Sashe 38
Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahyaan wajen Dr darma ta nufa sai b e kallesuba ya wuce Abinsa ciki kawai.....wani irin zafi da rad'ad'i yaji Azuciyarsa sakamakon jin sautin kukan nata, besan lokacin daya matso dab da ita ba yana furta to wai miye Abin kuka Anan Ahyaan ?"bakai bane kak'i hak'ura"shikenan na hak'ura ki dena kukan to"shikenan muje gida mana"ta fad'a tana goge hawayenta "yanata kallonta yana jin kamar ya mannata Ak'irjinsa ya girgiza kansa Ahankali yace"zamuje Amma sai idan munji yadda case d'in zai kasance"sanin kankine zasu iya burkitasa"sannan munyi waya da mamy na mata bayanin komai"dukta damu tace na maidoki gida"dama nasan dole mamy nah ta damu"bansan meye wasu daga cikin mutane masu dukiya suka d'auki kansu da rayuwa ba??"dama wannan banzar k'anwarsa ce?"Eh yafara labarta mata zuwansu Asibiti kwanaki da irin yarfin daya musu"ka kyauta broth"ta fad'a tana murmushi"sai kuma tace"Amma meyasa daya d'aukeka kwanaki baka sanar mun ba?"ta fad'a suna had'a Ido "d'an tab'e baki yayi kafin yace"lokacin naga bana gabanki kuma kina gaba dani.tana k'ok'arin mgn sukaji muryar mu'az Abayan su yana fad'in Abokinah kuzo kaida bestie naka a office d'in AC yana son mgn daku"yana fad'in hakan ya wuce bejira cewar suba"Dr darma ya kalleta yaga tunanima takeyi"kinji me yace?"uhmm"iya Abinda Aka tambayeki zaki bada Amsa"inkin san zaki kula saurayinki Acan to kije ke kad'ai....haba broth wane irin mgn kakeyi haka?"Eh kokin manta d'azun yakira ni da wani?"wato nine wani Awajenki ko?"yafad'a cikin zafin zuciya yana hura hanci"wai bakace ka hak'ura ba?"kumafa na nuna masa be kyautaba "yayi shiru "kaji bestie?"murmushi ya sub'uce masa saiya gyad'a mata kansa suka wuce ciki Atare. sun kwashe kusan mintina 30 suna tattaunawa Acikin office d'in AC"har mahaifin Abdallah Mashi da Abokinsa wani minister suka k'araso "sai gashi k'aramin case yakoma babba"wanda badan sbd mahaifin AA mashi ba da Mr mahuta ko Awa bazaiyi ba a cell daga shi har k'anwarsa "koda suka fito daga cikin office d'in kai tsaye cell d'in da Mr mahuta ke ciki Ahyaan ta nufa"yana tsaye ya cire malun malun nasa yana tura sak'o ta text message "yana jin motsin tsayawar mutum yasaka wayar Aljihu ya kalli daga gaban k'ofar suka had'a Ido da ita "tana binsa da mugun kallo "Amamakin ta sai taga ya kama b'abb'aka dariya yana nunata da yatsa bbu wani d'ar yace"Ina Mai tabbatar miki da cewa nanda 20 minit saina bar nan wajen"dake da banzan d'an uwanki na kalan dangi dashi wanda zaki Aura duk sai kun gane kuranku"sannan Ina kan bakana Akan ki saina yaga miki rigar mutunci"na lashi takobin kota tsiya kota Arzik'i saina huta dake...d'an murmushi Ahyaan ta saki Anutse tace"idan Allah ya yiwa bawansa sutura da rigar mutunci babu wanda ya Isa ya keta masa"inaso nanda 10minit kabar nan bama 20minit ba "Ina kuma me tabbatar maka da cewa daga kaina ka gama shiga harkan wata"daga kai har k'anwarka da shaye shaye ya gama lalata ma brain"karka manta Ina tare da kariyar ubangiji nah kai baka Isa ka cutar dani ba"ko nassarar saceni da kuka samu to dama Allah ya rubuta hakan saiya faru....K! dallah ya Isa haka kije mana"ni banga Amfanin zuwanki Anan ba"iya Abinda na sani ba'a game dani Atashi 0-0 ko 1-1"saidai Atashi 0-1"okay ba damuwa Allah yakaimu Monday lafiya zakaga firanmu dakai Ayanzun tana yawo"wawa lusarin namiji kawai ! kuma k'aramin d'an bariki...tana fad'in hakan tayi gaba"Mr mahuta ya zaro Ido yana y'an kalle kalle Acikin cell d'in gabansa na fad'uwa "jikinsa na bashi Akwai CTV camera kenan?"Atake jikinsa ya fara keto zufa"sai yaji beda k'warin gwiwar tura sak'on dayake so yatura..... Ahyaan kuwa ranta fari k'ar ta fito daga cikin police station d'in"dama Abdallah Mashi ne yabata shawaran suyi haka ranar monday Awatsa vedio d'in a news daga nan kowa yasan waye shi harda iyayensa "kafin su shiga koto"ta hakane zai gane yayi kuskuren had'o wasansa da y'an jarida....Dr darma da mu'az na tsaye gefen motarsa suna mgn "Abdallah Mashi shi kuma suna mgn da Abbansa da Abokinsa"cikin jin nauyi Ahyaan ta k'araso ta sanar masa komai ya kammala"Abba yabita da kallo yana jin kunyar yarinyar ta burgesa"shi dama besan taba Azahiri a TV yasan itace d'an nasa zai Aura....tun kafin AA mashi yayi mgn Ahyaan ta wuce wajensu Dr darma sbd tasan ita suke jira"bestie! ta fad'a tana kallonsa"mu'az yayi mamakin jin sunan data kirashi dashi"yayinda me gayya me Aiki beyi mamaki ba sbd d'azun ma da haka ta kirashi"saiya kalleta ta turo baki tana fad'in mungama mu tafi gida ko?"okay Abokinah zamu wuce"saima lokacin ta tuna bata gaida mu'az ba"ta juyo tana gaidashi"ya saki murmushi yace bazan Amsaba Ahyaan sai yanzun kika ganni"? Amata uzuri Abokinah "kasan Abin nan daya faru dukta furgice"danma ita d'in jarumah ce! kai bestie kaine dai jarumi"sukayi murmushi gaba d'aya"Dr darma yabud'e mata driver sit sbd shi bazai iya driving ba"bayan ta shigo ciki ya kalli mu'az dake cewa yanzun shine zaka dannata cikin mota baka bari tayi sallama da saurayin....wani banza kallo ya watso masa tare da cewa in ka gadama kaje nanda k'arfe d'aya da rabi zanzo gidan na dubata"be jira cewar saba ya shige mota yana hango Abdallah Mashi na satar kallon motarsu"Ahyaan kuwa ko Ajikinta ta bama motar wuta tana fad'in muje chemist kayi dressing d'in ciwon ko?"no muje gida Acanma inada kayan Aiki"yafad'a yana d'an lumshe Ido ya jingina bayansa Ajikin kujerar yana bin dogayen yatsun hannunta da suka k'awatu da Adon jan lalle sunata d'aukar Ido gwanin kyau da burgewa....shi bak'in lalle becika burge saba, yafi son yaga mace tayi jaa sbd irin Amfaninsa ga y'a mace"to Amma idan Aka d'an sirka ja da bak'in ko yaya yana d'an burgesa....daga yau ko Ina zakije bance ki koma hawan nafef ba"koda bakida mai Amota kimun mgn nazo ko inane na mik'a k'i"to broth zan kiyaye kasan k'addara ta riga fata"hakane Allah yak'ara tsarewa"Ameen yah Allah "naji dad'in zuwanka da taimakon ka gareni Allah....saurin dakatar da ita yayi da cewa" ki dena mun wata godiya bana so bestie"ya k'are maganar yana bud'e lumsassun idanuwansa "ta saki d'an murmushin daya mata masifar kyau Anutse tace"yabon gwani ya zama dole shiyasa"uhmmm! kawai ya fad'a Adaidai lokacin da Ahyaan ta gama parking Abakin get d'in gidan daga waje.... kusan Atare suka fito daga cikin motar "itace Agaba yana biye da ita"tun daga duga dugan k'afafuwanta har zuwa saman bayanta yake bi da kallo....*komai na bestie me tsari ne da burgewa* ya Ayyah Azuciyarsa suna ida shigowa cikin tsakar gidan Mamy"kusan su 8 suna zaune tsakar gidan, Abba,daddy,husnah,mamy,mama, khaleel da Abdul Aziz,sai kuma ummah data zo badan Allah ba ,sai dan taji taka maimai meke faruwa?"dan yanzun Alhamdulillah Abba yarage hantararta "ta kuma dena warin jab'a.kai tsaye jikin Mamy Ahyaan ta fad'a ta saki kuka mecin rai"itadai mamah kauda kanta tayi tana kallon nurah dake duk'e gaban iyayen nasu yana musu bayanin Abinda ke faruwa....oh duniya Ina zaki damu,wace irin fitina ce wannan??"zanje police station d'in dole Ashiga kotu Amata tsakani dashi da kuma k'anwarsa "Allah ya kyauta ya tsare gaba! Cewar ummah tana tashi tabar wajen"wanda tayi mamakin yadda Dr darma ya saida ransa yaje ceton Ahyaan....wai baza kiyima mutane shiru ba?"nurah yaka mata Ayi ma sannu bake ba"cewar mama fuska Ad'aure "nidai dan Allah ki k'yalemun yarinya da wani fad'a naki"kai kuma kaje kayi dressing ciwon mana"ta fad'a tana kama hannun Ahyaan suka Mike tsaye"ita kuwa ta saci kallon Dr darma Ashe ita yake kallo saiya d'age mata gira ya kashe mata Ido d'aya.... murmushi ya sub'uce mata "haka nan taji Abinda yayi ya burgeta ya sakata cikin nishad'i! saita kauda kanta tabi mamy "shima Dr darma be jimaba bayan fitarsu mamah ya wuce sashensa"saida ya fara yin dressing ciwon nasa sannan yayi wanka ya shirya cikin golden brown d'in t shirt da trouser black ya tafi masallaci da nufin idan yayi sallah ya wuce yaduba jikin matar mu'az. misalin k'arfe 4:48 pm Ahyaan ce kwance a parlour saman 3seeter tana kallon TV "sanye take da doguwar rigar lace d'inkin bubu"ta d'aure gashin kanta da Aka gyara d'azun da bant irin kalar kayan jikinta"tanata k'amshi me sanyi da kashe jiki"yayinda fuskarta da ligjt make up "Azahiri game kallonta zai d'auka hankalinta na wajen TV Amma Abad'ini ba'a nan yake ba"tunanin Abinda yafaru d'azun zuwa yanzun ne Aranta"ga wani sukuku datayi"duk idan ta tuna da Abdallah Mashi sai taji fad'uwar gaba",har kuma yanzun be kirata ba"ga kuma tunanin Ina Dr darma yatafi bayan shida bayada lafiya?"ko Abincin kirki bata ciba"wani irin Imani da tsoron duniya taji ta k'araji Aranta"musammun data tuna ikon Allah Akan bayinsa. Ad'azun da safe ko a mafarki bata tab'a zaton Abinda yafaru zai faruba ,gashi yafaru"kuma Allah ya fitar da ita"sai kuma ta tuna da Ikkhee "Atake taji sabuwar tsanar yarinyar Azuciyarta"wato son broth takeyi ko?"ta fad'a Azuciyarta Afili kuma taja tsaki....ke kuma keda waye kike jan tsaki?"taji sautin Amon jarumar muryansa yana Ida shigowa cikin parlourn rik'e da leda bak'a Ahannunsa"ga gudan hannun nasa yayi dressing"sai k'amshi ke tashi Ajikinsa"fuskarsa tayi fiyau gwanin kyau tana d'aukar idon me kallonsa....saida Ahyaan taji fad'uwar gaba dataji muryansa"tayi saurin tashi zaune tana kallonsa, sai kuma ta kauda kanta "gefenta ya iso ya zauna yana fad'in mamy fa?"tana gidan Hjy bata jimaba da fita"okay shi wannan fushin na meye ?"ga tsaki na samu kinayi?"shiru tayi tak'i mgn"kinji?"ba wannan banzar budurwar taka bilkisu take ba ko meye ba?"bestie baki gajiya niba budurwata bace"itace dai ke haukanta da yawan kirana ,na kumayi blocking nata tunima"na kuma fahimci itama bata san yayanta yasan kiba"ya daiyi Amfani da ita ne wajen cimmah manufarsa "sai bayan kinje wajensa ku tattaunah saurayinki yaje sukayi mgn da ita da wani police"tanan muka san hakan"wai *saurayinah*? k'arya nayi ne?"idan baki sonsa kin kawosa Asa muku Rana ne?"nidai kima gaya masa bai zama dole yatanka munba"na lura yanata wani shan k'amshi daji da kai,toko Aurenki yakeyi be Isa ya kafamun dokar yadda zanyi mgn dake balle be kaiga Auren naki ba"to yam....pls kadena zancansa kaji?"yayi shiru yana tab'e baki ya kalleta sbd ba kad'an ba ta masa kyau ba"ya gyara zamansa suna fuskantar juna"bakyajin mgn ko?"me kuma nayi broth?"na lura fitinah dani kake nema kuma ni yanzun na gaji da fad'a dakai"kin dai sare kawai yarinya "laifinki shine ba kyason d'aura d'an kwali"kuma gobe sunday kije Amaki kitso"ya k'are maganar yana zaro kud'i