Sashe 35
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
dazai Aureta"batun Aiki shima zamuyi Abinda za'a koreta"saidai komai daki daki zaizo. Amma boka...ku Ajiye sadaka ku tafi , Akwai masu son isowa nan suma suna hanya"ya fad'a yana gimtse fuska"hannunta na kirma ta Ajiye masa kud'i kusan dubu 50" K! kud'inki nera dubu d'ari ne"kuma kinzo dasu"haka zaki Ajiye ki wuce"Aiki ukku za'a maki"sbd haka idan baki shirya ba tafi ki bani waje"uwale tace haba luba ki Ajiye muje mana"ummah hannu na kirma ta zaro cikon ta Ajiye"Atake hayak'i yacika wajen,suka kama tari"ku rintse Ido sannan ku bud'e"da sauri suka rintse,suka kuma koma bud'ewa ,sai gasu gaban kwalo kwalo "ba k'aramin tsorata ummah tayiba"yayinda uwale ta kama dariya sbd batayi mamaki ba"zuwanta Anan na ukku ne Ayau"na farko zuwan kanta ne,na biyu wata ta rako,yanzun ma ta koma rakowar Akaro na ukku.sai zuzuta Aikin malamin uwale keyi har suka shiga cikin kwalo kwalo ya tsallake ruwan dasu"yayinda luba kejinta cikin farin ciki"dama burunta shine rayuwar Ahyaan ta k'untata"so takeyi Ab'ata komai Akanta sannan tadawo kan mama"sbd itama ba k'yaleta zata yiba..... misalin k'arfe 10:11 am na safiyar yau Asabar "garin yayi lullumi sbd hadarin dake A sararin samaniya"ga iska me dad'i na ratsa jiki"Ahyaan ta fito rik'e da wata k'aramar leda fara ta shopping Ahannunta"tana sanye da doguwar riga ta Atamfa red& white,sai mini hijab red colour"wacce tayi masifar yi mata kyau"ta k'awata kyakykyawar Choco face nata"yayinda plate shoes ne sanye Ak'afarta.sai sauri takeyi da k'yar mamy ta barta zataje gun saloon.....tana k'ok'arin fitowa daga k'ofar shiga shashen nasu shi kuma yana k'ok'arin shigowa! kusan fad'a masa Ajiki tayi"cikin hanzari tayi baya kamar zata fad'i "Dr darma yayi saurin rok'o hannayenta"Atake idanuwansu suka sark'e "Ahyaan dake jin wani iri Ajikinta sbd hannayenta daya rik'e"saita janye idanuwanta daga cikin nasa ta fara k'ok'arin zare hannayenta daya rik'e....ya kafeta da Ido tamkar yau ne ya fara ganinta"yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu wacce ta fidda shape d'in body building d'insa"ya k'ara haske da frash saidai fuskarsa da rama har yanzun "ga k'asumba ta cika masa fuska"be jima ba da tashi daga bacci ba ya watso ruwa ya shigo cikin gidan sbd yayi break fast"yana kuma fatan Allah yasa karya ganta"gashi Addu'ar tasa bata karb'uba.....pls ka cika ni naje broth "ta fad'a tana b'ata fuska"cikata d'in yayi sbd shima wani irin Abu yaji yana fusgarsa daya rik'e hannuwan nata"zuciyarsa na ingizashi daya rungumeta koya sami sassauci, Amma saiya dake....Ina zakije?"ya fad'a tamkar bayaso"kallonsa ta komayi saita turo baki tace"wai broth tamkar baka duniyar"kamar ya?"hmm ! rabon dana ganka harna manta ni"ta k'are maganar cikin mamaki tana d'auke Idanunta daga kansa"sbd ganin kusan 2 weeks rabonta dashi"wanda yayi daidai da wata biyu cif kenan da saka ranar su itada Abdallah Mashi "yawanci duk sadda zai shigo gidan da Asuba"ko bacci takeyi ko tana sallah"be kuma sake shigowa sai k'arfe 2:30 pm "lokacin kuma tadawo daga office tana bacci"sbd data dawo tayi sallah kwanciya takeyi sai la'asar take tashi"shiyasa sai tayi har sati biyu ko d'aya bata gansaba....uhmmm !idan kin damu da son ganin nawa Ai kinsan inda nake kwana ko?"sai tayi shiru,tarama rab'a gefensa ta wuce"ya d'age kafad'a irin ko Ajikinsa d'in nan "yama d'auka koda motarta zata fita"da wannan tunanin yayi gaba Abinsa"saidai hoton fuskarta na'a cikin zuciyarsa "gaba d'aya yau ta masa wani irin kyau"ga wata k'uruciya daya gani Atare da ita "sai ta masa kamar y'ar 20yrs.... Ahyaan na fitowa ta wuce bakin titi ta tari nafef"kai tsaye zainab beauty saloon Aka Ajiyeta "suna isowa ta sallami me nafef d'in ta wuce ciki.saida ta d'auki kusan Awa guda Aciki sannan ta fito sbd ta samu layi"daga gaban shagon taga me nafef ya kara gefe"har zata wuce taji yace Hjy tafiya zakiyi?"Eh "Ina zakije?"*baya jidda road*"to shikenan shigo muje kud'inki 500 ne"okay ta fad'a tana shigowa"basufi mintina 5 suna tafiya ba wata mace ta tsaidasu"tana sanye da face mask da eye glass bak'i"haka nan Ahyaan taji fad'uwar gaba da suka tsaya "saita dake kawai tana kallon matar da sauraren inda tace za'a kaita"wansa kusa da Anguwar sune"bayan sun gama mgn dame nafef saita shigo"da sauri Ahyaan ta kalleta sbd k'amshin turarenta yamata kama da wani k'amshi data tab'a ji"sai kawai ta basar taci gaba da kallon waje suna tafiya....can kawai taji an dafa kafad'arta "ta waigo da sauri"Ikkhee dake zaune gefenta ta watso mata wata powder fara"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ta furta tana tari"kasancewar jininta me k'arfi ne sai hodar batayi saurin gusar mata da numfashi ba"tana jin dariyar Ikkhee da ganinta bibbiyu"saita lumshe lulu eyes d'inta, Adaidai lokacin kuma Ikkhee ta kira Mr mahuta yana d'auka tace"yaya Abubakar gata nan mun kamota muna hanya ne...iya nan Ahyaan taji daga haka bata koma sanin inda kanta yake ba....... Sharhi kawai