Sashe 45
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin mahaifiyarta warwass a kasa yasata karasawa inda take a rude tana rukota koda ta dago gimbiya rumana ta kalli fuskarta abinda ta ganine ya furhitata yasanyata saurin sakin kanta kasa ta kume ta Mike a furgice "ummah meyasameki menene haka yake fito Miki a fuskarki"....jin haka yasa wadanda ke kusa da wajen daga Kai suna dogon wuya suna leke cikin kankanin lokaci wasu kananan kuraje masu ruwa su yayyabe fuskar gimbiya rumana caba caba dik Wanda ya kalla sai tsigar jikinsa ta tashi ga Kore sharrr da fuskar tayi....zainul na shigowa kallo ya koma kansu dagashi har sarkin dawaki har innah da ummaty take fada ta kaure da surutu....kowa na fadan albarkacin bakinsa wata tsawa Mai martaba yayi take kowa yayi shiru ya Shiga taitayinsa nan Mai martaba ya Soma magana "dik abinda kace zaka ginashi Akan turbar karya da son zuciya da mugunta da k'eta to tabbas komi Daren dadewa sai asirinka ya Tonu Koda a karkashin kasa kakeyi sai ya fito sanan dik Wanda zai Gina Ramin mugunta ya ginashi daidai kwaurinsa watakila ya fada da mutum shine kadai abinda Zan iya fada Dan abun ya dauremin Kai ya zarce tunanina ban taba tunani ko zaton haka ba sai gashi ta inda bana tunani tanan ya bullo sanan bincike ya nuna cewar akwai masu taimaka mata wajen aikata hakan kuma Basu kowa bane sai bayinta wadanda ke gefenta ciki kuwa harda hansa'u"...Dan haka hukuncin da Zan yanke harda hansa'u da yushau Mai kula da zainul...Dan haka gimbiya rumana nata hukuncin kenan cin guba da tayi shine daidai da ita a tunaninta bazai cutar da itaba Dan haka ni na saketa saki uku sanan ta Barmun gida na gobe gobe n nan sanan hansa'u da yushau na yanke musu hukuncin zama a gidan yarin wanan masarautar na tsawon shekara goma ciffffff sanan banaso su Kara awa daya cikin gidan nan batare da ankaisu can ba sanan ni na wanke sarkin dawaki da ahalinsa gabaki daya kuma zam biyasu diyyar sharri da akayi musu batare da hakkinsu ba bayan hakan banida abinda zance saidai ince Allah ubangiji yayi Mana sakayya Akan dik Wanda ya cutar damu Allah ya maida Masa da abinda sanan a karshe na bawa sarkin dawaki da iyalensa sashin gimbiya rumana su zauna halak malak"...Mikewa yayi cike da bakin ciki furucun Mai martaba yasa Babu Wanda Bai zubar da hawaye a wajenba musamman ummaty wadda take kuka tana murmushi na farin ciki yayinda ita kanta hajiya Kaka kukan tasa ta tako har inda ummaty ta rungumeta a jikinta "kiyafemun kinji jikata"....sharewa hajiya Kaka hawaye ummaty tayi "haba hajiya ba laifinki bane rashin fahimta ne na yafe Miki"....dik Wanda yake wajen jikinsa yayi sanyi ta wani bangaren tausayin Zahra ne ya cikasu yadda take kuka rungume da mahaifitartata tana trying number halima Amma Taki shiga....gimbiya bilkisu kuwa bayan Mai martaba tabi abinta....har inda take tsaye haris ya karaso fuskarsa a daure tamkar be taba dariya ba ya kalli agogo hannunsa karshe Sha daya da wani Abu na dare cike da izzah ya Bata umarni "ummaty muje inkaiki gida kedasu innah koma menene gobe a karasa banaso ki Kara Shiga motar wani"...yadda yake mgnar take binsa da kallo cike da faduwar gaba...ta dayan bangaren kuma zainul yace ta jirashi yayi sallar ishai ya kaisu gashi shine ya daukosu ya zatayi......
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
*HASKE WRITERS ASSO💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY✍🏼*
[1/23, 11:49 AM] 😍SLIMZY😍: 41
Batada zabi haka ta juya ta dubi innah a sanyaye ta ce "innah keda babah kubi motar ya zainul Bari inje haris ya saukeni Naga neman magana yakeyi"Sarai innah ta fahinci ummaty sai kawai tayi murmushi "toh shikenan Amma kar ya tsaya dake ko Ina ya kawoki gida kinji Koh"ummaty ta gyada Mata Kai....batada zabi haka ta nufi motar haris Wanda tasan tsabar rigima yakeji Dan Haka tana Shiga zainul na fitowa hannunsa rike da makullin mota yaga lokacin da ta shige motar haris sai ya basar kawai ya karaso wajensu innah "innah muje in saukeku dare yayi sosai"
.sarkin dawaki dake gefe besan wainar da ake toyawa ba ya Shiga waige waige bega ummaty ba "innah ummaty tayi?ko nan takesoh kwana?"
"Haris ya dauketa a motarsa sunyi gaba sun rigamu tafiya tun dazun".. wani mugun kishi ne ya tasowa zainul yaji zuciyarsa na bugawa fat fat...dannewa yayi dik yadda yakeji Amma haka yayiwa motar keyi ya bar kofar gidan...
Yadda haris ke driving tamkar bazasu tafi ba har motar su zainul tazo ta wucesu fiiiiii....murmushi haris yayi Dan Haka yakeso itakuwa ummaty bakin ciki ne ya Kara lullubeta "Wai ya Naga kana driving a haka?bayan kasan dare yayi?kana gani har motarsu innah tazo ta wuce Tamu?kana kuma Jin lokacin da innah tace karka tsaya Dani ko Ina zata iya min fada"cike da takaici Tai maganar kmr ta shakeshi...dariya ya Sanya Mata wadda ta Kara sata kuluwa batare da ta ce komi ba sai harara da ta watsa Masa .."Ashe kin iya masifa,to masifarki ce zatasa inyi sauri?hmmm so kikeyi muyi sauri muje ki hadu da masoyinki ko?to da kike cewa innah zatayi Miki fada ko kin manta cewar ni mijinki ne tunda kudin aurena na gidanku?kuma innah tasan cewar nidai ba Dan iska bane balle Dan Haka wallahi idan kikace Zaki Kara cewar wani Abu dangane da yadda nake tafiya parking zanyi mu kwana a nan sai asuba"...wani irin mugun haushinsa da takaicinsa ne ya lullubeta taji kuka na kokarin kwace mata ita tayi Masa halacci tayi gudun bacin ransa shine zaiyi Mata Haka Dan ya bakanta Mata Rai?dik yadda taso da danne zuciyarta Saida hawaye ya sauko a idanuwanta lokacin da ta dubi agogon wayar innah dake hannunta karfe shabiyu da minti ashirin na dare.....tana cikin tunani taga giftawar motar zainul a guje ta dawo ta bi motar da kallo Bata Ankara ba haris yaja motar da wani irin karfin gaske Wanda Saida tayi gaba kamar zata bugu ta dawo...ya Shiga sharara gudu a titin...faduwar gaba ce ta ziyarceta yadda yakeyi da motar kamar zai tashi sama ta juyo ta kallesa idonta tafff da hawaye yadda taga ya tsare gida yasa ta hadiye wani miyon bakin ciki ta hadiye kukan...Sarai ta fahinci inda ya dosa wato dama yayi hakan ne Dan kada ta hadu da zainul?sai da yaga wucewarsa sanan ya Soma gudun fanfalaki da ita?....Bata bawa kanta amsa ba kawai ji tayi mota ta tsaya tai furgigit ta juya taga sun kawo sai kukan karnuka kakeji a ko Ina Dan Haka batai wata wata ba ta bude kofar motar ta saka kafarta ya ruko hannunta ta juyo da sauri "saurin me kikeyi ba kiyi sallama da mijinki ba?ko fushi kikeyi Dani?"ya tsareta da ido da yasa ta sunkuyar da Kai kasa ta girgiza Kai "ah ah dare yayi ya haris Bari inje"
"Naji Zaki tafin Amma sai kinyimun murmushi"harara ta watsa Masa ya fashe Mata da dariya Dan Dole Saida tayi dariya sanan yace "kuma da wuri zanzo gidan nan gobe Dan ban goyi bayar ku koma gidan sarki ba tunda aka iya muku korar Kare dik halarcin da kukayi nan gaba ba fata akeyi ba wani Abu ya faru a Kara korarku Dan Haka nan gidan na canja takaddun sunan gidan tuni na mallakawa baba"...Baki bude take kallonsa kafin ta kwace hannunta tayi cikin gida da gudu ya bita da kallo Yana shafa kansa...da kyar ya tada mota yabar kofar gidan....
********
Zahra ce zaune rungume da mahaifiyarta wadda gabaki daya cikin kankanin lokaci Allah ya saukar da ikonsa akanta gabaki daya kamanninta sun canja ta koma masakiya complete tamkar ba gimbiya rumana ba wadda cikin awanni goma da suka wuce take cikin koshin lafiya tamkar ba gimbiya rumana wadda ta kasance kyakkyawar mace meji da mulki da iko ba... Tabbas annabi yayi gaskiya da yace Dan Adam Tara yake be cika gomaba kuma Babu wani Dan Adam da ake gamawa halitta sai ranan da ya koma ga ubangijinsa tabbas ga ishara ta sauka Akan gimbiya rumana... Jan numfashi Zahra tayi ta sauke tana cigaba da rera kuka tamkar wadda akaiwa mutuwa kasantuwar anan baban nuaiym ya barta...dakyar gimbiya rumana ta motsa bakinta saboda yadda takeso tayi magana ga mugun kishin ruwa da takeji ganin yadda take mutsu mutsu yasa Zahra riketa da kyau ta tallabota hade da kafeta da idanuwa da kyar ta iya furta "zansha ruwa"...ta rufe bakinta.. da sauri Zahra ta kwantar da kanta ta Mike taje ta zaro gorar swan water a cikin fridge ya dawo da sauri ta bude ta tallabo kanta tace "gashi ummah bude bakin Kisha"...
Tari ne ya sarke gimbiya rumana tun kafin ta Sha ruwan ta Shiga gwaro amai me kumfa kumfa Kore sharerrr da shi a wahale takeyin Aman tamkar ranta xai fita,tausayin mahaifiyarta ne ya lullubeta ta rungumeta sosai daidai nan yaronta dake bacci ya farka haka ta kwantar da ita ta ruga ta daukeshi ta rungume ta Shiga jijjigashi a tsaye tanayi tana waigen mahaifiyarta wadda ke sambatu kamar haka "niba ni bilkisu tayiwa asiri ta Shiga tsakanina da mijina Koh?...wato zainul abideen ya warke zai gaji sarauta to Basu isaba kuma wallahi Bari inji sauki saina Rama abinda sukayi min harda magani aka bani naci Koh?to wallahi dik sai sunci ubansu" ...haka taita maganganu marasa Kan gado har bacci ya dauketa"
********
Kiran sallar farko zainul abideen ya tashi yayi nafilfili kamar yadda ya Saba har akayi sallar asuba sanan ya gabatar da sallah da azhkhar dinsa ya fito sanye da jallabiya ya nufi sashin mahaifinsa ya Shiga zaune ta taddasu Kan dadduma shida mahaifiyarsa sun idar da sallar asuba kamar yadda ya Saba...ya tsugunna har kasa ya gaidasu cike da kulawa sanan ya shedawa mahaifiyarsa zai fita "Ina zakaje zainul da asuban nan?"
"Zansa aje a kwashewa su ummaty kayansu yanzun zaifi"
"Inaga zainul ai abari gari ya waye Koh?"
Murmushi Mai martaba yayi ya sako musu Baki "ah ah kibarshi yaje kinsan ance da zafi zafi ake bugun karfe"..Sarai ta fahimci abinda yake nufi itama dariyar tayi ta cigaba da Jan carbinta ta dagawa zainul Kai alamar ya tafi...ya Mike ya fice...