← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 69

Sashe 32

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wuce ciki waya kare gefen kunnanta tana waya harda d'an murmushinta....ya sauke Ajiyar zuciya Adaidai lokacin suma couples suka fito suka wuce ciki da tauwagar mutane"shidai Dr darma bema shiga ciki ba"saiya gyara zamansa saman motar yana danna waya "saida aka kira sallar magrib ya diro yayi lock d'in motar ya fito bakin titi ya nufi wajen wani masallaci "kasancewar Akwai tape yayi Alwallah yanufi ciki.... Acan ciki kuma Anata cashewa saidai babu babban Abokin Ango"sai kiransa marok'a keyi Amma tsit babu shi"ga couples nata rawa Ana musu liki....Ahyaan kuwa sarai ta fahimci ko shigowa wajen beyi ba"saidai batayi zaton komai ba saima ta d'auka yanada uzuri ne"tasowa tayi da nufin ta musu liki saita tafi gida sbd mamy ta gargad'eta karta wuce 7 pm bata dawo gida ba"Anutse take tafiyar harta iso tsakkiyar filin rawar ta zaro y'an 200 tafara yi musu lik'i"Atake Jameel shima yafara yimata lik'i da y'an 500....kamar daga sama taji An finciko hannunta"ta d'an zaro Ido zatayi ihu taji daddad'an k'amshin turarensa"Atake ta had'e rai "tana d'ago kanta suka had'a Ido dashi"fuskarsa babu rahama yama cire eye glass d'in"d'aure fuska itama tayi"sai kuma ta fara k'ok'arin turjewa"ga talaminta da tsini"saidai babu ma wanda ya lura dasu sbd yawan mutane da hayaniya da Ake tayi da kid'a..da k'arfi yajata ,ganin idan bata bishi ba zai Iyar kayar da ita da wannan Jan nata dayakeyi saita k'yalesa har suka fito bakin get "ya bud'e gefen me zaman banza ya:turata ciki yana huci murya Akausashe yace"in bacin mamy ta kirani tace kome nakeyi na Aje na maidoki gida,da babu Abinda yadameni dake balle har nataho dake"tunda ke kina ganin kin kai matsayin nuna mun jinkai da kuma kin Isa to badamuwa"ya k'are maganar yana rufe k'ofar da k'arfi,kafin ya zagaya ya shigo yaja motar Atsiyace"Ahyaan bata ce masa komai ba"saidai ranta yakai k'arshe wajen b'aci",tana ganin kodai sbd yaga tana zaune gidansu ne yake mata haka?"sai kuwa ta kauda tunanin Aranta"Atake taji zuciyarta ta Amince mata data zab'i *Abdallah Aliyu mashi Amatsayin miji!* sbd zaman datayi dashi wajen Aiki ta fahimci mutum ne me sanyin hali dabai d'auki duniya da zafi ba"tana ganin in har iyayenta sunyi bincike Akansa da halayensa zata Amince ya zama Abokin rayuwarta"idan tayi Aurenta ta tafi sai yayi fitinar da wacce zaiyi.....shi kuwa yaji zafin shirun nata matuk'a"suna isowa gidan daga bakin get ya, tsaya , ta bud'e k'ofar ta fito daga cikin motar ta wuce cikin gida....Adaren ranar ita kanta mamy ta fahimci Ahyaan nada damuwa sbd ko Abincin dare bata ciba"tayi mata tambayar duniya sai tace ba komai "washe gari da Asuba har kuka ta sameta d'aki bayan ta gama salla tana yi"tana ganinta ta goge hawayenta "gefen bed d'in ta zauna cikin fad'uwar gaba tace"Ahyaan dan girman Allah ki sanarmun meke faruwa?"kodai Nura ya miki wani abu ne jiya?"gaba tun jiya nak'i samun nutsuwar zuciya Ahyaan sbd damuwar dana lura kinada ita"gashi kuma yanzun kina kuka"tun d'azun nake jiran shigowarsa naji ta bakinsa meke faruwa ne?"mamy babu komai fa bama tsakanina dashi bane"tsakanina da Ammah ne da take fushi dani bata d'aukar waya ta"sai Aibata Abba takeyi bana jin dad'in hakan sam"rarrashinta mamy tayi da nuna mata komai ya kusan zuwa k'arshe ta daure cikin manemanta ta fidda wanda takeso Ayi mgn"saidai har lokacin mamy tak'i yadda da wannan shine dalilin damuwarta"saidai bata koma tambayarta komai ba....wajen k'arfe 10:23 am Dr darma ya shigo cikin parlourn sbd yayi busy tun Asuba ya fita zuwa masaukin da yayima friends nasu da suka zo d'aurin Aure."sai wajen tara da rabi yadawo gidan yayi shirin zuwa d'aurin Auren"sbd na k'arfe 11:00 am ne"farar shadda ce sabuwa dal Ajikinsa y'ar ciki da malun malun "Tasha Aiki da golden d'in zare"yasha kyau tamkar shine Angon "da k'yar mamy ta Amsa gaisuwar tasa tare da cewa muje Ina son mgn dakai"ta fad'a tana fitowa daga cikin parlourn fuska Ad'aure ta zauna kan kujerah dake tsakar gidan.shima kan kujerah d'in ya zauna yana tunanin me Ahyaan tace mata yayi mata?saiya d'ukar da kansa k'asa"me kayiwa Ahyaan jiya?"me kuwa zan mata mamy?"ko kuwa itace tace na mata wani abun?"ko d'aya,hasali na tambayeta meke faruwa? tace" ba komai"saidai raina ya bani wani abun kamata"sanin kankane bata tab'a cemun kamata wani Abu bayan idonkaba"koda zata fad'a gabanka zata fad'a cikin raha"na lura gaba d'aya dakai da ita bakuyin cikakken sati guda baku yi fad'a ba"to daga yau na haramta gaba tsakaninku, dole kamata mgn itama haka "Amma mamy itace ke nuna banida daraj.....kaga !bana son jin komai tana kitchen jeka kirata,kace tazo mun da wayarta"bece komai ba ya mik'e tsaye ya wuce ciki"Ahyaan na tsaye tana juya Miya sai k'amshi ke tashi Acikin kitchen d'in"sai d'an murmushi takeyi tana tuna wayar su ta d'azun da safe itada AA Mashi...daga bakin k'ofar ya tsaya yayi sallama! gabanta ya fad'i batare data juyo ba ta Amsa masa "kizo inji mamy tana tsakar gidan"kuma tace kizo tare da wayarki"ya fad'a Atak'aice yana fita"tabi bayansa da kallo"saima sannan ta tuna yaufa Ake d'aurin Auren mu'az"rage k'arfin gas d'in tayi kafin ta fito ta d'auki k'aramar wayarta baby Nokia ta nufo tsakar gidan"gabanta ya koma fad'uwa "daga gefensa ta rab'a ta duk'a Ahankali tace mamy gani! kanta mamy ta d'ago in a serious tone take furta, na rasa meyasa kuke haka?"shin yaushe zaku girma ne?"kaine namiji daya kamata kafita hak'uri da kauda kai nurah"Amma bakayi kune baku cikakken sati guda bakuyi fad'a ba"to daga yau in har na Isa daku na yanke gaba tsakaninku"dole kamata mgn itama haka "muda muke da burin har tsufanku ku tashi da wannan zumunci Amma shine kuke haka kamar wasu yara "haba Ahyaan! to daga yau na hana y'ar haka tsakanin ku kuna jina?"gaba d'aya suka ce uhmm"jikin Ahyaan Asanyaye tace"kiyi hak'uri dan Allah mamy in sha Allah zamu kiyaye"broth dan Allah kayi hak'uri kaji?"babu komai kema kiyi hak'uri"to ko kufa?"yanzun ma kunada number d'in juna?"sukayi shiru"meyafi haka kayan kunya dan Allah?"shidai jin mamy kawai yakeyi sbd yanada contact nata duka layikan ta guda biyu"yayi serving ya Ajiye cikin wayarsa bedai tab'a kirantaba....bashi wayar yasaka number nasa"ba musu ta d'ago kanta ta mik'a masa wayar"sai suka had'a Ido "ta janye idanuwanta shi kuma ya Amsa"bayan ya saka ya kira"dan wai karta gane ko yanada number d'in nata"gashi na kira ta shigo cikin wayata "batace komai ba ta Amsa ta mik'e tsaye"shima mik'ewa tsayen yayi yace"mamy na tafi wajen d'aurin Auren, nasan su daddy zasuje"Eh yace daga office zai wuce ta can"Allah yasa Alkhairi"Ahyaan dai batace komai ba ta wuce ciki shi kuma yafita. *Monday* wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000 Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251 dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba #Mommyn fareesa #Dr Nura Darma #Ahyaan #mr Mahuta #AA mashi #mu'az #Khairiyyah #Ammah #Ummah #ikkhee 7/21/24, 11:01 - Buhainat: *AGE MATES* *37&38* *Littafin kud'i ne!* *Monday* misalin k'arfe 10:38 am"Ahyaan ce zaune a office nata tana danne danne a laptop "saidai gaba d'aya hankalinta ba'a nan yake ba tana tunanin meyasa Dr darma yak'i sake mata kamar da?"ita ba damuwa tayi da hakan ba .kawai tana so tasan meyasa yayi hakan?"tun bayan mamy ta shiryasu,yanzun iya karta dashi da safe su gaisa shikenan "idan ya shigo tana a parlourn zaice mata sannu da hutawa"ya dena fira da ita kamar Abaya idan suna shiri,ya dena tsokanarta ,ya dena sakata Aiki "kawai dai hidima da ita ne be dena ba"idan yasan tana buk'atar Abu zai bada Abata ko kuma ya Aiko mata dashi"yanzun haka tanaso suyi shawarah game da soyayyar ta da AA Mashi"Amma bataga fuska ba Awajensa "danko fara'a yadena yimata shiyasa yanzun har kwarjini yake mata a fuska....dukan table d'in da Akayi ya saka ta sauke numfashi tana d'ago kanta suka had'a Ido dashi.yana sanye da suit sky blue da farin gilashi"ya wanku sosai"wani tattausan murmushi ya jefeta dashi yana furta tunanin me kikeyi haka *Aminatu* ? dam ! K'irjinta ya buga "wannan ne karon farko da taji Ainahin sunanta Abakinsa"dukda batayi mamakin jinba sbd Anan kowa dashi yake kiranta"saidai yadda ya furta d'in sai taji wani iri daban"gaba d'aya sai taji duk duniya kamar Dr darma yafi kowa iya furta harafin sunan nata har yayi dad'i....wai baza'a mun mgn bane na juya?"ya fad'a still yana daga tsayen"I'm sorry Ina d'an wani nazari ne, kasan yanzun nan na shigo sbd nad'an huta kafin 11 tayi mu cigaba daga inda muka tsaya ko?"hakane Amma niba wannan ne ya kawoni ba"nazo naji Amsata ne.ta sunkuyyar da kai "kinji?"ta sauke Ajiyar zuciya tana d'ago kanta ta juya fararen dara daran lulu eyes d'inta murya can ciki tace"na Amince dakai.... Alhamdulillah! ya fad'a yana yin d'an tsalle tamkar wani yaro"ta saki murmushi,yaja kujerah ya zauna yana tsura mata Ido"thank you so much my sweet heart"in sha Allah indai nine miji Agareki baza kiyi dana sani ba"so pls idan ba damuwa inaso ki sanar Agida zan cigaba da zuwa"sannan zanyi mgn dasu daddy sbd su bani damar turo magaba tana Ayi mgn sbd da gaske nakeyi Ina sonki da Aure.Atak'aice dai kinsan sunana"ni haifaffen garin nan ne"muna zaune nida iyayena Anguwar modoji "mahaifinah d'an kasuwa ne , Asalin sa d'an jihar MASHI LG ne"duk dangin mu nacan"kasuwanci yakawo mahaifinah Anan garin har yayi Aure aka samemu...mu 13 ne Agidan mu"nine d'a na farko "mu 7 ne wajen Ammi nah"sai Anty Amarya nada y'ay'a 6"Anan garin nayi karatu nah gaba d'aya har na kammala na fara Aiki"banida wani Amini sama da haisam"shi yayi Aure harda y'arsa.....wannan shine tak'aitaccen tahirina Ahyaan "idan kina son jin fin haka ko kuma halayena na baki dama kije ki bincika"ya fad'a yana d'an murmushi "ba tare data kallesaba tace" Masha Allah! ya jinjina kansa yana mik'ewa tsaye yace"bara naje kar Ace muna office muna soyayya ko?"kanta ta gyad'a masa shi kuma yafita.... zaune take A parlourn gidan su suna kallon TV itada yayanta da k'anwar su"dududu befi kwana 2 da dawowa k'asar ba....can Aka hasko kyakykyawar fuskar Ahyaan tana labarai"Atake Ikkhee taja tsaki tana kallon kausar tace"ke dallah
Chapter 32 · 0% Book details