"nidai gaskiya bazan iya jiraba muje dai je cikin gidan mana"shikenan ki barsa"wai broth meye haka ne?"yayi shiru yabi ta gefenta"shikenan kawo na rik'e kaje wajen daddyn zan jiraka "beyi mgn ba ya juyo ya mik'a mata jakar ya wuce"ita kuma ta nufi bakin get wajen flowers ta hango mashin nashi"tsaye tayi tana d'an murmushi sbd idan badan itama tana son Amfana dashi ba da babu wani hak'urin da zata bashi "d'an renin wayo "duk ta Ayyah na Aranta murmushi na sub'uce mata"kamar Ance ta juyo ta hangosa yana nufota cikin shegiyar tafiyar nan tasa ta k'asaita "d'an nutsuwa tayi batace komai tana kallonsa ta gefen Ido yajawo mashin d'in dake wanke goge ya hau"ta d'an lumshe Ido sbd k'amshin turarukan sa ba k'aramin dad'i yake mata ba"matsowa tayi ta Aza masa jakar daga gabansa tana fad'in to ustazah Allah yabada sa'a"sai kayi Addu'a idan zaka fara duba patient "dukda bansan ta wane sashen ka karantaba"idanunsa Akanta yace"fannin mata ne! yamutsa fuska tayi sbd haka kawai taji bata so hakan ba...ko zaki bini ne? yafad'a can ciki"Allah ya tsareni da koma hawa wannan mashin d'in naka kaje ka kayar dani ko?"idan Allah ya bamu motar daka ce saina dinga binka koma inane"uhmm !idan na tashi fita dake a mashin saiki hana"bak'ar mgn taso yab'o masa Amma sbd tuna zata Aikesa saita fasa....ga key nan ki gyaramun d'akina "batace komai ba ta Amsa Ahankali tace"broth dama pls zan baka sak'o idan zaka dawo?sak'on meye?"ta sunkuyyar dakai k'asa"idan bazaki fad'amun ba matsa na wuce"cikin shan mur tace wlh Dana maka rashin mutunci"to kimun ko yanzun mana"yafad'a yana tayar da mashin d'in"dama cream shaver nakeso pls"gashi sauka siyomun"meye zakiyi dashi?"me kasan Anayi dashi?"ta k'are maganar tana mik'a masa 2k"sai yak'i tankata yaja mashin d'in ba tare daya k'arbi kud'in ba ya wuce"yana d'an murmushi sbd yayi mamakin yadda ta nuna kunya"ya d'auka marar mutuncin batada kunya sai rainin wayo ta iya..... Kwance take saman 3 seeter Acikin wani had'ad'd'en katafaren parlour na Alfarma ,wanda yaji kayan more rayuwa...."idanuwanta Alumshe tana tunani"tayi iya bakin k'ok'arinta na ganin ta yakice guy d'in nan A cikin ranta Amma Abin yaci tura"ko muryarsa taji sai ta samu nutsuwa balle kuma uwa uba tayi tozali da kyakykyawar fuskarsa"taso ta hak'ura dashi ,kodan sbd taga Alamar beda kirki ,zafin kai had'e da shan k'amshi da Aji,duk tana lura yana dasu"k'ilan sbd yanada kyau yake hakan?"saidai ta saka wad'anda ta Amince dasu da suke kusa da chemist nashi sud'an bibiyesa taga ko watace ta janye hankalinsa"Amma yadda take jinsa Azuciyarta zata iya komai sbd ta mallakeshi..... Anty Ikhkhee! taji muryar sultan d'an yayanta"tashi tayi zaune saima lokacin ta lura shida daddynsa yake"hannun yaron ta kama ta janyosa saman cinyarta tana d'an murmushi tace"yaya Abubakar! Uhmm Autar Hjy"tunanin meye kikeyi haka yaronki na miki mgn Amma baki jiba?"waskewa tayi tace" kaina ke ciwo ne yaya Ina wuni?"lpy qlau"Mr mahuta ya Amsa yana zama kan kujera yad'an lumshe Ido yana girgiza k'afafuwansa "yaci burin zuwa guda zai komayi gidan su Ahyaan daga nan muddin babu nassara to wlh kota wane hali sai hak'arsa ta cimmah ruwa....itadai bilkisu na zaune tana satar kallonsa tana jin kamar ta sanar masa da matsalarta tasan yayanta yadda yake sonta zai iya komai Akanta"saidai ita bata so Arok'i Dr Nura Darma ya sota, tafi son ta jashi Ajiki tayi Amfani da k'irsan mu ta mata ta janye hankalinsa....shigowar hajiyar su cikin parlourn yasaka ta sauke Ajiyar zuciya.....saida Ahyaan ta gama Abubuwan gabanta sannan tana surutai da gulmarsa wai yacika takurata da yawan saka Aiki"2 days taji kasiririt da basu mgn shine yanzun daga sun koma mgn zai fara matsa mata"kasancewar tunda ya dawo Nigeria sai yau ne dataje kiransa ta shiga d'akin,sai kuma yanzun"komai na d'akin ya burgeta sosai"bama wani datti yayi ba"Anutse ta gyara masa saman bed d'in,ta goge mirror da table d'in da yake aza books na Addini "sannan tayi shara da mopping"kafin ta shiga bath room d'in "wow! wato gyara dai ya saka Aka masa shine sbd son kai mu be saka mana bath tub ba ko?"ta fad'a tana k'arema cikin toilet d'in kallo komai Atsare"ga kayan wankansa masu k'amshi"ko wane saida ta duba"in bacin taga rashin dacewar tayi wanka Anan datayi"Amma dukda haka saida ta wanke fuska da k'afafuwanta "data gama wanke bath room d'in"sannan ta fito ta sami turarukansa ta faffesa "ta kuma turare d'akin da turaren wuta"sannan ta rufe ta wuce cikin gidan "da farko mamy tama d'auka shine ya shigo da taji k'amshin turarensa saida taji maganar Ahyaan sannan ta fahimci itace ke k'amshin"mamy meye za'a girka?"ki bari sai Anjima Ahyaan kwanta ki huta"inaga fa mamy broth yauma yana Azumi ?bazan iya ganewa ba sbd yanzun wajen mamah yake cin Abinci mu nan laifi muka masa Ai"murmushi kawai Ahyaan tayi tama d'auka kodan sbd ta dena masa mgn kuma mamy na goyon bayanta ya saka yake fushin"saidai batace komai tayi kwanciyar ta har bacci ya d'auketa..... bayan sallar la'asar uban gayyar ya shigo cikin gidan Agajiye sbd rashin sabo da Aiki "ga chemist ma yad'an je ya zauna yaduba mutane da sallamar masu siyan magani"duk yad'an fad'a sbd gajiya da yunwar Azumi "koda ya kafe mashin d'in d'akinsa ya fara nufa sbd ya watso ruwa yad'an kwanta kafin time d'in shan ruwa yayi"kan wasu kujeru dake gefen barandar da d'akunan mazan gidan suke Anan ya zauna yakira mamy yasanar mata Ahyaan ta kamasa keys d'in d'akinsa "kasancewar beda contact nata"kuma zafin kansa ya hanashi ya nema"beyi zaman mintia biyar ba Awajen hamza ya iso wajen da gudu yana sanye da yunifoam farare na islamiya"yadda ya kallesa ya had'e rai ya saka yaron ya nutsu yana gaidashi ya mik'a masa"wato ita tafi k'arfin zuwa ta kawo shine ta Aiko?"ya fad'a Azuciyarsa yana Amsar key d'in tare da fad'in Ina Ahyaan d'in?"tana kitchen tana girki"be koma mgn ba ya mik'e tsaye ya wuce ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga.....k'amshin turarukan sa dana turarukan wuta yafara shak'a "Allah ya shirya ki *Aminatu* shine Abinda ya fad'a yana maida k'ofar ya rufe" ya kalli saman mirror ya girgiza kansa,sbd ya fahimci ta faffesa masa turaruka"ya fad'a saman bed d'in yana sauke Ajiyar zuciya "saidai k'afafuwansa na'a k'asa ko takalminsa be cire ba"sai y'an kalle kalle yakeyi ko Ina fes dashi"yafi mintinah goma Akwance kafin yayi
Chapter 17 · 0% Book details