← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 49

Sashe 6

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta soma magana yake bin ta da kallo da tsananin mamaki da rashin imani irin nata,tunawa da yadda zainul abideen yake Amma dikda hakan beyi mataba tafiso ta gansa a nakastat da tafi haka,dakyatya hadiye wani mugun miyau ya kalleta idanuwansa jajir yaga itama shi take kallo,karantar yanayinta yasashi fasa fadin abinda yayi niyya sai kawai ya furzar da iska mai zafin gaske yace "Fadi bukatarki daidai nake da inyi yadda kika umarceni Dan a halin yanzun banida maraba da Zama bawanki"

Can kasa ta sassauta muryarta Babu Wanda ke iyajin abinda take fada sai shi da ya ke sauraronta har ta Kai Aya a zancenta,a firgice ya dago Yana dubanta da tsananin mamaki da tsoro sai kawai ta gyada Masa Kai Tana fadin "zaa kawo aikin Kuma ummaty nakeso ta aiwatar da komi yadda ya dace yadda na fada maka mistake daya zaai wajen aiwatarwa komi zai lalace Zanyi asarar makudan kudin Dana kashe wajen yin wanan abun Dan haka ka kiyaye sanan ayi yadda nakeso rashin biyan bukatata tamkar rasa farin cikinka ne sarkin dawaki"...a gadarance ta karasa maganar,zufa ce take karyo Masa ta ko Ina Babu abinda yake ambata a ransa sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun....hakan yanaji Yana gani tai ficewarta ta barshi Nan zaune kamar mutum mutumi hotiho...

********
Zaune take a parlor hannunta rike da remote kanta Babu Dan kwali gashin kanta ya Sha gyara tayi matukar kyau,hankalinta gabaki daya Yana kan tv lokacin da taji sallama a parlorn da kyar ta maida dubanta ga bakin kofa sukai Ido biyu da zahira sai Kuma ta dauke Kai kamar bazatayi magana ba,

"Nifa tsiyata dake mugun Jin Kai tamkar wata sarauniya haka kikejin kamki warisat,yanzun idan ba iskamci ba ki juyo ki kallemu nida Yaya musaddik ki wani juyar da kanki gefe kamar Kinga Kashi"ta karasa maganar suna shigowa cikin parlorn,

"Daga zuwanki zaki fara complain sarkin rashin hakuri?sai kace wata bakuwa da zan tashi Ina rawan jiki kinzo"

"Yaayah musaddik fa da muke tare dashi ko baki ganshi bane?idan ni banci arzikin maraba ba?"...wani kallo takebim musaddik dashi ya kashe mata Ido sai kawai ta kauda kanta tamkar Bata san Yana yi ba,"barka da zuwa yaayah"shine abinda tace kawai ta Mike ta bar parlorn Tana tafiyar Nan Tata mai daukar hankalin Maza,

Shafa kansa yayi ya dubi zahira ransa Babu Dadi "nifa bana son wulakamcin yarinyar Nan shiyasa tun farko kikaga naki Nuna mata Ina sonta Dan dik son da nakeyi mata bazam dauki wulakanci ba"

"Ka kwantar da hankalinka ya musaddik zaka samu warisat a hannunka Nina fada maka da zarar ta shigo hannunka shikenan sai yadda kayi just be patient ok?"

Gyada Mata Kai kawai yayi batare da yace komiba yadda ransa ya baci,...shigiwar hajiya kubra mahaifiyar warisat yasasu sauri natsuwa suka tsugunna a tare suna gaisheta cike da ladabi,

"Zahira da musaddik ne a gidan namu?sannunku da zuwa"

"Yauwa momy ya gida?"

"Lafiya lau ya maman naku?"

"Lafiya lau take"

Warisat ce ta shigo dakin da alama ruwa ta watsa Tana sanye dadoguwar Riga mai launin ja ta amshi fatarta,wani mayen kallo yake bin warisat dashi ganin ko kallonsa batayiba yasa ya Mike ya fice a parlorn,

Gefenta zahira ta koma ta zauna "dadina dake sarauta kamar wata matar sarki,Koda yake bamu saniba ko Yar gida zaayi keda Yaya zainul"...ta karashe maganar Tana rufe baki cike da tsokana,

Wani mugun kallo warisat tabi zahira dashi cike da takaici ta dubeta "Amma kin cuceni zahira da badan ke bace kika fada da wani ne da Nika dai nasan irin hukuncin da zan dauka akanshi,kin Gama Dani zahira"

Dariya kasa kasa zahira keyi "akan me zakice hakan?bayan kin manta shine magajin sarki?"

"Wanan nakasasshen?kike hadani dashi?Amma zahira kin cuceni kingama Dani wallahi,ai ko Maza sun Kare a duniya bazan auri wanan halittar ba bazan taba sonshiba gara in karar da rayuwata a gida wallahi Dan ni banajin zainul zai warke"

Murmushi wanan karon zahira tayi "Amma kinsan yanada kyau?kin taba lura da hakan?"

"Kece kikaga kyaunsa kika tsaya kallon wanan halittar ni bazan iya kallonsa na second talatin ba Dan sai inyi amai saboda ka kazantar dake fitowa daga bakinsa na tsana....ke rabu Dani da wanan maganar ma mubarta"...take suka kauda maganar zahira ke shaida Mata date din da zasuyi resuming Nan da kwanaki goma zasu koma makaranta zasu shiga 200 level,

Nan zahira ta wuni tare da warisat har wajen yamma sanan ya musaddik sukazo da abokinsa yazeed Don daukar zahira,mahaifiyar warisat ce tacewa zahira ta fadawa ummanta su shirya suje gidan mai Martaba su karasa hutunsu tunda haka sukeyi......

*******
"Kai ya zainul Nasha fada maka ka rinka yawaita addua da zarar kajika a wanan yanayin,Kai da kanka kasan adduoi kala kala Wanda basai na fada maka ba Amma Sam bakayi narasa dalili, kullum Ina fada maka muhimmancin addua, Amma Sam bakayi"ta karashe maganar kamar zatayi kuka,

Kallon yanayinta yakeyi take tausayinta ya kamashi ,saboda yadda take dawainiya dashi Babu ranar da zatazo ta wuce batazo wajensa ba sanan Babu abinda yafi tada Mata da hankali irin ganinsa a halin rashin lafiya "ummaty Nima bansan dalilin da yasa nake tsintar kaina da kasa yin addua ba a dik lokacin da na fada cikin wanan halin dik yadda Zanso in motsa harshena inyi adduar nakan kasa yinta,wani lokacin Kuma nakan manta da yin wata addua saboda yadda nakejin kaina a wata duniyar ta daban,tamkar ana dagani sama ana yawo Dani a sararin samamiya wani lokacin Kuma nakan rasa hankalina na kankanin lokaci sai Kuma Inga na dawo"

Tunda ya soma maganar take kallonsa cike da tausayawa wata kwalla ce ta makale Mata a idanuwanta Wanda ta kasa matsota,..."ya zainul Dan Allah inaso ka yawaita karanta hasbunallahu wa niimal wakeel kaji,nasan kasani Ina Kara tunatar dakai ne".

"Ummaty Ina kokarin yin addua kinsani bakina Koda yaushe cikin ambaton isrigfari da salatin annabi nake Amma da zarar naji yanayin jikina na canjawa sai in tsinci kaina da kasa yin adduar"ya karasa mgnr cike da damuwa

Shiru tayi cike da tsananin damuwa zuciyata ta tsunduma cikin tunani kala kala,wanan wani irin mugun ciwo ne dake mantar da bawa daga fadin ambaton Allah yayi rashin lafiya?tabbas wanan ciwon na zainul abideen yana dauke da sirhiri ne na manyan aljanu,Dan inba aljanu ba Babu yadda zaayi ya kasa motsa bakinsa yayi addua yayin rashin lafiya,idan haka ne kuwa Dole su dage da addua,Dan itace zata kawo karshen wanan jarabawar...tayi nisa cikin tunani ta tsunkayi kuryarsa Yana fadin

"Ummaty bani da isassun kalmomin da Zanyi amfani dashi wajen gode Miki akan dawainiyar da kikemun "hawaye suka sauko daga idanuwansa,

Farin kyalle tasa ta share Masa hade da goge Masa miyaun gefen bakinsa "ya Isa ya zainul tsakanina da Kai Babu godiya kaji?ko ka manta Kai yayana ne?"gyada Mata Kai yayi Yana murmushin karfin Hali,

Aysha da fiyya kannensa ne suka shigo a tare suka zauna gefen gadon suna Jan ummaty da Hira sama sama take amsa musu Dan ita bamai yawan son magana bace...

*********
Mutum uku ke zaune a fadar sarki da sarkin dawaki wazirin sarki da sarkin aska,...dukkansu gurfane suke a gabansa suna tayasa jimamin jikin na zainul abideen,

"A ganina ranka ya Dade lokaci yayi da zaa duba ciwon yaron Nan a fahimci cewa ciwonsa ba na asibiti bane na gida ne,ni Nan inada Wanda zai iya yi Masa magani Kuma ya warke tamkar be Taba wanan ciwon ba ranka ya Dade,"cewar waziri Yana Kara gurfanawa a gaban mai Martaba Yana cike da alhini,

"Waziri ni kaina ciwon zainul abideen yana daya daga cikin abubuwan da suka tsayamum a rayuwata banida yadda Zanyi ne da kaddarar Allah wadda take rubuce akanmu Amma nima inada wanan tunanin...

"Inada hasashe akan ciwon Nan na zainul abideen ba haka kawai bane akwai wani Abu kasa ranka ya Dade da zaa kaishi wajen Mai magani da in akwai sa hannun wani a ciki ma komi zai bayyana"cewar sarkin aska

Jimm kadan Mai Martaba yayi Yana nazarin zamcen nasu "bana zargin kowa da sawa Dan Dana Haifa hannu Dan haka inhar maganin zaayi Masa to da zuciya tsarkakakkiya zaayi Masa shi"...

Hankalin sarkin dawaki ba karamin tashi yayi ba Nan da Nan cikinsa ya shiga kugi Amma sanin cewar magana daya zaiyi ya rushe maganar sauran yasa shi gyara Zama "ranka ya Dade me zai Hana a canjawa zainul abideen asibiti idan haka ne?ni a ganina a Gama na asibitin tukunna sanan a fuskanci na gargajiyan wadanan masu maganin mafi yawancinsu macuta ne"

"Nima hakan nake gani sarkin dawaki zuciyata Bata aminta da zuwa wajen masu maganin gargajiya ba sanin sunsan zainul din asalinsa da inda ya fito"

Waziri yace "ranka ya Dade yadda kakeso haka zaayi akai zainul asibiti muga abinda Allah zaiyi"

Sarkin aska dake gefe mamakin halin Mai Martaba ya Kara cikasa...

*********
"Zuciyata badan taso ba zahira hakan zanje gidan mai Martaba wallahi kawai Dan momy ta matsa sai munje ne"

"Ki shirya da wuri gobe ya musaddik zai kaimu zamuzo mu daukeki kinji?"

Badan taso ba ta amsa da to sukai sallama ta jefar da wayarta gefen gado Tana Jan tsaki

********
Shafa kansa gimbiya bilkisu takeyi yau "zainul jiki na samun sauki alhamdulillahi koh?"

Daga Mata Kai yayi "ehh ammiey kwana biyu banji abun Nan da nakeji ba"

"Masha allahu Ina ga magungunan Nan da aka canja maka sun amsheka kenan zainul zanyiwa mahaifinka magana akan magungunan sun amsheka"

"Toh ammiey"....

Ummaty dake gefe Tana faman hada Jakarta Dan tafiya gida ammiey ta dubeta "ummaty yau kinyi yamma a gidan Nan gashi ke kadai zaki tafi me zai Hana ki zauna tare dasu safiyya zan aikawa mamanki cewar zaki kwana a Nan"

Shiru ummaty tayi Tana wasa da yatsunta kanta a kasa batare da tace komi ba,...

Yanayin da zainul abideen ya Nuna Jin hakan ya tabbatarwa da gimbiya bilkisu yaji dadin cewar ummaty zata zauna a Nan din sai kawai tai murmushi ganin danta cikin farin ciki....

*********
Kaiwa da komowa sarkin dawaki yakeyi a cikin dakinsa Yana tunanin yadda zaa aiwatar da maganin da aka kawo batare da ansamu matsala ba gashi ummaty Bata dawo ba Tana can gidan tayaya zai ganta har ya yi Mata dabarar da ya sabayi?
Chapter 6 · 0% Book details