← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 69

Sashe 12

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hamshak'in Attajiri"nasan k'ilan kai baka sanniba "sunana *Ibarahm Abubakar mahuta* .nine babban d'ansa! yana fad'in hakan ya danna Landline phone"ba b'ata lokaci yaci gaba da cewa" mukhtar kamun kud'in nan dake cikin jaka"daga haka ya Ajiye land line d'in"har lokacin Dr darma na nan zaune yana saurarensa bece uffan ba"kimanin shud'ewar mintina 5 saiga yaro guda da Acikinsu suka kamosa ya shigo da wata leda viva bak'a Ahannunsa "bayan ya Ajiye ya juya ya fita"kallonsa yayi yace"ga wannan million biyu ne ciki" somun tab'i ne Dr kafin nan gaba saima yadda kake so za'a baka"na sami labarin har yanzun baka fara Aiki ba, shima zaka iya kamun takardun naka mu gani za'a kai inda Atake za'a daukeka Aiki "yanzun k asamun contact naka! ya fad'a yana sakin wani shegen murmushin rainin wayo"sbd Aganinsa dole Dr darma ya Ajiye zafin kai tunda yaga kud'i..... mik'ewa tsaye yayi Anutse yana koma sakin wani k'aramin murmushi "wanda yadaki zuciyar Mr mahuta dake zaune yana kallonsa da son jin ta bakinsa"gab dashi ya iso murmushin dake saman fuskarsa na dishewa"saida ya kallesa sama da k'asa kafin ya girgiza kansa Ido cikin Ido cikin iya tsara laffuzzan mgn yace" *wanda Ake d'auka ba komai bane sauda yawa wata ran shine ke zama komai" harma ya Amfani wanda ke ganin yafi k'arfin ya nemi ya masa wani Amfani* naji inada gadarar, kamar yadda kace"saidai Ina godiya ga Allah da yayini A talaka bamai dukiyar da zaiyi fahari ko tunk'aho itaba"iya Abinda na. sani da talaka dame kud'i duk Allah ne yayisu"fatan dacewa kamai muke nema"zancan Ahyaan dakake mgn ! Kaifa namiji ne? to meye zai Hana kayi Amfani da kanka wajen shayo kanta harta Amince maka?"Ina so kasani kud'i! basu bane komai" ka rik'e kud'inka bana buk'ata "iya Abinda na sani duk me jin kansa da nuna shi wanine tofa Agaban bainar jama'a yake gadararsa bawai ya tsaya yayita Abayan fage ba"idan har ka gama mgn dani Ina buk'atar na k'ara gaba"ban damu da matsayinka ko dukiyarka ba ,ko kuma zaka saka acutar dani"Abinda kawai na sani.....kai! kasan ko shi waye ne kake k'ok'arin gaya masa mgn?"cewar wani k'ato d'aya shigo ya tsintsi maganar Dr darma"saidai mahuta beso ya dakatar da shiba, yaso ya barsa yakai Aya "ya lura zafin kan yaron da izzarsa me girma ne"Amma daidai yake dashi....Dr darma kuwa murmushin takaici yayi yana nufar k'aton abazata yamasa wata wawar cakuma yana fad'in waye shi bayan *Ibrahim Abubakar mahuta*? Haihuwar sa Akayi kamar kowa ko kuwa daga sama yafad'o ne??"ya fad'a cikin zafin zuciya yana ingizashi da masifar k'arfi,ya daki bango"Atake wasu katti su ukku suka fito da manyan makamai Ahannunsu zasu nufesa"hannu guda Mr mahuta ya d'aga musu Alamar su bari"kafin ya mik'e tsaye sbd Al'amarin yaron ya fara bashi tsoro" yana ganin ba ta haka yaka mata yabiyo masa ba"Amma saiya basar ya kalli mutum biyu yana fad'in ku maidashi gida"daga haka ya d'auki ledar kud'in yabar parlourn.....kafin Dr darma ya juyo yaji wani k'yalle saman fuskarsa sun rufe masa Ido dashi "beyi mgn ba yana dai tsaye suka jashi suka fita suka shige mota...... k'arfe sha d'aya saura suka yi parking bakin titi basu shigo cikin layin suba"bece komai ba da suka janye k'yallen,kamar yadda suma basu maca komai ba, sai fitowa kawai da yayi daga cikin nafef d'in yana jan tsaki "ko Ajikinsa da Abinda Mr mahuta yayi na sakawa a d'akkosa"saidai zai nuna masa cewa raina kama kaga gayya"da wannan tunanin ya zaro wayarsa yaga 20 miss call"bema tsaya dubawa yaga kona waye, time kawai ya duba"jikinsa na bashi y'an gidan sune ke kiran sa"yaja tsaki yana nufar layin nasu da yayi tsit duk gidajen Anguwar suna a rufe ,sai d'aid'ai k'un motoci dake wucewa da mashina"tun daga nesa ya hango daddy da Abba da khaleel tsaye bakin get d'in shiga *gida biyu* suna mgn..... d'an huci ya furzan daga bakinsa"yana fad'in daidai nake dakai wlh mahuta tunda ka had'a wasanka dani"haka kawai sbd wani banza za'a tayarwa da iyayena hankali"ya fad'a Afili cikin yana yin jin b'acin rai yana tattaro nutsuwa da dakiya ya yafama kansa"cikin tausayin iyayen nasu ya iso gabansu....nurah! Ina kaje haka baka dawo gida da wuri ba, Anata kiranka ta waya baka d'auka ba??cewar Abba suna binsa da kallo....sunkuyar dakai k'asa yayi yana tunanin Abinda zai fad'a musu sbd su yadda"kasancewar be saba yin k'arya ba"kuma baya jin zai iya sanar musu Ainahin gaskiyar Abinda ya faru...wai bada kai Ake mgn bane?"cewar daddy Ad'an tsawace"kuyi hak'uri Abba Ina gidansu wani Abokinah k'anwarsa ce ta k'one "shine na tsaya na kula da ita da Abinda ya dace"wayarma tana silent yanzun me nafef ya saukeni"Ajiyar zuciya suka saki tare da fad'in Allah ya kyauta"daga haka suka wuce ciki"Dr darma ya rufe get d'in gidan ya nufi k'ofar d'akinsa yana tunanin Abinda yaga Mubarak nayi d'azun"da hanzari ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo ya kunnah haske ya nufi bath room "Agaggauce ya d'auro Alwallah ya fito ya kabbara sallar isha'i,bayan ya idar yayi shafa'i da wuturi "wajen k'arfe 11:30 pm ya fito daga cikin d'akin sanye da fara k'ar d'in jallabiya ya nufi inda yaga mubarak d'azun yaduk'a yana binnewa"k'arfen dake hannunsa ya saka yafara hak'o wajen.....k'irjinsa yayi wani irin bugu sbd ganin wasu layu had'e da Allurai da gefen zani da mayafi an yanka an daure"cike da mamaki da Al'ajabi ya d'aukesu ya Ajiye gefe ya maida ginar tsab ya rufe,kafin ya d'auki tarkacen layun yanufi d'aki dasu"dukda kasancewarsa masanin Abubuwa masu yawa yanada ilimi Akansu"Amma beyi gigin bincikaba ya barsu zuwa safe zaije wajen malaminsa daya koyar dashi Abinciki me layun suka k'unsa?"ransa yafi bashi kodai Ahyaan ko mama ummah tayima Asiri,shine ta bama Mubarak ya binne Acikin gidan"yaja wani kakkauran tsaki had'e da furzan da wani irin zazzafan huci daga bakinsa yana taunar lips nasa kamar zai hudasu"ya lashi takobin muddin harda Ahyaan Acikin wannan sihirin wanda yayi shi ya jama kansa"da wannan tunanin bacci yayi Awon gaba dashi ba tare da yama shiryama baccin ba.....washe gari misalin k'arfe 2:38 pm"Ahyaan na zaune kan kujerah y'ar tsugunno Atsakar gidan gaban tape tana wanke inner wears d'inta cikin roba"sanye take da plate d'in takalmi fashion pink colour masu taushin gaske"sunyi matuk'ar k'ara k'awata kyawun k'afar tata"yayinda da take sanye da doguwar riga ta Atamfa da hula navy blue tayi goshi style "fuskarta ba make up Amma tayi Shar da ita sai zuba k'amshi me kashe jiki takeyi"duka lips nata na cikin bakinta "tana pasin k'ofar shigowa tsakar gidan"mamy bata jima da fitaba wajen sunan k'anwar daddy"daga ita sai hamzavne Agidan"shi yana d'aki yana kallo"gaba d'aya cikin nishad'i take sbd tun safe Abba dazai fita ya Amshi takardunta ya tafi dasu"tana jiran dawowarsa"duka yau kwananta biyu da dawowa KT Amma bataje ko inaba in aka cire fitarsu ta jiya da Dr darma"har gidansu Khairiyyah taso taje yau mamy tace ta bari sai gobe Friday....k'amshin turarukan Dr darma masu kashe gangar jiki da zuciya suka fara rige rigen kaima kokafin hancinta ziyara ,kafin ta d'ago kanta har taji Amon jarumar muryansa me dad'in sauti na ratso kunnuwanta yana yin sallama "shi kuwa yana shigowa idanunsa Akanta suka fara sauka"sai Akayi sa'a ta d'an kallesa ta zabga masa wata uwar harara sbd tuna Abinda yamata jiya"kallon second 2 ta masa ta tab'e baki had'e da d'auke kanta"sanye yake da k'ananun kaya da p cap da takalmi sawu ciki"wanda sukayi shige da gogonsa da p cap d'insa "hannayensa na rik'e da ledoji guda biyu"fuskarsa ta d'an fad'a sbd Azumin daya tashi dashi"saidai ya k'ara haske"karan hancinsa yad'an fito"lips nasa sun k'ara yin jaa"directly inda take yak'ara so Aransa yaji dad'in ganin ta rufe gashin kanta"sosai yaji tausayinta dalilin binciken da aka masa d'azun akan layun dayaga Mubarak na binnewa"ita bata damu da rayuwar kowaba tana hidimar gabanta Amma wasu najin zafinta"ya Ayyana Aransa.......tsaye yayi gefenta in low voice ya furta"ba sannu da zuwa sai harara da za'a Aiko mun da ita *Amun dago* ? k'in tankashi tayi sai kuma ta dinga b'abb'aka dariya "ya tab'e baki yana fad'in Allah yaka miki sauk'i"hmmm! mlm ka wani shigoma mutane gida da ledoji kamar wani magidanci"sannu da zuwa Akanme zanyiwa k'anina sannu da....shiru tayi sbd ganin yayo kanta ta rintse Ido "yaja tsaki yana fad'in matsoraciyar banza"magidanci kuma saura k'iris na zama"bud'e idon tayi tace"Ashema tsoro?"ta k'are maganar Asadda take matse under ware nata"kiyi ki gama wannan wankin gulmar"Azumi nakeyi ki had'amun Abin bud'a baki "ya k'are maganar yana cin magani ya Ajiye lodojin gabanta"Anutse yaci gaba da cewa"kiyi mun kunun gyad'a "ga kayan fruit nan ina son fruit salad"wannan naman kiyi farfesu dashi"Allah ko?"ban sani ba"ni wlh kana bani mamaki da wannan Abin da kake mun"sai kace wata k'anwarka ko wacce kake iko da ita? kuma babuma irin ko dan Allah kimun Abu kaza "ah ah umarni kawai kake bani"Eh na baki ko bazaki yiba ne ?"Eh banayi"Allah bara mamy ta tashi saina gaya mata "uhmm! mamyn Ai bata nan ta tafi sunan gidan uncle nuhu"ki tashi ki matse kayan kije toilet ki shanya"daga yau na hanaki shanya inner wears Atsakar gidan nan"murmushi ta saki tana mik'ewa tsaye ta nufi gaban tape d'in tace"yanzun Agabanka zan shanya saika hana idan ka Isa...bece komai ba ya zaro Allura daga cikin Aljihun wondonsa dake cikin siringi harda ruwa ma cikinta"ya wani tsuke fuska yana binta da wani irin kallo me wuyar fassara yaga ta zaro Ido"murmushi yakusan sub'uce masa "kinsan Allah?"mintina 5 na baki muje Agabana ki shanya ki fito muyi Aikin nan nata yaki ko kuwa babu ruwana da lafiyan ki qlau Allura zan d'irka miki....haba broth wannan wane irin mugunta ne?"nidai ka maida Alluran bana son ganinta, Ai zanyi yadda kakeso "dama fa wasa nakeyi"shiru yayi yak'i mgn ya maida Alluran inda ya fiddota yana cin dariya Azuciyarsa"gaba d'aya jikinsa ya mutu sbd yadda ta kwantar da murya tana mgn Amairairai ce....to ka d'auki robar muje na shanya"Amamakinta bece komai ba ya d'aukar mata kamar yadda ta buk'ata.....har cikin toilet d'in mamy ya Ajiye mata sannan ya fito ya barta ciki ya tsaya daga cikin parlourn gefen k'ofar bed room d'in yana kallon hamza dake kallon TV "wanda yayi hakane sbd yasan zata iya zuwa ta rufe k'ofar bed room d'in "shi kuma beson kad'aicewarsu Adak'in su kad'ai ,yasan mamy bata
Chapter 12 · 0% Book details