Sashe 22
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonsa shekeke innah takeyi cike da mamakin mijin nata "malam bansan lokacin da ummaty ta tafi gidan Nan ba,sanan tun shekarun baya da ummaty ke zuwa gidan baka taba tunanin wani Abu zai biyo bayaba sai yau?me hakan yake nufi?malam bangane maka ba kwanakin Nan gabaki daya Dan haka inaso ka sanar Dani abinda yake faruwa kasani a cikin duhu"
A fusace ya soma magana "Baki Isa kisani inyi ko kada inyi ba kingane ko?ke harkin Isa ki tsareni sai na fada Miki abinda nake nufi?kece kike aurena ko Nike aurenki?sanan ke kika haifamun ummaty?ko kece ubanta?iyakadai kice kece uwarta koh?ni Kuma nine ubanta Dan hakan nikeda iko da ita bake ba saboda haka idan kika kuskura kika ce zakija da hukuncina zakisha mamakina nafada Miki"....kallo kawai innah ke bin sarkin dawaki dashi gabaki daya ya haukace Yana surfa masifa kamar tababbe.....
Ganin yadda yake huci yasa Bata sake cewa komiba ta cigaba da tankaden gari da takeyi....sai kanwarsa ce ta fito daga daki xani a hannu tana fadin "kayi hakuri bakada yadda zakayi Allah ya hadaka da yarinya kwadayayya Inba kwadayi ba an hanaki zuwa waje kin nace kamar tsohuwar mayya,ko da yake dik abinda ummaty tayi uwarta ce tasata Banga laifinta ba"
Sarkin dawaki na zaune gefe rike da linzamin doki yace "Aiko zamci ubanta Zanyi maganinta"....
"Da dai yafi"....
*********
Shafff ta mance da zancen wani magani da gimbiya rumana ta Bata hirar su kawai suke Sha dikda zuciyarta Babu Dadi tayi kokarin danne hakan Dan haka Koda ta tuna da zancen maganin gimbiya rumana wanan Karon bataji wata faduwar gaba ba Dan ta rigada ta shiryawa komi yadda zuciyarta ta Bata shawara,....dik wani tsoro ya Kau daga zuciyarta da dik wani kuka da tayi cikin awa daya tasamu mafita.....Dan haka Babu tsoro ta Ciro gorar maganin fari karrree ta dubi gorar sosai Tai murmushi sanan ta dubi zainul Wanda ke kwance Yana bin ta da kallo dik wani motsi nata...."ya zainul ga maganinka kwana biyu ban baka kasha ba koh?nasan kila ka manta da zancen maganin ma ko?"
Gyada Mata Kai yayi yana. Murmushin Nan nasa Mai tsada yace "to ai sauki ya fara samuwa shiyasa kika mance da zancen bani magani koh?"
Gorar takai bakinsa Babu musu yasa Baki ya soma Sha sosai tamkar me Shan ruwa .......Saida ya shanye sanan ta dire gorar kasa Tana bin sa da kallo.....dik faduwar gaban da take ciki Bata yarda ta Nuna Masa ba sai kawai tayi haramar tafiya gida saboda yamma da tayi gashi ga yanayin yadda tazo gidan yau Dan haka sauri sauri ta shirya Tai Masa sallama tabar gidan dikda yadda taga yanayi da jikin nasa tausayinsa ya lullubeta haka ta bar gidan tare da tararrabin abinda zai biyo baya....
**********
Tsaye yake a tsakar gidan minti minti yakan dubi agogon hannunsa yayi tsaki,har yanzun Bata shigo gidan ba... Wanan Karon Yana dago Kai yayi daidai da shigowarta cikin gidan a sanyaye tayi sallama gabanta na tsananta faduwa.....
"Daga Ina kike ummaty?a wanan lokacin?"ya daka mata tsawa Yana kallon agogon hannunsa....
Wani mugun miyau ta hadiye sanan ta tattaro dik wata jarumta tata tace "baba kayi hakuri naje wajen zainul abideen ne naje duba jikinsa naje in kula dashi kamar yadda kasani Kuma kake bani goyon baya Akan hakan"
"Dan ubanki ni kike fadawa hakan?....da Ina Baki goyon baya yanzun na daina bada goyon bayan sai me?shine kike taka mun doka kike tsallake umarnina?kinsan dalilina nayin hakan ne?"
"Baba bansan dalilin ka na hakan ba Amma yau ya Dace in rokeka wata alfarma wadda cikin kwanaki biyu naso rokonka ita,sanan akwai tambayar days Dace inyi maka ita Amma nakasa haka....."
Kallo kawai yake bin ummaty dashi zuciyarsa na harbawa sauri da sauri lokaci daya ya tsinci Kansa cikin tsananin faduwar gaba.....muryarta ce ta farfado dashi daga suman wucin gadi da yayi...."baba wani Abu ke damuna ba wani Abu bane face inaso intambayeka ko ya zainul yayi maka laifi ne kadaina karbo mishi magani kamar yadda kake karbo mishi a baya?"..
Tai tambayar hade da kafesa da idanuwa tanaso taga yanayin na mahaifin nata tanaso ta tabbatar da zargin da ya ke makale cikin zuciyarta Wanda takeyi cikin watanni uku da suka wuce.....
"Ummaty ni kike so ki tsare?Koko akwai wani tunani a cikin zuciyarki Wanda kika barwa zuciyarki kikeso yau ki tabbatar dashi?yasa kikazo ki tu kareni ki turkeni Akan kamin ubanki?zainul abideen ubanki ne?meye hadinki dashi?Naga Nina gadamar bashi maganin Kuma na daina sai me?"
Murmushin gefen fuska ummaty tayii ganin yadda babanta ya rikice gabaki daya ya haukace sai zufa ke karyo Masa a fuskarsa "kayi hakuri mahaifina, banyi maka wanan tambayar da wata manufa ba sai Dan ganin kwana biyu da baa bashi maganin ciwonsa ya daina tashi,shine nake tunanin ko maganar ta mutanene da suke cewa ciwon nasa ba asibiti ne shiyasa na tambayeka"..
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke batare da ya sani ba Wanda a kunnen ummaty yayi ta wanan Karon sai taga jikinsa yayi sanyi ya dubeta "ba wani Abu bane yasa nace kibar zuwa gidan gabaki daya banaso ki shaku da yaron har sarki ya ce zai aura Miki shi bayan kinada ranki da lafiyarki cukakkiyar mutum kamar kowa shiyasa "...a sanyaye yayi maganar take itama dabara ta Fado Mata,
"Idan har wanan shine tunaninka baba,ka kwantar da hankalinka,Babu wata soyayya tsakanina dashi,Babu wata shakuwa a tsakanina dashi da zaisa in yarda in amince da zancen aurensa Yana nakasasshe,dik wani Abu da Zanyi Masa inayi Masa ne tsakani da Allah don insamu Lada...Dan Kuma amimcim dake tsakaninka da Mai martaba shiyasa kawai"....Tai maganar tana duban yanayinsa....wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa Jin furucin da ummaty tayi dikda can kasan zucuyarsa a firgice yake da tambayar da tayi Masa da farko....
"Shikenan na amince Miki ki cigaba da kula dashi,kamar yadda kikeyi din"...murmushin nasara tayi ta durkusa har kasa tace "nagode baba Allah ya saka da alheri Allah ya Kara girma"...
"Ameeen"yace Yana Mai Zama a tabarmar dake kofar daki...har ta wuce ta dawo "baba inasu innah?"
"Taje gaisuwar mutuwa gidan malam madu da'nsa ya fada rijiya dazun Allah yayi Masa rasuwa"
"Allah sarki Allah ya jikansa"
"Ameen"
Tasa Kai tayi hanyar dakinta rike da Jakarta zuciyarta cike da farin ciki na samun nasara da tayi cikin sauki.....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS* *DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
**********
kuka kawai yakeyi Yana murkususu a cikin daki fasawansa suna danne dashi sai faman zufa yakeyi ,yadda yake ji a cikin jikin nasa wanan karon ya wuce misali.....abinda ya kwana biyu bai Yi ba shikeson samunsa Amma da yake yanada sauran karfi Allah ya bashi ikon karatun alkurani a bakinsa dik surar da ta fito bakinsa karantawa takeyi da adduoi kala kala ...kafafuwansa da hannuwansa sai lankwashewa sukeyi tamkar ana juyasu....
Dik yadda yusha'u yaso ya Kira iyayen nasa kin yarda yayi mutum daya kawai ya yarda Akira Masa itace gimbiya rumana....kallon yusha'u yayi cikin tsananin ciwo dakyar ya furta "kiramum ummah"...da sauri yusha'u yabawa lawal umarnin Kiran gimbiya rumana shi Kuma ya cigaba da rikesa Yana jijjigasa Yana tofa Masa adduoi...
Sanye take da hijjabinta har kasa ta shigo hankali a tashe "Yaya dai zainul Dan ummah?menene yake damunka?jikin ne?"dik a firgice take maganar ta karasa cikin dakin ta janyosa jikinta..
"Ummah jikina ciwo ko Ina hannuna kamar ana kakkaryamun shi kafafuwana"cikin tsananin ciwo yake maganar dakyar yana cije lebensa ga rawa da jikinsa yakeyi...
Kuka ta fashe dashi Tana shafa ko Ina a jikinsa "Yi shiru Dan ummah kaji Allah zai baka lafiya insha allahu Allah zai kawo karshen wahalar taka zatazo da izinin Allah"ta tallabo shi Tana sharar hawaye....can kasan zuciyarta kuwa tamkar ta taka rawa takeji wani farin ciki ne ya lullubeta,tabbas ummaty ta bashi maganin Nan tunda haka ta kasance taji dadin hakan....towel ta janyo kusa da shi ta dubi yusha'u dake tsaye "dibo mun ruwa Mai Dan sanyi insa Masa a jikinsa naji jikin nasa yayi zafi" jiki na rawa ya nufi toilet ya Shiga Nan da Nan ya samu Yar roba Mai kyau ya dibo ruwa ya kawo ta Shiga tsoma towel din ciki tana matsewa Tana shafa Masa a jikinsa,shi kuwa adduoi kawai yakeyi cikin zuciyarsa dik da azabar da yake Sha....
********
Ta Dade zaune a dadduma bayan sallahr asuba tana zuba adduoi akan abinda ta gudura a ranta Akan Allah ya Bata nasara ya dafa Mata,Tai adduoi sosai sanan ta janyo Dan karamin alkuraninta ta bude ta karanta suratul yaseen kamar yadda ta Saba ko wace asuba tayi sanan Ta rufe da addua ta shafa....
Jakarta dake nesa da ita kadan ta janyo ta Ciro gorar maganin ta ajiye a gabanta,...kirrrrr tayi da idonta tana kallon gorar maganin tunanin lokacin da mahaifinta ya daina Bata maganin zainul abideen takeyi da lokacin da gimbiya ta soma Bata magani tabawa zainul abideen......dafe kanta tayi zuciyarta na tsananta bugawa idan har Bata manta ba mahaifinta ya daina Bata magani da sati daya gimbiya ta cigaba da Bata magani tabawa zainul abideen....sanan abun mamakin da gora iri daya Babu banbanci,shin menene alakar gimbiya rumana da mahaifinta?shine babban abinda ya kamata ta fara bimcikawa yanzun Amma ta Yaya?ta cije lebenta.....sanan menene kudurin gimbiya rumana akan zainul abideen haka ?...tayaya zatasamu wadanan amsoshin waye zai Bata wanan amsar?
Wata zuciya ke ayyana Mata "amsoshinki gabaki daya suna shawarar da kika yankewa Kanki Yi a jiya?ta wanan hanyar kadai Zaki samu amsarki tare da samun mafita cikin wanan lamarin"...abinda zuciyarta ke fada Mata kenan....ajiyar zuciya ta sauke tare da zurfafawa tunaninta da shirinta da takeyi akan gimbiya rumana....wanan karon murmushi ummaty tayi ta gyada kanta cike da karfin gwiwa......
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
*HASKE WRITERS* *ASSO💡*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*SLIMZY😍*[1/23, 11:05 AM] 😍SLIMZY😍: 21