Sashe 24
Zainul Abideen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba lallai bane yaro ya fahimci yaren tsofaffi tunda shekarunsa basukai hakan ba,musamman ke me kananan shekaru wadda bakisan komi a cikin wanan duniyar ba,ballantana kisan abinda ke ninke a karkashin kasa a gidan sarauta...gidan sarautar ma babba Mai iyalai kala kala daban daban....Nan gaba kadan idan kinkasance me wayau da kaifin basira Zaki iya fahimtar Killin dake kwrkashi. Kasa"....
Tunda baabah kande ta soma rattabo wanan kalaman ummaty ta kafeta da Ido tana nazarin....ta tsinci wasu kalmomi biyu zuwa uku Amma zataso Karin bayani akansu...sanan tunda baabah kande ta furta hakan kenan tasan sirrin cikin gidan Kuma tasan sirrin gimbiya rumana kenan?.....ajiyar zuciya ummaty ta sauke batare da tace komiba ta kalli babah kande suka hada Ido sukai wa juna murmushi....firar dankalin takeyi tana tunani indai haka ne ko anzo wajen tasamu abinda takeso.....tasamu inda zata samu kadan daga cikin abinda take nema....tabbas tasan yanzun ne zasu fara Wasa itada gimbiya rumana dikda batasani ba cikin ita da ita Wanda zaiyi nasara....murmushi tayi kawai ta dire wakar hannunta ta dubi babah kande "Bari inje nasan ya zainul ya tashi yanzun"....
Gyada Mata Kai baba kande tayi Tana murmushi ta bita da kallo...ummaty ta bace Mata ta sauke ajiyar zuciya tace a fili "ummaty Allah ya taimakeki akan wanan bakar muguwar ya kawo karshen makircinta insha allahu komi zai warware....da yardar Allah zansa Miki hannu Koda a boye ne.....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA DARI BIYU NE KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN DAN KARIN BAYANI 08166177830 KO 07084161619*
💞 *ZAINUL ABIDEEN* 💞
*HASKE WRITERS ASSO💡*
*SLIMZY😍*
[1/23, 11:06 AM] 😍SLIMZY😍: 22
Kwance take Akan makeken gadonta Mai shegen kyau da tsada,kallo daya zakayiwa dakin kasan cewar naira tayi kuka a wanan dakin saboda yadda aka kawatashi da kayan kyale kyale na rayuwar duniya,dikda Babu wadataccen haske a cikin dakin Amma kana iya kallon komi dake ciki saboda dumm light ce a kunne,murginawa tayi ta kwanta rigingine tana kallon ceiling din dakin gashinta baje Akan pillow Dina....dik minti da zuciyarta ke bugawa tana bugawa ne da tunaninsa ,yau kadai da ta gansa ta rasa abinda yakeyi Mata Dadi ta kasa sukuni dikda cewar ba yau tasaba ganinsa ba Amma yadda ta ganta Yana nunar Mata da cewar ya soma samun lafiya,wani irin kyau da kwarjini yayi Mata Wanda be taba Yi Mata shi ba,...runtse idanuwanta tayi ta budesu hade da canja direction din kwanciya...shin menene nata na tunaninsa? menene hadinta dashi?da zuciyarta zata kasa sukuni sai tunaninsa idanuwanta Babu Wanda suke hasko Mata sai kyakkyawar fuskarsa Mai dauke da tsadadden murmushinsa?...tsaki tayi ta janyo wayarta ta kunna data kawai ta Shiga Instagram Dan ta kauda abinda takeji a ranta.....
*******
"Ni Kam warisah kinsan cewar Ina kwadayin hadaki aure da yaron Nan zainul abideen?"
Zumbur warisah ta Mike tana bin mahaifiyarta da wani irin mugun kallo lokaci daya ta soma numfarfashi saboda yadda zuciyarta ke bugawa sauri da sauri...."momy kinsan me kike fada kuwa?kodai kinyi batan Baki ne yasa kika Fadi wanan kalmar?kinsan wa kike cewar kina kwadayin in auresa kuwa?musakin momy?"
"Dan ubanki kinfi karfin auren nasa ne kike nufi ko me?daga nayi magana ki Mike kina wani numfarfashi kamar wata zakanya?Koko dukana kike Shirin Yi inci ubanki daddaren Nan,ke warisah nagaji da wulakanci da iskamcim da kikeyi akan yaron Nan kinaji na koh?to ki fita idona in rufe kinji na fada Miki,Dan hakan kibini a hankali Ina fadawa yayah Mai martaba wanan maganar amincewa zaiyi kuma ba jiran amincewarki zamuyi ba gara ma ki saurara tunda ba cewa nayi ayi aurenba",....
Yadda hajiya kubrah ke masifa ya Kara kular da warisah dake tsaye ta zunguro Baki gaba hannunta rike da wayarta,tsabar tsananin bakin ciki batasan lokacin da ta fashe da kuka Tai hanyar dakinta ba,
Hajiya kubrah ta bita da kallon mamaki har ta bacewa ganinta,girgiza kanta tayi hade da mikewa tabi bayan Yar lelen tata don ta lallasheta....
********
Kuryar daki gimbiya rumana ke ciki suna magana kuss kuss da yarta ta biyu halima baka iya sauraron hirar da sukeyi komi kasa kunnenka ,...sosai suke magana Mai muhimmanci baba kande tana gefe,minti minti takan girgiza kanta cike da al'ajabi....
Juyowa gimbiya rumana tayi ta dubi baba kande wadda ke durkushe Akan gwiwoyinta kamar Mai rokom gafara kanta a kasa cike da ladabi dikda tsufanta,"kande"..gimbiya rumana ta Kira sunanta Kai tsaye,
"Kinsan ke amintacciya ta ce cikin amintattun kuyangina da bayi na dake cikin gidan Nan koh"...baba kande ta gyada kanta 'haka yake uwargijiyata"
"To inaso maganar Nan da nayi a binneta a cikin dakin Nan banaso inji ko burbushinta a wani waje,dikda nasan kedin ko wacece Kuma nayi sirri dake da dama ban taba jinsu ko sau daya ba ban Kuma Baki taba tonamun asiri ba shekara da shekaru Dan hakan nakeso maganar Nan ta Zama sirri inkara Jan kunnenki sosai Akan maganar da kikaji munyi"
"Insha allahu Zaki sameni Mai sirri kamar Koda yaushe uwargijiyata Allah yaja zamaninki ya Kara girma gimbiya rumana uwar zahrau"gyada Kai gimbiya rumana tayi cike da gamsuwa sanan ta juyo ta kalli halima wadda keta hura hanci tana yatsine yatsine kamar uwarta,ita dama halima ko a cikin yaran gidan kafin tayi aure tafi kowa Nuna Isa da mulki sanan da ita ake fada da bayi da kuyangin gidan,komi nata irin na gimbiya rumana harta kamanninsu,Abu daya gimbiya rumana Tai Mata zarra dashi a Hali shine tanada faraa sosai sabanin halima da Bata dariya ko kadan sanan tazo ta auri Dan sarkin wata masarautar sai mulki da Isa da takama ya hadu,wanan yasa gimbiya rumana ke matukar ji da halima take alfahari da tana auren Dan sarki wanan yasa gimbiya rumana bataso yaran gimbiya bilkisu su samu daukaka kamar yaranta komi so takeyi ace yaranta sunfi...Dan haka take amfani da kissa da makirci da tsafi wajen juya hankalin kowa a wanan masarautar ciki kuwa harda uwar Mai martaba hajiya Kaka...
Shiru halima tayi na Dan wani lokaci sanan ta dubi mahaifiyarta cike da yanga da sarauta dakyar ta bude bakinta tace"ummah idan akai hakan kina ganin shine mafita?"
"Kwarai kuwa halima shine mafita,Kinga zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya,Kinga ummaty diyar sarkin dawaki tanayi mun aiki batare da ta sani ba Kuma inada tabbacin har yanzun Bata fahimci wani abuba dikda kwanaki yarinyar Naga kamar taso ta dagoni Amma nayi amfani da karfin iko da mulki na kifar da shegiyar yarinyar nan,inaso aikin Nan da ya kammala zansa a kasheta ko a batarmun da ita gabaki daya cikin ruwan sanyi Kuma ubanta be Isa ya ce wani Abu ba saboda akwai sirririka da dama Wanda Nima na sani nashi akan Mai martaba"
Yatsina fuska halima tayi "akan Mai martaba Kuma"
"Kwarai da gaske ko ke bakiyi mamakin yadda Mai martaba ya bawa sarkin dawaki muhimmanci fiye da waziri da sarkin aska ba?to juyar Masa da hankali yayi inda dik abinda yace shi akeyi a wanan masarautar infada Miki"...
Jinjina Kai kawai halima tayi hade da kishingida da kilisa ta runtse idanuwanta....ganin hakan yssa gimbiya rumana yin shiru Dan tasan alamu ne na halima tagaji da surutu,Dan halima bameson yawan surutu da hayaniya bace so dayawa ko magana Mai muhimmanci kakeyi da ita saidai ehh ko ah ah Kota girgiza Kai kawai Dan haka tai shiru hade da janyo babban farantin fruits dake gabansu ta dauko ayaba ta mikawa babah kande tace "baremun"...
*******
Sai wajen laasar halima Tai Shirin zuwa fadar sarki wajen mahaifinta Amma sai gimbiya rumana Tai Mata umarni da suje suga jikin zainul abideen idan yaso daga can sai taje fada wajen mahaifin nata....
Sunnah tv take zaune tana kallon waazin malam tukur almannar hannunta rike da carbi tana azkhar din bayan sallar laasar sukai sallama cikin patlorn tare da kuyangi biyu biye Dasu,
Zubewa kuyangin sukayi gaban gimbiya bilkisu suka kawo gaisuwa ta amsa musu hade da sakin murmushi ta dubi halima dake gefe sanye da alkyabba baka Mai adon golden a jiki Mai shegen kyau da tsada "halimah yaushe kika shigo ne"shine tambayar da gimbiya bilkisu Tai Mata fuska dauke da kulawa...
Murmushi halima tayi "ammiey ban Dade da shigowa ba wallahi nace Bari inzo ingaisheki ummah Kuma tace zatazo ganin autanta zainul"
Murmushi gimbiya bilkisu tayi tace "to Kinga baban naki ne?"
"Ehh yanzun idan Naga jikin brother zan wuce fada ingansa da zuwan na musamman danshi ne'
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya Lau ammiey,inasu fiyya da afee uwar rigima ayshah nasan tana sokoto hutu koh?"
"Dik suna wancen patlorn harsu musaddik suna Hira"...gyada Kai halima tayi tare da mikewa tsaye "ammiey Bari mu Shiga"
Jinjina Kai gimbiya bilkisu tayi hade da murmushi tana bin halima da kallo,har cikin zuciyarta tana tsananin kaunar halima fiye da kowa cikin yaran gidan saboda natsuwarta da kamun Kai uwa uba mulki da take dashi da Jan aji ,yasa take kaunar halima...
Jin alamar motsi yasa ummaty fahimtar zaa shigo duba zainul Dan takun da taji ya wuce na mutum daya take zuciyarta ta ayyana Mata gimbiya rumana ce da tawagarta,Bata Gama tunani ba suka kutso Kai cikin dakin,ganin wadda suke tare yasa ummaty saurin sunkuyar da Kai Dan kada su hada Ido da halima ta watsa Mata wanan kallon na wulanci data Saba,
Gefen gadon halima ta tsaya ta Mika hannunta ta ruko hannun zainul "my little brother ya jikin"tace tana kallonsa,
Murmushi yayi "jiki da sauki bayan kwana biyu bakizo kin ganniba"Yana maganar harshensa na Dan hardewa..
"Sorry brother kaji prince ne ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa London yasa ban samu na leko gidan ba saboda can munata hidindimu wallahi yanzun ma saboda Inga jikin naka nazo ko su samir da sabreen banzo da su ba, Muhammad ma bacci yayi nasa driver ya kawoni yanzun zan koma nace Bari inzo inganka kaji my lil brother"