← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 69

Sashe 14

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sha Allah kullum "saina baki mamah saiki bata tasha ta shafe jikinta"to nurah ubangiji yayi maka Albarka yabaka macen k'warai"Allah ya had'a mana kawu nanku ku d'ore da wannan zumunci"cikin nuna jin dad'in Addu'arta yace" Ameen" dan Allah ka dinga yima Ahyaan nasiha"ko yau da safe saida na mata fad'an yawo ba d'an kwali"saima tace kasiya mata huluna, nace taje ta saka"hakane mama bara na wuce ciki Amma ko mamy karkuyi zancen nan da ita, zata damu ko kuma ta sanarwa da Ahyaan d'in "to shikenan bazan sanar mata ba"dato ya Amsa ya mik'e tsaye yafita"mamah ta sauke Ajiyar zuciya Afili tace"na rasa gane kan yaron nan game da Ahyaan? "tunda ta dawo"zan dai biku da Addu'a"Ina mata kwad'ayin samunka Amatsayin miji domin nasan zatayi dace"saidai ita d'in da wuya tayi maka irin wannan kallon "saidai ita zatayi ta musu Addu'a"tuni take fatan idan yaran sun girma su had'asu Aure "sai kuma take gani kamar da wuya, musammun mace da tafi namiji girma"sai gashi shi ya fima Ahyaan d'in girma"sai wanda yasansu yake yadda ita sa'arsace"ita kanta yanzun so takeyi Ayima Ahyaan Aure kafin ta cika 30 yrs"kodan sbd gori da yada maganar da dangin Abba ke mata...... Dr Darma na fitowa daga sashen su mama Ahyaan da Khairiyyah suma suna fitowa da Alama rakkiya Ahyaan zata mata...siririn mayafi ne saman gashin kanta, tama cire hular,ga rigar Atamfar jikinta ta kamata sosai"yana ganin Khairiyyah ya sheda fuskar ta dukda ya jima be gan taba"yasan kuma tayi Aure"saidai shigar d'aya ganta da ita Ayanzun,ransa ya bashi da wuya idan tanada Aure gaskiya.daga ita har Khairiyyah d'in kallon second 5 ya musu ya d'auke kai cike da shan k'amshi sbd bema san ta kamasa raini gaban wata"saima yayi tsaye yana dannar waya"Ahyaan ta wani d'aure fuska tak'i kallon gefen da yake.....likitah bokon turai! cewar Khairiyyah data tsaresa da Ido tana mamakin ganin yadda yazama wani gentleman "yayi d'an murmushin daya masa kyau matuk'a yana fad'in kwana da yawa Khairiyyah?"wlh kuwa Ina wuni?"ta fad'a tana koma satar kallonsa tana kuma kallon k'awar tata, Aranta tana furta Masha Allahu! shidai da lafiya qlau ya Amsa daga haka be koma mgn ba"yana ta son su had'a Ido da mutuniyar tasa Amma tak'i yadda"ganin zasu wuce kuma bata damuba haka zata fita jiki bud'e ya sakashi had'e rai yana fad'in *Amun dago*! zo kiji wata mgn"saida taji fad'uwar gaba data juyo ta kallesa"ada masifa taso tayi masa Amma ganin yadda ya had'e rai saita daburce tama kasa yi masa musu"zo mana"to niba rakkiya zan mata ba"kije zan jiraki daga waje"cewar Khairiyyah tana tura k'ofar get ta fita"harara Ahyaan ta wurgo masa tana nufar gefensa taja ta tsaya tanata wani ciccin magani"kud'i y'an 1k guda biyar ya zaro daga Aljihun wondonsa ya mik'a mata had'e da cewa " ki bata tayi transport"to broth ta gode"ta fad'a tana d'an sakin fuska sbd taji dad'in hakan"karki nuna nine na bata ki bata Amatsayin kece"okay thanks"ki wuce ki koma ki saka hijab ko babban mayafi"Amma wlh ba zaki fita haka ba"ya fad'a yana shan mur ya wani matso dab da ita...wai dan Allah meyasa sai muna zaune lafiya kake son tado fitinah ne?"kece kike kallon haka"sbd nace ki rufe jikinki sbd shed'anu da kare mutuncinki da bin dokar Allah shine na tado fitinah?"batayi mgn ba rai b'ace ta nufi cikin gida"ya tab'e baki yana nan tsaye ta fito fuuuuu ta wuce kamar zata tashi sama ta wani had'e rai "tana sanye da d'aya daga cikin sabbin hijaban daya d'inka mata"shidai tab'e baki yayi yana tunanin bazai fasa kulawa da tarbiyan taba"da wannan tunanin ya nufi k'ofar d'akinsa, sbd yaje ya watsa ruwa ya tafi masallaci yayi zakirin kafin magrib.....da kallo kawai khairiyyah ta bita, sbd ganin yadda ta wani d'aure fuska da Alama ranta Ab'ace yake"ga kuma hijab ta ganta dashi bayan sadda suka fito ba dashi ta fito ba...kin gaji da jira ko? ta katse mata tunani "ah ah" nayi dai mamakin ganinki da hijab"wannan magulmacin ustazah d'in ne ya tilastani sakawa"wlh ina ga saina nunama yaron nan Ainahin true colour d'ina sannan zamu daidaita dashi"banida ikon kaina tunda nadawo KT sai yadda yaso haka nakeyi"dazun fa inner wears d'ina dana wanke, wlh hanani shanyawa yayi a tsakar gidan wai dole saidai na shanya a bath room "yanzun ma kona saka babban mayafi ko kuma na sako hijab"mitsssssuww! Wlh mugun gami zan masa da mamy "saurarenta kawai Khairiyyah keyi har tayi shiru, saidai batace mata komai ba,sbd gaba d'aya ranta ya fara yi mata hasashen wasu Abubuwa game dasu"Amma saita basar tace" muje na samu Adaidaita yamma tayi"ta fad'a suna jerawa suka nufi bakin titi "yayinda Ahyaan keta jan tsaki sbd yadda zuciyarta ke mata tuk'uk'in bak'in cikin Abinda ya mata...."uhmm k'awata kenan! Ashawaran ce ni banga Abin b'acin rai da damuwa ba Anan"gaskiya fa ya fad'a miki shine Abin damuwa?"karki manta kun taso cikin zumunci da had'in kai, idan kikayi wani Abu marar dad'i garesa mahaifiyarsa data shagwab'aki tamkar y'arta baza taji dad'i ba" dukda nasan ba zata nuna miki ko a fuska ba"ni wlh ji nayima ya burgeni"mutum d'an gayu, kamar bature"me ilimi duka ta kowane fanni"yayi wani irin kyau ,k'amshin sa fa har inda nake....kinga dallah ga Adaidai nan ki hau"na lura dama goyon bayansa kikeyi ba zaki gane me nake nufi ba"ta fad'a tana tsayar da me nafef d'in"bayan ta sanar masa zai kaita Anguwar malali quarters sannan ta shiga ta zaunah"Ahyaan ta matso ta mik'a mata kud'in tana fad'in gashi wannan magulmacin broth d'in can yace na baki Amatsayin nice na baki. ni kuma ban iya k'arya ba"Amma bakida kirki Ahyaan ,shine saikin fad'a shidan Allah yayi ai"oho masa ,bashi bane ya koya mun fad'in gaskiya Amagana da hanani k'arya yayin mgn tun muna yara"murmushi kawai Khairiyyah tayi sukayi sallama Ahyaan ta wuce cikin gida"saidai shashensu mamah ta wuce ta dubata sbd tasan kan maman na ciwo"sa munsu tayi zaune itada Asma'u suna cin soyan kaji"Ahhh mamah shagali kukeyi kenan?"kai Anty Ahyaan nasan kuma fa yaya Nura Ai yakai muku naku ko?"shiru tayi ta zauna kan kujerah ta cire hijab nata tana tunanin meyasa baya banbanta mama da mamy?"waike bazaki dena zama ba d'an kwali ba?"cewar mama fuska Ad'aure"shiru tayi ta d'auki cinyar kaza ta fara ci...sai bayan sun gama cin naman harma Asma'u tabar parlourn kafin mama ta kalleta fuska Ad'aure tace"na lura har yanzun baza kiyi hankali ki nutsu ba ko?"to wlh idan zaki farka ki nemi tsarin jikinki daga sharrin magauta ki farka ki nema"ita rayuwa basai An maka wani Abun cutarwa ba kake kulawa da kankaba da neman tsari ba"ah ah hausawa sunce riga kafi maganin mugunta"daga yanzun bayan ko wace sallah ki zauna kiyi Azkhar"sannan ki dinga d'aura d'an kwali"Akwai wasu Addu'oi da Aka sanar A sunna TV Anayi"zan dinga tofa miki su kullum kina sha kina shafe jikinki"daga baya ki cigaban dayi da kanki sbd kin iya"to mama zanyi in sha Allah "mama na k'ok'arin mgn hamza ya shigo cikin parlourn yana fad'in Anty Ahyaan yaya Nura yace kizo"banza tayi masa tak'i mgn "shi kuma yaron ya fita bema jira cewar taba"tsaki taja tana fad'in na rasa me yaron nan ya maidani? shi Nura d'in ne yaro?"cewar mamah da mamaki"Ashe bakida mutunci Ahyaan?"na d'auka yanzun wannan rashin jituwar da kukayi Abaya na k'uruciya ne Ashe har yanzun kin rainashi ko?"wai mama ba sa'ana bane laifine idan na rainashi....ganin tayo kanta ya saka tayi shiru ta sunkuyyar da kai tana bada hak'uri"in kin gadama kije kiji kiran da yake miki"duk ranar dana koma jin ko murya kin d'aga masa wlh sai ranki yab'aci marar mutunci butulu! ke kodan sbd mutumcin mamy har kin kamasa wargi"mutumin da yake kyautata ma iyayenki dake kanki Abin rainawa ne wajenki?ba zaki tashiba dan uwarki?"da sauri ta tashi ta mayar da hijab nata"Idanunta cike da k'wallah ta fito jikinta Asanyaye "tama lura mamah tafi son shi da ita....tana fitowa ta hangosa tsaye Adaidai k'ofar shiga shashen su mamy"red d'in jallabiyace jikinsa me gajeran hannu "yana sanye da silifas na maza irin na k'asar London"sai wani irin k'amshi me ratsa zuciya yakeyi"fuskarsa ba yabo ba fallasa"sbd yaji haushin tsayuwar mintina 7 da yayi Awajen yana jiranta"befi saura 15 minit Akira sallar magrib ba"saidai yadda ya lura da fuskarta ya fahimci batada walwala kamarma kuka zatayi"Aransa yace"sai yaushe ne yarinyar nan zata girma wai?....ganiiii! ta fad'a cikin shan mur batare data kallesaba "sbd nace kizo kiketa fushi?"kaga mlm bana son dogon zance, kiran meye kake mun?? wuce muje kiyi Alwallah "bana son musu kin kuma sani? sannan masjeed zan tafi yanzun"da matuk'ar mamaki tace"magrib d'in Aida sauran lokaci"kuma miye matsalarka dani da kuma sallatah??"ince kabarinka daban nawa daban ko?"bazaki wuce muje ba? yafad'a fuska Ad'aure"lallaima yaron nan "waye yaron?"yafad'a yana matsowa gabanta "tayi saurin ja da baya ta wuce ciki ya biyota yana fad'in kinsan Allah kizo kiyi Alwallah kije ki fara Azkhar kafin Akira sallar"wai yaushe ka rainani har haka?"na fahimci idan baka b'ata mun raiba baka jin dad'i shiyasa kake tur sasani sbd raina yab'aci ko? saidai nima nasan maganinka"gadai yadda kika fassarani ko?"ban sani ba"ta fad'a tana cire hijab d'in"kawo na rik'e miki "bazan bayar ba"shikenan Ai,dama wai naga tsakanin k'awa da Abokinta ba'a.....Allah ya kiyaye nayi Abota da k'ato "ta katsesa tana matsawa gefen tape d'in ta fara Alwallah"bece komai ba yana dannah waya sbd kiran Ikkhee daya shigo masa cikin waya saiya kashe yayi blocking nata gaba d'aya"Adaidai nan mamy tayi sallama ta shigo tsakar gidan"Alhamdulillah! Mamy nah ta dawo" shikenan kin b'ata Alwallah d'inki dayin mgn"ladar dakike samu ta zube"ya fad'a yana kallon Mamy ya mata sannu da zuwa "Ahyaan bata kula shiba tana dauraye k'afafuwanta tace"wlh mamy da kika tafi yayita bani wahala da cin zalin d'ina "fuska Ad'aure mamy ta kallesa yayi k'asa da kai yana fad'in wlh sharrinta ne"niban mata komai ba"ya fad'a yana fita Abinsa"Ahyaan ta turo baki tace"wlh mamy Allura fa yazo da ita wai zaimun idan na masa musu sbd zai sani Aiki"murmushi kawai mamy tayi Abin yaran ita yanzun yadena bata mamaki saidai Ido kawai....tana wannan tunanin hamza yazo da gudu ya rungumeta"kaini karka kayar dani Autah"ta fad'a gaba d'aya suna nufar cikin parlourn "mamy ta zauna ta cire hijab sai lokacin ta tuna da yau Alhamis Nura na Azumi "sbd basket d'in
Chapter 14 · 0% Book details