← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 69

Sashe 27

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauke ta Ajiye basket d'in saman center table d'in data gani gabansa ,saita zauna gefen sa tad'an dubesa suka had'a Ido"shine Ammah ta tafi koki sanar mun nazo muyi sallama da ita?"wai da gaske kakeyi broth ta tagk?"nifa bansan tama tafinba sai yanzun daka fad'a"shine ta tafi babu sallama sbd tana fushi dani ko?"ta kare maganar cikin shagwab'a kamar zatayi kuka "shi kuwa uban gayyar ya zuba Ido yanata Aikin kallonta"Atake ya fahimci tayi kuka "kukan meye kikayi keda baki gajiya da saurin kuka??"ya furta Afili ,wanda Azuci yaso yayi maganar"ita kanta Ahyaan saida taji k'irjinta ya buga"ga muryar tasa ta saka mata jin kasala"saita kasa mgn ta sunkuyar dakai"tambayarki nakeyi fa?"ya fad'a yana dannah waya"Abin mamaki yaga Ikkhee bata yanke wayar ba"sai yaja tsaki ya kashe wayar"okay tunda tsaki kake mun bara naje na baka wane, zuwan nawa beda Amfani "ta fad'a ranta Ab'ace zata Mike tsaye"bece komai ba sai wayar tasa daya Aza mata saman cinyarta ya nuna mata da hannu"saita tab'e baki ta kalli fuskar wayar taga number d'in Ikkhee da baiyi seving ba"ga just now ! Alamar yanzun suka gama waya"saita tab'e baki ta fara k'ok'arin ture wayar"nifa da wata nake bada keba ko *bestie*? Ai fushi ba naki bane keda kike da patient"dukda kin tafi kin barni har saida na Aiko kizo kuma"yanzun haka Ake jinya?kasa mgn tayi sbd mamakin sa"ga sabon suna daya saka mata "ganin tak'i yin mgn ya saka shi cewa laifin meye kika yiwa Ammah d'in?"saida ta kwab'e fuska kafin tace"Allah kasan broth bata kyautawa haka kawai saina yadda naso wani k'aton tuzuru daya gand'ame Agida ya tuzurance "bayan haka kuma nifa bemun ba"wai yana sona bayan yana sa'an uncle mustapha"kusan 45yrs"never wlh! d'an jim yayi sbd yanzun ya fahimci shiyasa sukazo tare da uncle mustapha"kuma Abba yazo d'azun sbd suyi zancen kenan?"dariya taci k'arfinsa ya dinga b'abb'akawa harda rik'e ciki"kamar ba d'azun shine kwance magashiyan ba"Broth ka gani ka dena mun dariya ko? Uhmmmm! *Aminatu* kenan! kece da abun dariya Ai"Amma tunda bakyaso na dena"dama shawarah zamu yi"saida ta hararesa tace"yanzun zaka nemi shawaran tawa bayan bakada mak'iyiyar data wuce ni?"nine yaka mata nace miki haka "Amma mu barshi bisaga Abinda ya wuce"kinga gobe sunday tunda ba office zanjeba zamuje ki rakani wajen friends d'in Fatima muyi mgn naji meye za'a basu na hidimar biki?"tab'e baki tayi tare da cewa Allah ya kaimu"Amma ni meye nawa na Aje dani?"kika san ko na samu budurwa idan ta miki saiki had'amu ko?"banza ta masa tana dannah waya, shi kuma yana kallon lips nata data tsuke.....wai yanzun bazaka ce Allah yasa Alkhairi da Aikin dana samu ba balle ka bani shawara me kyau?' "Inada niyar yin hakan sai kika yi maganar"tun last 2 days su Abba suka sanar mun nayi murna da Addu'a da fatan Alkhairi "batun shawara koda baki nema ba zan baki sbd wasu dalilai. Amma yanzun ki zubamin roman nasha inata jin k'amshi kin Ajiye "ba tace komai ba ta zaro kular ta bud'e k'amshin ya daki hancinsu"cikin wani plate me d'an zurfi ta zuba masa cinya da k'ugu(kwatar kaza) "gashi shine rabonka"ta fad'a tana wani shan mur"ya kalleta ya kalli plate d'in fuskarsa da d'an murmushi yace"haba bestie! koda rabon gaskiya zakiyi saiki zubamin k'irji da fiffike ko?"ya fad'a yana saka spoon ya d'ebi roman yakai bakinsa"lumshe Ido yayi sbd yamasa dad'i sosai"gashi yajin beyi yawa ba,beyi kuma kad'an ba"nidai shine rabonka gaskiya"to shifa wannan bread d'infa?"nazo maka dashi ne ka dinga dangwalawa da roman sbd nasan bakayi lunch ba, ka Isa jin yunwa yanxun"kamar kin sani"Ina jin yunwar Amma bakin ba dad'i"Amma ki zuba mana muci tare zanfi ci idan bani kad'ai bane"batace komai ba ta zuba kamar yadda ya buk'ata"d'an matsowa tayi suka fara ci"shi yafi cin bread d'in da romo"ita kuma naman Ayangance tana danna waya"k'asan zuciyarta tana mamakin wai Ammah ta tafi bata saka An kirata sunyi sallama ba..... k'arfe nawa zaki dinga zuwa wajen Aikin?"8 am, na dawo 1pm "tunda zuwa k'arfe d'ayan ne natashi, kaga bazan zauna ba zan dawo gida"banda ranar Friday da kuma week end"Asati sau 4 ne zuwan"okay Amma kamar wanne shirye shirye ne zasu baki?"Eh to saidai zuwa Monday d'in idan naje mugani"Amma dai nasan Akwai news na turanci da fassarasu"daga k'arfe 9 zuwa goma na safe"sai kuma Akwai shirin *mu gyara muhallinmu* "Amma duk ranar Wednesday ne Akeyi"duk shirye shiryen Akwai wacce zaku jagoranta tare da ita ne ?"bandai sani ba gaskiya"yayi shiru "can yace"da kamar 7 :30 am zaki iya gama shirinki saina jira ki mu wuce na saukeki"oh wai broth ba kama san nayi motaba ko?ban gane ba?"ga mota can gefen taka tamuce"uncle mustapha ne ya siya mun ita tun Ina KD"to dama nace saina samu Aiki zan fara hawanta"Masha Allah! naganta tayi kyau sosai"Allah yasa Alkhairi "da Ameen ta Amsa"d'an shiru ya biyo baya"can yad'an daure fuska tare da cewa"zancen gaskiya ki kula da kanki da nuna keme mutunci da tarbiya ce"domin duk inda mace ta shiga ta nuna Akasin hakan Tofa mutuncin gidansu ta zubar"bance dole ki saka hijab ba, Amma kiyi shigar data kamata"batun jan Aji da kamun kai dole Abaki 100% ta wannan b'angaren"sosai ya bata dariya har tayi murmushi dan kanta ya fashe....so ya kamata ki kama kanki da ajinki wajen iya hud'd'a da mutanan da kuke Aiki musammun maza"banda sakewa ko yin wata doguwar fira har akaiga jin sirrin juna"nidai shawaran da zan baki kenan...ni meyasa da zaka fara Aiki baka nemi shawarata ba game da yadda zaka mu'amalanci mutane ??"Abazata tambayar tata tazo masa"saida ya shanye romon daya deb'o kafin cikin cool voice d'insa yace"babu komai"Amma ko yanzun bata b'aci ba Abani shawaran zan d'auka..ya k'are maganar yana murmushi "Adaidai lokacin Abba ya wuce ta gabansu" wanda yayi mamakin ganinsu Ahakan suna cin Abinci cikin kwano guda" su ba suma lura dashi ba"Ahyaan kuwa tab'e baki tayi tana hararan plate d'in tace"saida nayi k'orafi sannan zaka so shawaran?"kuma ni ban yadda ba kafini cin naman ko?"shikenan juyo mana sauran mu cinye"Amma da dare meye zakimun na kwad'ayi?"zan soya maka kifi kaci da yaji"kina nufin shan yaji zaki koyamun?"bayan kema inaso ki dena ci"batace komai ba ta juye musu sauran"shi kuma ya d'auki fanta d'in ya bud'e yafara sha yana lumshe Ido"gaba d'aya jinsa yakeyi wasai beda wata damuwa"to muci mana"kece zaki fara"ni Allah kaine zaka fara ko?"sai yayi d'an murmushi sbd shi kansa yayi mamakin yadda Ayau taketa masa biyayya ba tare daya sha harara ko bak'ar mgn ba"cinya ya d'auka ya yaga "itama saita d'auki wani gefe me tsoka"kafin takai bakinta sai dungure mata lips da sauran cinyar kazar dake hannunsa yayi"Ai kuwa ta kai mata raruma ta wafce tsokar dake jiki tana dariya"hakan yafaru Akan idon mu'az da yake tunkaro inda suke "da Alama dubiya yazo yi.....sai kin biyani Abuna?"uhmm! ni kuwa dame zan biyaka broth?"komai ma"yayi maganar k'asa k'asa"saima lokacin Ahyaan ta lura da mu'az na nufosu"ba k'aramin kunya da nauyinsa na ganin nasu Ahaka tajiba"ita kanta bata san meyasa idonta ya rufe tayi wannan sakewar dashi haka ba?"bayan kusan wata nawa saiya gadama inya zama dole yake tankata"karfa yaga tama damu dashima yayi zaton shishshigi ne..... Atake y'an jan Ajin nata da izzar ta suka motsa"saita mik'e tsaye da hanzari tana jin mu'az na cewa" Abokinah barkanku da hutawa ! ba tare data kallesaba ta gaishesa. ya Amsa da kulawa da tambayar ta yamai jiki?"da Alhamdulillah! ta Amsa ta wucewarta zuwa sashen su mamah sbd tana so taji dalilin da yasa Ammah ta wuce bata neme taba...... uhmmm ?mutumi nah ka cika k'uminiya da Abu fa"kamar ya?"cewar Dr darma yana d'age gira"saida mu'az ya zauna kafin yace"naga kaida mutuniyar kun shirya ko?"gashi harda cin Abinci kukeyi tare"matsalata dakai sanya Ido"tunda kazo ganinka ya saka ta tafi Ai shikenan"batun shiri da kake mgn nima bansan meyasa muka shirya d'in ba?"hmm ! Anan gaba zaka sa dalilin daya saka kuka shirya"saidai fa kaida ita sai kukayi kamar irin sabbin Auren nan"ga wani kyau kunyi,ita sai tayi kamar Amarya....d'aure fuska uban gayyar yayi tare da cewa "kaga dan Allah kadena zancen daka san bama tabbata zaiyi ba"wannan samun namu dakayi sbd bani lafiya ne"shiru kawai mu'az yayi tare dashan Alwashin ya gama yima dr darma zancen Ahyaan "ya lura ko kallonta beso yanayi,saidai zuciyarsa ta jima da zargin Dr darma ya mace A soyayyar Ahyaan"kodan sbd masifaffen kishinta daya ke nunawa k'arara"jin kansa da izzarsa ya hanashi nunawa yaketa basarwa"Amma duk wanda yasan meye so ya gansu Ahaka dole ya zargi wani Abu...kaga mlm idan tasani gaba zakayi kana gulma kaida zuciyarka pls kaje kawai"okay to shikenan "ya fad'a yana d'age kafad'a ya mik'e tsaye"kana nufin tafiya zakayi da gaske bayan dubiya kazo?"of course zan iya tafiya tunda baka buk'atata"uhmm! kaga gobe zamuzo nida bestie muga friends d'in nata"Amma bana so yarinya sama da biyu tazo gaskiya"ya fad'a yana wani yamutsa fuska"dariya mu'az yayi yace"kana yadda kaga dama darma"wacece bestie kuma?"banza yamasa yak'i yin mgn "shi kuma ya dinga tsokanarsa wai babynsa ce bestie d'in.... Ahyaan na shigowa tsakar gidan ta sami innah Asabe da ummah zaune kan tabarma suna k'us k'us suna dariya"nunawa tayi kamar bata san da zaman suba ta nufi k'ofar parlourn su....ke! yanzun dan ubanki kina ganina Amatsayina na yayar mahaifinki ba:zaki gaisheni ba?"juyowa Ahyaan tayi ta kalleta sama da k'asa tana yamutsa fuska tace"karki koma zaginah! Iyye? kar kiyi mamaki yaya Asabe koni bata gaisheni"Ai tana gadara zata fara Aiki ko?"Aikin banza da wofi"da tayi Aikin Ai gara taje tayi zaman Aure "yo Allah na tuba da Ace y'ata na yawan gantali Asunan Aiki Ai gara Ace tana gidan mijinta....ya Isa haka yaya Asabe! kinzo inda bazan iya jurewa ba"Allah yaraba y'ata da yawon gantali"datayi Auren da shekaran na zagayo ta fito ta tulke mun Agida ba Aure ba karatu balle Aikin "Ai gara tayi Aikin zaifi riba "muna zaune Allah zai kawo mijinta da lokacin zuwansa yayi"da wanda keso da wanda beso"sai dai d'an bak'in ciki ya mutu"ni ban gaji da y'ata ba daga ni har mahaifin ta "to Akan me za'a sama na Ido sai kace bisa kan wani take.... shigowar Abba tsakar gidan yabsaka mamah tayi shiru "da Alama yana cikin Anguwar daya fita beyi nisa ba.....Ahyaan na huci tabar tsakar gidan ba tare data ce komai ba"saidai Azuciyarta taji
Chapter 27 · 0% Book details