← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karasowa tayi cikin dakin ta nemi kujerar data Saba Zama ta xauna tana Kare Masa kallo fuskarta dauke da guntun murmushi,fahimta da tayi Wai yayi fushi ne Nan,"ya zainul"ta Kira sunansa cikin wata irin murya Mai sanyi,shiru be amsaba ta Tai Yar dariya "bude idonka Mana ya zainul kaji?"Tai maganar cike da shagwaba tana tura Baki gaba,...sai kawai ya bude idanuwansa ya sauke akanta kamar bazaice komiba sai ya bude Baki a hankali yace "ummaty Ina kika Shiga yau?bakizo ba tunda muke dake Baki taba fashin zuwa ba sai yau,dik na damu ko kin fara gajiya Dani ne"yai maganar a sanyaye,

"Haba ya zainul banyi tsammanin wanan kalmar ta gajiya daga bakinka ba,Dan kawai yau daya baka ganniba sai kace Wai nagaji dakai?ban tabajin mummunar kalma kamar wanan ba gaskiya Raina ya baci Kuma nayi fushi"ta juya baya tana Kara turo bakinta gaba,
"Kiyi hakuri nayi laifi kinji,nayi kuskure bazan sake fadin wanan kalmar ba tunda bakyaso...kawaidai na damu ne dayawa shiyasa Amma na daina"ya kafeta da Ido,

"To shikenan ya wuce nadaina fushin"ta karasa maganar tana dariya,shigowar gimbiya rumana ne ya katse musu zancensu da murmushi dauke a fuskarta "d'iyata ummaty Ina kika Shiga yau bakizo ba sai yanzun?kinsa yarona rigima Wai be ganki ba harda Yan hawayensa?gaskiya karki Kuma,yanzun tabawa kecemun taga wucewarki Ina Shirin aikawa gidan naku ne inji ko lafiya dama"sunkuyar da kanta ummaty tayi "lafiya Lau ummah kawai yau natashi da ciwon Kai ne shine Nasha magani na kwanta da na tashi naji sauki shine nace Bari inzo"

"Toh Allah ya Kara sauki,Bari inje dama nazo inji motsinsa ne tunda Baki zoba Bari intafi tunda mutuniyar tazo ko zainul"murmushi kawai yayi ya daga Mata Kai,ta fice ta rufo kofar,

Jakar da tazo da ita ta bude ta Ciro sabon MP3 Mai shegen kyau tana murmushi "ya zainul kagani na biya kasuwa na siyo maka wanan Dan ka rinka sauraren karatun alkurani kaga har haddarka ma sai ka rinka tulawa ko?"sosai zainul abideen yaji Dadi daga ganin yadda yake faraa a fuskarsa,itama faraar takeyi ta Shiga har hadata "kagani har kurani nasa aka tura complete a ciki idan na saita maka sai insa maka a kunne idan ma sura ta Kare zai Shiga ta gaba ko?kaga idan kana sauraren karatun kur'ani zaka samu sassauci ko?Kuma kurani Kansa waraka ne Kuma haske ne ga ko wace irin cuta Gama al'ummar musulmi Baki daya"

"Nagode ummaty Allah ya biyaki da gidan aljannah"

"Ameen"tace ta Shiga gwargwada karatun...

********
"Sarkin dawaki nafada maka bana bukatar shakuwa a tsakanin zainul abideen da ummaty Amma abinda nake gani tamkar sun shaku har shakuwar ta wuce inda muke zato"Tai maganar Rai a bace,
"Shakuwar zainul da ummaty dole ne fa,tunda kullum suna tare Kinga Dole su shaku idan basa tare babu yadda zaayi hakarki ta cimma ruwa,idan Kuma Kinga kinfison a rabasu shikenan wanan ba matsala bace a wajena,Dan Nima Dole ce tasa ummaty take kusantar sa Dan baso nakeyi ba"ajiyar zuciya ta sauke "akwai abinda nake Jin tsoro nake gudu ne dangane da zamanta da shakuwarsa da shi"

"Me kike tsoro kike gudu ya wuce kice Mai martaba yace a hadasu aure?to harabada bazan Bari ummaty ta auri zainul abideen ba Koda warkewa yayi kuwa ballantana yadda yake a nakashe ah ah wallahi"gwauron numfashi ta sauke hade da lallausan murmushi,sai yanzun zuciyarta Tai Mata sanyi da Jin abinda sarkin dawaki yace,ballantana Bata fatan zainul abideen ya warke harabada.

*SLIMZY😍*
[1/23, 10:37 AM] 😍SLIMZY😍: *HASKE WRITERS ASSO...💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY✍🏼*
*Wattpad@slimzy33*

*Assalamu Alaikum.... Fan's a duk inda kuke ina muku fatan alheri. Wannan book na zainul Abiddeen na kud'ine, wanda yake sha'awar siya ze iya tura kud'insa ta wannan number akan naira dari biyu kacal.*

*2073065733
Sha'awa Ibrahim
UBA bank*
Tura shaidar biyan kudinka ga wanan number
08161306299

6019111117 keystone
Amina jibril
Shaidar biyanka ga wanan number 08166177830

Kokuma ya tura katin waya na mtn na 200 ta wannan number

08039424298 kokuma 07084161619

Kud'in littafin d'ari biyuce kacal game buqatar ci gaban zainul Abiddeen seya tuntub'emu.

*9*

********
Kwance suke su biyu kan makeken gadon dakin zahira da warisah gefe fiyya ce zaune kan kujerar hannunta rike da wayarta tana latse latse hankalinta na kan wayar,...shiru dakin babu me yiwa Dan uwansa magana kusan dama fiyya da warisah ba shiri sukeyi sosai ba ko wacce ji da kanta takeyi da sarauta musamman warisah da idan bakasaniba sai ka dauka cewa itace Yar sarki,

Dan tsaki warisah taja tai jifa da story book din dake hannunta ganin wayarta na haske,."lafiya dai kikejan tsaki haka?"

"Wanan Dan anacen ne yayanki zai dameni da Kira,yakira yakira ban daukaba Yana Kara kirana nifa ban fiyeson damuwa ba zahira kinsani ki fada mishi"mtsww taja dogon tsaki,"nikam warisah Wai me kike takama dashi ne haka?kikewa ya musaddik wulakanci?ba kyau kika fishi ba fa ballantana kice Zaki wulakantasa ba Kuma asali kika fishiba Dan asalinku daya yadda kike takama da mulki haka Shima hakan ,kawai dai soyayya gamon jini ce yasa ya nacce Miki ai ga Yan Mata Nan a family da yawa da be nemesu ba?ni ya fiyya ma naso ya nema"ta karashe maganar cike da haushin warisah,

"Kanki akeji,da kinsani kice ya nemi fiyyar Mana ya daina nacemun haka,ni dik ya takurani wallahi so yakeyi yazo Amma Wai beson zuwa Nan Dan kada Mai martaba ya fahimci akwai soyayya tsakaninmu ace ai Mana aure da wuri Wai ya kosa in dawo gidanmu,besan Nima a takure nake da Nan din ba kamar nazo prison wallahi,gashi bacci ya gagari mutum saboda numfashin wancen mutumin na daki ya isheni"

A hassale fiyya ta dago kanta wadda tunda suka soma hirarsu Bata bi ta kansu ba sai yanzun da warisah Tai wanan furucin "karki kuskura idan kina rashin kunyarki kice Zaki sako ya zainul ciki Dan shi ba saanki bane Kuma karki fara kice Zaki aibantashi Dan zan wulakantaki"

"Ni kike cewa Zaki wulakanta saboda yayanki nakasasshe?"a hassale safiyya ta Mike ta sharara Mata Mari Karo na farko tana nunata da yatsa "ki Shiga taitayinki warisah dik take takenki Ina kallonki ne Ina kyaleki tunda kikazo gidan Nan Amma kada kice Zaki Shiga gonar Dan uwana nafada Miki tunda bakida mutunci ko wanine kikaji Yana zaginsa ke ba me tare Masa bace?Amma har ki iya bude Baki ki aibantasa to kulll ya tsaya daganan ai Shima ba yin Kansa bane,Kuma insha allahu sai kinyi danasanin abinda kika fada sai kinzo da Kanki kina Neman ya kalli inda kike ma balle ya kulaki da izinin Allah"

"Saidai in a mafarki ne zanzo in nemi kulawar tasa ko kuwa warkewar tasa Kuma wallahi sai kinsan kin mare ni"

"Idan kece ke bada lafiyar saiki hanasa lafiyar Mara mutunci kawai,kizo har gidansu kina ci Masa fuska ko da yake gado kikai indai rashin tarbiyya ce da rashin mutunci"zuwa yanzun warisah ranta ya Gama baci wato ita fiyya ta kalla ta kirata da dangin marasa mutunci?su waye Mara mutuncin kenan?uwarta data kasance jinin Mai martaba kanwarsa uwa daya uba daya ko kuwa mahaifinta da ya kasance attajirin gaske Shima Kuma jinin sarauta?,Bata Gama tunani ba afnan ta shigo dakin tana binsu da kallo daya bayan daya sanan ta dubi safiyya tace "anty fiyya kizo Wai su ya Zahra sunzo Kuma ammiey taji Kuna hayaniya"tana Gama fadin haka ta juya Tai waje abinta cike da natsuwa,

Fiyya ficewa tayi Tana bin warisat da harara ,

Zama tayi gefen gadon cike da masifa take fadin "wallahi saina Rama abinda taimun sai NASA ya haris ya ramamun wanan wulakacin da taimun ai Ina sane da cewar soyayya sukeyi zatasha mamakin yadda zai wulakantata,kafin nata yayan ya warke ya wulakantani kamar yadda tace nawa zai fara yi Mata,sai na tar watsa Mata farin cikinta,tunda haka tace zamuyi mu zuba,Kuma yau din Nan zanbar gidan Nan in koma gidan ubana gidan marasa mutunci Kuma saina fadawa momy"ajiyar zuciya zahira Tai "da zakiji tawa da Baki Fadi maganar Nan ba Dan wata wutar Zaki Kara hasawa kinsan halin momynki dai nidai ba ruwana kada ace mune"

"Farar Kura matsoraciya ai bazaki iyaba,Toni zan iya me suka fimu dashi?mulki ko sarauta?(Fatima Zahra)ko dokiya?dik abinda suke takama dashi munadashi kawai dai Dan iyayenmu Mata ne ba maxa bane shiyasa Kuma Mai martaba shine kadai yaron hajiya Kaka shiyasa"

Shiru zahira Tai batasake cewa komi ba,Amma har ga Allah tasan abinda warisah tayi Bata kyautaba,Kuma wanan wulakacin da rashin mutuncin babu inda zai kaita sai danasani Mara amfani.

*********
"Ah lallai zainul jiki yayi kyau gaskiya kwana biyu kasamu lafiya,Dan ammiey da mukai waya tace tun daga ranan da ciwonka ya tashi yau kwana hudu kenan ciwon be Kara tashi ba Kuma gashi har kana iya dadewa zaune a wheel chair alhamdulillahi"murmushi yayiwa babbar yayar tasu Zahra "gaskiya alhamdulillahi ku Kara sani a addua Allah ya karamin lafiya"..

"Ameen kanina,kagani ga kula cen na shigo da ita favourite Dinka nayo maka da kaina nazo maka dashi"

"Dambun couscous anty?"daga Masa Kai tayi Tana dariya "ehh zainul shine kaji Dadi koh?" Shima daga Mata Kai yayi Yana murmushi batare da yace komiba,

"Ummaty ki zuba Masa Dan Allah ki tabbatar yaci sosai kinji kema ki zuba kici karkice Zaki fulatancin Nan naki Dan kin Zama Yar gida"sunkuyar da Kai ummaty tayi Tana murmushi kasa kasa,

"Fiyya muje sashen ammiey annnur ya gaisheta"tare suka fita da fiyya tana rungume da yaron babbar yayarsu Zahra,

Bayan fitarsu ummaty ta dubi zainul "ya zainul kwana biyun Nan jikin naka yayi kyau gaskiya alhmdllh"murmushi kawai yayi Mata yanajin kaunarta cikin jinin jikinsa,...a wanan zamanin samun kamar ummaty ba dik Mata ba...

********
"Ummah ai kam kwana biyu jikin zainul yasamu sauki yau bakiga yadda yayi kyau dashi ba kamar bashi ba wallahi,bakiji yadda naji dadin ganinsa ba Allah ya tasar Mana kafadarsa "

"Ameen" gimbiya rumana tace,Tana bin diyar Tata da kallo tamkar zata hadiyeta,
Chapter 9 · 0% Book details