← Book details Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya kusa aure kaikuma kana Nan kana binsa zarau zarau kamar wani lagwani Kai bakada niyyar auren kenan ko?to ka Shiga taitayinka nafada maka ban hanaka bin abokinka harkoki ba Amma ka sama Mana namu lokacin kana gani yau saura kwana hudu abbanku ya dawo ya Dace ayi Masa shiri Amma baka samu lokaci ba balle mu zanta"

"Kiyi hakuri momy andaina kinji ranki ya Dade"ya rike kunnuwansa yanayi mata dariya ta Kai Masa bugun Wasa ya goce yayi hanyar dakinsa Yana dariya....

*********
Zaune yake cikin Riga da wando jeans da polo shirt blue sun matukar karbar jikinsa saye yake da facing cap hannunsa rike da wayar ummaty ya Shiga gallary dinta hoto kwaya d'aya ne ciki Wanda ta dauki kanta da bakar Riga tayi masifar kyau ya kure hoton da idanuwa minti minti yakan sauke ajiyar zuciya....jujjuya wayar ya shigayi wani tunani ne ya darsu Masa cikin zuciya shin waye ya siyawa ummaty wanan wayar?shi ya fara zo Masa Dan Yana ganinta da wayar a kwanakin Nan Amma be taba tambayarta ba ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji motsin shigowa Dan hakan sai kawai ya jefa wayar cikin aljihunsa amminsa ce ta shigo dakin ta nemi waje ta zauna fuskarta dauke da damuwa....

"Zainul abideen"ta Kira sunansa cikin sanyin murya...

Memakon ya amsa sai kawai ya dubeta ya maida hankali kanta hade da kafeta da idanuwa alamar Yana sauraronta...

"Shin zaman da kakeyi hakan Kai kadai batare da kowa ba kana ganin bazai haifar maka da wani ciwonba?gashi ka gayyato damuwa ka sawa rayuwarka da zuciyarka abbanka yace tunda ka samu lafiya matukar baka Kori damuwa ka gayyato farin ciki ba aure zaiyi maka,kila matar ta sama maka farin ciki"...

Murmushin gefen kumatu yayi "ammiey ya zaayi ku ganni farin ciki bayan da kanku kuka rabani da farin cikin?...damuwa ko bani na gayyato ta ba itace tazo da kanta ta samawa kanta mazauni a gurbin da farin cikin ya tafi,bani da wani farin ciki Wanda ya wuce samun ummaty a kusa Dani inhar bansameta ba to tabbas nagama dariya harabada"

Kallonsa kawai takeyi zuciyarta Babu Dadi samm ta rasa yadda zatayi da zainul Akan wanan mayyar yarinyar...kallonsa takeyi Shima kallon nata yakeyi cikin kankanin lokaci idanuwansa suka canja kala sukai jajir "ammiey ki tallafi rayuwata ayi bincike Akan wanan lamarin Dan zuciyata na fadamin sharri akai Mata"

"Ba sharri akai Mata ba zainul gaskiya ce domin Kai da kanka kaga video din da kanka ya Dace ka yarda kodan wadanan hujjojin"

Cike da takaici yace "ammiey baxan taba yarda ba bazan taba amincewa ummaty zata cutar Dani ba ammiey ku duba wanan lamarin ku dawo da ita gareni"...

Mikewa tsaye tayi "sai kayi ai nidai nafada maka gaskiya idan kaga zaka dauka ka dauka idan damuwar zaka cigaba bismillah"Tai tafiyarta cikin fushi ta bugo kofar...

Iska ya kaiwa naushi cike da takaici ta Mike Shima yayi hanyar waje...

Kicibis yayi da ita a hanyar shigowa sashin tana ganinsa gabanta ya Fadi yadda ya daura fuskarsa tun daga nesa yake watsa Mata kallo tamkar yaga Kashi da sauri tace "ya zainul Ina yini wajenka nazo dama"

"Uban me Zanyi Miki?ke waini saan wasanki ne warisah ki Shiga hankalinki idan ba haka ba zanbaki mamaki"Yana Gama fadin haka yayi gaba abinsa ta bisa da kallo idanuwanta cike da hawaye ga bugun zuciyarta daya tsananta ta Sanya hannu gefen zuciyarta ta dafe ta soma tafiya....

Driver ya nema Nan da Nan sai gashi ta zo"fita Dani zakayi zuwa sabuwar unguwa a hankali nakeso ka taka Dani inaso Inga gari ne"....

******
Sanye take da hijjabinta a parlor ta tadda haris zaune Yana cin shin kafa da wake suna hada Ido ya kashe Mata Ido daya ta Dan hararesa "sai Kuma Ina?"yace Yana kallonta...

"Nidai ya haris fita Zanyi in zagayo ta titi don nagaji da zaman gidan Nan wallahi kafafuna dik sunyi tsami,"

Murmushi yayi Mata "kijirani ingama muje to"

Kada Kai tayi "na hutar dakai ka zauna da mama a gida yanzun Zan dawo Dan na rigada na shirya ban iya jiranka"Tai maganar cike da shagwaba...

Tabe Baki yayi cikin sigar tsokana "kije Zanyi Hira da innah ta Kuma karki Dade"ya kashe Mata Ido...itadai innah sai murmushi takeyi.

"Naji insha allahu saina dawo"...har ta Kai kofa ya bita ya rada Mata wani Abu ta rufe idanuwanta tana dariya ta fice.....

*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*

*HASKE WRITERS ASSO💡*

💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞

*SLIMZY😍*
[1/23, 11:43 AM] 😍SLIMZY😍: 35

Tafe take gefen titi hankalinta gabaki daya Yana can wani waje ga gaban da ya tsananta faduwa minti minti takan juya gefe da gefen hanya tana waige waige....ko Ina shiru ne wajen sai kukan tsuntsaye ga gidaje rerassss masu shegen kyau tamkar ba cikin garin da sukeba haka kawai ta tsinci kanta cikin tsananin nishadi Wanda rabinta da hakan tun kwana goma da suka wuce...

Tafe suke a mota ya tsurawa titi Ido tamkar wani ba kauye minti minti yakan sauke ajiyar zuciya wadda besan dalilinta ba,...juyowa yayi da Kansa gefensa na dama ya tsurawa gefen Ido tun daga nesa yake hangen tafiyarta da bayan hijjabinta Wanda ya Sanya shi saurin saka hannunsa ya murza idonsa ya budesa tamkar Wanda ya tashi daga bacci Kara murzar idonsa yakeyi Yana kallonta sosai ko a mafarki yaga kirar jikinta ko a cikin kurgumin duhu ne inhar zaa haskata to tabbas sai ya ganeta har sukazo gaffff da ita da sauri ya dubi driver cikin daga murya yace "tsayasaaaaaa Dan liti"a tsorace yaja burki "ranka ya Dade me kake bukata?kayi hakuri Ina gudu ko,?

Ko ta kan Dan liti beyiba ya fito a guje ya ruga gareta tana Shirin tsallaka titi ya ruko hijjabinta...cikin azama ta juyo da niyyar ganin ko wani Dan rainin wayau ne ya shakota sukai Ido hudu....cakkk ta tsaya dik wata hanya ta sadarwa dake jikinta Saida ta tsaya,,,,kallon juna sukeyi Ido cikin Ido ko kiftawa basayi....runtse idanuwanta ta shigayi tana furta "idan mafarki nakeyi bana fatan Allah ya farkar Dani daga wanan mafarkin me niima da Dadi .....gani ga ya zainul....Allah karka farkar Dani daga mafarkin Nan"...tana magana idanuwanta a runtse...hawaye na sauka daga cikin idanuwanta,...shiko tsaye yayi Yana kallon yadda bakinta ke motsawa,zucuyarsa na Kara bugu tamkar ana kada ganga ga wani mugun tausayinta daya lullubesa idanuwansa gabaki daya sun canja launi sun dauki lokaci Mai tsawo a haka ganin da gaske takeyi batada niyyar bude idanuwanta gani takeyi tamkar baccin takeyi yasashi matsawa daffff da ita ya Shiga hura Mata iskar bakinsa Mai sanyi da kamshin minti da ya gama tsotsa...a hankali take bude idanuwanta a Kansa ba tare da ta daina zubar hawaye ba...."kukan me kikeyi ummaty?...Ashe inada Rabon sake ganinki a duniya?"

Girgiza Kai tayi "gani nakeyi kamar mafarki nakeyi ya zainul ji nakeyi tamkar baa cikin duniyar da nake rayuwa bace,kuka na biyu ne na farko dai na farin cikin ganinka tsaye da kafafuwanka a doron kasa Babu wanan nakasar danasani Allah ya cikamun burina na samun lafiyarka dikda bani nayi sanadinta ba,...babban bakin cikina be wuce ka farka an sanar maka da mugun labarin cewar ga abubuwan Dana aikata maka ba shekara da shekaru...wallahi summa tallahi ya zainul ban..."rufe mata Baki yayi ganin dik yadda ta dimauce kuka Yana neman cin karfinta ba...girgiza Kansa ya shigayi alamar ta bar kukan ya sa hannu ya Shiga share Mata hawaye Yana jifanta da wani irin mayen kallo Wanda ke Kara narkar Mata da zuciya...ruko hannunta yayi Babu musu tabi bayansa har cikin mota yayi musu masauki a baya,ta gilashin mota sukai Ido hudu da Dan liti yace "bamu waje"..cikin azama Dan liti ya bude mota ya fice ya barsu ciki ya rufo musu kofofin motar...

"Share hawayenki"yace Mata Yana daura fuskarsa tamkar be taba dariya ba,kallonsa takeyi Ido cikin Ido ganin ya tsareta da Ido yasanya ta sadda kanta kasa ga wani mugun kwarjini da yayi Mata yadda ya tsare gida tamkar ba zainul abideen din da ta sani ba gabaki daya ya canja yayi mugun kyau ga sarauta da yake takama da ita..."idan kika Kara yimun asarar hawayenki ummaty Allah sai na ladabtar dake Dan Babu abinda na tsana dik duniyar Nan sama da ganin hawayenki sanan Babu abinda nake kauna kamar kyakkyawan murmushin Nan naki wadda yake bayyana ainihin kyawu da Allah yayi Miki....inaso ki kwantar da hankalinki Akan maganar da take yawo a gari cewan kin nemi hallakani Allah beyi ba nasani na tabbatar ummu salmata Yar aljannah ce ko cinnaka bazaki taba kashewa ba balle Dan mutum na yarda dake na amince dake dari bisa dari kinji?"...murmushi ta sauke hade da ajiyar zuciya Mai nauyi take ta tsinci kanta cikin tsananin nishadi Wanda ya haifar Mata da murmushi Wanda ya kasa gushewa daga fuskarta...ganin Bata da niyyar dago fuskarta yasanya shi sa hannunsa a habarta ya dago fuskarta suka hada Ido ta runtse Ido tanajin bugun zuciyarta na tsananta....dayan hannunsa yasanya ya shafo fuskarta tun daga goshinta har zuwa lips dinta Yana yawo da yatsansa...Yana kallo yadda kirjinta ke sama da kasa alamar bugun zuciyarta ya tsananta Dan haka murmushin gefen fuska yayi yanajin wata iriyar kasala na shigarsa tun daga Kansa har tafin kafarsa..ita kanta Bata taba tsintar kanta cikin wanan yanayin ba Mara misaltuwa wani irin Abu ke Yi Mata yawo cikin jiki tamkar magana disu...dukkansu sun shagaltu kusan minti goma Sha biyar sanan yayi gyaran murya ya saki habarta Wanda yasata sauri rufe fuskarta da tafukan hannayenta...

"Ummaty Ina sonki"ya furta cikin wata irin murya wadda batasanshi da ita ba,...da sauri ta kallesa ya kashe Mata Ido hade da dage girarsa sama Babu alamar Wasa a fuskarsa ya cigaba da magana "zakice bakisan Ina sonki bane?Koko kinaso kicemun ke Baki Sona ummu Salma,...hmmmm look wallahi summa tallahi Ina sonki Ina kaunarki Kuma banajin akwai abinda zai rabani dake dik runtsi dik wuya....na shiryawa gagarumin yaki ko wani irine ummaty indai akanki ne sanan idan Allah ya kaimu gobe Zan sanarwa da Mai martaba muradina"
Chapter 39 · 0% Book details