← Book details Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 69

Sashe 15

Age Mate's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

data gani Ajiye saman center table"saidai ranta bata yakeyi Anya Azumin sa na lafiya ne??...wai? Ahyaan kice Aiki Nura yasara miki?"bama me yawa bane Mamy"ki huta na zubo miki farfesun da nayi"bara na wuce nayi Azkhar"Nima bara na shigo nayi Alwallah d'in "daga haka Ahyaan ta wuce d'aki.....bayan sallar magrib..... wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000 Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251 dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba #Mommyn fareesa #Dr Nura Darma #Ahyaan #mr Mahuta #AA mashi #mu'az #Khairiyyah #Ammah #Ummah #ikkhee 7/21/24, 11:01 - Buhainat: *AGE MATE'S* *15&16* *Littafin kud'i ne!* ........bayan sallar magrib duk suna zaune Acikin parlour "mamy na shan farfesun da Ahyaan ta zuba mata itada Autanta"yayinda Ahyaan ke zaune kan kujerah tana danna waya"sai khaleel dake zaune shima yana cin Abinci "Ahankali Dr darma ya shigo cikin parlourn hannunsa rik'e da goran ruwa me sanyi"yayinda fuskarsa ke k'awace da tattausan murmushi....mamy yanzun hameed ya kirani gobe Ana son ganinmu FMC zamuyi inter view Acan "k'ilan monday mu fara fita office"ya fad'a cikin husky voice d'insa, ba tare daya jira An Amsa sallamar tasaba.....kai !Masha Allah Alhamdulillah! Allah ya Ida nufi "itama Ahyaan Allah yabata nata"cewar mamy fuska da fara'a "ya Amsa da Ameen yana zama can cikin parlourn kan carpet ya lankwashe k'afafuwansa yana satar kallon Ahyaan"yana ganin zata d'ago kanta ya maida hankalinsa Awajen waya"Allah Ida nufi broth"ya bada sa'a"Ameen ya Amsa Atak'aice cike da shan k'amshi "ita kanta mamy bataji dad'in yadda ya Amsa d'in ba "khaleel ma ya masa fatan Alkhairi"yayinda zuciyar Ahyaan ke tafasa sbd yarfin da uban gayyar yamata"Ada tayi niyar kamasa basket d'in gabansa, ta kuma je ta kamasa ruwa Amma ta fasa"yadda take jin zuciyarta koda Agaban mamy yace ta mik'o basket d'in wlh tsaye zatace baza tayi ba"danne danne ta din gayi Awaya tana jan khaleel da fira ta basar da darma tamkar bata san da zaman shiba"tana lura ta gefen Ido ya jawo basket d'in ya had'a tea ya fara bud'a bakin mutane nata damunsa da yawan kira"daga k'arshe wak'ar music Ahyaan ta kunnah ta wuce d'aki tana Addu'ar Allah yasa itama Abba ya dawo da labari me kyau game da Aikinta"tana nan kwance kiran Ammah ya shigo cikin wayarta"cikin farin ciki ta d'auka tana fad'in my sweet granny I miss you so much "daga d'ayan b'angaren Ammah ta saki murmushi tare da cewa takwara nima Ina kewarki"naso kidawo wajena da zama Amma talakan ubanki ya hana....d'aure fuska tayi tak'i mgn "ta rasa meyasa Ammah keyin haka?"tanafa son mahaifinta da kishinsa"Amma koda yaushe Ammah saita Aibata mata shi....kina jina?"uhmm! Mustapha ya sanar mun Akwai wani yaro Ahmed Abokinsa dake sonki....dan Allah Ammah Adena zancen bana so"haba mana! meye zanyi da babban mutum da zaiyi all most 45 yrs?"it can wlh.....iyye?cewar Ammah da mamaki"tana tunanin Anya jikar tata Qlau take?...haba Ahyaan! dukda bana so na miki tilas Amma ki duba yadda zaki huta da kuma darajarki da martabarki dazai k'aru"yaron nan tuzuru ne be tab'a Aure ba"yanada kud'i fiye da zatonki....haba Ammah! ke kud'i sune kawai damuwarki ba halaye masu kyau ba"dana Auri wanda zai haddasa mun ciwon zuciya yana kashemun million guda duk Rana"gara na Auri talaka me rufin Asiri da halin k'warai"idan Ina Aikina Ina samun kud'i bamai kallonah Awulak'ance....fisge wayar taji Anyi "tayi wata irin zabura tana tashi zaune ta gansa tsaye yana kashe wayar tamkar zakin fama ya had'e rai yace"ki tashi kiyi sallar isha'i"doguwar tsuka taja tak'i tankashi....ba k'aramin hassala zuciyarsa tayiba sbd ya tsani Amasa tsaki Arayuwa"bece komai ba ya Ajiye mata wayarta ya fita"sbd Aganinsa fitar shine daidai"ya lura yarinyar da baya mata jan Ido ba k'aramin raini zata kamsaba"shi kuma yana kulawa da ita da tarbiyanta ne sbd gobenta tayi kyau"Amma zaya barta tayi yadda takeso raini ne bazai d'auka ba.....da wannan tunanin ya wuce masjeed yayi sallah"be jimaba ya tafi shago"sbd masu yawan zuwa siyan magani da zuwa Allura "saidai me? gaba d'aya Ahyaan ce Aransa,tsakin data masa d'azun yak'i barin zuciyarsa"yayinda yake Aunah kalaman daya tsinta tanayi da tana watabitada kakarta"ya fahimci in bacin Ahyaan ta samu ilimin Addini da tuni Ammah ta b'ata mata tarbiya"shi kansa mamakin yadda ya zurfafa kan lamarin yarinyar yakeyi"wanda ada da ita da babunta duk d'aya ne Awajensa"tunda ya tafi London yayi 8yrs ko sau d'aya be tab'a cewa tana inaba? ko kuma Abashi ita su gaisa"wani lokacin yana jin sautin muryarta idan suna waya da mamy ko mamah"Amma yanzun tunda ya dawo ya ganta yakasa gane me zuciyarsa ke nufi Akan yarinyar? "hankalinsa be tashiba saida mlm tasi'u yafara nuna zalamarsa gareta"ga kuma mr mahuta"daya tabbatar ba mutumin k'warai bane"Abinciken da yayi kansa d'azun da safe"ya gano yanada mata guda da yaro d'aya"sannan tantirin d'an bariki ne kuma mashayi"shi kuwa mlm tasi'u yanada mata biyu da yara kusan 8 Aganinsa me Ahyaan zatayi dashi?"bayan haka ga matsalar sihirin dake jikinta wanda malaminsa ya tabbar masa da cewa" muddin be kareba bazata yadda taso wani namiji ba har tayi Aure "sannan babbar damuwarsa yana zargin zuciyarsa dajin kishin yarinyar...... doctor barka da zuwa! yaji muryar wani gefensa"sai lokacin ya dawo tunaninsa ya sauka dg kan mashin nasa ya bashi hannu sukayi musabuha "Ashe har ya iso shagon be sani ba"bud'ewa yayi ya shiga yaci gaba da sallamar mutane...... misalin k'arfe 9: 18pm" numfashi me k'arfi ya saki yana kad'a kai tamkar wani k'adangare" saida ya busi sigari kafin yace"shawarah guda honorable na yanke Akan yarinyar shine,zanje na tunkareta itada iyayenta na musu b'arin kud'i"sai yanzun naji na zancen naka dama ban saka gadararren yaron nan ba cikin zancen balle harya d'agamun kai ya gayan mgn son ransa "Amma na barsa sai hak'ata ta cimmah ruwa Tukum zan waiwayesa ta hanyar dawowa da tarkona Akansa"honorable rabiu na sakin shegen murmushi yace"tuni naso kayi hakan Abokinah"Amma jarabar son ka kasance da yarinyar ya hanaka kayi wannan hangen"sbd haka da zafi zafi Ake dukan k'arfe"kaje kawai goben"to shikenan idan kuwa nayi iya yina banci sa'a ba wlh kota halin k'ak'a sai burinah yacika Akanta"dariya honorable rabiu yayi yace"zanso naga yarinyar yatake, sai kace hurul ini ce ita? Irin wannan susucewa dakayi lokaci guda a kanta"duk yadda kake Jan mata ak'asa Amma yanzun itace ke Janka" itama zan jata idan hak'ata ta cimmah ruwa" na maka uzurin baka ganta bane"Amma idan ka ganta zaka fahimci mena gano"daga haka suka kece da dariya..... washe gari Ahyaan ce zaune kan carpet gaban iyayenta"fuskarta d'auke da damuwa sbd rashin Aikin da ba'a samar mata ba"saidai Abba ya kwantar mata da hankali da nuna mata cewa ta dage da Addu'a suma zasu tayata"za'a dace da izinin Allah"dato ta Amsa kanta sunkuye"ummah lubah dake lab'e bayan labule tamkar ta taka rawa sbd murnah"dan dama harda hanata samun Aiki ta saka Ayi"cikin farin ciki ta wucewarta"Ahyaan kuwa tare da mamah suka fito daga cikin parlourn Abba suka nufi d'aki "kai tsaye rubutu da kuma had'in maganin da darma yamata Addu'o yakawo da Asuba shine mamah ta mik'a mata tana fad'in baki dai ci komai ba ko? Eh banci ba"to shikenan yi bissimillah ki fara shan rubutun"dato ta Amsa tana jin fad'uwar gaba ta fara shan rubutun"kafin Tasha ruwan maganin ta shafe jikinta dashi"sai kawai mamah taga ta dafe kanta da Alama sara mata yakeyi"ba tayi mgn ba dai tana kallonta"sai taga ta kwanta saman kujera, bata jumaba bacci ya d'auketa.....misalin k'arfe 12:11 pm"Ahyaan na zaune tsakar gidan da k'ananun kaya Ajikinta Amma basu kamata sosai ba"tayi kyau harta gaji"saidai fuskarta ba walwala"me lalle na zaune gefenta tana zana mata"shima mamy ce tace Amata "ko Aikin girkin Rana mamyn ce dame Aikinta sukayi tace Ahyaan d'in ta huta"ita kanta tausayi take bata sbd rashin samun Aikin da ba'a yiba"dukda ba wani fira sukeyiba da me lallen "tad'an ji damuwar tata ta ragu "suna nan Ana mata"Dr darma ya shigo da sallama "yaci wankan suit bak'ak'e"yayi wani irin fitinannan kyau,tamkar bak'in bature haka yayi"yasak'alo suit jacket d'in gefen k'afadarsa da hannu guda"yayinda gudan hannun nasa ke xube cikin Aljihun wondonsa,da Alama daga wajen interview d'in yake"fuska ba yabo ba fallasa ya shigo da sallama "me lallen ce kawai ta Amsa tanata kallonsa"yayinda Ahyaan ko kallo be ishetaba"shima da yake ba baya wane wajan jin kai sai yanuna kamar be gansuba"sau biyu me lallen na gaishesa yayi kamar be jiba ya wuce parlour"sbd yana jin zafin d'azun da safe Ahyaan tak'i gaishesa har su khaleel da Isma'il ta gaidasu gabansa Amma shi marainin wayonta saita sharesa kallo be ishetaba"yaci burin fita harkanta sbd ganin raini ya gama shiga tsakaninsu"ko fatan Alkhairi bata masaba d'azun tana jin mamy dazai fita tana masa Addu'a.....ka dawo ne?"cewar mamy tana kallonsa"saida ya zauna yace Eh shirin masallaci zanyi"yanzun muna jiran kiran nasu gobe satday "in har An dace Monday zamu fara fita Aiki"to shikenan Allah ya kaimu lafiya "ya Amsa da Ameen"Amma kamar bakayi kari ba ka fita ko? nasha Lipton Ai mamy"wanda sarai sbd yaga Ahyaan ce keta sallamar kowa d'azun shiyasa yak'i nuna son yayi break fast d'in Anan,sai yaje yacema mama ta had'a masa Lipton"ga Abinci can kaje kaci mana"waye yayi girkin?"tamkar tace wani Abu sai kuma tace"nice nayi"yau Ahyaan d'in batada walwala ga ciwon kai tana yi,ga damuwar rashin Aikin nata da ba'a samu ba"tab'e baki yayi tamkar ba zaice komai ba sai kuma yace"in sha Allah za'a samu"to Allah yasa "daga haka ya fito tsakar gidan"ya samu sadeeq d'an yayar daddy tsaye suna gaisawa da Ahyaan "gaba d'aya yaron yamaida duk wani nutsuwarsa da hankalinsa kanta"tsaki marar sauti yaja yarab'a su ya wuce"yana jin yadda sadeeq ke mata mgn cikin kwantar da murya ita kuma tanata ya mutsa fuska da shan k'amshi"ya fahimci sadeeq d'in bema lura dashi ba"koda kuma ya lura dashi d'in baya jin zai iya tankashi"gaba d'aya zuciyarsa Ajagule take ya nufi d'akinsa yayi wanka"cikin sabon wani had'ad'd'en yadi me laushi fari ya shirya"komai bak'i ya saka yama jikinsa wanka da turare"duk yadda yaso yabasar karya koma cikin gidan "Amma zuciyarsa tak'i barinsa"so yakeyi yaga har yanzun shin
Chapter 15 · 0% Book details